Showing 1 words to 3000 words out of 3851 words
Chapter 1 - Kogon Annoba Book 2 Complete Littafan yaki Writing by Sarkin Marubutan Yaki .txt
Kogon Annoba Book 2
BABI NA UKU
Kamar yanda boka Zulwal ya fada haka al amarin ya kasance wato tun da dukun dukun safiya sarki Siyamul ansar da su yarima Yarima Nazmar sukayi shiri bayan sun rabu da mahaifiyarsu suna masu zubar da hawayen rabuwa
da juna suka dauki hanyar tafiya tare da dakaru masu yi musu rakiya mutum dubu biyu tafiyar sa'a uku sukayi suka iso wani daji mai tattareda kayan ni'ima nau'i nau'i daban
daban koramai na gudana acikinsa atsakiyar dajin akwai wani dan madaidaicin gida shi dai wannan gida da zallan duwatsun wuta masu kwarin gaske da isowarsu bakin kofar gidan
sai sarki Siyamul ansar ya sauka daga kan dokinsa yaje ya kwankwasa kofar gidan wanda ta kasance mai tsananin tsawo da kaurin gaske saida ya kwankwasa sau uku
ba tare da yaji motsin alamun za a bude taba koda ganin haka sai su yarima da boka Zulwal suka sauko daga kan dawakansu suka
tako har izuwa kofar gidan suna masu yin cirko cirko domin suga an bude kofar tsawon dakika dari biyu shiru ba aji sautin bude kofar ba al amarin da yayi matukar dugunzuma
hankalin sarki Siyamul ansar ya dubi boka Zulwal yace ya sarkin bokaye shin yanzu me nene abinyi? har boka Zulwal ya budi
baki da nufin yace wani abu sai kawai aka hango wani kyakkyawan saurayi mai cikar kamala da annurin fuska ya tunkaro
kofar gidan kallo daya zakayiwa saurayin ka fahimci ya kasance gwarzon mayaki mai karfi na Allah ya isa saurayin yana sanye da
kayan fata riga da wando takalmin dake kafarsa anyi shine da patar damisa akafadarsa yana dauke da wata qatuwar zakanya.
Koda isowarsa inda su sarki Siyamul ansar ke tsaye sai ya bisu da kallo cike da mamaki ba tare da yace da dayansu uffan ba yasa hannu daya ya tura gofar gidan ta bude ya kunna
kai izuwa ciki yayin da sarki Siyamul ansar da tawagarsa sukayi arba da qatuwar zakanyar dake dauke akafadar saurayin kuma sukaga yadda ya bude kofar gidan da hannu
daya wanda sai karti majiya karfi mutum ashirin sun taru sannan zasu iya bude kofar sai suka cika da tsananin mamaki domin basu taba gani ko jin jarumin da yayi wannan jarumtaka ba suna nan atsaye a kofar gidan sai
sukaga saurayin ya fito daga cikin gidan ya tako da kafafunsa har izuwa inda suke ya dubesu cikin nutsuwa yace aminci ya
tabbata agareku yaku wadannan baki shin menene ke tafe daku izuwa gareni koda jin wannan tambaya sai sarki Siyamul ansar yayi
gyaran murya yace yakai jarumi Huzaifal bin masnur kayi sani cewa ba komai
ne ke tafe dani izuwa gareka ba face wata muhimmiyar bukata bukatar kuwa itace inaso kayi mana jagora izuwa
gidan boka Jabarul sihir domin nemowa wadannan 'ya'yan nawa maganin da zai warkadda su larurar dake damunsu ta rashin
jin magana kuma har su mayar da abinda suka daukowa wadansu tsuntsaye
wadansu tsutsaye inason ka fadi dukkan abinda kake bukata da ya danganci dukiya da mulki ni kuwa zan baka shi. Koda jin wannan
jawabi daga bakin sarki Siyamul ansar sai.jarumi huzaifal yayi shiru yana mai sunkui da kansa kas ya shiga dogon nazari daga
can sai ya dago kai ya dubi su Yarima Nazmar gimbiya Hulaisa sannan ya dubi sarki Siyamul ansar yace yakai wannan sarki mai daraja kayi sani cewa fiye da shekaru goma ubangijina ya baiyana mini cewa zakazo gareni da wata bukata
na amince zanyi maka wannan aiki amma sai dai bisa sharadi guda daya jal wanda sai ka 08137237071amince dashi zanyi wannan gagarumar tafiya
da jin haka sai sarki Siyamul ansar yace fadi sharadinka ya jarumin kwarai Huzaifal yayi gyaran murya a karo
na biyu sannan yace sharadina shine bayan na samu nasarar debo ruwan ma'ul diya'u wanda shine zai warkar da su
Yarima zaka yarda kayi imani da ubangiji kai da jama'arka baki daya idan ka daukar mini wannan alkawari
shikenan ka biyani dukkanin aikina ba tare da ka bani dinare da ko wani yanki na masarautarka ba koda jin wannan
batu sai sarki Siyamul ansar yayi shiru duk tattaunawar da akeyi tsakanin Jarumi Huzaifal da sarki Siyamul
ansar boka Zulwal da su Yarima Nazmar suna sauraro koda Boka Zulwal yaji sharadin da jarumi Huzaifal ya gindayawo
sarki sai hankalinsa ya dugunzuma ainun domin ya tabbatar idan sarki Siyamul ansar yayi imani cewa zai karbi addinin
musulunci duk shirinsa zai tarwatse na son mallakar birnin SARIRUL AIWAN da ya dade yana muradi yana cikin wannan hali ne wani tunani ya fado masa tunanin kuwa shine
tunda sarki Siyamul ansar umarninsa yakebi bana jarumi Huzaifal ba lallai akwai tabbacin burinsa zai iya cika sa'adda yazo nan a tunaninsa sai ya cika da farin ciki a ransa sarki
Siyamul ansar ya kada shirun da ya wanzu a tsakaninsu ta hanyar bude baki yace yakai jarumi Huzaifal hakika na amince da wannan sharadin naka matukar 'ya'yana zasu
daidaita yanda nake bukata amma kuma wani hanzari ba guduba menene batu a gameda cewa su yarima sune zasu zamo ajalina da jin wannan tambaya sai murmushi ya subucewa jarumi Hullzaifal har fararan
hakoransa suka baiyana farare qal ya dubi sarki Siyamul ansar cikin annurin fuska yace kada ka damu ya shugabana kasani cewa matukar kana tare dani kuma kayi imani da ubangijin musulunci mahaliccin sammai
da kassai da abin dake cikinsu babu yanda za ayi 'ya'yanka su zamo ajalinka yanzu dai abinda za ayi shine ku biyoni izuwa
cikin gidana kudan shakata kafin abinda ya kamata ayi tunda na lura cewa kun gaji ainun kuma a tsarin addininmu ubangiji ya
umarce mu da mu girmama ma'abota mulki matukar basu hana mu bauta masa ba. Koda gama fadin haka sai jarumi Huzaifal ya juya ya shige gaba yana mai.kunna kai izuwa
cikin gidan yana mai yafito su sarki Siyamul ansar na hannunsa ba tare da bata lokaci ba sarki Siyamul ansar Yarima Nazmar gimbiya Hulaisa boka Zulwal ne a karshe suka suka biyo
bayan Huzaifal yayi musu jagora har izuwa cikin gidan da shigarsu izuwa cikin gidan sai suka cika da tsananin mamaki abinda
ya basu mamaki shine yadda aka tsara gidan bisa tsari da kayatarwa gidan yana dauke da manyan dakuna guda uku masu girma da fadi suna da kofa ɗai ɗai da tagogi guda
biyu a wani daki ne dake kallon yamma cikin gidan jarumi Huzaifal ya sauki su sarki Siyamul ansar aciki dakin cike yake da kayatattun
kujeru kuma an shimfide kasansa da kilisai masu taushi wani daddadan kamshi ya mamaye turakar bayan jarumi Huzaifal ya sauke
su acikin turakar sai ya fice daga cikin dakin jim kadan sai gashi ya dawo dauke
da wani dogon paranti cike da nau'in kayan marmari da gasasshen naman zakanya
gamida tatacciyar madarar shanu ya ajiye agaban su sarki Siyamul ansar a bisa wani dan madaidaicin tebur na katako a tsakiyar turakar yana ajiye abincin ya dubesu yace ai sai ku
dan kimtsa cikinku ko yana gama fadin hakan ya fice daga dakin sarki Siyamul ansar da boka Zulwal suka bishi da kallo cike da matukar mamaki tayaya akayi har ya sarrafa
naman zakanyar da ya farauto acikin kankanin lokaci haka kuma a inama ya samu wannan tatacciyaro madarar shanun al halin babu wata dabba dake rayuwa acikin dajin saida suka kammala kimtsa cikinsu suka
huta sannan aka dunguma gaba daya suka fice daga gidan har jarumi Huzaifal suna ficewa ya mayarda kofar gidan ya rufe ta ruf kawai sai suka ga ya kusanci wani
bangare adajin mai tattare da sarkakiya sai gashi ya janyo wani ingarman doki fari sol mai kyawun launi bayan ya hau dokin ne
kowa ya hau abin hawarsa sai aka nausa cikin daji aka fara tafiya dakaru masu rakiya na biye dasu ana fara wannan tafiya ne
jarumi Huzaifal yaki yarda ya jera da kowa face Yarima Nazmar da gimbiya Hulaisa yana mai satar kallonsu fuskarsa
cikeda annuri ana cikin hakan ne Yarima Nazmar ya dube shi yace yakai wannan jarumi a dazu da kuna magana da abbana
naji kace akwai wani ubangiji da kake bautawa wanda ya halicci sama da kasa bayan abin bautarmu. Koda jin
wannan tambaya sai Huzaifal yayi murmushi ya dubi Yarima Nazmar yace tabbas akwai ubangijin da ya halicci duniya da
abinda yake cikinta kuma yake aiwatar da duk abinda yaso da ace zaku gwada neman taimakon ubangijin nawa da kun
kasance jarumai kamar yanda har kullum kuke muradi sa'adda Yarima Nazmar yaji amsar wannan tambaya sai ya cika da mamaki yace wacce hanya zanbi in samu taimakon
ubangijinka Huzaifal yace ai abune mai sauki kawai duk sa'adda wani abu ta taso maka kace kana neman taimakon ubangijin gaskiya ubangijin da yayi rana da wata yayi mutum da aljan dabba da tsuntsaye ruwa da iska
ubangijin da babu wani ubangiji bayan shi a ranka ba tareda ka furta wani yaji ba lallai kai da yar uwarka inason ku boye mini wannan sirri dake tsakanin mu Yarima
Nazmar da yar uwarsa sukace ai kuwa babu wanda zaisan da wannan sirri har sai gaskiyar abinda kake gaya mana ya baiyana daga wannan kuma Huzaifal ya shiga basu daddadan labarai masu sanyaya nishadi da annashuwa
haka dai aka cigaba da wannan tafiya babu sassauci ana cikin tafiyar ne kwatsam ba zato babu tsammani sai aka hango jibga jibgan mutane masu tsawo da kauri qirar mutanen farko yawansu yakai dubu biyar suna da
miyagun makamai masu baraza ga rayuwar mutane da aljan nan fa gaba daya dakarun sarki Siyamul ansar suka firgice sukaji tamkar su cika wandunansu da iska amma sai sukaga
mutanen sunyi musu kawanya suna masu fitowa daga kusurwar dajin. Lokacin da mutanen suka kammala yi musu kawanya sai aka fara kallon kallo daga can sai akaga
mutanen sun ɗane sun sake bayar da wata yar siririyar hanya a tsakiyarsu da mutum zai iya wucewa sai ga wani garjejen qato ma'abocin kwarjini da ban tsoro ya ratso hanyar
ya fito izuwa gaban mutanen ya dubi su sarki Siyamul ansar a wulakance sannan ya bushe da mahaukaciyar dariya mai kama da haniniyar doki sannan daga bisani ya
turbune fuska tamkar an aiko masa da sakon mutuwa ya bude wawakeken bakinsa mai dauke da wadansu wargatsattsun hakora cikinsa marasa kyan gani cikin kakkausar
murya yace yaku wadannan kwari maza ku sallama kanku izuwa gareni kafin in zare muku ruhinku daga gangar jikinku kafin garjejen
qaton ya gama rufe bakinsa jarumi Huzaifal ya tari numfashinsa yana mai maida masa da cewa shin wanene kai kuma menene
nufin ka agaremu garjejen qaton ya bushe da dariya a karo na biyu sannan ya kurawo Huzaifal idanu masu kama da garwashin wuta yace eh lallai da kyau yan samari shin
har kanason kasan wanene ni to inaso kai da abokan tafiyarka kusani cewa nine sadauki RAUZAM shugaban yan ta'addar
wannan nahiyar baki daya amma fa na yaba da jarumatarka matuka ganin yanda ka iya yin magana baki da baki dani amma
lallai bazan bar dayanku a raye ba jarumi Huzaifal ya katse shi da cewa amma idan har ka cika namijin duniya muyi fada da juna
kuma kada dayanmu ya rike makami a gwada yar qashi idan nayi nasara akanka na cinye ka da yaki idan kaine kayi nasara
ka kashe ni sai ka kashe abokan tafiyata. Koda jin abinda Huzaifal yace sadauki Rauzam ya takarkare ya kwarara uban ehu da ya
firgita gaba daya jama'ar dake wajen sannan yace da kyau jarumin kwarai haka akeson namiji da zuciya irin ta manya yana gama
fadin hakan sai kawai ya daga annayensa sama ya falfala da gudu izuwa inda Huzaifal ke tsaye duk sa'adda ya ajiye kafarsa daya sai dai kaji kasa na amsa kuwwa tamkar zata rufta
Yana gama fadin haka kawai sai ya daga hannayensa sama ya falfala da gudu izuwa inda Huzaifal ke tsaye duk Sa'adda ya ajiye kafarsa daya sai sai dai kaji kasa ta amsa tamkar zata rufta koda ganin haka sai Huzaifal ya sauko daga kan dokinsa yana mai gyara tsayiwarsa gamida dunkule hannayensa biyu da isowar sadauki Rauzam yakai masa wani wawan naushi a fuska ya sunkuya hannun Rauzam ya naushi iska sannan duka kacame da azababben yaki mai matukar ban al'ajabi da ban mamaki ana fara wannan gumurzu nefa Huzaifal ya fahimci cewa Rauzum ya fishi tsagwaron karfin damtse domin idan ya naushe shi a fuska ko a jiki inda ya nausa din sai jini ya taru Huzaifal ya daka tsalle tamkar an harbo shi daga cikin baka ya daki kirjin Rauzum da kafafunsa biyu saboda karfin dukan sai da Rauzum yayi sama tamkar an janye shi daga qugiya yayi katantanwa a sama sau uku cikin gwaninta jarumi Huzaifal ya daka tsalle sama yayiwa Rauzum luguden naushi sau goma sannan suka sauko kasa a tare yana mai dora kafarsa a wuyan Rauzum alokacin da jini ke juba a hannayensa a hancinsa da bakinsa kuma numfashinsa ya fara sargewa Huzaifal ya dube shi yace yakai wannan dan ta'adda kayi sani cewa matukar zaka bayarda gaskiya ga ubangijina kuma ka daina wannan haramtacciyar sana'a taka zan kyaleka ka cigaba da rayuwa koda jin haka sai Rauzum yayi murmushin karfin hali ya furzadda gudan jini a bakinsa cikin kakkausar murya yace ai da inyi mubaya a agareka gwara ka kashe ni domin za a shaida cewa ni jarumi ne kafin Rauzum ya gama rufe bakinsa Huzaifal ya zare takobinsa ya datse masa wuya. Koda sauran yaransa sukaga abinda ya faru ga shugabansu sai sukayi kururuwa suka afkawo su jarumi Huzaifal aka kacame da azababben yaki sai da aka shafe tsawon sa'a biyu ana wannan yaki sannan Huzaifal suka samu nasarar hallaka gaba daya yaran Rauzum a inda kowanne daga cikinsu Rauzum a kashe dakarun rakiya mutum saba'in dayake duhun dare ya fara kawo kai sai kowa ya sanyawo kansa magani kuma aka kafa tantuna sannan akayi kalaci saida aka shafe tsawon kwanaki biyu a wannan daji a iya wannan kwanaki jarumi Huzaifal ya koyawo su yarima yadda ake yaki kuma bisa mamaki sai gashi suna rike duk abinda aka koya musu al'amarin da yayi matukar bawo sarki Siyamul ansar mamaki kenan domin sau tari yana koya musu yaki amma basa rikewa da hantsi aka sake yin shiri aka cigaba da tafiya saida suka shafe kwanaki hudu ana keta miyagun dazuzzuka amma bisa taimakon ubangiji basu sake haduwa da wani abin cutarwa ba sau tari idan miyagun dabbobi suka hango su sai kaga sun tarwatse sun bazama izuwa cikin daji al'amarin da yayi matukar bawa sarki Siyamul ansar da boka Zulwal mamaki kenan abinda basu sani ba shine kawai tsananin addu o in da jarumi Huzaifal ke karantawa ne suka tsare su daga sharrin dabbobin a iya tsawon wannan kwanaki babu abinda ke tsaida su face idan lokacin bacci yayi ko lokacin gabatar da sallan jarumi Huzaifal a ranar kwana na biyar ne da yamma sakaliya suka hango gidan boka Jabarul sihir akan tsakiyar wani qaton dutse da ba a ganin karshensa. Lokacin da ya zamana saura taku ashirin atsakaninsu sai kowannensu yaja linzamin dokinsa ya tsaya suka sauko sannan suka raka da kafafunsu suka durfafi gidan suna masu zare makamansu da isarsu izuwa bakin kofar gidan suka tarar kofar ta kasance doguwa mai tsawo da fadi kuma anyi tane da zallar mulmulallen karfe Huzaifal ya matsa kusa da kofar ya karanta ayatul kursiyyu da tsarkakakken sunaye yana mai tofawa ajikin kofar sai gashi ya tura kofar da hannu daya tamkar ya yaye labule kawai sai ya kunna kai izuwa cikin gidan sarki Siyamul ansar boka Zulwal yarima Nazmar gimbiya Hulaisa dakarun rakiya ne a karshe suka bi bayansu da sauri da shigarsu suka tarar da wata hangamemiyar fada ta gaban kwatance gaba daya fadar gidan anyi shine da zallar farin gilashi idan mutum ya kalli ko ina a fadar sai yaga hoton surar jikin gilashin aqalla girman fadar yakai gari guda kai tsayawa misalta tsaruwa da kawaitar fadar yakan iya zamowa kauyanci sai dai abinda ido ya gani wani abin ma idan mutum ya gani bai taba gani ko jin sunansa ba abangaren yamma afadar bisa wata matattakala mai hawa shida aka ajiye wata qasaitacciyar karagar mulki ta gaban kwatance boka Jabarul sihir ne zaune bisa karagar fuskarsa cike da annuri tamkar wanda aka bawo mulkin duniya boka Jabarul sihir ya kasance garjejen qato mai tsawo da kauri tamkar toron giwa duk da kasancewar shekarunsa sun dan ja kallo daya zakayi masa ka fahimci cewa ya kasance gwarzon mayaki mai tarwatsa maza afilin daga a wannan lokaci boka Jabarul sihir na tsaye ne cikin doguwar alkyabba da akayi mata cin baki da zaren lu'ulu'u akansa yana sanye da kambun mulki da akayi shi da zallar zinare yana walwali da daukar idanun mai kallonsa duk inda mutum ya kalla ajikinsa guraye ne da layun tsafi zaune bisa wadansu qayatattun kujeru afadar yan majalisansa ne na jinsin mutum da aljan kuma gaba daya fadar kewaye take da wadansu irin zaratan dakaru masu matukar muni da ban tsoro suna dauke da makami masu barazana da rayuwar bil adama lokacin da boka Jabarul sihir yayi arba da su sarki Siyamul ansar sai ya mike tsaye zumbur daga kan karagarsa ya tako matattakalar fadar ya sauko kasa yana mai takowa da kafafunsa yana kusantar inda suke fuskar cike da annuri tamkar zai sadu da yan uwansa na jini. Koda ganin hakan sai su jarumi Huzaifal suka dafe takubbansu lokacin da ya zamana saura taku goma tsakaninsu sai boka Jabarul sihir yaja ya tsaya ya dubi su jarumi Huzaifal ya bushe da dariyar farin ciki sannan ya budi baki cikin kakkausar murya yace lale marhabun da manyan baki masu daraja na dade ina jiran zuwa wannan rana mai cike da farin ciki agareni yanzu sai ku miko min kwan sihirin da su yarima suka dauke mini akogon Annoba koda jin wannan batu sai sarki Siyamul ansar ya daka masa tsawa yace kai tsohon la'ananne kai sani cewa baka isa mu damka maka kwan sihiri ba face ka amince zaka debo mana ruwan koramarka wanda dashi ne zan warkar da 'ya'yana koda gama fadin haka sai sarki Siyamul ansar ya zura hannunsa a aljihu sai gashi ya fito da wani kwai