Header Ads
Showing 3001 words to 3851 words out of 3851 words

Chapter 2 - Kogon Annoba Book 2 Complete Littafan yaki Writing by Sarkin Marubutan Yaki .txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

mai girma tamkar gwanda yayin da boka Jabarul sihir yayi arba da kwan sihiri sai ya takarkare ya kwarara uban ihu paruwar hakan keda wuya sai gaba daya duhun ya yaye sai ga boka Jabarul sihir cikin gagarumar shigar yaki a hannunsa yana rike da wata zabgegiyar adda mai tsawo da tsinin tsiya koda ganin hakan sai sarki Siyamul ansar ya zare takobinsa boka Zulwal yayi koyi dashi suka ruga izuwa kan dakarun fadar jarumi Huzaifal kuwa ya zare takobinsa ya ruga kan boka Jabarul sihir aka kacame da azababben yaki ana cikin hakan ne sai su yarima Nazmar sukaga wadannan miyagun tsuntsaye na ratsowa ta saman fadar tamkar yadda danshi ke ratsa kasa suna dura a gabansu daya bayan daya koda ganin hakan sai yarima Nazmar da gimbiya Hulaisa suka falfala da azababben gudu izuwa kan tsuntsayen suna masu rayawa azuciyoyinsu cewa muna neman taimakon ubangijin musulunci ba tare da sun riki wani makami ba suka afkawa tsuntsayen da yaki su kuwa dakarun rakiya sai suka zare makamansu suka tari wadansu dakaru afadar dake bangaren yamma aka yamutse da fada abu kamar wasa sai gashi jarumi Huzaifal da boka Jabarul sihir sun shafe tsawon sa'a biyar suna yaki ta hanyar kaiwa juna miyagun hare hare. Lokacin da boka Jabarul sihir ya fahimci cewa ya kasa samun nasara akan Huzaifal da karfin damtse sai ya fara amfani da karfin sihirin tsafi har ya zamana yana yin amfani da dukkanin sirrikan tsafinsa tabbas boka Jabarul sihir ya hadu da gamonsa dakyar da siɗin goshi ya samu nasarar zabgawo Huzaifal daushi aciki ya bazadda shi kas koda Huzaifal ya fahimci halinda yake ciki sai ya kira sunan ubangiji karfi yana mai neman taimakonsa take ya samu wani gagarumin karfi kawai sai ya mike tsaye zumbur yayi tsalle sama tamkar an harbashi daga cikin baka ya dira akan boka Jabarul sihir yana mai rarraba kafadunsa cikin zafin nama ya sanya hannayensa biyu ya murde masa wuya sannan ya dako tsalle ya dira bisa kafafunsa cikin gwaninta adaidai wannan lokaci ne gawar boka Jabarul sihir ta fadi kasa racaca jini ya kwaranya nan take dakarun gaba daya da suke yaki da su sarki Siyamul ansar suka qame suka zama gumaka kuma komai na fadar ya sandare ya zamana saura tsuntsaye dasu yarima suke cikin yaki nan fa jarumi Huzaifal boka Zulwal da sarki Siyamul ansar suka zuba idanu suna kallon fafatawar da akeyi babu abinda yafi basu mamaki sama da yadda su yarima Nazmar ke ragargazar tsuntsayen babu sassautawa a inda za kaga sun kirbawa tsuntsu naushi sun karya kafa ko fukafuki nan fa ya zamana ihu da kururwar tsuntsaye ya mamaye fadar jini kuwa ya dinga kwaranya yana malala tamkar an balla teku su kansu su yarima sunyi matukar mamakin irin wannan gagarumin karfi da suka samu sai da dakika dari da sittin ta shude sannan yarima Nazmar da gimbiya Hulaisa suka samu nasarar kashe gaba daya tsuntsayen amma gaba daya jikinsu ya rine da jini tamkar an tsomasu cikin tekun jini cikin matukar farin ciki sarki Siyamul ansar ya ruga inda 'ya'yansa suke ya rungumesu a kirjinsa cikin tsananin farin ciki daga can su yarima suka janye jikinsu daga na mahaifinsu suka dube shi sukace ya abbanmu kayi sani cewa dukkanin wannan nasara da kaga mun samu akan wadannan tsuntsaye mun samu taimako ne daga ubangijin jarumi Huzaifal saboda haka munyi imani da ubangijin musulunci koda jin haka sai sarki Siyamul ansar boka Zulwal da dakarun tsakiya sukace muma munyi imani da ubangiji mahalicci cikin matukar farin ciki jarumi Huzaifal ya karanta musu kalmar shahada suka maimaita.
Faruwar hakan keda wuya sai sukaji gaba daya fadar ta kama girgiza koda ganin hakan sai jarumi Huzaifal ya falfala da gudu izuwa kofar fita dake fadar yana mai yiwa su sarki nuni da su biyo bayansa ai kuwa suna kammala fita daga fadar sai gaba daya ginin fadar ya dinga rushewa kuma gaba daya ya nutse cikin karkashin kasa Huzaifal ya dubi su duka su hudun yace bamuda bukatar nemo ruwan ma"ul diya'u dan warkar da su yarima imani kadai da sukayi da ubangijin musulunci ya warkar dasu daga lalurar dake damunsu ta rashin jin magana koda gama fadin haka sai jarumi Huzaifal yaje ya kama dokinsa ya hau sannan kowa ya hau nasa aka cigaba da tafiya sa'adda lokacin sallah yayi sai jarumi Huzaifal yayi umarni aka tsaya da tafiya bayan an samu ruwa a wata korama anyi alwala su yarima sun sauya tufafin dake jikinsu sai Huzaifal ya shige gaba yayi musu limanci sa'adda su sarki sukaga yana yin ibadar bisa tsari mai ban sha'awa sai sukaji kaunar addini ta kara shiga ransu bayan an kammalane aka dauki hanya yayin da aka isa birnin sarirul aiwan sai aka kafa tutar musulunci jarumi Huzaifal ya auri wata baiwar sarki Siyamul ansar mai suna ZARIMAT BINTU FANNAS daga wannan rana jama'ar birnin suka kasance cikin farin ciki da kwanciyar hankali ya zamana babu manyan jarumai kamar su yarima Nazmar da sanin ilimin addinin musulunci.




ALHAMDULILLAH




Marubuci


MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
Wthapp number
08137237071

Ads At the End of Article
1
2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads