Showing 1 words to 430 words out of 430 words
Chapter 1 - DIMAUTA Book Complete New Adventure By Kwalisa.txt
Kyawawan samari ne majiya karfin damtse su uku, mai matukar kwarjini da ban tsoro. Na farkonsu yana rataye da waɗansu zaratan takubba guda biyu a gadon bayanshi kuma ya kasance mai matuƙar kaurin jiki fiye da 'yan uwanshi.
Saurayi na biyu yana dauke da wani irin KWARI DA BAKA mai daukar hankali,jikinsa a murde yake ya tara kwanji,
kallo daya zakayi masa kafahimci cewa ya fi sauran yan uwansa kirar sadaukantaka.
Na ukun kuwa yana ɗauke da dauke da dogon nashi mai baki biyu,
bakin yakasance daga farkon sa yayi fadi daga karshe yayi tsini ya fitar da baki biyu.
Babu abin da zai burge ka ga samarin sama da yadda suka yi shigar yaƙi iri daya sak,
kuma suna zaune abisa jajayen dawakai ingarmu.
Samarin uku suna tafiya ne acikin wani daji ma,abincin dogayen bishiyoyi,koramu,
tare da kwazazzabai.gaba daya yanayin dajin ya banbanta da sauran dazuzzukan da idanuwa suka saba gani.
Domin hatta kwari da tsuntsayen dake cikin sa abin tsoro ne.awasu lokutan sai kaga tsuntsaye na dauke da fuskokin bil,adama,hatta bishiyoyin dajin suna canza launi zuwa launi,
Tabbas dajin yana da matukar kwarjini ga duk jarumin daya tsinci kansa acikin sa dolane ya razana
Haka dai zaratan samarin uku suka cigaba da tafiya adajin Babu alamun razani atattare da fuskokinsu Lokacin da suka shafe tsawon sa,a daya da dakika talatin suna tafiya acikin dajin,a dai dai wannan lokaci ne suka fara hango wani katafaren gida kwaya daya jal adajin,
Al,amarin da yayi matukar basu mamaki kenan suka ce acikin zukatan su.taya za,ace wannan kasurgumin daji ace an gina wannan kerarrran gida a cikinsa.
Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kansu kenan, suka cigaba da tafiya,
Da isar su bakin gidan suka tarar da gidan ya kasance tankameme Tamkar gari guda.gaba daya ginin anyi shine da waɗansu manyan duwatsun wuta wadanda ido bai taba gani ba,
Katangun gidan sun kasance masu tsawon gaske.akwai ƙatuwar kofa guda daya jal mai tsawo da kauri inda za,a sanya karti majiya karfi mutum hamsin bazasu iya ture ta.
Nanfa samarin suka yi cirko-cirko suna nazarin kofar tsawon dakika arba,in dayansu bai ce uffan ba.
Daga can sai daya daga cikin su wanda ake kira da suna Hilwas yayi gyaran murya yace "yaku 'yan uwana yanzu mene ne abinyi?
Gashi yanzu mun iso gidan boka kimraz,naji ajiki na cewa dukkan baiwar da muke da ita bazata yi mana wani amfani ba face muyi Amfani da fasahar da muke da ita."
Koda jin wannan batu sai sharwas yayi caraf ya tari numfashin Hilwasa
yace"Ni shawarar dazan bamu muyi tunanin hanyar da zamu bude Wannan kofa,
kunsan masu iya magana na cewa abari ya huce shi ke kawo rabon wani, kuma da zafi-zafi a kan daki karfe."