Header Ads
Showing 6001 words to 9000 words out of 9529 words

Chapter 3 - SILAR FYADE by Ummu Maheer (miss green).txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

sunan mai gidan,duk gidan da ka gani sai ka ƙara kallonshi saboda ƙyau da tsaruwarsa.






Gidansu Anty Rabi ma gida ne mai ƙyau ga shi ƙato gwanin sha'awa sanyi da Ƙanshin flowers suna ta yi maka barka da zuwa,ji na yi kawai an rungume ni Laila na gani a gaba na tana ta dariya ta amshi Afrah a hannuna ni kuwa sai kallonta na ke yadda ta ƙara fari ƙal ga wata uwar ƙiba da ta yi,acikin lokaci ɗaya na tuno da yadda na ke ada.
*** *** ****




Motoci ne sun kai goma suka shigo ƙyaƙyawar unguwar a cikin ta tsakiya ne na hango Admiral A.yana zaune da system ɗinsa a hannu,yana ɗan wani nazari bisa wani bincike da ya ke.


Wayar sa ce ta ɗauki ƙara ganin mai kiran ya sa ya ɗauka a hankali,cikin girmamawa ya ke gaishe da mahaifiyar ta sa cikin yaren yoruba.


Ta ke tambayarsa ya iso Nigeria ne? ya ce mata eh ya shigo?nan ta ƙara yi masa nasiha akan ya kula da matansa musamman ma Rasheeda don ita ce ƴar uwarsa,to kawai ya ce mata sannan sukayi sallama.




A cen ɓangaren su Rasheeda da kuma Salimat kowaccensu taci ƙwalliya ta alfarma don taron miji musamman ma da yau suka cika ƙwana biyar a ɗakinsa ba tare da sun saka shi a idanuwansu ba.














*Ummu Maher ce*
*🍀SILAR FYAƊE🍀*






NA💋
*UMMU MAHER(MISS GREEN💚)*


Wattpad user name
Rabiatu333


Arewabooks
rabiattu0444






19⬜20




Kai tsaye ɓangarensa ya nufa bai nemi kowaccensu ba,Rasheeda kuwa ta kafa ta tsare tana jikin windon ɗakinta ta saman bene tana hango Admiral A.sanda ya shigo don haka har komawa ɗaki ta yi ta ƙara shafa hoda da janbaki tare da ɗakko wani turarenta mai mugun ƙarfi ta shafa.




Ita kuwa Gimbiya Salimat tana kan sallaya ta ɗaga hannuwanta biyu tana roƙon Allah akan Allah ya mallaka mata ziciyar Sojanta.




Tana cikin wannan addu'ar jakadiyarta ta shigo tana neman iso,tana shigowa ta ce"uwar ɗaki na kuma uwar gida a wajen angonta Admiral A.Yanzu naga motocin Admiral sun shigo gidannan, don haka na garzayo don inzo in gaya miki wannan albishir.
Ɗan murmushi Salimat ta yi sannan ta ce"nima ina yi mishi barka da dawowa Allah ya tsare mana shi a duk inda ya saka ƙafafunsa,amman bazan je ɓangarensa ba don a yanzu hutu ya ke buƙata don haka nasan da kansa zaizo".


kallonta Jakadiyarta ta yi sannan ta ce"haba uwar gijiyata kin fa san ba ke kaɗai ce matarsa ba yana da wata,ba kya tsoron ita yanzu taje ke baki je ba."




"Hmm Yaya na fuskanci abinda ki ke nufi amman nasan kinfi kowa sanin ƴaƴan sarauta da kuma yadda suke gudanar da sha'aninsu na sarauta,don haka ba zan iya zuwa wajensa ba saboda kada ajina ya zube".




Jakadiyarta dariya ta yi tana ganin wauta da kuma ƙuruciya ce ta ke damun Salimat don haka bata ƙara cewa komai ba ta fita daga ɗakin don tasan halin ƴaƴan sarauta akwaisu da kafiya.




Tun rana Aliyu ya dawo amman ko nan da cen baije ba,don yana shiga ɗakinsa da ya yi wanka yabi lafiyar gado ya ƙwanta don baya son hayaniya.






Rasheeda kuwa tana cen hankalinta a tashe don tana saka ran dawowar miji amman kuma taji shiru,don haka da kanta da daddare ta shirya cikin wasu arnan kayan bacci wanda sunansu sabon salon fanɗarinka a waje.




Sannan ta ɗakko wani turarenta wanda Hajiyar Aliyu tayo mata oder ɗinsa tun daga Sudan,matuƙar namiji ya shaƙesa to fa ya gama aiki.






A hankali ta fara ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin,shi kuwa Aliyu ya zata mai kawo mishi abinci ne ya ce"come in".




Babu wani jan aji Rasheeda ta shigo tana wani takunta kamar wata munafuka,tana shigowa ta cire hijabinta kai tsaye ta yi wajen Aliyu.














*Miss green ce*


Kuyi min afuwa rashin charge ne👏🏻




Na gama littafin darasi free page,don haka idan mutum yana da buƙata ya tintibeni ta wannan no ɗin.






Ga ɗanɗano da ga littafin darasi na payments.




DARASI!DARASI!!DARASI!!!






Alokacin General A.ya shigo da muƙarabansa waɗanda suka rakosa motoci sunfi goma sha,tun daga nesa ya ke kallon kyakkyawar halittar Fahima ga gashinta sai ɗagawa ya ke kamar wara ba indiya ko balarabiya,ya yi tsaye yana kallonta yana mamakin a ina aka samo wannan kyakkyawar yarinyar?.




Dai dai lokacin aka tsuge da ruwan sama mai tattare da ni'ima da ƙanshin ƙasa haɗi dana flowers ɗin gidan,ga wata iska mai daɗi.






Tsalle Fahima ta ke tana wasa da ruwan kana ganinta ka ga yarinya,a hankali Ammar ya biyo ta bayanta ya cire rigar sanyin da ya saka ta sojoji ya lulluɓawa Fahima,da sauri ta juyo cikin tsoro,aka yi rashin sa a ta zame ta faɗo ƙirjin Ammar yadda kasan awani indian film haka abin ya faru,daga shi sai singlet,gashin ƙirjinsa ya ƙwanta kamar wani gashin jariri.




Kallon ƙuda suka shiga yi babu ko ƙiftawa zuciyoyinsu sai bugawa suke kowannensu zai iya juyo ta ɗan uwansa.






A dai dai wannan lokacin kuma hancin motar Hajiya Sakinat ta shigo,bata kula da abin da ke faruwa ba sai da ta fito sai da ta da fa murfin motarta sannan ta iya tsayawa da ƙafafunta,idanunta sunyi jawur kamar gauta wata wutar jaraba da wutar kishi Sakinat taji a ƙirjinta,cikin wani irin mahaukacin sauri ta tunkaro inda su Ammar da Fahima suke.
_*🪁SILAR FYAƊE*🪁_


📃BOOK 2


UMMU MAHER(MISS GREEN🍀)




_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._




--------
*SIRRINKI👂🏻*


ƳAR UWATA ANASO BAYAN KIN GAMA AL'ADA KIDINGA TSARKI DA GANYEN MAGARYA,YANA CIRE INFECTION DA SAURAN ƘARNIN JINI👏🏻.


DAGA DR UMMU MAHER.
21🟪22


Yana kallon Rasheeda har ta shigo cikin kyakkyawan Ɗakin mijin na ta Babu ko gaisuwa ballantana sannu da zuwa ta ce"ashe ka dawo"?.


ta FaƊi hakan cikin yarensu na yoroba,banza ya yi mata ya tashi zaune sannan ya ce"kije ki kirawomin Salimat ku sameni a babban farlona".


yana faƊar hakan ya yi waje ko ajikinsa don duk wani iyayin da Rasheeda ta ke ko kallonta bai yi ba,ballantana ma yaga wata ƙwalliyar da ta yi mai.




Haushi da kuma dana sanin zuwanta ɗakin admiral A. Ya kama ta sai zagin kanta ta ke don sam arayuwarta ta tsani wulaƙanci tana matuƙar son admiral A. Shiyyasa ma ta ke shanye duk wani shariyarsa.




Sanda ta isa mangaren gimbiya Salimat wani ƙamshi mai mugun daɗi ya ziyarci hancinta,wani malulun baƙin ciki ya dirar mata,bata ƙara jin wani haushin ba sai da ta saka ƙafafunta a wani lallausan kafet mai mugun laushi ta haƊiye wani mugun yawu na baƘin ciki ta Ƙara sa shiga babban farlon wanda ya gaji da haɗuwa,duk kyan kayan Rasheeda sai taga na Salimat ya ta ka na ta a kyau da kuma tsaruwa komai na farlon white ne da kuma pink ya yi matuƙar yin ƙyau.




Tana cikin kallon farlon ne,jakadiya ta ce"baiwar Allah lafiya?baki iya sallama bane?"duk alokaci ɗaya jakadiya ta yi wannan tambayar.




Wani banzan kallo Rashida ta yi mata sannan ta ce"ki gayawa ita uwar mulkin maigidan yana son ganinta".


Da sauri Jakadiya ta ce"to bacci ta ke amman bari in tashi gimbiyar mata."tana faɗin hakan ta yi hanyar ɗakin Salimat.




"Ke dai ta ke gimbiyarki amman ni ba gimbiya ta ce ba".
Ado sosai Salimat ta yi da wata lifaya mai ƙyau fara ƙal sai ɗaukar ido ta ke,ta sha turaruka masu ƙamshi.




Sai da Rasheeda ta raina kanta ganin irin ƙwalliyar da Salimat ta yi.




Sallama ta yi sannan ta gaishesa,yaji daɗin gaisuwar da Salimat ta yi masa don ko babu komai ta girmama sa.




Rasheeda taji haushin abinda ya yi na amsa gaisuwar Salimat da ya yi ai kuwa ta cukule fuskarta tamau.




Abin yaso ya bawa Aliyu dariya amman sai ya basar da hakan,nasiha ya yi musu mai ratsa jiki sannan ya tabbatar musu da cewa Salimat ce uwargidansa tunda aurenta aka fara ɗaurawa.




Ai kuwa Rasheeda taji haushi sosai cikin yaran yoruba ta ce"gaskiya tun a yanzu ma nasan ba adalci za ayi ba".




ko kallonta baiyi ba don yasan abinda ta ce,sannan ya ce su tsara kwanakin da yafi yi musu,Rasheeda ta yi banza Salimat kuwa ta ce kwana biyu ya yi.


Tana faɗar hakan Rasheeda ta ce baiyi mata ba Aliyu ya ɗaga mata hannu sannan ya ce duk wacce ta nemi ta yar masa da hankali to fa zai yi displing ɗinta yadda ya kamata.


A take ta yi shiru don tasan waye Aliyu.




A ranar ya kamata Salimat ta amshi ƙwananta amman har dare ta rasa yadda za ayi taje wajensa don wata kunya da girman kai ta keji.






Kuyi haƙuri na yi typing kaɗan ayi manage.








*Miss green ce*
_*🪁SILAR FYAƊE*🪁_


📃BOOK 2


UMMU MAHER(MISS GREEN🍀)


Wattpad user name
Rabiatu333


Arewabooks
rabiattu0444






---------
SIRRINKI👂🏻


ƳAR UWA KI KASANCE MAI RUFE SUTURARKI AKO DA YAUSHE,RUFE JIKINKI YANA TAIMAKA MIKI WAJEN YIN RIGAKAFI GA MUTANE DA KUMA SHAIƊANU.




23🟩24




. . .. Har Ɗaki jakadiya Binta tabi Gimbiya Salimat don tasan tau ya kamata Salimat ta ƙwana a ɗakin mijinta Admiral A.tunda itace uwargidansa don aurenta aka fara ɗaurawa.




Tana zaune ta yi ta gumi ta sameta,Jakadiya ta samu waje ta zauna a ƙasa ta ce"uwar ɗakina idan babu damuwa aƙwai maganar da na ke so muyi da ke".
Salimat tasan maganar don haka bata ce komai ba ta tashi ta shiga bathroom Ɗin da ke manne ajikin Ƙaton ɗakin na ta,ɗan murmushi Jakadiya ta yi tana mamakin hali irin na Salimat kamar ba ita bace ta ke kukan son Aliyu ba,yanzu kuma ta sameshi sai ta yi wasarere dashi,ta yi wa mahaifiyar Salimat alƙawari tun kafin ta rasu za ta kula da Salimat kamar ita ta haifeta.
Kafin ta fito da sauri ta fita daga ɗakin taje ta ɗauko mata wani magani na sirri da ta aika aka kawo mata tun daga garinsu don ta yi dabarar sakawa Salimat a cikin madara don tasan ta da shan madara,shi wannan sirrin na dabanne wanda ke saka mace ta mallake mijinta ta hanyar shimfiɗarta.








***


babu abinda zance da zamana agidan ƙanwar mahaifiyata don babu abinda na nema na rasa,twins sun ƙara yin wani ƙyau da kuma ƙiba don suna samun abinci mai gina jiki,nima jikina ya ƙara ƙyau ni daman ya ya lafiyar kura don jikina jikin manyan mata ne na ƙara cika da ƙiba.




Ɗakina ma kaɗai abin kallo ne saboda yadda aka ƙawata shi gwanin sha'awa ga kuma suturu sai wanda na ke son zaɓa don wadrope ɗina cike ya ke da kaya masu ƙyau.




Rannan da yamma muna zaune a farlon Anty Rabi Layla ta ce"Sister don Allah inason ki rakani super marker in ɗanyo shopping".


ɗan murmushi na yi sannan na ce "babu komai Allah ya kaimu".


Idris ƙanin Layla ya ce"gaskiya ba za'aje da twins ba a barmin su muyi wasa."Dariya na yi na tashi na ce"ai ni daman yanzu na barmaka twins"dariya ya yi tayi yana murna wai na bar masa twins.


Ƴaƴan Anty Rabi huɗu ne uku maza mace ɗaya,maza biyun suna Germany acen suke karatu.
***
Ƙwalliya Salimat ta yi cikin wasu kayan bacci masu matuƙar ɗaukar hankali,sannan ta feshe jikinta da turaruka kala2,Sallama Jakadiya ta yi sannan ta ce"uwar ɗakina ga madara mai sanyi nasan kina so".


amsa Salimat ta yi tasha tana mai jin daɗin madarar,ta saka lifayarta mai ƙyau ta yi hanyar ɗakin oga Admiral A.




Ta saman bene Rasheeda ta hango Salimat za ta je ɓangaren mijinsu,wani irin malolon baƙin ciki ne ya ɗarsu a zuciyarta ta saka a zuciyarta matuƙar tana numfashi sai ta tarwatsa fadar Salimat,don ta yi alƙawarin sai ta wargaza fadar Salimat awajen Aliyu don ta lura tun yanzu fadarta mai yawa ce awajensa.










Kuyi haƙuri matsalar charge na ke da ita.




*Miss green ce*
_*🪁SILAR FYAƊE*🪁_


📃BOOK 2


UMMU MAHER(MISS GREEN🍀)


Wattpad user name
Rabiatu333


Arewabooks
rabiattu0444




*addu'ar samun lfy ga ko wani irin ciwo*


an rawaito daga Aisha (R.A),tace manzon Allah(S.A.W)ya kasance idan mara lfy yazo wurinsa da kokena rashin lfy ya kan ɗauka hannunsa na tsakiya ya sanya a bakinsa sannan ya dangwali ƙasa sannan ya ɗaura a inda kewa mutumin ciwo,sai ya karanta wannan addu'ar kamar haka;


"bismillahir turbati ardina biriqati ba'dina yashfa Taqimuna bi'izni rabbina".






25/26




Da sallamarta ta shiga ɗakin hankalinsa na kan system ɗinsa ya ɗukufa da aiki ya amsa mata ya ɗan kalleta kaɗan sannan ya cigaba da aikinsa,waje ta samu aɗan kaɗan da nesa dashi ta ce"ina wuni"a hankali shima ya ce "lafiya"sannan ya kashe system ɗin ya ce mata yana zuwa.




Bai daɗe ba sai gashi ya shigo da wata ƙatuwar farar leda sannan ya ajje ya shiga bayinsa ya yi wanka da ɗaura alwala a inda ya barta anan ya dawo ya sameta ta sunkuyar da kanta ƙasa tana wasa da gefen mayafin lifayar ta ta,ya ce"tashi ki ɗauro alwala zamuyi sallah".a hankali ta tashi ta shiga banɗakin alwala tayo ta fito banɗakin nasa ya ƙawatu sosai wanda har sai da ya burge ta banɗakin kamar na mace komai fes dashi yana daga cikin abinda yasa ta ke matuƙar son Aliyu kenan aƙwai tsafta sosai.




Tana fitowa har ya tada sallah ta bishi suka yi har suka idar,a hankali ya ɗaga hannuwansa sama yana addu'ah tana amsawa da amin har suka gama tana jin ninkin ba ninkin ɗin son aliyu don bata Ƙara gasgata ilimin da ya ke dashi ba sai yanzu.


Ya kama goshinta ya shiga karanto mata addu'ar nan da manzon Allah(S.A.W) ya mana"alluhuma inni as'aluka khairaha wa khaira ma jabaltaha alaihi,wamin sharri ma jabaltaha washarri ma jabaltaha alaihi".






Kaza ce ƙatuwa mai girman gaske sai fresh milk ƙaton ƙwali uku mai sanyi sai shawarma wacce tun kafin a buɗeta ƙamshinta ya cika hancin mutum.


Tura mata kazar ya yi dukkanta sannan ya tsiyaya madarar yasha ya buɗe swan yasha sannan ya Ƙwanta ya ce"sai da safe".




wata ƙwallace ta biyo ta kuncin salimat ta kula kara kawai ya ke mata don kada ta fuskanci ba ya sonta,har cikin zuciyarta taji abin ya yi mata zafi amman yanzu ta wacce hanya ya kamata ta janyo hankalin aliyu don ya sota?babu mai bata amsa don haka ta Ƙwashe kayan ta kai fridge sannan ta Ƙudunduna a Ƙasan kafet ta Ƙwanta,aliyu yana kallonta sai da ya bari tayi bacci sannan ya sungumeta ya Ɗorata akan gadon sannan shi ya sakko Ƙasan ya Ƙwanta.










****


Da wuri na shirya na fito ina yiwa twins dariya don da sunga naci ado sai suyi ta maƘale min wai zamu tafi unguwa,yanzun ma haka ne ya faru suna hannun mama suka miƘomin hannu dariya mama ta yi sannan ta ce ai kuwz baza a tafi daku ba in rasa Ɗan hira".




ƴar dariya na yi sannan laila tace"ai kuwa ba zamu tafi dasu ba sun saka ayi ta ganin mamansu matar aure gwara mutafi siƘau Ɗin Mu".






har muka fito daga supet market na duba hannuna sannan na ce"ai kuwa laila na yi mantuwa"tsayawa ta yi a waje ni kuma na shiga don Ɗauko abinda na manta Ɗin wani anu naji na buge dashi kamar mutum don haka na juyo,,wata irin muguwar faƊuwar gaba naji tun daga kaina har Ƙasa na".






ina godiya sosai fans ɗina na darasi da sauran littattafaina ina godiya sosai akan nuna kulawar da kuka nuna min alokacin da na yi rashin lafiya,lol saƙo har yanzu sunyi min yawa,don Allah waɗanda ban duba nasu ba suyi min uzuri ina godiya.👏🏻🤝




*miss green*
_*🪁SILAR FYAƊE*🪁_


📃BOOK 2






*UMMU MAHER(MISS GREEN🍀)*




Wattpad user name
Rabiatu333


Arewabooks
rabiattu0444






27🟩28


Sosai gabana ya faɗi don ganin wanda na gani,bansanshi ba?ban san daga inda ya ke ba?amman kana ganinsa ba sai an faɗa maka ba matuƙar ka kalli twins ɗina zakaga babu abinda ya banbanta su kawai abinda ya banbantasu shi babba su kuma yara.




Kasa barin wajen na yi shi kuwa yana ta siyayyarsa ya fito ta hanyar da na ke,wani glass ne na ɗora hannuna akai ban sani ba ina kallonsa kawai sai naji ya faɗi ƙasa ya tarwatse baki ɗaya,nan ta ke hankalin kowa yayo kaina,nima cikin tsoron na kalli glass ɗin.




Aliyu ma kallo inda yaji ƙarar glass ɗin ya yi sojoji biyu ne a tare dashi,kallona ya shigayi sosai ammanfa bani ɗin ya ke kallo ba hannuna ya ke kallo wanda ya yanke har yana fidda jini amman ni ban san yana fidda jinin ba saboda tsoro da firgici.




A hankali yazo inda na ke nima a lokacin kallon nasa na ke kawai don har yanzu mamakin kamannin na ke.




"Baiwar Allah kina bleeding baki sani ba".da sauri na kalli hannun wanda sai a yanzu naji zafin hannun,alokacin securities ɗin wajen sunzo suna ƙwashe glass ɗin da ya fashe.




Alokacin Layla ta shigo hankalinta a tashe tayo kaina don ganin hannuna yana fidda jini tana tambaya ta me ya faru?amman ban ba ta amsa ba baki na yana rawa na ke nuna mata Aliyu,kallon inda hannuna yabi ta ke yi,a ta ke itama tayo waje da idanuwanta tana kallon inda na ke kallo.


Aliyu mamaki ne ya kamashi ganin suna ta nuna sa alhali basu sanshi ba,ganin shima mamakin ya ke yasa Layla ta buɗe wayarsa ta tako a hankali wajen Aliyu ta buɗe mishi hoton twins.




Shima waro idanu waje ya yi ganin waɗannan yaran masu mugun kama dashi ya yi imanin cewa ko da ƴaƴansa ne da ƙer zasu yi irin wannan kamar.
Da sauri ya ce"baiwar Allah wannan yaran yaranki ne?".


A hankali Layla ta juya ta kalli Rabiatu sanman ta nuna ta da ɗan yatsa,kallon Rabiatu ya yi sosai ganin wai wannan ƴar yarinyar ce mahaifiyar yaran wacce ko a fuskarta bata nuna alamar ta taɓa haihuwa ba a ƙiyasce ma bata fi shekara 18 ba.






A hankali Aliyu ya ta ka ya i'sa wajen da Rabiatu ta ke wacce har a lokacin kallon Aliyu ta ke,a hankali ya ce "baiwar Allah biyo ni waje

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads