Showing 42001 words to 42437 words out of 42437 words
Chapter 15 - KATANGA COMPLETE DOCUMENT By RABEE'AH SHU'AYB NABABA.txt
a raina da ku kuma na tashi, tun da mukai sallar asuba nake son kiran wayarku amman na k'asa, sai na ji ana rad'a mini a kunnena wai ke ba mahaifiyata bace, Umma ce mahaifiyata ko kuma ace su Yayarmu ba 'yan uwana bane Nimha ce kad'ai 'yar uwata, na san Yayarmu ta damu sosai amman wallahi ko muryarta ba na son jin, ina cikin damuwa zuciyata ta na mini zafi, da na san haka auren zai zo mini da babu abinda zai sakani yinshi. “
Ta na kawowa nan ta fashe da wani matsanancin kuka, Mama kuwa Innalillahi kawai take ambata a zuciyarta, yayin da Nusrat duk ta na jin abubuwan da Shukhuran ta fad'a, had'a kanta tai da guiwa ta fashe da kuka me ciwo, 'yar uwarta da take sonta fiye da son da takewa kanta yau itace ta furta ba ta son jin muryarta, me yake shirin tunkaro rayuwarsu ne, waye me buk'atar rusa Katangar farin cikin da suka dad'e da ginata a zuciyoyinsu?
Majina Shukhura ta jaa taci gaba da cewa.
"Mama kicewa Umma me mukai mata take son rusa rayuwarmu gaba d'aya, in wani abu mukai mata sai mu nemi yafiyarta, na san dai itace ta shiga tsakaninmu saboda da sassafe ita na fara kira na gaisar, bayan ko anan cikin gidan ba kullum nake gaisheta ba. “
Numfasawa Mama tayi tace.
"Umma ba ta isa ta miki komai ba Shukhura, ki saka hakan a ranki, babu wani abu wanda yake faruwa a rayuwa face dole sai da wani zare da ya haddasa hakan, kuma bama iya ganin zaren, shi wannan zaren shi ake kira ZANEN K'ADDARA.
Dan haka kada ki kuma danganta abinda ya same ki da wani d'an adam, duk abinda ya sameki to ki tabbata yana cikin k'addararki, ki kuma kai kukanki ga Ubangiji domin shi kad'aine zai baki ikon cinye jarabawar da yai miki har ya yaye miki abinda ke damunki, yanzu kije kiyo auwala ki d'auki qur'ani ki karanta za kiji sanyi a ranki, maza jeki, Allah yayi miki albarka, ki kuma daina wannan kukan.“
Muryarta can k'asa tace.
"Tom“
Mama ta kashe wayar ta lumshe idonta kana ta bud'esu akan Nusrat da ke gurshek'an kuka......
Jiya ba ku jini ba, chargi ne ban samu ba wutarmu ta lalace, gobe da jibi ba lallai ne ku jini ba saboda muna hidimar biki.
300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i.
0567838462
NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK
In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta.
09037093702
In katin wayane 400 zaku biya.
Allah ka k'arawa
mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin.
#N.W.A
#Team KTG
#Son so fisabilillah