Header Ads
Showing 1 words to 1499 words out of 1499 words

Chapter 1 - SARAUNIYAR DAJI Complete Book Writing by Abdul'aziz Sani Madakin Gini .txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

SARAUNIYAR DAJI
ABDUL’AZIZ SANI MADAKIN GINI




Rana na daf da faɗuwa, mutane na ta qoqarin haɗa kayayyakinsu a cikin qaramar kasuwar garin, shi dai wannan garin wani yankine dake sashin qasar Hindu da ake kira Mawardi.
Gaba daya mutane garin ba su wuce mutum dari uku ba mazan su da matansu, dukkanin jama’ar wannan gari sun kasance mafarauta don haka ba su da wata sana’a wacce tafi farauta. Gaba daya dazuzukan dake cikin wannan yanki na su sun laqance su ainun kamar yadda suka laqanci sana’arsu.
Asalin mutanen garin mawardi basa zama a waje daya ko da yaushe a cikin yawon daji suke suna shiryawa kansu gasa ta farauta kala-kala, duk wanda aka shiryawa gasa shi za a tattarawa duka dukiyar da aka samu a dajin a bashi wakilcin siyar da ita a can babbar kasuwa ta cikin birnin Hindu don haka duk ribar da aka samu sai kason shi yafi na kowa yawa.
Mutanen qabilar mawardi sun kasance ‘yan kadan a qasar ta Hindu kuma suna da sa’a da nasibi a duk abinda suka sa a gabansu shi yasa suka fi sauran qabilun nasibi a kasuwanci siyar da fatun dabobbin daji da kuma duk wani vangare na sassan jikin dabobbi da ake buqata don yin magani ko tsafi hakan yasa arziqin mutanen ya riqa havaka kuma a dalilin hane yasa suka kafa wani gari a wannnan yanki dake can bayan birnin Hindu suka daina nisanta kansu da birnin sosai.
Ko shekara ba su yi da kafa wannan gari na mawardi ba sai fatake da attajirai manya ‘yan kasuwa suka mayar da garin babbar cibiyar ta kasuwanci fatu dabobbi daji, ya zamana anata gine-ginen manya gidaje kuma ana qawata shi da abubuwa irin na zamanin waccan zamanin.
Sarkin wannan garin na mawardi ya kasance matashi wanda shekarunsa ba su wuce arba’in ba, kuma ya gaji sarautarne a wajen mahaifinsa yana da matan aure guda xaya me suna Rasina kuma suna da ‘ya guda xaya ‘yar shekara bakwai ana kiranta da Lashmin.
Tun Lashmin bata wuce shekaru huxu a duniya ba mahaifinta ya fara koya mata yadda ake yin farauta a daji, kuma ya rinqa bata horo na jarumtaka da cire mata tsoron daji da duk irin hatsarin da take cikinsa, ai kuwa tana cika shekara bakwai ta rinqa yin abubuwan ban al’ajabi wanda shi kansa mahaifinta bai tava yin kamarsa ba a lokacin da yake da shekarunta kamar nata. Tana da shekara bakwai take sulalewa ta shiga daji ita xaya tana yin farauta, sai dai aganta ta dawo janye da matacciyar damusa ko vauna wacce ta kashe da hannnunta tun tana yin farautar yini daya har ya zamana cewar tana iya shafe kwanaki uku ita kaxai a cikin daji tana yin farauta kuma ta dawo gida cikin qoshin lafiya.
Koda mahaifin Lashmin ya sami labarinn irin gagarumar bajintar da take yi sai ya qaryata al’amarin ya buqaci da su tafi daji tare shi da ita domin idanunsa su ga yadda take yin tatta farautar.
Bisa wannan shirin su uku wato har da mahaifiyarta suka xauki guzuri suka hau dawakai guda uku suka fice daga cikin garin mawardi suka nausa cikin daji cikin nishaxi da farinciki.




***
A can Babban Birni Hindu kuwa sarkin da yake mulki a wannan lokacin ya kasance qasurgumin azzalumi ana kiransa da suna Danbola.
Sarki Dambola ya kasance kamar annoba a qasar gaba xaya domin kuwa hatta manyan fadawansa tsoronsa su kaji saboda a su kansu baya xaya musu qafa wajen karva harajinsu kuma idan kana da mace me kyau da zarar ya qyallara ido ya ganta zai qwaceta. Idan kuma ka yi qoqaron hanashi ita zai kashe ka ne ya gaje komai naka. Hakane ya saka sarki Dambora ya tara matan aure har xari da sittin da uku.
Wani babban abin mamaki shi ne duk yawan waxannan mata mace xaya ce jal ta haihu da shi, itace uwar gidansa wacce aka yi musu auren saurayi da budurwa ana kiranta da sunan shanina. Abinda shanina ta haifa xan shekara goma sha xaya ana kiransa da suna Ashtar.
Barewa bata gudu xanta ya yi rarrafe, sarki Dambola ya kasance gawurtaccen jarumi wanda ya yi shuhura a qasar Hindu gaba xaya, bai gaji sarautaba da qarfin tsiya ya kashe sarkin dake kan karagar ya karvi sarautar alhalin ya kasance xan bawa.
Ashtar ya gado mahaifinsa a vangaren jarumtaka sosai amma kuma ko kaxan shi baya zallunci kuma baya son zallunci hakane ya janyo rashin shaquwa a tsakaninsa da sarki Dambola harma ya daina janshi a jikinsa.
Kisa qwace ba komai bane a wajen sarki Danbola amma Ashtar ya tsani hakan idan ma yaga sarki Danbola ya aikata irin wannan zallunci sai ya yi ta kuka, koda sarki yaga cewar Ashtar yana da raunin zuciya sai ya hanashi zuwa fada kuma ya aiyana a ranshi cewar bashi da magaji.
Wata rana da daddare sarki Dambola na kwance a cikin turakarsa shi kaxai yana bacci, sai ya farka a firgice cikin tsananin ximauta, nan fa ya miqe tsaye ya koma kai kawo a cikin alamun tsananin tashin hankali, al’amarin da ya janyo bacci ya qauracewa idanunsa kenan haka dai ya kasance zaune ko tsaye har gari ya waye.


Da sassafe tun kafin rana ta fito sarki Dambola ya tura aka kirawo babban bokan qasar Hindu wanda ake kira da suna Kuljaru. Boka Kuljaru ya amsa kira ya bayyana a gidan sarauta aka yi masa iso izuwa wani babban xaki inda sarki Dambola yake ganawar sirri da manya mutane masu daraja.
Lokacin da sarki Dambola da Boka kaljaru suk kaxaita sai sarki ya buxe baki da nufin ya yi magana amma sai kaljaru ya xaga masa hannu ya tsaida shi sannan ya dube shi a cikin nutsuwa yace.
“Ya kai sarki mai daraja ta xaya ka yi sani cewar tuni nasan abinda kake so ka sanar dani, jiya ka yi mafarki a cikin mafarkin naka kaga wata bishiya mai qafafu kuma rasa bishiyar hannaye ne da yawa haka ne?” Sarki Dambola ya jinjina kai alamar haka ne Boka karjalu yaci gaba da cewar “Wannan bishiyar ta ratso har cikin wanna birni namu ta kashe gaba xatan mayaqanmu kuma ta riske ka har cikin turakarka ta tsire maka reshe a cikin jikinka ya volo ta gadon bayanka ka zamo gawa haka ne?” Sarki Dambola ya sake amsawa da haka ne duk abinda ka faxa haka na gani shin wannan mafarki zai faru ne a gaske?”
Boka kurjalu ya yi shiru kuma ya miqe tsaye ya yi ‘yar tafiya taku uku sannan ya juyo ya dubi sarki Dambola yace.
“Tabbas babu makawa sai wannan al’amari ya faru a gaske, idan kuma bai faru ba to ka xauki matakin yanke wannan bishiyar da take tofowa a yanzu uma ka qoneta qurmus yadda ba zata ci gaba da rayuwaba” Koda jin wannan batu sai sarki Dambola ya miqe tsaye zumbur cikin tsananin fushi har fuskarsa ta kama yin gatsine ya dubi Boka kurjalu yace.
“A ina wannan bishiyar take naje duk inda take na sassarata gunduwa-gunduwa kuma na saka a qoneta qurmus sai ta zama toka” Boka kurjalu ya yi ajiyar zuciya yace “Ita wannan bishiyar ta kasance mutum kamarka. Yarinyace qarama wacce ba tafi shekara bakwai ba a duniya, yanzu haka tana iya shiga daji tayi farauta ta kwana uku kuma komai hatsarin dabba tana iya yin gumurzu da ita kuma ta samu nasarar kasheta saboda ta kasance basaudaukiya kuma jarumar gaske” Sarki Dambola ya tari numfashi Boka karjalu a lokacin da jikinsa ya kama tsuma ya xaga murya yana mai cewa.
“A ina wannan yarinya take ka faxa mun yanzu naje na qarar da duka zuri’arta da qabilarta gaba xaya” Boka qarjalu yace ‘Ai ba a nesa suke da kai ba, tana cikin qabilar mawardi waxannan tsirarun mutanen da suka gina birninsu a yamma da wannan birni namu sunan yarinya Lashmin kuma ta kasance ‘ya ga sarkinsu Amjadu, idan har ka bari wannan yarinya ta girma har ta cika shekara goma sha takwas to zata zama sarauniyar dukanin dazuzukan dake cikin wannan qasa tamu to daga nan ne kuma za ta yi harin karagarka zata shigo har cikin gari ta ci mu da yaqi kamar yadda ka gani a mafarki”Koda Boka Karjalu ya zo nan a maganarsa sai Sarki Dambola ya bushe da dariyar mugunta sannan ya dubi Boka Karjalu yace “Haba ya kai abin dogaron Hindu ta yaya zan bari wannan abin kunya ya riskeni shin ka mance cewar gaba xayan mutanen garin mawardi basu wuce su xari uku ba, na rantse da kabarin babana a yau xinan zan kashe gaba gaba xayan mutanen garin mawardi mazansu da matansu sannan nasa a qone komai na garin har sai ya zama to9ka kai ko ciyawar garin ba zan bari ta sake tofowa ba”.
Nan take sarki Dambola ya yi shirin yaqi ya xebi wasu zaqwaquran mayaqansa guda dubu xaya suka xebi makamai suka hau dawakai suka nufi hanyar da zata kaisu can birnin na mawardi kai kace yaqi za su yi da wata babbar qasa.
**


A dakaci fita ta 2 zuwa gobe idan rai ya kai mu.


Domin neman karin bayyani kira ko whasApp 08069524699

Ads At the End of Article
1

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads