Showing 1 words to 573 words out of 573 words
Chapter 1 - BABBAN KUNDI BOOK Complete Writing by Kabiru Yusuf Anka.txt
kasance mashahurin sarki kuma gagarumin attajiri da babu kamarsa a kaf nahiyar baitul wahir
yana da matar aure guda daya kyakkyawar gaske mai suna NUZRA BIN SHA'ARAN a rayuwar sarki siyamul ansar babu wani rayuwar jin dadi da ya nema ya rasa face rashin haifuwa
duk da irin tarin dukiya da karfin mulki da yake dashi ya tashi a banza domin bashida wanda zai gaji karagarsa
Akalla ya ziyarci manyan bokaye sama da dari akan wannan matsala ta rashin haihuwa amma abu ya citra a wani shekara ne ya ziyarci wani boka acan birnin KUBA mai suna zulwal
lokacin da sarki siyamul ansar ya bijirowa da boka zulwal da buka tunsa na rashin haihuwa sai kawai boka zulwal ya bushe da dariya har sai da ya fado daga kan kujerar da yake zaune kuma idanunsa suka ciko da kwalla
al amarin da ya daurewa sarki siyamul ansar kai kenan kuma
ya fusata ya dakawa boka zulwal tsawa yace dashi shin ina dalilin yin wannan dariya taka cikin nutsuwa da biyayya boka zulwal ya koma akan kujerarsa ya zauna yayi gyaran murya
sannan ya fara magana karo na farko muryarsa mai kama da kukan jaki yana mai cewa asi ya huci zuciyarka ya sarkin sarakunan masu isa kayi sani cewa ba komaine
ya sanya ni wannan dariya ba face bisa ganin yanda ka wahalar da kanka wajen fadin bukatar da take tafe dakai ya sarki mai cikakken iko kasani cewa tabbas ayanzu matarka
na dauke da juna biyu nan bada dadewa ba zata haihu kuma ina mai farin cikin sanar dakai cewa 'ya'ya biyu zata haifa mace da namiji sai dai inda gizo ke sakar shine 'ya'yan da za a haifa maka zasu kasance hatsabibai marasa jin magana wadanda sune zasu zamo ajalinka.
Yayin da boka zulwal yazo nan a jawabinsa sai hankalin sarki siyamul ansar ya dugunzuma fiye da kowane lokaci ya dubi boka zulwal yace ya sarkin bokaye shin babu wata hanya da za abi 'ya'yan da zan haifa basu kasance hatsabibaiba? .
boka zulwal ya nisa yace ai bakin alkalami ya bushe lallai wannan al amari haka zai kasance koda jn wannan batun sai sarki siyamul ansar ya sunkuyar da kansa ka
s yana mai zurfafa cikin kogon tunani abu na farko daya fado masa arai shine yanzu babu wata mafita face kayi murna da wadannan yara da za a haifa maka domin sune zasu gajeka bayan ranka tabbas bakada nadama
koda sun zamo ajalinka ai da ace wani ne zai gaji karagarka gwara ace dankane na cikinka can kuma wata zuciyar tace ka cigaba da bincike ya za ayi ace 'ya'yan mutum sune zasu kasance ajalinsa lokacin da sarki Siyamul ansar yazo nan a tunaninsa
sai ya dago da kansa ya dubi boka zulwal yace tabbas na amince 'ya'ya na su zamo ajalina matukar zasu gajeni bayan raina.
Gama fadin hakan keda wuya sai sarki Siyamul ansar ya debi dukiya mai yawa ya bawo boka zulwal saboda tsananin murna sai da boka zulwal ya dinga birgima akasa tamkar
wanda ya samu ciwon hauka domin tunda yake a rayuwarsa bai taba samun dukiya mai yawanta ba kumama yana da wani babban buri akan dukiyar yana son ya hada wani maganin tsafi da ita tun daga wannan rana
sarki Siyamul ansar ya kasance cikin tsananin farin ciki kuma ya zamana dare da rana baya rabuwa da uwargidansa nuzra yana bata gudunmuwa wajen rainon juna biyun har ta sauka lafiya
ta haifi 'ya'ya biyu kyawawa