Header Ads
Showing 1 words to 272 words out of 272 words

Chapter 1 - ANTARU DAN SHADDADU New Adventure Story Writing Nasir G. Ahmad Yan Awaki.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

ANTARU DAN SHADDADU
Rubuta Labari
NASIR G. AHMAD YAN AWAKI
Littafi na farko
Haƙƙin Mallaka
©Mansur Usman Sufi
Shekara Rubutu
3 Shawwal 1445
Wthapp number
08137237071












BABI NA FARKO






Fadar ta ƙawatu ainun da nau'ikan kayan ƙawa da alatun jin daɗin rayuwar duniya, gaba ɗaya ginin fadar an yi shi ne da zallar waɗansu duwatsun wuta masu ƙwarin gaske, a wannan lokaci fadar cike take da al’umma an yi jigum! Tamkar masu zaman makoki, idan ka ɗauke sautin numfarfashin al’umma babu abin da kunne ke ji, dakaru na kai komo a fadar ɗauke da miyagun makamai domin tabbatar da cikekken tsaro.
Duba ɗaya za ka yiwa jama'a ka fahimci cewa akwai wani abu dake damun su, abin da zai tabbatar maka da hakan shine, idan ka kai duban ka izuwa kan wani zagayeyyen tudu da aka ajiye karagar mulki babu kowa akai, wata ƙila damuwar ta su bata rasa nasaba da rashin fitowar sarki daga cikin gidan sarauta.
Ƙasaitacciyar turaka ce da aka ƙawata ta da dukkanin nau’ikan kayan alatun jin daɗin rayuwar duniya, idan mai kallo ya kai duban shi a tsakiyar turakar zai yi ido biyu da wani dattijo kwance magashiyan a bisa wani ƙasaitaccen gado na ma’abota mulki, zaune a gefen shi akwai wani mutum ma’abocin shekaru sanye da tufafi na hamshaƙan matsafa, idanuwanshi sun kaɗa sun yi jajaur,
Sarki Shayubul-Auzur dake cikin halin matsanancin ciwo ya dubi waziri Rufyan dake zaune daf da shi cikin sarƙewar murya ya ce “ya kai abokina kuma babban aminina ka yi sani cewa, naji a jikina cewa wannan cuta tawa ba ta tashi ba ce

Ads At the End of Article
1

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads