Showing 39001 words to 42000 words out of 42437 words
Chapter 14 - KATANGA COMPLETE DOCUMENT By RABEE'AH SHU'AYB NABABA.txt
yace to yanzu ta koma taje ta kawo masa k'asar da Mustapha ya taka, idan ta kawota to tabbas da kansa zai zo yace ya fasa wannan aure, shi kuma Saminu za mu juyar masa da ra'ayi da kansa zaice ya fasa auran Nimha, kinga daga nan sai mu juyo da hankalin Mustapha kan Nimha.
Farin ciki sosai Umma tai da jin jawabin Malamin, aikuwa ranar da Mustapha yazo ta k'asa ta tsare ta na jiran shigowar Shukhura ta yi sauri ta fice ta d'ebo k'asar da Mustapha zai taka, aikuwa ta na ganin shigowar Shukhuran ta yi saurin ficewa ta 'yebo washe gari taje ta kaiwa malamin aikuwa yace ta na kwance za ta ji kyakkyawan labari...
300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i.
NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK
In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta.
09037093702
In katin wayane 400 zaku biya.
Garab'asa gareku masoyana duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a layina muyi magana.
Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin.
#Team KTG
#N.W.A
[10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: *KTG*
Wattpad@Rashuna
https://my.w.tt/Cjpv9nxoJ9?utm_
____________
*TEN*
KWANCI TASHI
Gurin Ubangiji ba wuya, su Shukhura har sun yi candy, sati d'aya da yin candynsu aka kawo lefen su.
Akwatina 6 haka Saminu yaiwa Nimha, kuma ya yi iya k'arfinsa kayanta babu kushe ko d'aya, Shukhura kuwa akwatina goma sha biyu dank'are da kaya na alfarma, sark'ok'in daham kuwa zasu kai 6 a ciki, nan da nan hankalin Umma ya k'ara tashi, ta fuskanci wannan malamin kawai kud'inta yake ci dole ta canja shik'a.
Wani k'ungurmun boka ta kuma samowa shi ya sanar mata.
"Duk wanda yace miki wannan aure bazai tabbata ba to tabbas yai miki k'arya, kud'inki kawai yake ci, wannan aure muk'addari ne daga Ubangiji kuma babu makawa sai ya faru, don haka kije ki rungumi k'addarar da tazo miki da hannu bibbiyu.“
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, yanzu babu wata mafita? “
" Babu wata mafita indai akan hana auran nan ne, sai dai wani da ban kuma, don wannan ba makawa sai ya tabbata. “
Shiru Umma tai hankalinta in yai dubu ya tashi, yanzu dole ta koma ta d'ebi cin kashi gurin kishiyarta, haka za ta zauna ta na kallon Shukhura na d'agawa da fariya ta na auren me kud'i, komai ta yayibo ta kaiwa uwarta ta na zaune kamar jaka, 'yarta kuwa sai dai ta yayibo kantar talaucinsu ta juye mata, ina bazai yuyu ba da sake, to kuma ta ya ya?
Koma ta yaya ne ta bawa zuciyarta amsa daga bisani ta kalli bokon za tai magana ya dakatar da ita da hannu d'aya.
"Kud'in aikinki dubu d'ari biyu, za ki kawo mini dubu hamsin da bak'ak'en kaji guda shida, idan aiki ya tabbata sai ki ciko dubu d'ari da hamsin, amman idan har kina so aikin ya kama jikinta sosai sai idan babu ran mahaifiyarta. “
'Ta yadda da ingancin aikin bokan nan, tun da har ya san abinda ke zuciyarta, to amman kuma ta ya ya mahaifiyarta za ta rasu bayan ranta ba a hannunsu yake ba?.'
Maganarsa ce ta dawo da ita daga tunanin da ta tafi.
"Zan tura mata ciwon da zaiyi sanadiyar mutuwarta, daga nan ba ki da sauran Katanga tsakaninki da Shukhura, ke za ta dingaiwa kallon mahaifiyarta, amman kafin nan sai an fara raba tsakaninsu da me gidanku, a kuma rufe bakinsa, babu case ga wannan tsohuwar matar idan har kina sakar mata abin Duniya. Su kuma 'yan uwanta za'a raba soyayyar da ke tsakaninsu, saboda ta na matuk'ar son su fiye da son da takewa kanta.“
Farin ciki ne ya dabaibaye zuciyar Umma, ta dinga sharara masa godiya, suka rabu akan za ta dawo ta kawo masa abinda ya Buk'ata.“
Akwatinan Nimha ta kwashe da wasu kaya daga ciki taje ta sayar ta kai masa kud'in da kajin da ya buk'ata, ya bata wani ku'ullikan magani, d'aya ta zuba a cikin abincin da Mama za ta ci, d'aya ta zuba cikin ruwan turaren da za'aiwa Shukhura kamu da shi, d'aya cikin abincin da Baba zai ci, sai laya da za ta saka a bayan gadon Shukhuran, babu wanda zai lura da layar sai ita da ta saka da kanta, sauran abubuwan kuma shi zai ji da komai.
Shirye²n biki su Mama suke hankali kwance, don yanzu saura sati guda a fara shagul gulan biki, duk da Mama ta fara fuskantar wasu sauye² daga Baba hakan baisa ta tayar da hankalinta ba, da Allah ta dogara shi kuma taci gaba da mik'awa buk'atunta, don a 'yan kwanakin nan wasu mugayen mafarkai take mara dad'in ji ko kad'an, kawai ta na danne damuwarta ne saboda yaranta, don wani abu da Shukhura kuma ta tsira shine, duk dare sai ta sanyata a gaba ta na kuka ta na rok'onta akan a fasa wannan bikin, ta na jin kamar wani babban al'amari zai tunkaro su idan har akayi wannan auran, sai dai ta lallasheta da nasihohi masu ratsa jiki, don babu damar tunkarar Baba da wannan maganar, bare ya dube su, don ita kanta Mama yanzu ba ta buk'atar auran, to Baban gaba d'aya yanzu ya sauya musu da Nusrat kad'ai yake zama ya yi hira, hakan ya kuma tayar da hankalinsu gaba d'aya amman a haka suka daure suka cigaba da shirye shiryen da ba'a rasa ba.
Ranar juma'a akai kamu anan cikin gidan, Iya ce ta kama duka amaren guda biyu, yayin da taiwa Shukhura amfani da turaren Nimha, taiwa Nimha da na Shukhura wannan kuma duk tsarin Umma ne.
Ranar juma'ar da daddare akai Dinner d'in gidan su Mustapha, da Baba yace Shukhura ba za ta ba, da k'yar Nusrat ta lallab'a shi ya barsu suka je, kuma diner d'in ta k'ayatar da dukkan wanda ya halarci gurin.
Washe gari asabar sukayi walima anan cikin gidan don Baba ya hana DJ kuma walimar ta yi gwanin ban sha'awa.
Washe gari lahadi kuma aka d'aura auran.
Safiya Abdullahi Ahmad da angonta
Mustapha Faruoq Fanda
Zainab Abdullahi Ahmad da angon ta.
Saminu Yusha'u Hamza.
Tun da aka d'aura auran Shukhura da Nusrat ke kuka, gaba d'ayansu suna jin wani miki a zuciyarsu ya na musu ciwo amma ba su san dalili ba, Mama ce tai k'ok'arin rarrashinsu duk da itama ba ta jin dad'in jikinta, amman saboda mutanen da ke shigowa ana kallonsu shiyasa ta rarrashesu, su d'aki falle d'aya bare tace su shiga ciki suyi kukan nasu babu wanda ya gansu, ta san dai kukan rabuwa suke, wannan kuka kuwa dole su yishi, sun taso tamkar 'yan biyun da suka zauna a mahaifa d'aya, suna matuk'ar son junansu ko kyauta za'a yi musu sun fi son ayi musu a tare, idan kwa aka bawa d'aya to tare zasui amfani da shi, musamman Shukhura da ki mata kyauta gara kiyiwa Nusrat za ta fi matuk'ar farin ciki, hakan da Mustapha ya gani ne yasa komai zai yiwa Shukhura sai ya yi musu tare da Nusrat , wataran ma Nusrat d'in kad'ai yakewa kyauta don kawai yaga farin cikin sahibarsa.
K'arfe biyar dai² aka kawo motocin d'aukar amarya Shukhura, ita Nimha sai bayan sallar Isha saboda babu nisa, a lokacin kukan Nusrat da Shukhura ya k'ara k'arfi suka rungume juna suna kuka kamar ba sa rabu ba, Iya ce tazo ta janye Shukhura ta na sababi.
"Meye kuma na kuka bayan Allah ya 'yanta ki ya kaiki gidan daula, ki daina biyewa Nusrat bak'in ciki take miki don ita Allah ya yota me nauyin k'afar tsiya har yau ko mashin shini babu. “
Shukhura kukanta kawai take, Iya ta dank'ata hannun Aunty Maryam suka shiga da ita d'akin Baba, yayin da Mama ta rungume Nusrat ta na jin itama kamar ta fashe da kukan, takai dubanta ga Yusra da take ta aikin matse k'walla, da hannu ta yafito ta itama tazo gareta ta rungumesu ta na jin wani iri a zuciyarta.
Nasihu masu ratsa jiki Baba ya yi mata, ban da kuka babu abinda take ta cikin mayafinta daga k'arshe Baba ya sanya mata albarka aka fito da ita, ganin ana k'ok'arin fita da ita yasa ta fisge hannunta ta ruga d'akinsu da gudu, jikin Mama ta fad'a ta ruk'unk'umeta ta na kuka me ban tausayi, ta na jin kamar shi kenan daga yanzu sun rabu rabuwa ta har abada, shafa kanta Mama ta yi, don ta kusa sanyata zub da k'walla kawai ta na jajircewa ne.
"Allah ya yi miki albarka Shukhura, kije kiyi hak'uri ki kuma rik'e gaskiya a duk in da kike. “
"Mama ki yafe mini.“
"Babu abinda kika tab'a yi mini Mamana, ko da kinyi mini nan gaba na yafe miki Shukhura Duniya da lahira, fatana ki rik'e 'yan uwanki da daraja, kada ki bada damar da za'a rusa ginanniyar katangar k'aunar da na gino a tsakaninku tun kuna yara, idan kikai mini haka kin biyani Duniya da lahira, Allah ya yi muku albarka baki d'ayanku, Amin, muje maza ana jiranki. ”
Ta rik'o hannunta had'e da na Nusrat, don Yusra tun d'azu ta fice k'ilama har ta samu mota, a hannun Aunty Maryam Mama ta kuma dank'a ta had'e da fad'in.
"Allah yasa ki shiga a sa'a, insha Allah mutuwa ce za ta fito dake daga wannan gida cikin salama da aminci, Allah kuma ya baku zaman lafiya na har abada amin, Yayarsu kije ki raka 'yar uwarki d'akinta. “
Daga haka ta saki hannun Nusrat d'in ta shige d'aki, daga jin k'arshen maganarta ka san kuka take.
Sai da aka kai Shukhura gurin Hajiya Suwaiba da gurin Inna kana aka huce da ita sashenta dake gefen gidan.
Sashen Shukhura gaskiya ya had'u iya had'uwa, komai walwali yake da k'yalli, bed room d'inta ma ciki da falo ne, anan aka yi amfani da kayan da Baba ya siya mata, don cewa sukai ba sai an mata komai ba, Baba yace a barshi dai ya siyawa 'yarsa mutumci, ko ba komai itama za tayi alfahari da haka, kamar yadda ko wace amarya ke yi.
Kayan da Baba ya yi musu suma ba laifi sun yi kyau iya kyau.
Kowa ya watse daga Shukhura sai Hidaya da suke jiran angwaye su zo suma su kama gabansu, tara dai² Mustapha ya kira Shukhura yace gasu a k'ofar gida zasu shigo don haka sai suka k'ara d'an kimkimtsawa suka fito da ita babban falo suka zauna, abokan nasa biyune sai shi cikon na uku, addu'oi aka yi akan Allah ya basu zaman lafiya kana abokan sukai musu sallama suka fita yabi bayansu don ya yi musu rakiya, su Nusrat ma suka tashi zasu tafi, rik'o hannunta Shukhura ta yi gam tace.
"Dan Allah Yayarmu kar ki tafi ki barni.“
Ta fad'a jikinta na rawa, hawaye ne ya zirarowa Shukhura haka zalika Nusrat d'inma suka rungume juna suna kuka, karo na farko kenan da zasu nesanta da juna tun tasowarsu, gurin kwanciyarsu d'aya, filon da suke d'ora kai guda d'aya a haka zasui bacci Shukhura ta rungumo Nusrat ta baya, ta gaba kuma Yusra ta rungumeta, gashi yau zasu kwana ba tare da Shukhuran ba, aure kenan me kawoka wata sabuwar bigiren rayuwa.
"Kar ki tafi ki barni, ba na son ki barni, ki zauna tare da ni kinji Yayarmu don Allah.“
"Ai muna tare Shukhura, ba wai mun rabu kenan ba, gobe ma insha Allahu zamu zo, ke dai ki rik'e nasihohin da akai miki, azkhar d'in nan na safe da yamma kada ki sake ki wasa haka zalika nafil fili ma. “
Daga haka ta zare jikinta daga nata ta bi bayan Hidaya saboda tun d'azu Mustapha yace su fito abokansa su sauke su a gida, ledar kaza da youghort Mustapha ya bawa Nusrat ta yi godiya ta shiga motar suka tafi shi kuma ya juya cikin gidan.
Ya sha rikici sosai da lallami ya lallamata har sukai sallah suka mika godiyar su ga Ubangiji, daga bisani suka d'an tab'a kazar amarcin don dukkaninsu basu saki jiki sun ci ba, sun d'an jima a zaune, ta na kwance a jikinsa ya kanainayeta kana sukai shirin bacci suka kwanta, Mustapha ya hankad'o ni daga d'akin yace mini.
"Asuba ta gari kema kije ki huta. “
Don haka na tafi hutawa sai kuma gobe in kun jini......
300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i.
NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK
In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta.
09037093702
In katin wayane 400 zaku biya.
Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin.
#N.W.A
#Team KTG
#Sonso fisabilillah
[10/8, 3:43 PM] Binta Lawan: *KTG*
Wattpad@Rashuna
https://my.w.tt/Cjpv9nxoJ9?utm_
____________
*ELEVEN*
(ZANEN K'ADDARA)
A wannan dare su Nusrat basui bacci ba, zazzab'i ne me zafin gaske ya rufe Mama da kuma matsanancin ciwon kai, wanda bacci ya k'auracewa idanuwanta, haka zalika ma Nusrat ba ta iya rintsawa ba ko kad'an har garin Allah ya waye.
Fitowa ta yi ta nufi d'akin Baba don ta sanar da shi sai taji muryar Umma tace.
"Nusrat.“
Juyowa ta yi ta na kallonta don ba magana ce ke had'asu ba, face gaisuwa idan Nusrat d'in ta gaisheta.
"Cewa na yi Shukhura kuwa ta kiraku? Kinga ni har ta kirawo ta gaisheni."
"Ai tun da nai sallar asuba mukai waya da ita. “
Nusrat ta ba ta amsa, don yanzu ba lokacin da za ta tsaya yin tunani akan maganar ba ne, d'akin Baba tai shigewarta, ya na kishin gid'e bacci har zai fara fusgarsa ya ji alamun shigowar mutum, a hankula ya sauke idanuwansa akan fuskar Nusrat yace.
" 'Yar baiwa lafiya? “
"Baba, Mama ce ba ta da lafiya tun cikin dare. “
"To sai akai ya ya kuma. “
Tsura masa ido Nusrat tai, kamar ba Baban nan nasu ba, mai k'aunar mahaifiyarsu, ta hango lokacin da tai wata rashin lafiya yadda duk ya firgice ya fita daga hayyacinsa, ya zamo tamkar shine mara lafiyar.
Wani yahu me tauri ta had'iye tace.
"Dama chamise zamu je. “
"To sai kun dawo don ni ficika ba na magani. “
Ba tace komai ba ta juya ta bar d'akin, dama ba kud'insa suke buk'ata ba, kawai dai ta gaya masa ne a matsayinsa na me jagorantarsu gaba d'ayansu.
Umma kuwa bak'in ciki ne yai mugun kama ta da taji wai Shukhura sun yi waya da Nusrat, a yadda bokanta ya sanar mata idan har Shukhura ta kwana a kan gadon nan to sunyi rabuwa ta har abada ita da 'yan uwanta, tsakaninsu kuwa sai dai kallo, ita kuwa Mama na mutuwa, to tabbas ita za ta zamo mahaifiyar Shukhura kuma babu wanda ya isa yai magana akan hakan, dad'inta d'aya ne da ta fuskanci Mama ba ta da lafiya, tsakanin Shukhura da Nusrat kuma za ta zuba ido ta gani.
Sun ci sa'a me chamise d'in ya fito, ya yi mata allurar zazzab'i ya bata kuma magun guna, kud'i ya kama 1500 Nusrat ta bashi 2000 ya basu cangin 500 suka kamo hanya suka taho gida.
To Alhmdlillh sai jikin nata ya d'anyi sauk'i kad'an, har Nusrat ta had'a mata shayi me kauri ta sha, ganin jikin Maman ya yi sauk'i sai a sannan ta yi tunanin Shukhura har yanzu ba ta kirasu ba, amman gashi ta kira Umma sun gaisa, ta na cikin wannan tunanin sai ga Hidaya ta shigo tace mata tafiya zasuyi, amman zasu fara biyawa gidan Nimha da Shukhura in da sak'on da za'a kaiwa Shukhura a bada, kafin Nusrat ta mik'e ta bawa Hidaya sak'on sai wayar Hidayan ta yi k'ara sai Hidayan cewa ta yi.
"Kinga ma Shukhuran na kirana bari muji meye to. “
Ba ta jira me Nusrat d'in za tace ba ta d'aga wayar, ta can b'angaren Shukhura tace.
"Hello Hidaya kice a had'o mini duka akwatinana ku taho mini da shi.“
"To, shi kenan za'a taho da su, ga Nusrat za tai miki magana. “
Hidaya ta fad'a don ganin kallon da Nusrat d'in take mata, alamu ne na ta na son magana da 'yar uwar ta ta, k'ittt kike ji Shukhura ta kashe wayarta mamaki gaba d'aya ya kama su, a haka Nusrat ta shiga had'awa Shukhura duka akwatinanta da abubuwan da ba'a rasa ba, suka samo yara duk suka fita da su aka zuba a mota, kana sukai sallama da su Hidayan Nusrat tace.
"Ku gaishe mini da Shukhuran ku gaya mata Mama ce ba taji dad'i ba."
A tunanin Nusrat idan aka cewa Shukhura Mama ba taji dad'i ba za ta kira waya, in ma fishi take da ita ko tai mata wani laifin da ba ta sani ba ai ta kira layin Maman ta ji, amman har dare Shukhuran ba ta kira ba, ganin yadda duk Nusrat d'in ta bi ta damu yasa Mama tace.
"Bani wayata na kirata. “
Saboda tun d'azu Mama tace ta kirata tak'i, saboda ta na ganin kamar ta na da dalilin da yasa tak'i nemansu gara su d'an d'aga mata k'afa su gani. “
Ringin d'aya Shukhuran ta d'aga da murnarta tace.
"Hello Ma.......“
Cak taji maganarta ta tsaya ta kasa furta Maman da take buk'atar fad'a, Mama ji tayi gabanta ya yanke ya fad'i a hankula ta furta.
"Innalillahi wainna ilaihir raji'un.“
Kafin taji saukar kukan Shukhura a kunnenta.
"Shukhura lafiyarki kuwa?“
Cikin kuka tace.
"Nima ban san me ke damuna ba, daku na kwanta