Header Ads
Showing 15001 words to 16768 words out of 16768 words

Chapter 6 - TSUTSAR NAMA Book 4 Complete Original Document end writing by bilyn Abdull .txt

Ads the beginning of article before Image

07 Jul 2024

547

Ads at the middle of Article

nan ma naƙi na motsa, sai da yay ta uku sai kuma a hankali ya ɗaura da faɗin,
“Dama Ummie c....”
A zabure na yaye bargon gaba ɗayansa. Na ware dukan girman idanuna a kansa. Lips ɗina na rawa a marairaice na ce, “Ummie mi?”. Maimakon amsa min sai kafe cikin idanuna yayi da nasa cat eyes ɗin masu matuƙar girma da yalwar gashi. Wani irin tashi tsigar jikina tayi, sai kif-kif kawai nake faman yi da idanu. Sai faman kokawa nake da numfashina dake seizing.
“Stubborn girl”.
Nakasashiyar muryarsa ta daki cikin kunnena duk da kuwa cikin low voice yayi ta, badan ma idanuna na akansa ba babu yanda za'ai na jisa dan pinkish lips ɗinsa ne kawai suka motsa a hankali. Kamar wata sakarai na jujjuya masa kaina a hankali. Motsa lips ɗina dake ƴar rawa na shiga yi, da ƙyar na iya haɗa kalmar, “Mi ya sa mu Um mie?” a rarrabe ina rissinar da idanuna da suka ciko da hawaye. Dan duk yanda na ƙudirci masa tsiwa ko kallon cikin idanunsa nayi magana sai naji sam na gagara yin hakan. Mutum ne mai masifar kwar jini da cika wuri. ALLAH ya azurtashi da wani irin girma a gaban duk wanda ya tsaya koda ace ya fisa a shekaru da matsayi. Saukar tattausan tafin hannunasa saman fusakata ya sani sake ɗago idanu da sauri na kallesa. A cikin nashi cat idanun suka sake faɗawa. Kallon juna muke a wani irin yanayi har na tsawon shuɗewar wasu sakanni. Kafin a kasalance na motsa nawa dake tara ƙwallan da ban san na minene ba. Shi ko har a lokacin kallon nawa yake yi batare da ya ƙyafta ba, sai ma cikin wani irin soft voice and silent and slowly ya furta, “She is missing you, and she need you”.
“I miss her too”. Na faɗa nima a hankalin ƙwallar data cika min idanu na gangarowa. Idanunsa ya sake ɗan lumshewa tare da buɗewa a lokaci guda ya cigaba da kallona ina kuka sosai harda shashsheka. Shi bai lallasheni ba, bai kuma janye hannunsa dake a kan fuskata ba har yanzu. Tsawon mintuna biyu ina kukana, dan shirunsa sake tunzurani yake. A bazata matuƙar bazata cikin low voice ɗin sa ya furta,
“Samrh”.
Cak na tsaya da kukan da nake, tare da ɗago jiƙaƙƙun idanuna na kallesa. Kallon nawa shima yake da shanyayun nashi da suka canja launi zuwa golden an blue.
“Why are you crying?”.
Ya sake faɗa muryarsa na sake komawa can ƙasan maƙoshi. Samun kaina nayi da sake sakar masa sabon kukan. Tare da riƙo hannunsa dake akan fuskata na ƙan ƙame.
Idanunsa da suka gama canja launi kawai ya zuba mata. Sai Adams apple ɗinsa ne ke faman kaiwa da komawa a cikin maƙoshinsa. A hankali ya kai ɗayan hannunsa saman kafaɗarta, riƙota yayi tare da ɗagota gaba ɗayanta batare da ya janye hannun nasa data ƙanƙame ba sai da ya kaita gab da jikinsa sannan ya janye ya turata cikin jikin nashi gaba ɗayanta. Tsam ya rungumeta yana mai lumshe idanun nasa ƙam-ƙam shima saboda zafin da jikinta ya ɗauka duk da da akwai kaya a jikinsu su duka sai da ya bala'in ratsashi.
Ni kam jina a jikin nasa ya sakani sake fashewa da kuka. A hankali na fara ɗan dukan bayansa ina faɗin, “Why! Why? Why? Suke wahalar da rayuwarta? Mita musu da zafi haka? Da ga ganinta She is an innocent and strong woman. Basu barta haka ba, sun rabata da ku jininta da zata ji sanyi a wajen ku. Natsane su, wlhy na tsanesu. I promise my self sai na ɗaukar mata fansa koda zasu maidani fiye da yanda suka mata. Sai na sakasu gudun ceton rai da babu mafaka Ya Awwab. I promise....”
Kuka ya sake sarƙeta. Sai wani irin jan nunfashi take a sarƙe kamar mai ciwon asthma. Da sauri ya rabata da jikinsa, tare da kwantar da ita a kan cinyarsa. Sosai numfashin nata ke fisga, hannayensa ya saka duka biyu a kumatunta ya shiga ɗan bubbugawa da kiran sunanta.
“Samrh! Samrh! Please keep calm. I know you can, please calm down. Hundred percent I am with you.”
Ina da gaske ƙoƙarin ƙwacewa numfashin nata yake. Ai baima san ya figi bottle na ruwa dake a side drawer ba ya zuba a hannu ya shafa mata duk da kuwa tana numfashi, sai kuma yay saurin kai mata ruwa a baki amma bakin ya gama datsewa ruwan yaƙi shiga. Da sauri ya kai kan nasa bakin ya zuƙa, batare da wani tunani ba ya ranƙwafo kanta ya ɗaura lips ɗinsa a saman nata ya shiga juye mata ruwan tare da riƙe hancinta. Wani masifar jan nunfashi tayi ta baki sai gashi ta zuƙe ruwan gaba ɗaya. Hancin nata ya saki tare da janye bakinsa. Ita kuma ta fara tari sosai. Sake ɗagota yayi a hankali ya maidata jikinsa ya rungume suna sauke ajiyar zuciya a tare. Sunfi mintuna uku a haka sai da ya tabbatar zuciyarta ya gama sauka sannan ya raba jikinsu ya kwantar da ita a gadon a hankali...
Kasa buɗe idanuna nayi, sai ajiyar zuciya kawai nake saukewa a jajjere. Jin saukar abu mai taushi da ƙamshi a saman fuskarta ya sani buɗe idanuna a hankali. Shine ke goge min hawaye da farin handkerchief ɗinsa tass. Idanunsa ya saka cikin nawa har ya gama. Batare da ya janye handkerchief ɗin ba da ɗan yanayin lumshe idanu da buɗewa ya furta, “Miyasa fitina baya miki wuya? Samrh! Ba'a gaggawa a al'amarin maƙiyi, idan ba haka ba zai fika gudu ne wajen cimma manufa. Lokacin da zaka isa sai ka samu shi har ya gama ya juyo. Be a gentle okay”.
Sosai zantukan nasa suka shigeni tare da canja min wasu tunanina da yawa a kansa. Cikin suɓutar baki muryata a dusashe na furta, “Kana nufin kaima duk abinda ke faruwa kana sane?”.
A bazata naga ya wani ɗan taɓe gefen small pinkish lips ɗinsa da lumshe idanunsa sannan ya saki murmushi. Bily idan nace miki kaɗan ya rage zuciyata ta ɓaro akan murmushin nan nasa da salon da yayisa ki yarda da ni kawai. Badan yafi kowa iyawa bane, sai dan murmushi ya kasance ba ɗabi'arsa bace. Amma tabbas magana ta gaskiya murmushin ya ɗebeni iya ɗiba. Dan kaɗan ya rage na fallasa ɓoyayyen al'amarin da na jima ina binnewa a kansa.
(Kin sani a duhu mutuniyar, kodai kin jima kina son Maash ne?).
“Hummm Bily kenan abar dai zancen sai lokacin yinsa yayi”. Na faɗa cikin ƴar dariya.
(Lallai kam, to shike nan na bari muje zuwa labari).


Yanda yay murmushin har ban san na kafesa da mayataccen kallo ba. Idanunsa ya ɗan waro min waje da ɗagesu alamar kallon fa?. Cikin sauri na kauda fuskata gaba ɗaya ina tura baki da faɗin, “Miye abin kallon ma anan”.
Bai tanka min ba, sai ma ɗan kauda kansa da yay gefe. Banyi zaton jin shirunsa a wannan gaɓar ba. Amma nima dai sai na basar kawai tare da ture hannunsa na janye sauran jikina dake a nasa tare da jan bargo na juya masa baya. Dan in banyi hakan ba akwai babbar matsala, dan komai zai iya fitowa saboda yanda zuciyata ke bugawa da sauri-sauri abinda ke can ƙasanta a ɓoye na azalzalota.
Shiru ban sake jin motsinsa ba. Ban kuma yarda na kallesa ba har fin mintuna biyar. Sai a lokacin naji motsin buɗe ƙofa, ɗan juyawa nai kaɗan. Sauka idanuna sukayi akan bayansa dai-dai yana ƙarasa ficewa da jan ƙofar ya rufe a hankali. Nima lumshe idanuna nayi ina sauke ajiyar zuciya. Sai kuma na sake dunƙule jikina a cikin bargon dan ji nake kamar zazzaɓin na ƙaruwar min ma. Mintuna bai fi huɗu da wasu sakanni ba aka sake buɗe ƙofar, idanun na sake buɗewa a hankali. Yanzun kam Mama Balki ne da Doctor sai shi a ƙarshen shigowa. Hannayensa duka biyu a cikin aljihun baƙin wandonsa. Idanun na maida kawai na rufe, dan nasan bai wuce akan zazzaɓin jikina yaje yayo min wannan gayyar ba.


🩸🌟🌟🌟🩸


A hankali take faman kaiwa da komawa a cikin ɗakin nata kai kace safa da marwa take ko motsa jiki. Sai dai sam ba haka bane. Abubuwane masu yawa ke matuƙar damunta da cizar mata zuciya. Dan tun zaman da sukai da Yallaɓai ɗazun da magrib ta gagara samun sukuni. Gaba ɗaya taji ta kasa komawa asibitin da taci burin komawa dan akwai wani baƙo da zatai mai muhimmanci. Maganganunta da Yallaɓai ne suka shiga dawo mata dalla-dalla tamkar a yanzu suke tattauna su....
“Yaushe yarinyar nan tazo aiki gidanku? Waye kuma ya kawota?”.
“Lokacin muna Dubai muma zuwa kawai mukai muka sameta anan. Amma ance Mashi'a ce ta kawota”.
“Mashi'a?!”.
“Yes ita fa. A cewarta kuma ta kawota ne as a birthday gift wa mahaukaciyar matar can. Tunda masu aikinta sun sake guduwa a lokacin babu mai kula da ita”.
“A ina ta ɗakkota?”.
Ɗan jimm tayi, sai kuma ta ce, “Gaskiya wannan ne ban sani ba”.
Kasa sake cewa komai yayi, sai ma kai-kawo daya shiga yi hannayensa goye a bayansa..........✍️






_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._




_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*




_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

Ads At the End of Article
4
5
6

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads