Showing 1 words to 1678 words out of 1678 words
Chapter 1 - JARUMI DA GIMBIYA littafin Yaki Book Complete writing by Abdul'aziz Sani Madakin Gini .txt
JARUMI DA GIMBIYA
Abdul-aziz Sani Madakin gini
Su bakwai ne dukkaninsu sun yi shigar baqaqen kaya sama da qasa, idanunsu kaxai ake gani. Kowannnensu yana rataye da takobi a bayansa kuma suna xauke da waxansu taurari na qarfe ma su kaifi da tsini a jikinsu ma su xan yawa.
Lokaci guda su bakwai suka dira akan rufin sama na gidan sarautar suka qarewa gidan gaba xaya kallo. A qalla akwai dakaru kimanin guda xari uku a tsaitsaye a ko wanne lungu da saqo na harabarr gidan masu tabbatar da tsaro. Jaruman bakwaiu suka kalli junansu sannan suka kalli shugabansu wanda akwai alama ta zanen jar tsuntsuwa a jikin rawaninsa, kawai sai shugaban ya nunawa ko wannen su zai nufa da hannu. Nan take suka dako tsalle qasa daga saman gininn kai kace fuka-fukai ne a jikinsu duk da cewa tsawon ginin daga saman zuwa qasa ya kai kamu ashirin da biyar.
Lafiya qalau kowannensu ya sauko qasa ba tare da anji motsin durowarsu ba, nan fa suka fara watsawa dakarun gidan sarautar waxannan taurarin na qarfe suna zubewa qasa matatta, kai kace wata guba suke busa musu dan ko motsin kirki basa iyaye. Abinda zaifi xaure maka kai shi ne zafin naman waxannan jaruman guda bakwai domin ko gani su ka yi badakare zai faxa kan wani abu da zai samar da qara wacce zata tona asirin zuwansu sai kaga sunyi sauri sun ruqoshi da hannu, sun ajiye shi qasa a hankali. Haka da jaruman bakwai suka ci gaba da bazar da dakarun tsaro na wannan gidan sarauta har suka qarar da su, su xari uku nan. Kai tsaye shugaban na su ya tunkari turakar Gimbiya sazira.
Qofar shiga turakar a rufe take kuma dakaru biyune tsaye a wajen. Koda suka hangoshi ya durfafosu sai suka yunqura a lokaci guda. Xaya ya zare takobinsa domin ya tare shi, xayan kuma ya kai hannunsa izuwa kan wani qaho dake rataye a sama domin ya xauko shi ya busa amman sai shugaban dakarun sumamen ya yi wuf ya zaro taurarin qarfe guda biyu, cikin zafin nama ya watsa musu. Taurarin qarfen suka cake akan goshinsu duk su biyun suka sulale qasa matattu.
Ita dai wannan babbar qofar ta shiga xakin Gimbiya sazira a rufe take ta ciki da sakatu da makullai. Shugaban dakarun sumame ya sunkuya ya leqa ciki turakar ta cikin kafar kubar qofar sai ya hango kuyangin su da yawa a kwance cikin wani qaton falo suna ta sharar bacci. Qofar shiga cikin ainahin xakin barci na gimbiya sazira na gaba kaxan.
Koda ganin hakan sai ya rikixe ya zama haske ya shige ta cikin qofar. Yana baiyana a falon ya sake tunkarar qofar xakin gimbiya kai tsaye. Qarar takun sawunsa yasa kuyanginta suka fara farkawa daga bacci amma duk wadda ta buxe ido tayi arba da shi sai ta kasa miqewa tsaye kuma ta kasa buxe baki tayi magana saka makon wata hoda da ya rinqa busa musu daga cikin wani lofe dake bakinsa kuma ya toshe hancinsa da rawaninsa. Nanfa kuyangin suka rinqa komawa suna kwanciya sakamakon bacci me nauyi da ya rinqa xaukarsu. Da isarsu qofar xakin Gimbiyar sai ya tsaya cak domin gimbiyar ya hango ta cikin tagar xakin zaune akan gado ta qura masa idanu. Babu alamar tsoro ko wata fargaba a tare da ita. A wannan lokaci tana sanye da wata doguwar farar riga barci me bayyana kyakkyawar surar jikinta.
Gashin kanta a tsefe yake ya zuba har qasan kwankwasonta. Macece me dara-daran fararen idanuwa hancinta dogone a qasansa xan qaramin bakine, qirar jikinta ta kalanguce, kaurin jikinta madaidaici, fatar jikinta mai haskece, sumul sumul tamkar ko quda bai tava sauka a jikinta ba, tamkar ana tabata jini zai fito. Nan take wannan shugaban dakarun sumame ya ximauce bisa ganin tsananin kyawun Gimbiya Sazira saboda dama bai tava ganinta ba, labarinta kawai yake ji.
Bayan sun yi kallon-kallo na ‘yan daqiqu ashirin zuwa talatin sai Gimbiya sazira ta sauko daga kan gadonta ta nufo bakin qofar xakin kai tsaye ba tare da wata fargababa. Tasa hannunta ta zare sakatar qofar xakin guda huxu ta buxeta ta dube shi fuskarta da murmushi irin na mugunta tace “Kaine shugaban dakarun sumamen da ake bani labari na birnin samhar ko?” mamaki ya kama shi ya kasa cewa komai.
“An gaya mun cewa sarki muraka yasa an baku horo na wata shida kai da yaranka ku shida domin kawai ku zo nan birnin kamlaz ku sace ni, tabbas na yaba da qoqarinku da kuma kaifin sihirinka na tsafi tunda har kuka iya ratsowa cikin gidan sarautar nan harma kai ka sami nasarar shigowa vangaren turakata. Nasan kun sami nasarar kashe gaba xayan dakarun dake tsaron wannan vangaren da nake kuma ka sakawa kuyangina bacci me nauyi. Tofa ka sani ba’anan gizo yake saqar ba, idan kana ganin za ka iya xaukata da qarfin tsiya ko da qarfin sihirin tsafi ka kaini wajen sarki muraka babban maqiyin mahaifina to ga fili ga mai doki. Daga ni sai kai mu jarraba mu gani, babu wanda zai kawo min taimako, taho mana, zo ka xauke ni idan ka isa”.
Mamaki ya qara kama shugaban dakarun sumamen ya dubeta da murmushi na raini ya buxe baki yace “Ya ke wannan ‘yar sarki ke kuwa me kike taqama da shi har da kike tunanin zaki iya kare kanki daga farmakina?” Gimbiya sazira ta yi murmushi tace.
“Ina taqama da duk abinda kake taqama da shi, amma kasan wani abu sai an gwada sannan ake sanin bambanci a tsakanin aya da tsakuwa. Kai nake jira kawai idan kuma ka karayane, to ka juya ka fice mun na yi baccina da ka katse mun” Koda jin wannan batun sai shugaban dakarun sumame ya fusata ya nufo Gimbiya sazira da nufin ya kamata da hannunsa. Cikin zafin nama ta damqi hannun nasa ta murxe ta doki gadon bayansa ya tafi taga-taga zai faxi amma sai ya tsaya daram ya juyo suka dubi juna yana mamakin irin wannan jarumtaka tata. Kafin ya ankara sai kawai yaga ta dako tsalle daga inda take tsaye tamkar kibiya aka harbo ta kawo masa wawan naushi a fuska. Koda ya goce hannunta ya samu wani gunki me siffarta dake tsaye sai gunkin ya rushe ya zube qasa. Nan fa suka kacame da azababben faxa suka wanzu suna kaiwa junansu naushi da bugu hannu da qafa.
Abinda ya yi matuqar xaure masa kai shi ne duk irin salon faxan da ya yi sai yaga itama ta iya irinsa. Zafin namansa da juriyarsa duk sai suka zamo iri xaya. A duk sa’adda ya sami nasarar naushin jikinta sai yaga ta shanye naushin kuma ta rama nan take cikin daqiqu kaxan suka haxawa juna jini da majina. Sai da suka shafe daqiqu ma su yawa suna wannan gumurzu ya kasa kaita qas kuma ya kasa galabaitar da ita.
Bisa dole duk su biyun suka ja da baya saboda gajiya suka yi carko-carko suna kallon juna sakamakon gajiya sai haki suke yi. A wannan lokacine hankalin shugaban dakarun na sumamen ya tashi saboda yasan cewa idan ya qara vata lokaci shirinsu na sace Gimbiya Sazira zai wargaje saboda xaya vangaren na gidan sarautar za su iya sanin abinda yake faruwa anan tunda asuba ta kusa.
Kuma har ya hango ragowar abokan aikinsa dakaru shidan sun iso babbar qofar shigowa turakar Gimbiya sazira sun tsaya suna jiransa. Bisa dole ya yunqura cikin zafin nama ya nuna Gimbiya sazira da hannayensa biyu, wata irin iska mai qarfin gaske ta sauka akan ta tana qoqarin zuqota gareshi. Kawai sai itama ta nuna iskar da hannayenta biyu, take wata jar iska ta tari tasa iskar suka kama hautsinewa. Ya yi iyayinsa amma ya kasa zuqo gimbiya har shi da ita suka jiqe sharkaf da gumi, kawai sai ya saki hannayensa qasa, itama ta saki suka kama haki suna kallon juna kai kace sa’a uku suka shafe suna yin aikin qarfi.
Shugaban dakarun sumame ya juya zai fita daga cikin turakar sai tace “Idan ka koma birnin kilmaz ka gayawa sarki muraka cewa tunda ya kasa satoni to ni zan zo da kaina na sace xansa Yarima Andaz”. dajin haka sai ya juya ya dubi Gimbiya sazira yace.
“Ba kasa satoki na yi ba, kwanaki goma aka bani na kai ki can birnin kilmaz kuma yau kwana biyu kacal don haka zan ja da bayane domin na sake yin shiri. Ina mai tabbatar miki da cewa kafin cikar kwanakin goma sai na kaiki gaban sarki” Gimbiya sazira ta bushe da dariya sannan tace “Duk irin shirin da za ka je kayi nima zan yi irinsa anan, ba zaka tava samun nasara a kaina ba, kuma ka sani nima na yi alqawarin da girman gemun mahaifina kafin cikar kwana gomannan sai na shiga har cikin birnin kilmaz na sato Yarima Andaz. Ka sani na sani a tsakanin mahaifina sarki Ridwan da sarki muraka duk wanda ya sami nasarar sace jinin xaya tamkar mallake qasarsane, ba zan tava bari ku mallake qasarmu ba saboda tsohuwar gabar da take a tsakaninmu tun iyaye da kakanni. Kafin ka fita daga nan ina so ka bani amsa amsar tambayayona guda biyu, wane kai a cikin qasar kilmaz kuma saboda me ka siyar da rayuwarka domin ka farantawa sarkinku rai? Wane alqawari ya xaukar maka har da ka yi wannan qundumbalar haka?”
Shugaban dakarun sumame ya yi kamar ba zai ce komai ba sannan yace “Ni ba kowa bane a cikin birnin kilmaz face jarumi me zaman kansa. Ba zan iya baki amsar tambayarki ta biyu ba, sai mun sake haxuwa a karo na biyu” Yana gama faxin haka sai ya juya ya fice daga cikin turakar, Gimbiya ta biyoshi da gudu amma yana isowa inda abokan aikinsa suke su shida sai su duka suka daka tsalle sama suka dira a cikin rufin saman gidan. Nan take itama Gimbiya sazira ta dako tsalle sama tamkar daga cikin baka aka harbota ta dire akan rufin gidan amma sai ta neme su sama da qasa ta rasa.
Cikin tsananin baqin ciki ta diro qasa bisa qafafuwanta ta koma cikin turakarta. Adaidai wannan lokacine taji an busa qaho, alamar angane cewa baqi sun shigo gidan. A wannan lokaci asuba ta kawo kai.