Showing 1 words to 584 words out of 584 words
Chapter 1 - KARE KUKANKA Book 9 end Complete Writing by Abdulaziz Sani M-Gini .txt
Kasaitacciyar turaka ce da aka kawata ta da nau'ikan kayan kawa da alatun jin dadin rayuwar duniya.
Babban abinda ya kara fito da kyawun turakar shi ne wadansu fararen kushin na alfarma da aka kewaye turakar dasu kowacce kusurwa a turakar an kawata ta da wasu kawatattun fitulu na azurfa.
idan mai kallo ya yi duba daga bangaren yamma a turakar bisa kayatattun kujerun zai yi arba da wani sadauki zaune shirye cikin gagarumar shigar yaki Mai matukar kwarjini da ban tsoro Duba daya zaka yi masa ka kawar da fuskar ka saboda tsananin munin sa,
A bisa wata karaga ta alfarma wani mutum ma,abocin kyawun fuska da kwarjini,
yana sanye da tufafin sarauta na alfarma sun yi matukar yi masa kyau kai da gani kasan yana jin dadin duniya.
Shiru ne ya wanzu a tsakanin su Sai Daga bisani ne Sarki shardasu Ya katse shirun da ya wanzu ta hanyar budar baki yayi gyaran murya
yace "yakai dirkar birnin baitul-na,im kayi Sani Sani cewa ban kirawo ka nan ba Sai domin na tunasar dakai cewa lokacin gudanar da GASAR JARUMTA ya gabato nan da kwana talatin kacal!
Lallai ina so a fara shirye shiryen wannan gasa. Kasani cewa awannnan karon akwai manayan sarakunan nahiyoyi hudu da zasu halarci wannan Gasa Sannan salon gasar zai canza izuwa rukuni uku .wato fadan takobi,
Sai kuma na KWARI DA BAKA da kuma ta KARFIN DANTSE.
Koda Sarki shardasu Ya zo nan azancensa Sai Ya zira hannun sa aljihunsa na Riga ya dauko wata doguwar takarda ya mikawa sarkin yaki,
Cikin biyayya ya sa hannayen sa ya karba Sannan ya warware ta yafara karanta abinda ke kunshe a cikinta.
Koda kammala karantawar Sai yaji zuciyar sa yayi bakikkirin bakomai ne ya sanya shi cikin wannan hali ba Sai domin a cikin sunayen jaruman gasar da aka bashi yaga sunan yarima kinzaru Wanda tsakanin su akwai rashin jituwa,
Saboda sarkin yaki yana matukar kaunar kanwarsa gimbiya lashmira Tsakanin lashmira da yarima kinzaru akwai rashin jituwa saboda kowannen su na kwadayin ya gaji karagar mulki,
Sa,adda Sarki yaki Ya zo dai dai nan a tunanin sa Sai ya cika da matukar bakin ciki yana cikin wannan hali ne Sai ya lura akwai sauran rubutu a ayan takardar. Cikin matukar farin ciki ya juya takardar ai kuwa Sai yayi arba da sunan gimbiya lashmira,Bawa Hilwas, sharwas da bawa kahzib,
saboda farin ciki bai San sa,adda murmushi ya subuce masa ba,
yayin da ya hada idanu da Sarki shardasu sai ya sunkui da kansa kasa cikin alamun rashin gaskiya Sarki shardasu Ya dubi sarkin yaki da duban dake nuna fahimtar wani abu game da murmushi nasa Sannan yayi gyaran murya yace
" ya dirkar birnina kayi Sani cewa inaso ka gaggauta sanar da dukkan Wanda sunan sa ke kunshe a cikin wannan takardar jaruman Gasa kuma a tabbatar da cikekken tsaro daga yanzu har izuwa bayan gasa domin wannan gasa ce ta musamman.
Koda gama fadin hakan sai Sarki shardasu Ya mike tsaye tsam! daga kan kujerar sa ya taka da kafafunsa ya nufi wata har siririyar kofa a turakar.
Yana tafiya cikin kasaita da BAKAR IZZA! yana isa bakin kofar wadansu ZARATAN MAYAKA na sihiri suka bayyana su kimanin arba,in shirye cikin gagrumar shigar yaki suka Mara masa ba ya har ya kule izuwa cikin Gidan sarautar.
Hakika Sarki shardasu Ya zurfafa acikin ilimin tsafi da kamo kafar shi sai mutum yayi da gaske.
Nan take Sarki yaki Ya mike tsaye ya fice daga turakar zuciyar sa cike da tunane - tunane iri - iri.