Header Ads
Showing 1 words to 2468 words out of 2468 words

Chapter 1 - GWARZON SADAUKI Book 2 Complete Littafin yaki by Abdul'aziz Sani Madakin Gini .txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

GWARZON SADAUKI
Littafi Na Biyu (2)
Part C
Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini
Typing: Abubakar Saleh






Ita dai wannan da'irar an kewayeta ne da wasu karafa da kuma igiyovi akan wani gini mai tudu wanda duk jama'ar da ke wajen ke iya hangota. Bayan an budewa Insam da'irar ya shiga ya tsaya sai aka jcho masa sanda ya cafe sannan aka kirawo bawa na biyu wanda shi ne abokin gwaminsa mai suna Janas.
Janas wani katon Bawa ne dogo kuma kakkaura domin ya ninka Insam sau biyu 2 girma da kwarjini, kuma fuskarsa babu annuri ko kadan. Janas na shigowa cikin da'ira gasa sai shi ma áka jeho masa tasa sandar ya cafe sannan ya gyara tsayuwarsa suka fuskanci juna.
A wannan lokaci ne jamaa suka rude da shewa gami da tafi. Kawai $ai aka buga gangar fara wasa. Jana ya ruga da gudu i zuwa kan Insam ya kawo masa wawan bugu da sanda a kai, cikin zafin nama Insam ya kare dukan suka ruguntsume da azababben fada ya zamana cewa Şuna kai wa junansu duka ta sama da Kasa. Sai da suka shafe dakika dari da tamanin suna kai wa junansu hare-hare ba tare da dayan su ya $ami wata nasara ba, sannan suka ja da baya suka gyara tsayuwa suna tunanin irin sabon salon fadan da kowannensu ya kamata ya yi don ya samu nasara.
Lokaci guda suka ruga da gudu a karo ha biyu suka kacame da sabon masifafien fada. A wannan lokaci kowannensu ya zage damtse yana fadan ne da iyakar karfinsa da kuma kwarewarsa.
Tun a farkon fara wannan gumurzu tsakanin Insam da Janas sarki Zamrall na lura da Gimbiya Sulaisa Duk sa'adda ta ga an kai wa Insam wawan hari har yana neman faduwa sai hankalinta ya tashi alamar fargaba ta bayyana karara akan fuskarta amma da zarar ta ga cewa Insam ke da alamu nasara sai fuskarta kama annuri da murmushi. Ganin hakan ne kishi ya turnuke Sarki Zamral ya ji kamar ya bayar da umarnin nan take a kashe bawa lnsam.
Ba wani abu ba ne ya sa Gimbiya Sulaisa ta ji tana son bawa Insam anganin farko face yana tsananin kama da masoyinta wanda ta so ta aura akanhanata wato Sarki Marhat na birnin Misra.
Sai da aka yi gasa ta dukiya a tsakanin sarakuna goma sha daya sannan aka fitar da gwanin daya sami damar auren Gimbiya Sulaisa kuma ba wani ba ne ya lashe gasar face Sarki Marhat amma a ranar da za a kai amarya birnin Misra aka nemeta aka rasa ashe Sarki Zamral ne ya tura aljanu suka sato ta. Sai da aka shafe shekaru uku ana nemanta ba ganta ba har
masoyita Sarki Marhat da nahaifinta suka hakura suka rungumi kaddara,
Duk irin karfin tsafin Sarki Marhat na birnin Misra bai ya gano inda Sulaisa take ba. Bayan shekara.uku ne Sarki Zamral ya shirya bikin aurersa a Sirrance a gidan sarautarsa ba tare da ya gayyaci Sarki ko guda daya a Nahiyar ba. A ranar da amarya za ta tarc aka shirya wannan gasa ta jaruma tsakanin bayin gidan sarautar.
Ko da fara wannan artabu karo na biyu sai fadan ya sauya ya zamana cewa insam ne yake kai wa Janas mugayen hare-hare wadanda da kyar yake iya kare su kuma baya iya mayar da martani. Ana ciki haka ne lnsam ya shammaci Janas ya doki kafafunsa da sanda Janas ya sama kafin ya fado kasa lnsam ya sake doka masa sanda akan kirjinsa, take Janas ya fado kasa tim, bisa gadon bayan sa ya furzo da gudan jini daga cikin bakinsa kuma ya kasa mikewa tsaye.
Nan fa yan kallo suka rude da shewa gami da tafi Gimbiya Sulaisa kuwa ba ta san sa'adda ta mike tsaye ba, tana yi wa lnsam ta fi sai da Sarki Zamral ya riko hannunta sannan ta koma ta zauna.
Daya bayan daya sai da jarumi.Insarn ya yi fadan sanda da wadannan bayi guda goma sha shida kuma ya yi nasara a kansu, đayansu bai sami nasarar koda dukan jikinsa ba sau daya. Ana gama wannan gasa ne Sarki Zamral ya ja amaryarsa
suka shiga cikin gidan sarautar, taro ya watse kowa ya kama gabansa.
Lokacin da bayi da kuyangi suka raka amarya Sulaisa cikin turakarta suka fito suka bar ta ita kadai jal a zuane gefer gadonta na alfarma sai ta fashe da matsanancin kuka na bakin cikin wannan auren dole da ta yi. Ga shi an rabota da kasarta ta haihuwa iyayenta ma ba ta san ranar da za ta sake ganinsu ba, kuma ga shi an rabata da masoyinta Sarki Marhat
To wai shin jarumin da na gani yanzu mai kama da masoyina Marhat waye shi? Anya kuwa ba shi da wata nasaba da Sarki Marhat domin kamannin nasu ya yi yawa matuka.
Tana cikin yin wannan tunani ne da kuka Sarki Zamral ya shigo cikin turakar. Koda ta ga ya durfafota gadan-gadan sai ta sauko daga kan.gadon da gudu ta nufi kan tebur da aka ajiye ya'yan itatuwa da wuka Kawai sai ta dauki wukar ta đoral a kan wuyanta ta dube shi ta ce, Idan ka kara yin tafiya taku d'aya izuwa gareni na rantse da darajar iyayena sai na kashe kaina.'
Ko da in wannan batu sai hankali Sarki Zamralya.dugunzuma ya yi taku biyu sannan ya dubetal ya |ce, "Ni ma na rantse da darajar nawa.iyayen daga yau ba zan sake kusantariki ba har sai kin bukace ni da kanki Amma ki sani cewa wannan bawa da ya lashe gasar jarumta mai kama da tsohon masoyinki duk anar da kika kusance.shi ko kuka yi magana da juna ba ki sake ganinsa ba domin kurkuku zan kai shi a yanke masa hukuncu
daurin rai da rai."
Gama fadin hakar ke de wuya sai Sarki Zalmar ya juya da baya a fusace cikin bakin ciki ya fice daga cikin turakar.
Kashegari da safe kuwa aka nemi.amaryal Sulaisa sama da kasa aka rasa a cikin gidan sarautar. Al'amarin da ya dugunzuma hankalin Sarki Zalmar kenan ya baza dakarunsa a
nahiyar aka yi ta nemanta amma ko duriyarta ba a ji ba a tsawon kwanaki bakwai. Bisa wannan dalili ne Sarki Zalmar ya zargi Bawa Insam a kan cewar akwai sa hannunsa a batan Gimbiya Sulaisa don haka ya sa aka kama shi aka yi ta gana masa azaba iri-iril har tsawon kwanaki goma sha daya inda Sulaisa take.
Bayan an gano cewa babu sa hannunsa a 6atan Sulaisa sai kuma aka yanke masa hukuncin daurin rai da tai aka kai shi kurkuku. Sau uku yana guduwa ana kamo shi daga karshe aka kai shi babbar kurkuku inda Gadaraz ke shugabancin dakaru.
Lokacin da Insam ya gama tunanin wannan al'amari da ya faru a baya sai Gadara ya dafa kafadarsa ya ce "Na san yanzu ka gama tuno komai. Shin ka san ko waye ya sace amarya Sulaisa kuwa?"
Insam ya ce, Ya za a yi na sani sai zargi da aka dora mani aka zalunce ni bada hakkina ba.
Gadaraz ya ce "Haka ne to ba wani ba ne ya sace ta face ni di nan, kuma na mayar da ita gidan sarautar Sarki Marhat nd babban abokin gabata domin na dawo masa da farin cikinsa sannan kuma yanzu daga baya a na same ku kai da Barsad
zan je na rushe dukkan farin cikinsa da arzikinsa kuma na cika burina a kansa. Hadin kanku kadai ya rage mani yanzu na cimma burina. Ku sani idan wannan buri nawa ya cika har abada kun tsira daga sharrin kowane $arki a wannan nahiya kuma zaku zama manyan Sarakai na manyan biranc a wannan nahiya ta mu."
Sa'adda Insam da Barsad suka ji wannan batu sai suka kamu da farin ciki amma sai Insam ya dubi Gadaraz ya ce, To yanzu ta ya ya zaka iya rushe farin cikin Sarki Marhat kuma ya zamu yi da barazanar Sarki Zamral tunda dole ne ya cigaba da farautarmu saboda ya san cewa kai ne ka taimaka mana muka sami nasarar guduwa daga kurkuku?"
Gadaraz ya yi ajiyar zuciya ya ce "Duk abubuwan da ka ga nayi yanzu a lissafe suke kuma a shirye tun shekaru uku baya da suka gabata. Sai da na auna komai na tanadi komai da sannan na fara aikina, hatta kai a Barsad kana cikin mutanen da na tanada don cika wannan burni nawa. Abin da na ke bukata da ku kawai ku daukar mini alkawarin cewar duk wuya duk tsanani kuna tare da ni ba za ku ci mini amana ba. Idan kun amince ga hannuna kowannenku ya dafa shida hannunsa na dama.
Sa'adda Insam da Barsad suka jii wannan batu sai suka dubi junansu sannan suka tsaya suna tunanin abin yi.
Insam ne ya fara dora hannunsa a kan na Gadaraz sannan shima Barsad ya dora nasa a kan na Insam. Koda ganin haka sai ita ma llaila ta.đora hannunta a kan na Barsad ta ce, Ni ma ina tare da ku dari bisa dari."
Wannan shi ne abin da ya faru ga su jarumi Insam bayan shugaban dakarun kürkukun birnin Kisira wato Gadaraz ya taimaka musu suka sami nasarar guduwa.
A can baya kuwa lokacin da Gadaraz ya sace Gimbiya Sulaisa, sai da ya kai ta har kusa da gidan sarautar birnin Misira amma ba ta san wane ne ya satota ba. Kawai ta san cewa ta kwanta ta yi barci a can birnin Kisira amma sai farkawa ta yi ta tsinci kanta a kan doki wani mutum na rike da ita a gaban dokin yana tsala gudu.
Ko da ta waigo sai ta ga fuskarsa a rufe take za ta yi magana ke nan sai ta ji ya ja linzami takc dokin ya yi turjiya gami da daga kafatuwansa na gaba sama yana haniniya sannan ya ajiye su kasa.
A sannan ne suka sauko daga kan dokin. Sulaisa ta dubi gabas da yamma, kudu da aewa kawai $ai ta hango gidan $arautar masoyinta wato $arki Marhat.
Nan take ta kamu da tsananin mamaki gami da dimbin farin ciki ta dubi mahayin ta de "Wane ne kai kuma saboda me ka sato ni daga wajen wancan azzalumin sarkin ka dawo dani hannun masoyima?"
Lokacin da mahayin ya ji wannan tambaya sai ya kwaye fuskarsa. Ko da ta yi arba da shi sai ta sake cika da mamaki saboda ba wani ba ne face Gadaraz.
Gadaraz ya yi murmushi ya ce, "'Na san za ki yi mamaki domin kin sanni a matsayin amintaccen hadimin sarki Zamral amma kuma ga Shi naci amanarsa, ki sani na yi haka ne domin na cika wani buri nawa. Ina so ki sani cewa shi ma wannan masoyin naki azzalumi ne ya cutar da rayuwar mutane da yawa amma ba ki sani ba Shawarar da zan ba ki ita ce ki yi bad-da kama ki.shiga gidan sarautar a matsayin.baiwa domin ki gano ainihin wane ne Sarki Marhat sannan ki yanke shawara a kan za ki iya ci gaba da rayuwa da shi ko a'a."
Gadaraz na gama fadin hakan sai ya kama dokinsa ya haye sannan ya dubi Sulaisa va ce "'Sai mun sake haduwa a wani karon. Yana gama fadin hakan sai ya juya da dokinsa baya ya zabure shi da gudu ya nufi hanyar da suka fito.
Ita kuwa Sulaisa hankalinta ne ya dugunzuma ta rasa abin dake mata dadi domin ta tsinci kanta acikin wasu-wasi ákan shawarar da Gadaraz ya bata.
Ga shi dai yanzu tana farin cikin rabuwa da Sarki Zalmat wanda yake kokarin aurenta bisa dole kuma gashi ta dawo garin masoyinta Sarki Marhat wanda ta ba wa amanar Zuciyarta da ámanar rayuwarta.
Idan abin da Gadaraz ya gaya mata gaskiya ne to ai kuwa ba ta ga amfanin zama da azzalumi ba gwara ta goge Sonsa daga cikin ranta har abada.
Gama ayyana hakan ke da wuya sai Sulaisa ta nufi wannan hanya wacce za ta kai ta gidan sarauta. Sai da ya rage bai fi tazarar tafiyar dakıka dari biyar ba sannan Sulaisa ta rabe bayan wata bishiya daidai mararraba hanya mai zuwa cikin gari.
Dama Sulaisa ta rufe kanta da mayafi da duk jikinta, kuma ta sunkuyar da kanta kása. Da vake Sulaisa ta san duk iri abubuwan dake faruwa a cikıa gidan sarautar Sarki Marhad a kowane lokaci sam ba ta da wata damuwa domin da ta dubi lokacin da ake ciki yanzu sai hankalinta va kwanta saboda nan ba da dadewa ba wata amintacciyar kuyangarta zata fito daga cikin gidan sarautar domin zuwa kasuva yin siyayya.
Haka dai Sulaisa ta ci gaba de jira |har tsawon yan dakiku, kwatsam sai ta hango baiwa ta fito daga cikin gidan sarautar kuma aka yi Sa'a ita kadai ta fito tana rike da wani kwando.
Sai da kuyanga Rasimat ta gifta wannan bishiya wacce Sulaisa ke rabe sannan Sulaisa ta kira sunanta.
Cikin firgita ta waigo har tana sakın kwandor dake hannunta ya fadi kasa. A zaton Rasimat gamo ta yi. Ko da ta vi arba da Gimbiya Sulaisa sai ta kamu da tsananin mamaki ta rugo da gudu izuwa gareta suka rungume juna.
Rasimat ta janye jikinta daga na Sulaisa tana murmushin cikin farin ciki ta ce "Ya $hugabata wai su waye suka sace ki, kuma ya ya aka yi kika dawo nan yanzu?
Sulaisa ta ce "Duk wannan wani abune mai tsawo sai na nutsu, abin da nake so da ke shi ne mu tafi kasuwar tare amma a can zan batar da kamannina na dawo a matsayin baiwa saboda ina son na gano wani al'amari a tare da sarkil Ina bukatar ki rufa nin asiri kuma kada ki bari Kowa ya gane ni.
Sa'adda Rasimat ta ji wannan batu sai ta yi nmurmushi a ce Ya shugabata ai wannan abu ne mai sauki a wajena tamkar cire silin gashi daga cikin tandun mai, A matsayina na shugaba kuyangin gidan nan zan iya yin abin da ya fi hakarn, muje kasuwa kawai."
Nan take Rasimat da Gimbiya sulaisa suka jera suka nufi kasuwa.suna hira abin su tamkar baiwa da ৮aiwa.
Bayan sun hattama duk siye-siyen da ya kamata ne sai Rasimat ta kai Sulaisa shagon wata mace inda take siyen kayan Sawa na bayi da kuma kayan shafe-shafe na mata. Anan ne aka zabowa Suiaisa kayan da suka yi mata daidai, sannan aka yimata wani irin gyaran gashi gami da shafe-shafen fuska wanda ya canja kamanninta gabadaya. Duk irinn sanin da mutum yai mata bai isa ya gane ta ba. Daga nan ne suka kama hanya suka koma gidan sarautar.
Ba su sami matsalar komai ba, tun daga kofar farko ta shiga gidan suka yi ta kutsawa suna wuce dakaru, bayi, fadawa da hadimai har suka iso bangaren da turakar Rasimal takc
Rasima ta sa mukulli ta bude kofar dakin har ta sa kafarta guda ciki Sulaisa na biye da ita kawai sa suka ji muryar Sarki Marhat a bayansu ya ce Yau kin dade a kasuwa tun dazu nake neman ki."


Kuyi hakuri wallaahi exam muke yi ne shiyasa kuka jini shiru kwana biyu, yanzu ma space na samu yi maku wannan posting din saboda yadda kuke a cikin zuciyata.


Daga karshe ina mai neman Addu'arku yan uwa na gode 🙏🙏🙏

Ads At the End of Article
1

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads