Header Ads
Showing 1 words to 3000 words out of 15604 words

Chapter 1 - BARIKI GADO NAH. By Oum Aphnan.txt

Ads the beginning of article before Image

14 Jun 2024

396

Ads at the middle of Article

[5/31, 22:11] 😘😘😘: *💙🤍BARIKI🤍💙*
_(Gado nah)_
Book 1
Page 1&2

Oum Aphnan✍️
Bismillah!

_Gargaɗi_
Ban taɓa zagi akan littafi ba ,Amma bana duk wacce ta karanta mun littafi bata biya ba ,ko aka ɗaura mun Littafi a wani shafukan sada zumunta ko utube mutum shi da Allah. Don haka in kinsan zaki siyane don ki ba ƙawarki kawai na hutar dake karki siya,haƙƙin mallaka nane naki karantawa.


_Paid Book_
Regular 300#, Vip 500# , Special 1000# via Hassana Mohammad 7782217014,Fcmb or wxp dix Number 09065990265


_Laraba,2pm._

"Malam kaiwa darajar tsohuwar ka ,yau dai ka barni in shiga Dan girman Allah!,makona uku kenan ina sintiri ka hanani shiga"
Wata wahalalliyar mata da a ɗebe zamu bata shekaru 25 da haihuwa amma tsabagen wuya,duba da yanda bakinta ya bushe ya tsage yina fidda jini ta tsakiyan leɓenta na ƙasa,ga hijabinta tamkar anci wasar sallah akai,ƙafarta sai kace wacce ta kewaye Nigeria da ƙafa,ya daddare da faso gashi yayi buɗuɗu, Kallon Farko sai an bata shekaru Arba'in . Haka ta manne a jikin ƙarafunan get ɗin ta kakkama tana cigaba da roƙon sikyuritin dake jingine da get ɗin wajen ,saidai tamkar baisan tana magana ba ,sai latsa baby Nokiar wayarsa yike . Alamu dai ya nuna inda sabo ya saba da Nacinta

Sarewa da roƙonsa tayi ,don haka taja wata doguwar Ajiyar zuciya ,saiga hawaye masu raɗaɗin fita suna gangaro mata a dakalin kuncinta

"Ya Allah,Ya Sarkin da kayi talaka kayi mawadaci ,kayi mugu kayi wanda ake zalunta Ubangiji na,ka kawo mun wanda zai tausaya mun ,ya dubi rauni na ya Rabbb" wani shasheƙane ya sarƙeta maganar ya daina fita kawai sai ta haukace da tarin Azaba saboda yanda numfashinta ke barazanar ɗaukewa a ƙirjinta.


Alhaji Saddam Mamman Tamkar wanda aka tsikara ya kalli agogon dake manne a katafaren office ɗinsa, zumbur ya miƙe ganin lokacin azuhur ya shiga ,yina fitowa daga ofishin sa kuwa ma'aikata dake dakon jiransa ,suka dafe masa baya ɗuuuu sukayo waje ,zasu nufi masallacin dake ta bayan wajen .

Har zuwa lokacin bata fasa tari ba ,ga idanuwarta sun duddulo waje sun jajir tsabagen Azaba .

Alhaji Saddam dakatawa da tafiya yayi sannan ya ƙwalawa securityn kira

"Malam Tukur!"

Zumbur yayi ,sannan ya yi saurin jefa wayar a aljihu ,ya amsa a furgice ,sannan ya waigo inda take yana mata alamar gargaɗi da yatsa.

"Dakata!,meke faruwa ne anan wajen?"
Sunkuyar dakai yayi ,ya ɗanyi gungunan maganar da baza'a taɓa fahimta ba

"Shikenan ban son jin komai a buɗe mata ta shigo"
Ji yayi kamar kar yabi umurninsa amma ya ya iya?

Buɗe mata get ɗin yayi ,aikuwa cikin bala'in gudu ta shigo harabar tana cigaba da tarin taje ta zube a gabansa
"Yallaɓai kayi mun rai ka ceceni kasheni zai yi ,kwanakin mutuwa na a ƙiddidige yike yau saura kwana biyar!!!"

A mamakance ya ɗan kalli gabansa da ta turmusu, ya ɗan tattare giran sama da ƙasa

"Baiwar Allah tashi tsaye ,ban fahimceki ba ,waye zai kashe ki ɗin"

"Mijina ne yallaɓai, mijina ne "
"Mijin ki?!" Ya tambaya a mamakance
"Eh,wallahi da gaske nike ku taimaka mun,Allah shine mai hukunci ,amma kuna taimako,ku taimaka mun kune ƙarshen fatana ,idan kuma baku taimakeni ba,to zan haƙura zan koma maƙabarta da kwana har zuwa ranar mutuwata don nasan tsimayinta nike!"

Kallon wani ɗan sanda dake gefensa yayi "A bata ruwa da Abinci ta natsu muna dawowa daga sallah"

Yina gama bada umurnin ya ɗauki hanyar masallacin ,ya daɗe rabon da yaci karo da irin mutanen nan ko don yakai ƙololuwa ne oho!

****
Bayan minti Arba'in

Tananan zaune yasa aka kirawo ta ,jikinta ko na azaban rawa ta bi bayan massenger Alƙalin

"Baiwar Allah meye kuken ki?"
Hawaye ne ya cigaba da mata Ambaliya a fuska ,da ƙyar take basa bayani cikin azaban raunin ta ,tsam da rai yayi ,kafin ya umurci massenger ɗinsa da ya kira wanda zai rubuta ƙaran ,sai a kai ma mijin nata sammacin kotu

"Baiwar Allah meye sunan wanda ake ƙaran?"
Shiru tayi ,ta ƙi magana

"Malama ,faɗi sunan mijin naki" cikin sadaƙarwa da raunin murya tace

"Alhaji Sallau Achisu ,Inkiya MAYE!"

Ai bata rufe baki ba ,fuskokin kowa na ofishin ya sauya.,mai rubuta ƙarar a hanzarce ya kekketa takardan Hannunsa
"Wannan matsalar ku ce ta cikin gida Malama ,bazaki tsoma rayukan mutane da yawa a watangariri ba ,tashi ki fita!!" Ya daka mata wani mugun tsawa ,wanda saida taji kamar zata tsullo fitsari a wando

"Me yasa zaka koreta ehem muntari?,A taƙaice ma me ta faɗa da zafi daya tunzura ka?"

"Ranka shi daɗe ,MAYE fa kaji ta ce shine mijinta? Maye fa ,mutumin da ko tsuntsu ya gifta ta inuwar garden ɗinsa kwanansa ya ƙare ......yallaɓai case ɗin matar nan sanannen case ne da ta saba zaga kotuna da ofisoshin ƴan sanda da dama a ƙasar nan kuma kokenta ɗaya shine Su raba mata AURENTA da maye......Amma saidai duk mutumin da ya karɓi ƙarar a ranar baya kwanan duniya !! ,Nikuma a gaskiya ban shirya maida yarana marayu ba ,Matana bazawarai!!..."

Tsam ta miƙe jiri da hajijiya na kwasarta ,a ranta tana Ayyana nan ɗinma babu Nasara,har ta fice ta nufi harabar kotun ,sam bata damu da Muryar dattijon da yaso taimakonta ba dake faman ƙwalla kiran "Baiwar Allah"

A daf da get taja ta tsaya saboda get ɗin da aka kware ma wata ƙatuwar mota ƙirar prado Baƙa da baƙar tint,cak ta tsaya tana jiran su shige ta fice

"BEEEE!!" Wani zabura tayi ta fara waige² tana son ganin ta inda zata mutum ɗaya jal a duniya dake kiranta da Wagga suna

A hankali aka buɗe murfin motar ,wani Ingarman namiji ne ya fito ma'abocin choco skin cikin Black suit da sukayi bala'in kwanciya a jikinsa

Cikin Izzah wanda ya gama bin jinin jikinsa ya ja ya kwanta a jikin motar sannan yasa hannu ya ɗage baƙar shade ɗin da ya sakaye ƙwarar idonsa

Cikin dakuwar bugun zuciya ta nuna shi da yatsa
"SARKI ! .... " Kawai sai hannunta ya fara rawa

Ko a jikinsa da halin da yaga ta shiga saima hannunsa daya nitsa a cikin sumar kansa ,cikin lallausar muryarsa yace

"Na'am MAKAMA TA!...Zo nan "

Kallon kanta tayi tun daga sama har ƙasa ,bata taɓa zaton sak ta zama bata da banbanci da mahaukaciya ba sai yau,ina ita ina raɓar Sadiq a haka? ,aikuwa da sauri ta ciɓa ƙafarta tayi waje harda ƙarawa da gudu da sassarfa


"Ku bita kar ku bari ta ɓace" yina bawa yaransa umurni ya danna kai cikin kotun ransa na azalzalarsa

"Me ya kawo ta ?me take so?"
Tambayar da ya soma jifansu dashi kenan ,cikin rawar murya suka labarta masa mai ya faru da tarikhin waye shi mijin nata

Da ƙarfi ya dunƙule hannu ya daki tebur ɗin gaban alƙalin wanda yasa printer ɗin dake kai yayi tsalle ya faɗi gefe ya farfashe

"Zanci uwarka maye ,Sai na raba auren dan uwarka ,yau ina so in bar duniyar"

Abokinsa Yusuf fagachi da sauri ya zo ya dafa kafaɗarsa "Allah ya huci zuciyar yareeman mu,a bi sannu yallaɓai"

A zafafe ya juyo ya watsa masa Idanuwarsa da suka rine suka zama jajaye nan take

"Ina wasa da kaine Yusuf?"
Shiru yayi sannan ya sunkuyar dakai don ba ƙaramar aikin Prince Sadiq bane yanzu ya tsinke sa da mari batareda ya duba abokantakarsu ba.

"Allah ya huci zuciyar yareema" fuuu ya fice ,wanda suka zo tare suka dafe masa baya


Shikuma Yusuf fagachi lafewa yayi a jikin mota ya kwaɗawa Gimbiya Ramlah kira a waya

Ramlah da tashinta a barcin kenan tun da tayi break fast ko kayan barci bata cireba,wani mugun miƙa tayi ta saki Hamma ,sannan ta ɗan jawo wayar ta saki tsaki gamida ɓata fuska

Muryarta can ƙasa a dushe "Fagachi yadai? Ina mijina yike?"

Ɗan jan fasali yayi ,kana ya magantu


"Ranki shi daɗe ,ina tunanin yaufa akwai ƙura ,koda sarki ya dawo ki lallaɓasa don kafiyarsa da taurin kansa da ya sassauto shekarun baya da suka wuce ,to ina ganin ya dawo ,mutum na haiƙe masa yina iya fyarɗe sa,murus mutum zai shaiƙa barzahu "

Zare ido tayi sannan ta dafe ƙirjinta da sauri kamar yina tsaye yina kallonta

"Yusuf? Kana haukane ? Yariman kake jifa da miyagun zantuttukan nan? Ni ban auri ɗan ta'addaba kar ka sake kiran min miji da siffofin nan,wani shashanci kenan ,kar kayi tunanin don yarimana ya kasance abokinka bazai iya maganinka ba..."

"Ki dakata ki saurareni " ya faɗa a daidai sanda yike shiga motarsu

Tsaki taja ta kasha wayar tana cigaba da ƙunƙuni ,kafin ta fara ƙwallawa kuyangarta kira .

******
Yareema kam tun da ya shige mota ya manne fuskarsa da baƙar shade ɗinsa bai ƙara tamka kowa ba ,tunanin sa ya tafi wajen tuna Abubuwan da suka faffaru a baya ,har abada bai taɓa tunanin Bilqees zata tsinci kanta a kwatankwacin irin wannan Rayuwar ba.

Haɗe Hannuwarsa yayi waje ɗaya ya matsa da ƙarfi sukayi ƙara
"Ni na ja maki Bilqees inada nawa kamashon zunubin ,dole wannan gayen ya karɓi hukunci daidai laifinsa ,muzuba Ni Ko shi............."


*Waiwaye...🚶‍♀️*
©Alheri Writers Association


*Filin Mu Tallata Hajarmu*
Kema zaki iya badawa a sanya maki tallar hajarki a pages ɗin littafina akan kuɗi 2k a page ,a status ɗina kuma 1k.

Mata kuna ina???
Ehem Akace in kin ji kira samu ne
*Hajja mai gyaran aure* ta taho maku da zafafan magungunan mata ƴan gaske,tafiyayyu maras Algus,iya kuɗinki iya shagalinki ,ko mijin ki bai saba ihu ba ,Alƙawarine wannan sai yayi , Magunguna na dai ,Akwai garurruka
Gumba
Tsimi
Tabaje
Jigida me matsi da niima
Jigida mai saka farin jini awarwaron farin jini da mallaka
Zobban farin jini da mallaka
Haɗin Ƴar gata
Zuma na musamman
Cicciɓi
Kaza dahuwar uwargida da amarya .
Ƴan shila
Haɗin kifi
Ɓata jikin Kishiya
Maƙale mata
Haɗin karya gado .da sauransu.
Mu ƙa'idar maganinmu bamu badawa sai mun maki bincike in baki da infection in kuma akwai sai mun maki magani
Hajiya ,maganina nagartattune an daɗe ana yabonsu ,kar in cika ki da zance wani abu sai kin amfani dashi wallahi sai kin kawo ƴar uwarki
Domin ƙarin bayani ki tuntuɓi wannan Numbobin 09060703187
Serious masu saya don Allah🙏🏻
[5/31, 22:11] 😘😘😘: https://chat.whatsapp.com/HsUdTNhf6FkAaXY64sBS0O

*💙🤍BARIKI💙🤍*
_(Gado nah)_
Book 1
Page 3&4

Oum Aphnan✍️

*Gargaɗi*
Littafina Na kuɗi ne ,ban yarda A ɗaukar mun a saka a kowata kafa ta yanar gizo ba.


_Gidan Makaman Gari_

Gidane Tafkeken gaske,Na dandaɓaryan ginin laka,amma an masa zanen gidan sarauta da Hannun magini Tundaga fuskar gidan har can sama wajen indaroron da yike fidda ruwan saman soron gidan musamman lokacin damina....., Gidane mai zurfin gaske da sai ka wuce zauruka guda tara masu tsananin duhuwa,wanda tsabagen duhu da rana sai an sakawa zauran tsakiya fitilar aci balbal. Gidane na dangi ɗaya mai ƙunshe da sasuka biyar ,wanda yafi kowanne girma nan ne sasan MAKAMA

Kaf gidan sasan Makamane kaɗai aka mulmule da sumunti ,akayi wa ƙofar ɗakunan matarsa biyu shaye a gaban ɗakunan su ,kaman varenda luwai da sumunti ,amma sauran tsakar gidan dandaɓaryar ƙasa ne tataaa iya ganinka ,sai ƙatuwar bishiyar mangoro da ta cika sassan da rassan ta wanda ya baiwa ilahirin yaran makama inuwa ,nanne wajen daka da sussuke nanne wajen shimfuɗa taburma aci abinci ko hira .


Ɗuƙe take a ƙarƙashin turken dokin makaman sai faman yankewa dokin farata take da abun datsewa ,gefenta munjagara ne ta kwashe rankatakaf dattin dokin ta tara a gefe ,tana jiran ta ida yankan kofaton ta kwashe ta ɗure a buhu

Ba zato ba tsammani taji an ƙwalla mata kira

"Balkisu?....Balkisu wai kina Ina ne?"

A furgice ta saki abun yankan ,ta ɗago ta sharce zufan da ya tsatsafo mata a goshi

Buɗe iya Muryar da ilahu ya bata tayi ta Amsa da "Na'am umma ina zuwa" ta kwasa a guje zuwa hanyar ɗakin su .

Sadiya da Rahma dake zaune ƙarƙashin Inuwar mangoro ,kallonta sukayi ta yanko a karce suka bushe da dariya

"Wohoho iska na wahalda mai kayan kara ,ƴar na gada ,a gama iyayin dai tas ,ƙarshen alawa ƙasa an tsotsa iskanci dai a nono ko ya kikace sadiya"

Daganan rahma ta miƙo hannu suka tafa da safiya
ɗan jim tayi ta kasa motsa ƙafarta bare ta tafi ,habaicin ƴan ubanta na ɓata mata rai amma ya ta iya? Ji tayi tamkar yau ɗai ta tamka su ,saidai Ummanta ne a wannan karon ta kuma ƙwalla mata kira harda ƙari da mulmuleliyar Ashar.

Ɗauke kai tayi ta shige ɗakin da sauri "Gani umma"

Wata ƙosashiyar Hajiya na gani zaune cikin adon doguwar rigar Atamfa ,kan ɗaya daga cikin jerin wasu ƙosassun kujeru zaka rantse da Allah ɗakin nan ba a cikin gidan yike sbd ynda yasha adon manyan dardumai en Saudi da tafka tafkan labulai ,fanka na sama da na tsaye sai wulwuli suke yi suna fidda Iska

Hannunta riƙe yike da wayarta tana shafa shi a hankali ,tamkar ba itace ta ƙwalla kiran Bilkisu ba da manyan Ashar ɗin da ta zuzzuba .

Ɗan raɓewa Balkin tayi a ƙofa ta riƙe labule,tana kallonta a ido a ido

"Na'am Hajiya mama gani"

Kafeta tayi da daƙwa ²n Idanuwarta cikin tsantsan takaici ,A ranta tana ƙissima wai ɗiyata ce wannan??

Hakan ya bani daman yi mata kallon tsaf Ni kaina.

MashaAllah Yarinya ce matashiya da bazata haura shekaru Goma Sha huɗu ba ,saye cikin wata dark maroon ɗin Abaya da yayi mugun dacewa da kalar fatar jikinta ,farace ,irin tar tar ɗin nan kyakyawace ita tun yanzu kafin maƙerin ƴan mata ya ida zanota ,saidai ƙafafuwan ta da hannunta sunyi futu futu da ƙoran sasan doki

"Balkisu ke wata irin jaka ce? Eyee ?"
Sunkuyar da kai tayi cikin sadaƙarwa tasan yau zata lallasu

"Jibi jikinki...in ƙici in ƙi sha in siya maki Riga dubu sha takwas kije ki gurfana a turken doki kina ma dawakan ubanki bauta ? "

Karkaɗe hannuwarta ta shiga yi "Umma hannu ne kaɗai na ɓata Allah bansa gwuiwana a ƙasa ba ,kin ma gani"

Wani malolon takaici ne ya ɗebeta ta rarumi wani kofin gefenta ta cillota dashi .
Tsalle ta daka tayi baya da sauri

"Kina taka ƙofar ɗakin nan sai na lahira ya fiki jin daɗi ,kinsan ke nike jira da inda zamu ko?"


Cikin rawar jiki ta ɗauki buta taje ta wanko ƙafarta da hannu ta shafa Vaseline ta wuce kwabanta ta ɗauki hijabinta ta saka ,ta fito falon ta sameta tana nan zaune tana aikin shafa waya

Kallon wutsiyar ido tayi mata ,kana tace "mayafin kayan fa?"

Idonta fal ƙwalla ,ta sunce hijab ɗin ,ta warware ɗankwalin da ta kindima ɗauri dashi ta ɗan naɗeshi a wuya

Sai sannan ta ɗan sakar mata ɗan murmushi
"Maza jeki wajen matar audu in ta gama shirya Abdul ta bakishi ,mu tafi"


Da "Tohm umma" ta Amsa ,ta fice zuwa farfajiyar gidan , fuskarta ba yabo ba fallasa ,Su sadiya sai sannan suke karyawa da wata irin tsinkakkiyar koko da ƙuli ƙuli ba sugar,aun barbazu ƙuda sai parade suke a inda suke

Raɓesu tayi ,ta shige ɗakin matar audu ,wacce ta kasance matar wan babansu ne da ya rasu amma ƴar ɗakin umman bilki ce sosai ,duk wani jugu jugu da yaranta ,hidimar makaranta ,wanke ² itace duk don ta ɗan bata abu mai daɗi

"Mama Sala wai ki kawo Abdul zamu tafi " washe baki tayi ,ta zabura ta saɓa Abdul a kafaɗa kamar ƙaramin baby
"Je kira Habu yanzu na gansa zai fice aiki kinga sai ya sauke ku da ɗan sahunsa '

Da sauri tayi hanyar sauro saboda kar ya fice basu haɗu ba

"Habu ance ance ka jira mu zaka kaimu hanwa da umma yanzu gamunan zuwa" ta faɗa da muryanta mai kama dana shagwaɓaɓun yara
"tohm banda abinki bilkisa ai aiki zani,wayace ki kirani??"

"Mamanku"
"To kuyi maza ina jiran ku a bakin garko"

" uhmmm " ta faɗa tana juyawa da sauri dan gani take kaman lokaci baya tafiya ta juya abinta ta tafi ,Bako gaisuwa dama bai ɗaura aka ba inji ɓarawon hula....Inda sabo ya saba yaran basa gayar da mutane,itace ma mai saffa saffa tunda ba rashin kunya

Tana hanyar Juyawa saiga Mamanta ,ta fito hannunta riƙe da ƙanninta kallonta tayi ta kwasa mata harara ,ɗan nishi ta tsaya yi,kafin tace "Maama wai ya fito dashi mu yike jira "

"Ke ja can bani wuri ballagaza kawai" daga haka ta wuceta anan tsaye , noƙai noƙai tabi bayanta suka wuce ,kofar gidan shake yike da tsoffi wanda yawanci iyayen mijinta ne ,amma haka ta shori takalmarta tayi waje da shararan mayafi ta faɗa ɗan sahun Habu suka bar unguwar.

******
Gidan Commisioner of Police (CP)

Hajiya Ladi wanda Akewa laƙabi da _Ladi Police_ Zaune take a makeken falon ta sanye cikin kayan Barcin ta ɓingilar riga rabin cinya mai jikin Nylon da yabi tsokar jikinta ya lafe ,matace shirgegiyar gaske ,ta ɗaura ƙafa ɗaya kan Table ɗaya ta Aje a ƙasa ,mazan kukunta sai kaiwa da kawowansu suke suna gudanar da Aikace²n Girkin gidan .

Tunda Napep ɗin ta tsaya ita ta fara fita bata jira umman nata ba ta zura cikin gidan da ƴar gudunta

"Anty Ladi Ina kwana"
Ware hannu tayi ta miƙo mata alamar ta shiga jikinta ta rungume ta

"Oh my daughter yakike ,ina mama?"
Lafewa tayi akan makamakan nonuwan Hajiya ladi sannan ta nuna mata ƙofa daidai sanda su Hajiya binta suke shugowa

"Aminiya Barka da zuwa "
A hankali ta zame Balkisu a jikinta ta muskuta ta miƙe sukaje suka rungume juna ,a hankali cikin dubara ta maka ma ɗuwawun Hajiya bintan ɗan marin wasa "Washhh ƙawata ya yau "

"Zuii na faɗa maki, ya week End ɗin"

"Wallahi lapiya " daidainan CP ya shiga gangarowa daga stairs yina Amsa waya cikin Shirin fitarshi

Yina hangota ya shiga washe mata baki tun daga Saman matakalan benen har ya sauko ,sakin juna sukayi da hajiya Ladi ta koma kan hannun kujera ta zauna ,itakuma yina zuwa ya kashe wayar ya miƙa hannu suka tafa da Hajiya bintan "Baby girl...Baby girl "

"Alhaji Bala gomnati...Mai Ƴan sanda mai motoci ,to ya ?"
"Wallahi komai daidai ,kin gani ina hanyane mai girma gomna zai shigo zarian zan sorting yarana da zasu taho tare "

"Eh naga Alama ,to bye" kashe mata Ido ɗaya yayi "Baby girl...Baby girl😉",ya sake maimaita Nick name ɗin Hajiya bintar yina nufan hanyar waje ,gamida ɗagawa matarsa Hajiya Ladi da take zaune ,gefensu Bilkis tana jin shirmensu tana masu wasa ,ko A jikinta

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads