Header Ads
Showing 1 words to 3000 words out of 5833 words

Chapter 1 - LABARUN SHEHU JAHA Complete Book Writing by Nasir G Ahmad Yan Awaki .txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

LABARUN SHEHU JUHA
Rubuta Labari
Nasir G Ahmad Yan Awaki






SHEHU JAHA DA BAKONSA


Wata rana Shehu ya dawo da rana ya gaji, da kyar ya bi matakalan gidan sama na gidansa ya hau, ya bude tagogi ya kwanta.
Bacci ya fara kwashe shi sai ya ke ji a na bugun kofar gidansa bugawa na gayya, ya tashi da kyar ya leko ta taga, sai ya ga wani mutum mai kiba, Shehu ya ce: Malan wurin wa ka zo?
Mutumin ya ce: wurinka na zo, Shehu ya ce: to ina jinka, mutumin ya ce: magana ce zan fada maka, Shehu ya ce: ba za ka fada mun daga nan ba? Ya ce: yallabai a yi hakuri a dan sakko.
Shehu ya tattaka ya sauka, sai mutumin ya ce: Yallabai dama na zo ka taimaka mun ne Ina da wata matsala ce, Shehu ya ji wani haushi ya kama shi, ya yi kokari ya danne, ya ce: mu hau sama.
Su ka hau sama, katon mutumin nan da kyar ya ke hawa, bayan sun kure sama, sai Shehu ya CE: Malan Allah ya ba mu Sa'a, mutumin nan ranshi ya baci, ya ce wa Shehu: MAI YASA KA HAWO DANI BAKA FADAMIN TUN A KASA BA?
Shehu ya ce: KAI MA MAI YA SA KA SAKKO DA NI BA KA FADA MUN TUN INA SAMA BA? Haka mutumin nan ya sauka dakyar ya fece 🤣🏃‍♂️


Shin ko shehu ya kyauta kuwa?






JAKIN DINARI DAYA


Wata rana jakin Shehu Jaha ya bata, aka yi neman duniyar amma ba’a samu ganin shi ba. Tun Shehu yana sa ran za’a iya ganin jaki har ta kai gay a fitar da rai. Don haka sai yace a ransa “wallahi idan na gane jakin nan dinari day azan sayar da shi” alhali jakinsa akalla zai kai dinari hamsin.


Bayan yan kwanaki cikin ikon Allah sai aka gane jaki gas hi Shehu ya riga yayi rantsuwa cewa zai sayar da shi akan dinari daya.


Da dai yaga dole sai an sayar da shi akan hakan tun da yayi rantsuwa sai kamo jakin nan ya hada da magensa ya daura masu igiya daya sannan ya tafi kasuwa yayi ta zagayawa yana talla yana cewa “ina wanda zai sayi jaki akan dinari daya tare da mage akan dinari dari amma da sharadi sai dai a sayesu a tare”


Mutane duk wanda ya zaburo ya kwashi banza da zaran yaji sharadin cewa dole sai an hada da mage ita kuma dinari dari sai yaja baya. A haka Shehu ya kare yawonsa ko tayawa babu wanda yayi.


LABARIN SHEHU JAHA


YAYA NA GA KANA TAUSAYA MASA?


Wani mai kudi ya gayyaci Shehu wata walima da ya shirya, sai ya kawo masa wani karamin dan akuya gasasshe. Sai Shehu ya rika ci da sauri, da sauri, sai mai walimar (wanda mutum ne marowaci), ya ce da Shehu: “Yaya na ga kana yi masa cin rashin imani, ko uwarsa ta tunkuye ka ne?”


Sai Shehu ya ce “yaya na ga kana tausaya masa ko uwarsa ta shayar da kai ne?”






LABARIN SHEHU JAHA


ME ZAI HANA NA YI WA JAKI KUKA?


Matar Shehu ta mutu, amma bai zubar da hawaye game da mutuwarta ba. bayan nan kuma sai jakinsa ya mutu, sai ya rika kuka ba kakkautawa.


Sai mutane suka nufo shi suna mamaki, suka tambaye shi da cewa: “kai kuwa me ya same ka, matarka ta mutu ko digon hawaye ba ka zubar ba, amma jakinka ya mutu kana ta kuka?”


Sai ya ce da su: “to mene ne laifina game da wannan? a lokacin da matata ta mutu sai mutane suka yi ta zuwa wajena suna yi mini tayin na auri 'ya'yansu mata, wani ma cewa ya yi shi zai dauki dawainiyar bikin gaba daya, amma da jakina ya mutu babu wanda ya ce zai ba ni wani maimakon sa.”




LABARIN SHEHU JAHA


ALWALA ZAN CANZAA
Shehu Jaha yaje wanka rafi yana cikin wanka sai
yara suka kwashe kayansa suka gudu. Da ya fito
ya rasa yanda zai yi ya shiga gari. Da yake yamma
tayi sai ya tafi makabarta ya zauna, da dare yayi
ya kwanta tsakankanin kaburbura ya kama bacci.
Da gari ya waye da sassafe sai ga jama'a an taho
za'a binne wata gawa da tayi kwanan keso. Har
suka karaso Shehu na kallonsu, amma su basu
basu
hangeshi ba, da suka iso suka fara kokarin haka
rami, duk hankulansu sun koma akan aikinsu. Da
dai Shehu ya ga sun dukuta aiki sai ya taso dagaa
inda yake ya nufo wajensu.
Daga kan da jama'a zasu yi, sai suka ga mutum
yayo kan su tumbur, ba riga ba wando, tun daga
nesa suka ce dashi "'malam lafiya?"
Sai yace musu "lafiya lau alwala tace ta karye na
fito na daura wata na koma."
Koda jama'a suka ji haka kowa sai yayi nasa waje
da gudu.
Shehu kuma yazo ya dauki zanen da aka
lullubawa gawar ya yafa ya shiga gari.






SAI SHEHU! SAI SHEHU!!


Wata Rana Shehu Jaha ya dawo daga gona a Gajiye sai ya


kwanta a gindin wata bishiya a kofar gidansa. Bayan wani


lokaci har barci ya Fara daukansa sai ga yara a tafe suna


waka:


Sai Shehu! Sai Shehu!! Sai Shehu!!!


Har Shehu Jaha ya farka a firgice sai yaga ashe yara ne suke


waka, Shehu ya kori yaran nan amma suka ki tafiya. Koda


Shehu yaga yaran nan ba zasu barshi yayi barci ba, sai wata


dabara ta fado masa.


Sai Shehu Jaha ya juya yace da yaran nan kuje Gidan Alhaji


Barau ana biki a gidan, kuma akwai tuwon shinkafa da miyar


kaza da naman shanu da madara da zuma kuma ana rabawa


yara Sulalla (Kudi).


Koda yara nan suka ji haka sai suka juya suna murna suka nufi


gidan Alhaji Barau, Shehu kuwa yaji dadin hikimar nan da yayi


ya rabu da yaran nan.


Can Shehu yana zaune bayan kamar minti 15 yaga dai yara


basu dawo ba sai Shehu ya fara tunanin anya kuwa abinda ya


gayawa yaran nan ba gaskiya bane ba kuwa?


Shehu ya kara jira ya ga yara basu dawo ba sai ya dauki


takalmansa yana cewa "GARA INJE IN DUBA WATAKILA


ABINDA NA GAYAWA YARAN NAN GASKIYA NE, NIMA IN


SAMI RABONA.”




LABARIN SHEHU JAHA N


RIJIYOYIN SAMA A KASA
rana Shehu yayi tafiya shi da abokinsa zuwa
birnin Koniya. Sai abokin nasa ya rika ganin
dogayen hasumiyoyi na masallatan birni. To
dama bai taba ganin hasumiyaba sai ya dubi
Shehu yace. "abokina don Allah ta yaya suka yi
wannan dogon abu haka?"
Sai Shehu yace da shi "yanzu kai baka san
wannan ba? Lallai ka cika dan kauye! Ai wannan
rijiyoyi ne aka juyasu sama a kasa"
😂😂😂😂😂
wai kuna ganin shehu ya bada amsa DAIDAI kuwa? 😂😂😂




AI SAI NA ZAMA SHASHASHA HAWA BIYU:
Wata rana Shehu ya tafi ya kai alkamarsa wajen nika,
da ya isa gurin sai ya rika diban tafi daidai daga buhunan
mutane yana zubawa a buhunsa. Sai mai nika ya ce:
Lafiya kuwa, mene ne haka? Sai ya ce kai ni fa shashasha
ne, duk abin da hankali na ya shirya mini shi nake yi. Sai
mai nika ya ce: To, idan kai shasha ne me ya sa ba ka
debo alkama daga buhunka ka zuba a buhunan mutane?
Sai ya ce: Ai ni shashancina mai sauki ne, idan kuwa na
aikata abin da ka fada, sai na zama shashasha hawa biyu.😊😊😊😂😂😂🍞👬👬👨‍👨‍👦👨‍👨‍👧‍👦👨‍👩‍👧‍👦
To fa in Kaine wannan Mai nikan Mai zakacewa shehu????






Watarana shehu jaha suna zaune da wani suna shira sai CE shehu nikuwa sonake gone ka aramini jakinka sai ai jakin bayanan sai yace to sai akaci gabada shira can sai jaki ya daddage ya tafka kuka,sai mutuminnan yace shehu kace bayanan kawai sai shehu yace katyatani ka gaskata jaki.




LABARIN SHEHU JAHA


YO NI WAWA NE?


Wata rana almajiran Shehu sun taru suna ta jiran shi, ya zo ya basu karatu. Shiru-shiru Shehu bai iso ba, har almajirai sun fara shirye-shiryen kama gabansu sai ga Shehu ya ɓullo.


Ɗalibai suka ce "akramakallahu lafiya yau kuka makara har mun fara tunanin ba zaku samu damar fitowa ba?"


Shehu yace "a'a wallahi dirhamin wani bawan Allah ne ya faɗi"


Ɗalibai suka ce "Allahu akbar ka ji salihan bayin Allah, kuna can kuna taya shi neman dirhamin hala?"


Shehu yace "mtseew! Yo ni wawa ne? Ina ganin dirhamin nasa ƙafa na take shi, nayi tsayuwata akai"








KOWA YA TAFI GA MAHAIFIYAR SHI


Wata rana hatsaniya ta hada Shehu da matarsa, sai matar ta fusata ta shiga daki ta fara tattara kayan ta a jaka. Sai Shehu ya shigo ya same ta ya ce: “ina za ki je?”


Sai ta kalle shi a fusace ta ce: “gun mahaifiyata zan tafi”


Koda jin haka sai shima Shehu ya jawo jaka ya fara tattara kayan sa. Sai tace; “ina kuma za ka je?”


Sai ya ce: “nima gun mahaifiyata zan tafi”


Sai tace “toh idan ka tafi wa zai kula ma da yayanka guda 6 da ke nan?”


Sai Shehu ya ce “ke zaki tafi ga mahaifiyarki nima zan tafi ga mahaifiyata suma sai su tafi ga UWARSU!! kinga shikenan”.




LABARIN SHEHU JAHA


WANE TSINANNAN NE YA FADA MUKU?


Shehu ya cika aljihunsa da nunanniyar goba, yana tafiya sai ya gamu da wadansu abokansa, yace da su: “Duk wanda ya fada mini abinda ke cikin aljihuna, zan bashi gobar da tafi kowacce girma daga ciki.”


Sai suka ce da shi “goba ce.”


Sai ya yi mamakin yadda suka gane, ya ce da su: “wanetsinannen ne ya fada muku?






NAFI SON MAI SHUDIN ABIN WUYA


Shehu Jaha ya kasance yana da mata biyu. Sai ya ba wa kowaccensu shudin dutsen abin wuya, ba tare da 'yar 'uwarta ta sani ba, kuma ya ja kunnen kowaccensu da kada ta kuskura ta nuna wa 'yar uwarta, domin wannan dutsen shi ne alamar da take nuna wadda yafi so.


Ana nan wata rana sai suka turke shi, suna neman lallai ya bayyana musu wadda ta fi dauke masa hankali watau wanda yafi so kenan.


Sai ya ce: “ni nafi son wadda take da shudin dutsen wuya.


Ta haka kowaccensu ta dauka cewa ya fi son ta akan 'yar 'uwarta




SHEHU A MAKKA


Wata rana Shehu yaje Saudi aikin hajji, sai aka hada shi masauki da larabawa to lokacin larabcin Shehu ba har can ba. Sai ko ya shiga bandaki zai yi bahaya, ya shiga bai jima ba, sai wuta ta kama ya rasa ya zai yi ya fada musu wuta ta kama. Kawai sai yayi kururuwa ya ce "innalillahi Shehu fin naar”


Ko kula shi basu yi ba wuta kuma sai kara ci take. Ya sake maimaitawa shiru ba wanda ya kawo masa dauki kawai sai ya ce "innalillahi! Shehu fin naari jahannama kalidina fiiha”🤣🤣🤣🤣








LABARIN SHEHU JAHA


SHEHU BAMU SAN KA BA


Watarana Shehu Jaha ya dawo daga kasuwa akan jakinsa. Sai wasu samari suka ce “Bari yau dai mu zolayi Shehu, muji ko me zai ce”


Sai suka ce da Shehu “Shehu bamu san ka ba, amma mun san jakin ka.”


Bada wani bata lokaci ba, sai Shehu ya basu amsa da “ai dama su jakuna junansu kawai suka sani.”




GIDAN MU SUKE NUFI


Wata rana Shehu na zaune shi da danshi suna hutawa. Sai ga jama'a dauke da gawar mamaci zasu wuce, a can karshen baya kuma wata mata ce ke tsalle tana tuma tana kururuwa gami da fadin cewa "yanzu me gida shikenan za a kaika gidan da babu shinfida, ba katifa, babu gurasa ba zuma...."


Koda dan gidan Shehu Jaha yaji zantukan wannan mata sai ya waiwayo ya dubi uban nasa yace "Shehu wallahi gidanmu suke nufi zasu kaishi"






JARABAWAR SHEHU JAHA


Wata rana a makaranta sai malamin su Shehu ya shiga aji don yiwa su Shehu jarabawa, a cikin tambayar sai malamin ya tambayesu: “ka dauka kai soja ne da kuka dawo daga filin yaki, rubuta abubuwan da suka faru a lokacin kuna filin daga"
Lokacin da malamin ya fara tattara takardun dalibai sai ya ga takardar Shehu bai rubuta komai ba, sai malamin yake tambayarsa "me yasa baka rubuta komai ba?" Sai Shehu yace " ai tun a farkon yakin aka kashe ni”


Yanzu ka dauka kana karanta wannan hikaya wanne Comment zakayi 😁




LABARIN SHEHU JAHA


.SHEHU FI JAHANNAMA KALIDINA FIHA😆😆😆🤣🤣😂😂😂. (Shehu yaje aikin haji ya shiga bayi wuta ta kama)),😂😂🤣🤣🤣😆😆😆🤣🏪🏪


Wata rana Shehu yaje Saudi aikin hajji, sai aka hada shi masauki da larabawa to lokacin larabcin Shehu ba har can ba. Sai ko ya shiga bandaki zai yi bahaya, ya shiga bai jima ba, sai wuta ta kama ya rasa ya zai yi ya fada musu wuta ta kama. Kawai sai yayi kururuwa ya ce "innalillahi Shehu fin naar”
Ko kula shi basu yi ba wuta kuma sai kara ci take. Ya sake maimaitawa shiru ba wanda ya kawo masa dauki kawai sai ya ce "innalillahi! Shehu fin naari jahannama kalidina fiiha”
,🤣🤣🤣😆😆😂😂😂😂




ZAN BI UMARNINKA


Lokacin da Shehu yake yaro, ya kasance a koda yaushe mahaifinsa ya umarce shi da wani abu shi kuma sai ya aikata kishiyarsa. Har mahaifinsa ya fahimci cewa wannan dabi’a ta zama jiki a gareshi.


Don haka idan zai umarceshi da wani abu, sai aa umarceshi da kishiyarsa.


Alal misali, idan yana so ya ce masa tsaya nan, sai ya ce masa tafi can, shi kuma sai ya tsaya.


Ana nan wata rana sun dawo daga nikan alkama, sai ya zamana jakinsu ba zai iya bi ta kan gadar wani rafi ba. Saboda haka sai mahaifinsa ya umarce shi da cewa ni zan bi ta kan gada kai kuma kada ka ja jaki ta cikin rafi ku tsallaka gaci.


Sai Shehu ya kama dabba ya ja ya bi ta wurin da ake ratsawa a wuce.


Suna cikin ratsa ruwa sai buhun alkama ya soma gangarowa daga bayan jaki alamun zai fada ruwa. Sai uban ya daka masa tsawa, yace “kai ga buhun zai fada ruwa kada ka taba shi”


Sai Shehu ya waiwaya wajen babansa yace:


“Baba na dade ina saba maka wajen abin da ka umarce ni da shi,


to yau zan aikata abin da ka umarce ni da shi.


Kawai sai ya kyale buhun alkama ya cigaba da gangarowa daga bayan jaki, ji kake tanjam!!! Buhun ya fada ruwa.






LABARIN SHEHU JAHA


KADA KA ZARGENI


Wata rana Shehu ya ji shigowar barawo gidansa da daddare. Sai ya tashi ya shiga siton kayan abinci ya buya a ciki.


Barawo yayi ta bincike abin da zai sata bai sami komai ba. Ko da ya duba haka sai ya ga sito sai ya ce “bari na shiga nan ta yiwu na sami wani abu”


Sai ya bude ya shiga, shigarsa keda wuya sai suka yi arba da Shehu sai barawo ya razana amma duk da haka ya yi ta maza ya ce “me kake yi anan”


Shehu yace “ranka ya dade kada ka zargeni na san cewa ba zaka sami abin da zaka sata a wannan gidan ba saboda haka na buya don jin kunyarka.”






KU AURA MA WANDA YACI WAINA


Shehu yayi aure, sai abokansa suka shirya masa walima mai kyau, to daga cikin abincin da aka shirya akwai waina mai rai da lafiya, amma da suka zo cin abincin sai suka manta basu kira shi ba, har suka cinye wainar.


Shi kuwa Shehu ya kasance mai son waina kwarai da gaske. Saboda haka sai ya cika da fushi.


Daga baya suka neme shi basu same shi ba. Sai can suka same shi tare da wani dan uwansa, suka taho dashi. Da ya zo sai abokan nasa suka ce dashi: “yaya ana bikin ka kuma kayi tafiyar ka naka guri?” Sai yace “ai bana bukatar auren, ku aura wa wanda yaci waina”


🤣🤣🤣🤣




IDAN YA KAWO KUDIN A BA ALKALI


Wata rana Shehu Jaha yana cikin tafiya sai wani matashi ya mareshi don haka yace ba zai yarda ba, da aka je gaban alkali sai alkali yace “mu anan kasar idan aka mari mutum za a bashi fam daya”


Don haka ya umarci wannan yaro da yaje yazo da kudi a ba Shehu. Ashe yaron dan ammin alkali ne don haka yayi mai inkiya da kada ya dawo.


Shehu yayi jira har ya fara gajiya yaro bai dawo ba, don haka sai ya lallaba kusa da alkali ji kake tasss !! Shehu ya kwashe alkali da mari yace “idan ya kawo aba alkali kudin”
MUMMUNAR AMARYAR SHEHU








An aura wa Shehu wata mace mummunar gaske. Da gari ya waye, yayi nufin zai fita, sai ta tsaya a gaban sa tana wata karairaya, tana shagwaba tace “ina so ka fayyace mini 'yan 'uwanka maza wadanda ka amince na nuna musu fuskata, da kuma wadanda ba ka yarda su gan ni ba.”


Sai nan da nan Shehu yace da ita: “ke dai kada ki nuna mini fuskarki, amma kina iya nuna wa duk wanda kika ga dama.”


MENENE FARASHI NA?


Watarana ana zaune a fadar Sarkin garinsu Shehu sai Sarki ya dubi Shehu yace: "yanzu ace ana cinikin bil-adama Shehu kana ganin zanyi nawa?”


Sai Shehu ya kada baki yace: "ranka shi dade zaka yi fam dubu"


Sai Sarki yace: "Hmm to ai ko kuftar dake jikina tayi fam dubu"


Sai Shehu yace: "ai dama ita na kalla nace zakayi fam dubu idan an fiddata ai ba me sayenka ko kobo".


😂😂😂






LABARIN SHEHU JAHA


ASHE DAFAFFIYAR KAZA TANA KWAI?


Wani attajiri ya fito kasuwanci zuwa wani gari sai ya bi ta garin su Shehu Jaha, ya kwana a Otel, da safe Manaja ya kawo masa kaza daya da kwai biyu ya karya kumallo. Ya kaiwa dabbarsa ciyawa, da zai tafi sai yace wa Manaja sai idan ya dawo daga garin da ya nufa zai biya, Manaja yace “ba komai” Ya tashi ya tafi.


Bayan wata uku sai ya dawo, ya sake sauka a Otel dinnan, aka sake kawo masa kaza daya Kwai biyu, aka baiwa dabbarsa abinci, da ya gama sai ya kira Manaja yace "Ina son ka gaya min duk kudinnan in biya ka saboda kudinka sun dade a kai na".


Manaja yace "Ai sai dai inyi maka sauki kawai ka biya ni, amma idan nace zamu yi lissafi, lissafin mu yana da yawa, ka bayarda dirhami dari biyu kawai shikenan" Nan da nan Attajiri ya harzuka saboda sanin darajar kudi, ya kama fada yana cewa “daga kaji biyu kwayaye hudu shine zaka ce

Ads At the End of Article
1
2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads