Wuta a masaƙa: Sabon littafi kan nazarin adabin Hausa
Admin
01 Aug 2024
37

SHARHIN LITTAFI
Wuta a masaƙa: Sabon littafi kan nazarin adabin Hausa
LITTAFI: Hausa Prose Fiction: A Reader
EDITA: Yusuf M. Adamu
WALLAFAWA: Bayero University Press
SHEKARA: 2021
SHAFUKA: 305
DAGA IBRAHIM SHEME
Fagen nazarin adabin Hausa waje ne mai faɗin gaske wanda za a ɗauki tsawon lokaci ba a gama nome shi ba. Ga ma'aikatan nan da dama - malaman jami'a da na kwalejoji da ɗalibai, da kuma sauran mutanen gari masu sha'awar irin wannan aikin, su na ta bada himma wajen fito da littattafan nazari a fagen. Hakan ya sanya jefi-jefi za ka ji wani ma'aikacin ya kai kuyyar sa.
Ɗaya daga cikin masanan adabin Hausa, Farfesa Yusuf Adamu na Jami'ar Bayero, Kano, ya kai tasa kuyyar kwanan nan da ya wallafa sabon littafi a kan wani sashe na adabin Hausa, wato rubutun zube na ƙirƙirarrun labarai, a matsayin edita. Sunan littafin, wanda aka yi da Turanci, shi ne 'Hausa Prose-Fiction: A Reader'.
Littafin ya ƙunshi maƙaloli 16 da kuma hirarrakin wasu marubuta guda huɗu. An kasa shi gida uku. Kashi na farko ne ke ɗauke da maƙalolin nan 16 waɗanda masana ko manazarta daga wasu jami'o'i da manyan kwalejojin ƙasar nan da na ƙetare, har ma da waɗanda ba malaman makarantu ba ne, su ka rubuta. Ban da cikin Nijeriya, an samu gudunmawar maƙalolin daga Nijar, Poland, Amurka da Jamus, wanda hakan na nuna cewa manazartan sun fito ne daga sassa daban-daban na duniya.
Kowace maƙala ta taɓo wani al'amari na musamman da ya shafi cigaban rubutun ƙirƙira na zube na Hausa, irin su tarihin rubutu, ƙungiyoyin marubuta, rubutun mata, gudunmawar gidajen rediyo, da kuma kasuwancin littattafai.
Sanannun manazartan da su ka bada gudunmawar babi-babi ga wannan kundi sun haɗa da Abdalla Uba Adamu, Balbasatu Ibrahim, Chaibou Elhadji Oumarou, Novian Whitsitt, Asabe Kabir Usman, Mariusz Krasniewski da shi kan sa Yusuf M. Adamu.
Kashi na biyu ya dubi gundarin abin da waɗansu littattafai su ka ƙunsa. Masanan sun yi sharhi kan littattafai da su ka haɗa da 'Shaihu Umar' na Abubakar Tafawa-Ɓalewa, 'Baƙin Duhu' na Fauziyya D. Sulaiman, da littattafan Zaynab Alkali da na Abubakar Imam, Balaraba Ramat Yakubu da na Bilkisu Salisu Ahmed Funtua, da matsayin boka a labaran ƙirƙira na Hausa, da dai sauran su.
A kashi na uku ne aka kawo hirarrakin da aka yi da marubuta huɗu, wato Abdulƙadir Ɗangambo, Ado Ahmad Gidan Dabino, Bilkisu Salisu Ahmed Funtua da Hafsat Umar Ɗantanko. A nan za a ji tarihin kowannen su da yadda aka yi ya zama marubuci da tunanin sa game da sha'anin rubutu da irin ayyukan sa a fagen rubutu da dai sauran su, duk daga bakin da ba ya ƙarya. Waɗanda su ka yi hira da waɗannan marubutan su ne Sa'idu Ɓaɓura Ahmed, Ismail Bala, Ibrahim Sheme da Umma Aliyu Musa.
A ƙarshen littafin an kawo taƙaitattun bayanai kan waɗanda su ka bada gudunmawa ga wannan littafi. Tun can farko kuma akwai ta'aliƙin da Farfesa Sani Abba Aliyu na Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya, ya yi wa littafin da kuma gabatarwar da editan littafin, Farfesa Yusuf M. Adamu, ya yi.
A ta'aliƙin, Farfesa Aliyu ya nuna muhimmancin wannan littafi, inda ya ce irin wannan aiki da wani ɗan ƙasa ya yi ya dace ƙwarai, domin bai kamata a ce mu zauna mu zura ido sai wasu baƙi daga ƙasar waje sun zo sun riƙa yi mana nazari kan adabin mu ba; mu ya kamata mu ja akalar mu da kan mu. Ya yaba wa editan kan dagewar sa har littafin ya fito, kuma ya yi kira ga dukkan ɗalibai da malaman nazarin adabi da ma duk wani mai sha'awar wannan fage da ya nemi littafin ya karanta.
Shi kuma editan, Farfesa Yusuf M. Adamu, ya kawo cikakken bayani ne kan asalin littafin. Ya fara da ambato tarihin nazarin adabin Hausa irin su nazarce-nazarcen da aka yi tun daga shekarun 1960 zuwa yau. Ya ce ya gano cewa babu isassun nazarce-nazarce kan rubutun zube na ƙirƙira, domin waɗanda aka yi ba su fi cikin cokali ba. A cewar sa, hakan ce ta sa Ƙungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA), reshen Jihar Kano, ta ɗauki nauyin sa ya yi wannan aikin. Editan ya ce ya yi aiki kan littattafai biyu ne bisa wannan maudu'i, na Hausa da na Turanci. To, na Turancin ne ya fito, amma na Hausan ma, mai suna 'Nazari A Ƙagaggun Labaran Hausa', ya na nan tafe nan ba da jimawa ba.
In ban da 'yan kurakurai na ɗab'i da na gani, waɗanda za a iya gyara su a bugu na gaba, ni dai ban ga wani naƙasu ko aibu a wannan littafi ba. Bugun ya yi kyau, haka yadda aka tsara shi, har aka samar da wasu hotunan masu kala a ciki.
Shakka babu, ko makaho ya shafa ya san lallai Farfesa Yusuf M. Adamu ya yi ƙoƙari matuƙa wajen ɓata hankalin dare har ya kammala wannan muhimmin littafi. Littafin zai ƙara haske a duhun da mutane da dama su ke ciki game da rubutun ƙirƙira na Hausa, musamman zube. Ɗalibai har ma malamai za su ƙaru da ilimin fagen, sannan za su riƙa lalubo littafin a duk lokacin da su ke so su gano wani abu game da wannan maudu'i. Daɗin abin shi ne kowane babi na littafin ya na magana ne kan wani jigo na daban.
Haƙiƙa za a iya cewa wannan littafi kamar ana zaton wuta a maƙera ne amma sai ta tashi a masaƙa. Dalili shi ne Malam Yusuf ba malami ba ne mai koyar da adabi a aji. Shi masanin ilimin labarin ƙasa ne, wato Geography. To, waɗanda ba su san shi ba ne za su yi zaton ya yi shigar sharo ba shanu, domin fa duk da yake malamin ilimin labarin ƙasa, ya daɗe a fagen adabi inda ya ciri tuta wajen rubutu da kuma nazari. Zan iya bugun ƙirji da cewa ba kowa ba ne zai iya karawa da shi har ya buge shi a fagen. Hakan na nuna cewa sha'awar abu na sanyawa a ƙware a abu; wato dai kamar yadda Hausawa ke faɗi, zama da maɗaukin kanwa ya kan sa farin kai. Saboda haka, Farfesa Adamu ya cancanci yabo matuƙa. Da fatan a amfana da wannan aiki da ya yi.
A ƙarshe, zan rufe da cewa wannan littafi ƙalubale ne ga sauran manazarta na su ƙara zage damtse wajen fito da ayyuka irin wannan. Kamar yadda na ce a can sama, gandun ya na da faɗi sosai. Ba rubutun zube na ƙirƙira, akwai rubutun waƙe da na wasan kwaikwayo da na adabin baka. Malam Yusuf dai ya kai tasa kuyyar, sauran mu ga wanda nasa noman zai samar da wata kyakkyawar yabanyar.
Ibrahim Sheme shi ne daraktan yaɗa labarai a National Open University of Nigeria (NOUN), Abuja
Leave a Comment
Your email will be kept private. Required fields are marked *
Search
Categories
-
(5)
-
(2)
-
(2)
Recent Article
david beckham
Read More
ASALIN HARSHE
Read More
Adabin Hausa
Read More
Sharhin Littafin Gwagwarmayata Da Cutar Sikila
Read More
Sharhin Littafin Zube Na ‘Sidi Ya Shiga Makaranta’ Na Umaru Ladan Da Michael Crowder (1)
Read More
Wuta a masaƙa: Sabon littafi kan nazarin adabin Hausa
Read More
Abubakar Imam
Read More
Ado Ahmad Gidan Dabino
Read More
Balaraba Ramat Yakubu
Read More
0 Comments