Showing 9001 words to 10628 words out of 10628 words
Chapter 4 - ANTI ROMANCE Book Complete by Oum Aphnan.txt
Dije najin haka tai zumbur ta Mike ta dirke Naja a bayanta ta yayibo dankwalin da suke zaune a kai ta ci ɗanmara dashi.
“Ahayyyeee 😳Ni zaki duka? Kar shirun da nayi maki ya baki damar neman kawo mun hauka... Wabillahillazi hauka na ya girmi na uwar ki... ” Ɗaga hannu tayi zata mareta, ai kamar kura ta cafki wuyar hannunta, ta matse gam!
“karki kuskuren taɓa jikina, don zai zamo kuskuren ki da zaki yi na karshe a duniya... " A fusace ta watsar da hannunta a iska
Da sauri ta rike hannunta da take jin kamar an tunɓuke mata daga jikinta.
“Ni kike nemar nakastawa? ”
“kash, na lura damben nan dai kike so ayi ni kuma tausaya maki Nike, don kwarankwatsa yanzun nan lahira zatai baƙo, yoo wani ma yayi rawa bare ɗan makaɗa! Ni da na saba shan ɗamara in dambe da maza majiya ƙarfi????! ”
Da gudu ya ƙaraso gabansu har yana tuntuɓe da gima gimandutsen murhun da ta kafa masu a tsakar gida sai hayaki yake
“Na shiga uku sajida me kike yi haka? ”
Dije ɗaga yatsa tayi tai tsalle ta dungure ma shi goshi ba tareda ta dubi girman darajan sa ba
“Ɗan lami, kaine rikaƙƙen munafukin, mugu kawai mumugunci, Saida ka ɗirka mun ciki, sai ka gudu ka barni shekara 7 yunwa da fatara na ƙoƙarin kashe mu .... Humhun Ji inda kake rayuwa kana jin daɗin ka!! Wallahi Allah ya Isa..... To duk ma ba wannan ba ina binka a saffa saffa wannan matar mai ruwan karas zubin zabiya da ban sani ba matarka ce ko wacece wai har zata zo tace mun in fita... Halan baka bata labarin Dukiyar da kake tunƙaho dashi ba NAWA NE! ”
Ras!!! Gaban Sajida ya faɗi “Ke ke kin ga dakata karki ci ma mijina fuska, waye ke”
“Mijinki ko mijina, Sannan na faɗa dukiyar nan nawa ne ni Dije ba nashi bane, bare kuma ke da kike wani gwalangwalaso har kike cewa in fita a gidan, kece zaki bar gidan nan DUN UBAN KI!!!”
TOPAH KAJI ZAGIN MAGUZAWA😆
MUJE ZUWA AKWAI TARIN CAKWAKIYA A LITTAFIN NAN, WANDA NASAN DOLE KI YI NISHAƊIN KARANTA SHI
WANNAN KUMA SHINE FAJIN KUSA DA KARSHE NA KYAUTA, DAGA PAGE NA GABA NA KYAUTA YA KARE.
KI BIYA KUƊIN KI TA WANNAN ASUSUN
7782217014
MOHAMMAD HASSANA
FCMB
KO KATIN WAYA TA NUMBER NAN
09065990265
[2/10, 11:15 PM] Chuchu👻: ANTI ROMANTIC
Page H
Last free pg
_____
Zarah
Maimakon zarah da ta fito daga gidan su besty ta wuce kasuwa, saidai kash zuciyarta rarrabuwa ya dinga yi damuwa yana sake cinkushe mata rai, numfashinta na fita sama²
A daddafe ta kai kanta gida,.
Tunda ta shige bedroom ta fara rusa kuka irin mai ƙarfin gaske din nan , tana wulli da pillows kamar mahaukaciya, gashin kanta ya hautsine, wai dama duk mazan duniya haka suke mayaudara maciya amana ko nata kalar mijin kenan?
Shiru tayi kana ta girgiza kai, No! Farouk ne!
Ta daɗe a cikin wannan yanayin na kunci da ɓacin rai har wajen 4.30pm kana da sauri ta dirka akan gadon ta shige bathroom ta yi wanka ta ɗauro alwala, shiru tayi a gaban Mirror jikinta sanye da abaya mai faɗi, ƙurrr ta kafe kanta da ido tana ganin tsananin ramar da tayi.
Oh no zarah don't kill your self, haka tayi ta rarrrashin kanta kamar wata taɓaɓɓiya, hannunta riƙe da praying mat. It took her long again, kafin ta wuce ta shimfiɗa darduman ta tayar da sallar Asr, saida tasha kukanta a sallah still sannan ta idar, ta ninke darduman ta fesa turare ta nufi Kitchen.
Simple Egyptian fried rice tayi masa, da macaroni salad bata da strength din haɗa drinks musamman ganin 6 ta kusa don haka ta ajiye masa kwalin 5alive da roban ruwa sai Glass cup da spoons.
Da sauri ta koma ɗakinta tayi wanka a tsanake ta fito ta na bulbula kamshin turaren wanka, ta saka gown na atamfa fitted mai ruwan ja da kwalliyar maƙuba, ta gyare gashinta ta buga ɗaurin Turban, daga nan ta saka takalmin ta mai tsinin diddigi Ja, ta saka dan kunnenta da sarka da wrist watch na Gold, ta sake kara ma kanta turare daga nan kuma ta sauko ƙasan living Room dinsu ta zauna tana Daura kafa daya kan daya tana playing TV channels din falon da Remote din hannunta.
It is 6.15pm she started to be worried kar dai yau ma dukda tana gida daren zaiyi tare da ashararen ƴan matan shi? A take wata zuciya ta fizge ta ta fara koɗa masa kira ta waya
Ringing biyu ya ɗauka “Hello My Angel ”
“Yes bebe kana ina”
“Uhm Driving nake... ”
Ƙwaƙwalwarta ne ya hautsina, a ranta tana cewa, ina fada tambayarka kana ina kai kuma kana fada mun kana tuƙi, anya kana da gaskiya?
“Ok, dama na Girka maka one of your fav. Meal ne shine nace can you be home , like Asap”
Washe baki yayi cikin nishaɗi ya ɗaga hannu yana kallon wrist watch dinsa, still l've time
“Shi yasa kullum nake ƙara sonki My chef My wife, ganinan, ki Bani minti 15”
“Oya now, see you” ta kashe wayar tana jujjuya kan wayarta
**
As he said mintuna 15 a cikin falon yayi masa, tana jin ya shigo ta rufe idonta kamar me barci, sam batason ko buɗe ido ta kalleshi
Cikin sanɗa ya saɗaɗo ya manna mata Kiss a goshi
Wohoho ji tayi kamar ya watsa mata maniyyin budurwarsa a goshin, da sauri takai hannu ta goge wajen miyaun bakinsa
“Baby Love? Kin gaji da yawa, daga dawowa daga tafiya ba barcin gajiya an fara aikin lada”
A fakaice ta banka masa harara amma a zahiri sai jan hannunsa tayi
“mu je rest Room kayi wanka, ka sauya kaya then you eat your food”
Da ɗan sauri ya ce “Aah wify yunwa plz a fara Bani abincin ”
Har Dinning ta raka shi, fuskarta a sake take serving dinsa, ta gama ta zuba masa ruwa Glass cup. Ta tsaya a saman kansa tana massaging wuyar sa zuwa kafaɗa, tana lura da yanda wayarsa keta haske alamun ana kiransa
“Honey pick like yor Phone is ringing”
Ɗan daburcewa yayi “mtsew mutanen office ne wlh kinsan meeting gareni by 7 to 10pm , amma ina jin zan fasa ne kawai saidai in uwargida ta Amince”
Dariyar yaƙe tayi gami da taune leɓen ƙasa
“Oh ni na isa na hanaka, ko so kake ƴan office dinku su cigaba da korafin na shanye ka😊”
“kuma fa hakane, luv dan Bani Hollandia ne banson 5alive shi na sha duk ranar yau” jinjina masa kai tayi , tana kissima abubuwa a ranta, tabbas sun shirya haɗuwa da waccen karuwar , now what would I do?
Tab ai wallahi saidai dani dake kowa ya rasa.
Kitchen ta koma tana zancen zuci ta dauko Glass cup sabo ta buɗe robobin preservatives dinta ta ciro wani farin kullin leda, mai ɗauke da tablets ƙananu, tayi maza ta dauko daya ta saka a Glass cup din ta ɗiga ruwa , nan take kuwa ya narke.
Da karsashinta ta fito falon tana tafe tana murɗe bakin Hollandia ɗin, idonta na kansa shi kuwa yana can yana typing a jikin wayarsa da sauri da sauri.
Ƙarar sautin duddulowar Hollandia din ne ya dawo dashi hayyacinsa, murmushi ta kashe shi dashi gami da mika masa.
“Nagode zinariya ta”
“My pleasure zuma na”
Ta koma ta hakince kan daya daga cikin kujerar dining din ta tsiya yi wani Hollandia din tana sipping
“wai kam kai wani irin Hollandia, hmmm ni dai na fi son wannan, the vibes kill me aswer😆”
“Nima fa? Kinsan nafi sonsa wai ina Little? ”
“Ana can ana shan soyayya da besty”
Dariya suka fashe dashi a tare yana ƙara tuttula yoghurt din a cikinsa, sai da ya shanye tas ya ɗaga hannu zai ƙara duddulo sabo a kofin yana cewa
“mun ga ƙaryar besty, ai daga kanmu aka daina evarlasting besty.... Kash hhh.... Ishh............. Ahhh” ya saki cup ɗin yana rike wuya.
A ruɗe zarah ke tmbyr sa lafiya
“Like I chocked but give me Glass of water i'll be fine” wani kallon gefen ido tayi masa tadan tsiyayo ruwan tana mika masa taga ya langaɓe a kujeran hannunsa rike da wayar.
“Honey?! Honey!!... ” shiru ka keji
A hankali ta ɗage hannunsa ya kuwa saki yararaf wayarsa dake hannunsa zata fado, ai kuwa da sauri ta cafe tana Dariyar ƙeta.
“Baka sanni bane, I'm the Murder”
_“All My expectation na wajenka, gabaɗaya tsuliya ta ta jiƙe jagwab, plz quickly come”_
Wani jiri² ya ringa ɗibar ta ganin sakon da aka turo masa ta WhatsApp, da sauri ta shiga ta bata amsa
“Baby baki kai ni ba,abata fa tun safe take a ɗage kuma kinsan tun abunda muka yi jiya ne a car, So Trust me My heart is with you ina nan Madam ta rike ni da jagwagwalon abincin ta, ki Bani 30 minutes zan zo inda kike, yau a wajenki zan kwana”
“awwwwn are you sure? , shknn kayi sauri kasan ban biya kudin Room din ba ”
“Ok Room nawa kike, kuma wani Hotel ? ”
“Hotel ɗin mu mana, Sweet spirit Hotel Room 21....you better come Bani da 55k for Room and ina jin yunwa ”
“On My way , My baby... Kinsan kinada dadi ko wani appointment dina na kashe babu asara... ”
Da gudu tayi ɗakinta ta dauko mayafin da zai shiga da kayanta ta suri car keys dinta ta fice gidan a zafafe......
..DA WATA A ƘASA
* SHIN ME ZAI BIYO BAYA?
*ZARAH TA KASHE FAROUK
*ME ZAI FARU ITA DA FARKAN FAROUK?
*INA LABARIN DIJE DA ƊANLAMI DA MA SAJIDA?
*DA GASKE NE KUƊIN ƊANLAMI NA DIJE NE? KO KUWA DAI TAYI MASU IRIN NA HAUSAWA NE
_KYAN FAƊA ƘAGE... 🤪_
_ABEG DON'T DARE MISS THIS BOOK , ZAKI NISHAƊU KUMA ZAKI ƘARU, UWA UBA AKWAI SEX AND CO..... 😁MASU TSAYAWA A ZUCIYA_
KU BIYO ALKALAMIN OUM APHNAN
ZAKI IYA BIYAN KUDIN KI TA ƊAYA DAGA CIKIN WANNAN HANYOYIN
7782217014
MOHAMMAD HASSANA.
FCMB
.
SHAIDAR BIYA TA NAN
09065990265
OUM APHNAN✍🏽💖