Header Ads
Showing 3001 words to 5833 words out of 5833 words

Chapter 2 - LABARUN SHEHU JAHA Complete Book Writing by Nasir G Ahmad Yan Awaki .txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

in baka dirhami maitan, na menene, ko cutata kuma zaka yi?” Manaja yace "Ai na gaya maka dama sai dai in maka sauki kawai in ce ka biya, amma tunda kafi son gwari-gwarin, bari a yi maka.


Kazar nan da ka cinye tun wata uku, da ace ka bar mana abar mu kullum zata dinga saka mana kwai biyu ne, kuma zamu dinga sakawa kazar da take kyankyasa ta kyankyashe mana su, suma zasu girma su dinga saka kwayayen...... a haka dai zuwa wannan wata ukun Allah kadai ya san yawan kajin da zamu samu ta hanyarta, amma ka cinyeta, shi yasa nayi maka wannan arahar!"


Da Attajirinnan ya ji haka sai ya kai kara gun wani Alkali, Manaja kuma da yaje ya nunawa Alkali zai bashi agwagi biyu manya da wasu kudi. Nan da nan Alkali ya birkita magana, yace "Ai tunda baku yi da Manaja ga abinda zaka biya ba in ka dawo yanzu dole abinda yace shi zaka biyashi" Da dai ya ga za'a cuce shi sai ya nemi a dage shari'ar, Alkali kuwa ya amince.


Ana dab da komawa shari'a sai wasu samari suka ce da shi ya je ya sami Shehu Jaha yayi masa bayanin wannan makirci da ake shirin yi masa. Yaje ya sami Shehu yayi masa bayani gabadaya, sai Shehu yace "To goben idan kaje kace ina nan zuwa kotun kafin a fara shari'ar" Yace "Toh" Ya tashi ya tafi.


Washegari an cika ana ta jiran Shehu ya zo a fara shari'a can rana ta daga sai ga Shehu nan da sauri ya shigo kotu. Alkali yace da shi cikin fushi "Kai me yasa ka zaunar da mutane muna ta jiran ka zamu fara shari'a, kaje ka bata mana lokaci" Shehu cikin nutsuwa yace "Allah Ya gafarta Malam ina neman afuwa, abinda yasa na samu jinkiri, na sa an dafa min wata ragowar alkama ne kuma naje gona na shuka ta sannan na taho" Alkali ya dube shi a fusace ya daka masa tsawa yace "Rufe mana baki, kai jama'a waye ya ta6a jin inda aka shuka dafaffiyar alkama a cikinku, mu zaka mayar mahaukata?"


Shehu yayi gyaran murya yace "KUMA BA'A HAKA ASHE HAR AKA SAMU DAFAFFIYAR KAZA TAKE YIN KWAI? Har ma a kyankyashe kaji masu dimbin yawa?" Nan da nan Guri ya hargitse da hayaniya, Alkali ya ga bashi da wata mafita akan wannan zalunci da yake shirin aikatawa! Nan dai ya sallami Attajiri yace ya biya Manaja iya kudin kajinsa biyu da kwai hudu. Attajiri yayi godiya ga Shehu Jaha, yaje ya biya Manaja kudinsa ya tafi.




LABARIN SHEHU JAHA


MASU GEMU MA YA SA SU BACCI BARE JARIRI?


Matar Shehu ta zo wajensa cikin dare hankalinta a tashe, tana cewa da shi: “Na rasa abin da ya sami yaron nan; babu abin da yake yi ban da kuka a koda yaushe, kuma na yi masa irin duk abin da zan iya don ya yi bacci, amma abu ya gagara! ka yi masa wani dan kokari mana, ko ya samu ya yi bacci, ko dai ka yi masa abin da ka ga ya fi dacewa, ni duk hannayena sun gaji da daukar sa da jijjiga shi.”


Sai ya ce da ita: “Saboda me kika rude haka? Dauki wannan littafin ki buda shi, ki ajiye a gabansa.”


Sai matar ta fusata tana fada, tana cewa: “Yanzu wasa za ka yi mini game da wannan lamari? Haka kuma za ka yi mini, bayan ka auro ni tun da kuruciyata, ka gama biyan bukatarka da ni, ka bar ni cikin yunwa da tsumma, alhali ina ta faman yi maka hidima ba-dare-ba-rana, kuma wannan yaro danka ne, ba agola ba. Saboda me za ka rika wasa da hankalina a kowane lokaci?”


Sai Shehu ya amsa mata da cewa: “Haba Hajiya, ai kuwa ina yin bakin kokarina, wajen kyautata rayuwarki, saboda me za ki rika yi mini irin wannan magana mai zafi, kina tayar mini da hankali?”


Sai matar ta rage karfin muryarta, sannan a fusace ta cigaba da cewa: “To wannan littafin na menene, kuma wace fa'ida za'a samu a cikinsa?”


Sai ya ce: “Kwantar da hankalinki, wannan littafin "KADURI" ke nan,


(wani littafi ne maras ma'ana da ya kunshi bayanai na rashin kan gado) wanda duk lokacin da na karanta shi ga almajirai a masallaci, sai bacci ya kwashe su, wasu ma har ka ji suna minshari. To idan kuwa har zai iya sanya bacci ya kwashe magidanta masu gemu, kamar wadanda aka yi wa sihiri saboda tasirinsa, me zai hana ya sanya jariri ya yi bacci kamar ya shaki banju?”




LABARIN SHEHU JAHA


TA YIWU GIDAN KOFA BIYU CE


Wata rana daliban Shehu suka zo gidansa sai ya shiga don ya gyara musu gurin da zasu zauna, ko da ya ga matarsa sai ya ce da ita “akwai baki a kofar gida ina ganin ya kamata ki san hikimar da zakiyi ki sallame su”


Sai ta tafi wajen mutanen ta tsaya daga bayan kyaure ta ce “wa kuke nema”


Suka ce “Shehu muke son gani”


Sai tace ai kuwa baya nan”


Sai abin ya basu mamaki suka ce “ai kuwa yanzun nan muke tare da shi, sai ya shiga gida kuma shine ya kirawo mu”


Ita kuma ta tsaya kai da fata cewa ba ya nan. Jayayya ta tsananta tsakaninsu da ita, ko da abin ya ishi Shehu sai ya leko ta taga ya ce da su:


“kai don allah ku rabu da wannan baiwar Allah haka, ku ka sani ko gidan kofa biyu ce da shi ya zamana shi ya fita ta dayar kofar?”






LABARIN SHEHU JAHA
BAKON ALLAH AI DAKIN ALLAH YAKE
TAFIYA



Akwai wani mutumin kauye kunyarsa ta yi karanci,
zuciyarsa ta mutu, ya lalace, ya zamana ba shi da wata
sana'a sai roko. Har ta kai idan ya je gidan mutum ba ya
yarda ya tafi sai an ba shi wani abu. Haka kuma, ya
kasance idan ya je wani gurin sai ya nemi tufafī, a wani
gurin kuma ya nemi abinci. Haka kuma, babu abin da
yake damun sa idan an kore shi ko an lakada masa dan
Karen duka. Sai ya zamana ya dami Shehu da zuwa ya
kuntata masa. Ana nan wata rana sai bakauyen ya je
gidan Shehu, ya bubbuga masa kofa. Sai matarsa ta ce:
wane ne? Sai ya ce: Wata magana ce ta kawo ni wajen
mai gida. Sai Shehu ya sauko daga kan bene. Ko da ya ga
wannan mutumin ne, sai ya tambaye shi da cewa: Me
kake nema? Mutumin ya ce: Ni bakon Allah ne.
Sai Shehu ya ce: To taho mu tafī, sai mutumin ya bi shi.
Sai da suka isa kofar babban Masallacin juma'ar garin,
sai ya ce: To, dama kuskure ka yi ka je wajenmu.
Wannan shi ne dakin Allah, kai bakon Allah.
😂😂😂😂😂😂😂




LABARIN SHEHU JAHA


ITA CE TA BA NI TA CE NA CI


Shehu ya kasance yana cin gasasshiyar kaza, sai wani mutum ya zo ya ce da shi: “Don Allah sam mini naman kazar nan na taba, yunwa nake ji.” Sai Shehu ya ce: “Wallahi dan'uwa ni ma ba kazata ba ce, ta matata ce.” Sai mutumin ya ce: “Amma ai ga shi nan kana ci.”


Sai ya ce: “To yaya na iya? Ai ita ce ta ba ni ta ce na ci.”






SHEHU DA ATTAJIRI


Wani attajiri ya ba wa Shehu fan ashirin da biyar ya ce “malam ga wannan a roka mini ALLAH bayan kowace salla daga sallolin farilla”


Sai Shehu ya ciri fam biyu daga ciki ya mayarwa attajirin yace “Alhaji yanzu dare ba shi da tsawo saboda haka ina fatan zaka yi hakuri dani domin ni ba na iya tashi nayi sallar asuba akan lokaci sai dai nayi ta ramuwa don haka bai dace na karbi ladan addu'ar sallar asuba ba, kuma ina jin kunyar ALLAH ta'ala game da karbar abin da ban cancanta na karba ba.”
LABARIN SHEHU JAHA


WA YA FI SAKARCI?


Wadansu sakarkaru su biyu, sun kasance suna tafiya a kan hanya, sai dayansu ya ce da dayan: “Dakata kowannen mu ya fadi abin da yake fatan ya samu.”


Sai abokin nasa ya ce: “ni fata na shi ne, a ce na mallaki tumaki dubu.”


Sai dayan kuma ya ce: “ni kuma so nake a ce ina da kuraye dubu, wadanda za su cinye tumakin naka.”


Sai kuwa mai fatan samun tumakin nan ya fusata ya zagi dan'uwan nasa. Sai fa nan-da-nan suka harke da fada suka yi ta doke-doke.


Sai Shehu ya zo wucewa ya ga suna fada, sai ya ce: “me ya hada ku haka?”


Sai suka shaida masa abin da ya faru. to a lokacin kuwa ya kasance yana dauke da gora guda biyu a kan jakinsa cike da zuma. Sai ya sauke su, ya tuttular da zumar a kasa, sannan ya ce: “Allah ya zubar da jinina kamar yadda na zubar da zuman nan, idan ku ba sakarkaru ba ne!”




TSAYA NAN NA GWADA MAKA YADDA ZAN YAUDAREKA


Wata rana Shehu yaji wani yaro yana kirarin cewa shi babu wanda ya isa ya yaudareshi ko ya damfareshi. Sai yace dashi: "To tsaya nan, ni kuwa bada jimawa ba zan gwada maka yadda zan yaudareka."


Sai yatafi ya bar shi a wajen yayi ta tsayuwa awowi masu yawa, amma bai ga alamar Shehu ba, har dai ya gaji da tsaiwa, sai ya rika lanlankwashewa. Da abokansa suka zo wucewa sai suka ce dashi kai kuwa tsaiwar me kakeyi a nan?


Sai ya basu labarin abinda ya wakana, sai wani abokinssa ya tintsire da dariya yace dashi: Amma ka cika sakarai. To ai gashi nan ya yaudareka, dabara ta kubuce maka.


LABARIN SHEHU JAHA NA 06


YADDA KA YI HAKA ZA’AYI MAKA


Wata rana Shehu ya ba wani makwabcinsa sako ya sayo masa man girki kwalba daya. Da mutumin ya karbi kwalbar, sai ya cika fiye da rabinta da fitsari, sannan ya zuba mai dan kadan a saman fitsarin ya aikowa Shehu. To dama matarsa ta yi shirin toya dankali, sai ta dora kaskon tuya akan wuta, ko da ta dauki kwalbar Mai ta tuttula a cikin kasko, sai tartsatsi ya rika tashi tare da wani mummunan wari maras dadi.


Sai Shehu da matarsa suka fahimci ha’incin da makwabcinsu ya yi musu. Shehu yace “yanzu ni ya yiwa haka? To bakomai!”


Sai yayi kamar yayi watsi da maganar, sai da aka sami ‘yan kwanaki sai ya sami ‘yan kananan kwalabai guda biyu iri daya, ya zuba Angur (Shake) a daya daga cikinsu, a dayar kuma sai ya zuba nikakken kashi, to dama makwabcin nan na Shehu mutum ne maison anguru, sai Shehu ya tsaya a kofar gida yana shakar angur yana jin dadinsa, yana cewa “Kai wannan Anguru da kyau yake, sai kace turaren Anbar”.


Da makwabcin Shehu yaji sai ya fito waje ya ga Shehu, sai yayi sha’awar Angurun, ya matso kusa da Shehu ya ce “Don Allah ka sam mini Angurun naka mana, nima na shaka” da farko sai Shehu ya hanashi don ya sake jawo hankalinsa, da dai yaga ya nace masa da magiya sai yace “Nima Alkali ne ya sam mini wannan Angurun jiya aka kawo masa hadaya”, daga nan sai ya fito da daya kwalbar daga aljihu ya mika masa ita. Sai kuwa mutumin nan ya yi sauri ya karba yana godiya ya bude kwalbar da rawar jiki ya tuttulo da Angur mai yawa akan ‘yan yatsunsa ya sheka da karfi. Haba! Da ya shiga cikin kansa, sai yayi kamar ya suma saboda tsananin warin da ya barbazu a cikin makogwaronsa da kwanyar kansa.


Sai y ace da Shehu “Amma Allah Ya isa tsakanina da kai, wannan kuma wane irin Angur ne ka bani?”


Sai Shehu ya dube shi ya ce “Wannan ba Angur bane, shine sakamakon Man gyadar da ka kawo mini ran nan, domin yadda duk kayi haka za’ayi maka”.




LABARIN SHEHU JAHA NA 04


ASHE DAFAFFIYAR KAZA TANA KWAI?


Wani attajiri ya fito kasuwanci zuwa wani gari sai ya bi ta garin su Shehu Jaha, ya kwana a Otel, da safe Manaja ya kawo masa kaza daya da kwai biyu ya karya kumallo. Ya kaiwa dabbarsa ciyawa, da zai tafi sai yace wa Manaja sai idan ya dawo daga garin da ya nufa zai biya, Manaja yace “ba komai” Ya tashi ya tafi.


Bayan wata uku sai ya dawo, ya sake sauka a Otel dinnan, aka sake kawo masa kaza daya Kwai biyu, aka baiwa dabbarsa abinci, da ya gama sai ya kira Manaja yace "Ina son ka gaya min duk kudinnan in biya ka saboda kudinka sun dade a kai na".


Manaja yace "Ai sai dai inyi maka sauki kawai ka biya ni, amma idan nace zamu yi lissafi, lissafin mu yana da yawa, ka bayarda dirhami dari biyu kawai shikenan" Nan da nan Attajiri ya harzuka saboda sanin darajar kudi, ya kama fada yana cewa “daga kaji biyu kwayaye hudu shine zaka ce in baka dirhami maitan, na menene, ko cutata kuma zaka yi?” Manaja yace "Ai na gaya maka dama sai dai in maka sauki kawai in ce ka biya, amma tunda kafi son gwari-gwarin, bari a yi maka.


Kazar nan da ka cinye tun wata uku, da ace ka bar mana abar mu kullum zata dinga saka mana kwai biyu ne, kuma zamu dinga sakawa kazar da take kyankyasa ta kyankyashe mana su, suma zasu girma su dinga saka kwayayen...... a haka dai zuwa wannan wata ukun Allah kadai ya san yawan kajin da zamu samu ta hanyarta, amma ka cinyeta, shi yasa nayi maka wannan arahar!"


Da Attajirinnan ya ji haka sai ya kai kara gun wani Alkali, Manaja kuma da yaje ya nunawa Alkali zai bashi agwagi biyu manya da wasu kudi. Nan da nan Alkali ya birkita magana, yace "Ai tunda baku yi da Manaja ga abinda zaka biya ba in ka dawo yanzu dole abinda yace shi zaka biyashi" Da dai ya ga za'a cuce shi sai ya nemi a dage shari'ar, Alkali kuwa ya amince.


Ana dab da komawa shari'a sai wasu samari suka ce da shi ya je ya sami Shehu Jaha yayi masa bayanin wannan makirci da ake shirin yi masa. Yaje ya sami Shehu yayi masa bayani gabadaya, sai Shehu yace "To goben idan kaje kace ina nan zuwa kotun kafin a fara shari'ar" Yace "Toh" Ya tashi ya tafi.


Washegari an cika ana ta jiran Shehu ya zo a fara shari'a can rana ta daga sai ga Shehu nan da sauri ya shigo kotu. Alkali yace da shi cikin fushi "Kai me yasa ka zaunar da mutane muna ta jiran ka zamu fara shari'a, kaje ka bata mana lokaci" Shehu cikin nutsuwa yace "Allah Ya gafarta Malam ina neman afuwa, abinda yasa na samu jinkiri, na sa an dafa min wata ragowar alkama ne kuma naje gona na shuka ta sannan na taho" Alkali ya dube shi a fusace ya daka masa tsawa yace "Rufe mana baki, kai jama'a waye ya ta6a jin inda aka shuka dafaffiyar alkama a cikinku, mu zaka mayar mahaukata?"


Shehu yayi gyaran murya yace "KUMA BA'A HAKA ASHE HAR AKA SAMU DAFAFFIYAR KAZA TAKE YIN KWAI? Har ma a kyankyashe kaji masu dimbin yawa?" Nan da nan Guri ya hargitse da hayaniya, Alkali ya ga bashi da wata mafita akan wannan zalunci da yake shirin aikatawa! Nan dai ya sallami Attajiri yace ya biya Manaja iya kudin kajinsa biyu da kwai hudu. Attajiri yayi godiya ga Shehu Jaha, yaje ya biya Manaja kudinsa ya tafi.








DAUKI ALWALARKA KA DAWO MINI DA TAKALMANA


Wata rana Shehu ya yi alwala a bakin wata korama da ya gama ya yi nufin ya sanya takalmansa sai daya da cikin takalmansa ya fada cikin koramar ruwa ya tafi da shi.


Sai Shehu ya juya wa kogi baya ya daka masa tsawa mai kama da aradu sannan ya juyo ya ce dashi “dauki alwalarka ka dawo mini da takalmana!”




Rubutawa
Mal. Nasir G Ahmad Yan Awaki
07032707179

Ads At the End of Article
1
2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads