Header Ads
Showing 27001 words to 30000 words out of 42437 words

Chapter 10 - KATANGA COMPLETE DOCUMENT By RABEE'AH SHU'AYB NABABA.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

tak'adiriyar yarinya irin Shukhura ba, Iya na cewa Nusrat 'yar aljanu ai Shukhura ce 'yar aljanu ba Nusrat ba.“
Maganar da Umma ta yi kaf a kunnen Shukhura suka sauka, wani murmushi ta yi a ranta tace.
'Allah ya had'amu za kwa kiyi kallon tak'adiranci.'
Kowa na gidan sai da ya shiga ya duba Iya, Nusrat da Shukhura a tare suka shiga duba ta, abinda ya bawa Nusrat mamaki ganin Iya ta kirata da Nusrat abinda tsawon rayuwarta ba ta tab'a kiranta da shi ba, sai dai ta kirata da Ai, ba ma za tace Ayshan ba, duk don Malam ya ji haushi.
Sannan kuma har suka fito ba ta sanyata aiki ba, kasancewar duk sanda ta shiga gurin ba za ta fito ba sai ta moreta ko ya ya ne, kuma ta na kallon Shukhura ta na ta sunkui da kai ta na matse dariya, shine da suka koma d'aki ta dubi Shukhuran tace.
"Wai dariyar me kike ta matsewa ne a d'akin Iya? “
"Yo ba dole na yi dariya ba, kinga kuwa goshinta kamar mulmuleliyar daddawa sai shek'i yake. “
Ta fashe da dariyar da ke cinta tun d'azu.
"Allah ban yadda da ke ba Shukhura, duk yadda akai ta dalilinki Iya ta ji ciwon nan. “
" To ni me ta mun da zan saka ta ji ciwo? “
Ta fad'a ta na d'an turo baki gaba.
"Kefe kika ce sai kin saka tsorona a zuciyar duk me takura mini, kuma yau kallon da Iya ta yi mini ya bam bamta da wanda ta ke mini a kullum.“
Rik'o hannuwanta Shukhura ta yi had'e da fad'in.
"Tabbas 'Yar baiwa ce ke Yayarmu.“
Kana ta shiga labarta mata yadda sukai da Iya ta na dariya, murmushi Nusrat ta yi tace.
"Tabbas Iya tai namijin k'ok'ari da ba ta sume miki ba, don in nice wallahi sumewa zan yi, a gaskiya kin d'au hak'k'in 'yar tsohuwa, don ta tsorata sosai tun da gashi ko labarin ainihin abinda ya faru ba ta bayar ba.“
"Wallahi ba wani hak'k'in ta da na d'auka, in hakane ita sau nawa ta na d'aukar hak'k'unanmu. “
Girgiza kai Mama ta yi, a kwance take duk a tunaninsu bacci take, duk abinda Shukhuran ta fad'a ta jishi, kuma ta na nemawa 'yar tata shiriya, don Baba yace da kansa zai dingai mata rubutu ta na sha, don abin nata ya fara yawa duk abinda akai mata tace sai ta rama ko ta halin k'ak'a.
"Kya ci gidanku, bari Babanku ya dawo sai na gaya masa, kuma ki tashi kije yau ke za ki mata shara ki wanke mata band'aki. “
Zunb'uro baki gaba tai ta mik'e, don in ba ta ta shi ba ta san Mama na iya jefo mata duk abinda ke kusa da ita, bayan fitarta Mama ta yi tunanin may be taje ta kumai mata wata muguntar don haka ta shiga k'wala mata kira kafin ta tashi ta bi bayanta.......







300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i.
0567838462
In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta.
09037093702
In katin wayane 400 zaku biya



Garab'asa gareku masoyana duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a layina muyi magana.






Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin.






#Team KTG
#N.W.A
[10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: *BEBE'ARTH*




Wattpad@Rashuna




*KATANGA*





____________
*FOUR*


Washe gari da safe misalin goma da rabi, zaune suke suna cin jolof in taliya a babban tray, kasancewar Baba ba ya nan ba a gida ya kwana ba kuma girkin Umma ne sai tak'i toya k'osai ta dama zallar kunu kad'ai ta bawa Nimha 200 ta siyo musu iya su da Iya kawai, wannan dalilin ne yasa Mama ta yi musu jolof in taliya saboda kunu kad'ai bazai rik'e cikinsu ba kuma Nusrat ba ta shan kunu sai koko.
Muryar Hidaya suka ji ta na k'wallowa Nusrat kira tab'e baki Shukhura ta yi bayan ta zuba taliyar a bakinta tace.
"Ga su shafi da mai nan an faso. “
Wata muguwar harara Mama ta jefeta da shi, kawai sai tai murmushi ta sunkui da kai, daga bakin k'ofa Hidaya ta tsaya, ta tsuguna har k'asa ta gaisar da Mama kana ta dubi Nusrat da ke kallonta ta na murmushi, ta yafitota da hannu had'e da fad'in.
"Kizo Yaa RJ ne ke kiranki, tsam Nusrat ta mik'e dama jikinta da hijabi saboda ba ta rabo da shi a jikinta ta bi bayan Hidaya suka fice Mama ta bita da idanuwa, Shukhura ce tace.
"Nifa Mama sai nake ganin Aunty Maryam kamar ba ta son Yaa RJ ya na kula Yayarmu.“
"Rufe mini baki ko na dakar miki shi da hannuna, na fa gaya miki ba na son irin magan ganun nan ko? Idan ma ba ta son ya kulata naga ta dalilinta duk kuka sanshi.“
"Yi hak'uri Mama, amma kuma in saboda kar wata alak'a ta shiga tsakaninsu ne to ta sha kurumunta in Allah ya yarda mijin Yayarmu ba daga tsatson mijinta zai fito ba ehe. “
Girgiza kai kawai Mama ta yi don zuciya ta kusa ciyota ta k'wala mata mificin da ke kusa da ita, zama Shukhura ta gyara had'e da gyara murya tace.
"Mamarmu nidai na gaji wallahi, ko yaushe sai ki dinga hanamu fad'a ana kuma k'wararmu, nidai wallahi idan Baba ya dawo zan kwashe duk abinda matarsa ke mana a gidan nan in gaya masa, haka kawai yanzu da ba dan muna da wannan taliyar ba sai dai fa mu zauna da yunwa har rana da ranar ma ba wani ishashh......“
Dakatawa ta yi da maganar sakamakon mificin da Mama ta rafka mata don taga hararar da take wurga mata ba za ta saka ta rufe mata baki ba sai ta had'a da duka, mik'ewa Shukhura ta yi ta na zunb'uro baki, ta figi hijabinta da ke kan k'ofa, ta na matsar k'wallar k'arya ta fice ta na.
"Wallahi na kusa yin maganin wata a cikin gidan nan.“
Ta fad'a da k'arfi yadda Umma da ke d'aki za ta jiyo ta.


Aunty Maryam na shiga d'aki ta tarar da Iya da kumburarran goshi.
"A'a Iya me ya sameki haka?“
"Zamewa na yi na fad'i na buge da bango. “
"To wannan karcewar ta gefen fuskarki fa?“
"Ke nifa ba na son tambaya, na gaya miki zamewa na yi na fad'i, me kuma kike son ji, kin wani titsiyeni kamar wata uwata sai kinji abinda ya sameni sai kace wani abu za ki iya a kai, mtssss. “
Taja tsaki taci gaba da sababi yayin da Aunty Maryam tace.
"Allah ya huci zuciyarki.“
Ta fice daga d'akin, in ba haka ba ba za ta daina sababin ba, ta shiga d'akin Umma don su gaisa.




A cikin mota Nusrat ta samu Yaa RJ, tun fitowarta yake sakar mata murmushi ta cikin gilashin motar har ta k'araso gaban motar, a bud'e murfin motar yake don haka ta shiga ciki ta zauna suka had'a ido da Hidaya da ta juya ta koma cikin gidan.
Shiru ne ya biyo baya sai kanta da ta sunkuyar k'asa ta na watsa da yatsan hannunta, yayin da shi kuma ya kafeta da idanuwansa, ya na jin wani sabon yanayi a kanta, ya san Nusrat yarinya ce ta yi k'ank'anta ya furta mata kalmar soyayya, amma ya na jin tsoron ya dawo ya tarar wani ya riga shi nasarar karb'ar soyayyarta, sanyin halinta, yanayin tafiyarta, yanayin maganarta komai ya yi dai-dai da yadda yake son matarsa ta kasance.
"Ina wuni Yaaya?“
Nusrat ta katse shirun da yake tsakaninsu ta kuma katse shi daga tunanin da ya tafi, rintse idanunwansa ya yi ya busar da wata iska mai sanyi saboda yadda muryarta ta shiga jikinsa ta zauna, wani siririn zoben azurfa ya ciro daga d'an k'aramin yatsan hannunsa.
"Muga hannunki. “
Zara zaran yatsunta ta mik'a masa ya zira mata a yatsanta na kusa da babban yatsa.
"Daga nan kaduna zan wuce ta nan jirginmu zai tashi zuwa Uk nan da shekara uku zan kammala karatuna na dawo, ki mini alk'awari ba za ki bawa ko wani saurayi damar k'ulla soyayya da ke ba. “
Ba ta gane inda maganarsa ta dosa ba, don haka ta tsira masa idanuwanta kamar me karantar amsoshin tambayoyin da ke dank'are a zuciyarta, yayin da shi kuma yake jin kallon da take masa har tsakiyar zuciyarsa.
'Meye dalilin da yasa ka bani zobe, me yasa zan maka alk'awarin k'in kula ko wani saurayi bayan ba ni da tabbacin sona kake,
idan ma sona kake anya auranmu zai yuhu kuwa, kana ganin Aunty Maryam za ta bar Katangar alak'ar da take ginanna a tsakaninsu taci gaba da ginuwa?'
Wa'yannan tambayoyin sune cunkushe a ranta amman ta k'asa furta ko da kalma d'aya, ji take bakinta yai mata matuk'ar nauyi.
Hannunta ya matsa had'e da fad'in.
"Pls Nusrat. “
Tsintar kanta kawai ta yi da d'aga masa kanta, ya saki kyakkyawan murmushi, ya d'auko wata leda ya d'ora a kan cinyarta.
"Na gode Nusrat, Allah ya baki ikon cika mini alk'awarina, bari ni zan wuce, ki gaida mini da su Mama. “
"Za su ji insha Allah, Allah ya kaika lafiya, ya kuma baka sa'a akan karatun naka.“
"Aminnnnn“
Yace yana me jin dad'in addu'arta yayin da ita kuma ta fice ba tare da ta d'au ledar da ya ajiye mata ba, murmushi ya yi don ya san za'a rina, a dai-dai lokacin Shukhura ta fito ta na zunb'uro baki, da hannu ya yafitota tazo gareshi, d'an risinawa ta yi ta gaisheshi yace.
"Ga leda nan d'auki ki kaiwa Mama kice ina gaisheta.“
"Tom, an gode. “
Ta d'auki ledar shi kuma ya ja motarsa yai gaba.






_RIDWAN JIBRIL shine cikakken sunansa yayin da ake masa inkiya da RJ, mahaifinsa da Yusuf mijin Aunty Maryam uwarsu d'aya ubansu d'aya, mahaifinsa ya rasu tun ya na yaro a gurin mahaifiyarsa yake da take aure a kaduna, tun bayan auran Yusuf da Aunty Marya ya d'auko RJ ya dawo gurinsa da zama suka rik'eshi tamkar d'ansu na cikinsu, bayan gama karatunsa na_ _secondary ya turasa Uk acan yake had'a karatunsa a fannin jarida._
_Hidaya da Nusrat tasu tazo d'aya sosai, suna k'aunar junansu hakanne yasa Nusrat take yawan zuwa hutu gidansu, yayin da shak'uwa me k'arfi ta shiga tsakaninta da Rj, har ta rikid'e ta koma soyayya a zuciyar RJ, idan har zaije kaduna gurin mahaifiyarsa sai ya fara tsayawa gurin Nusrat ya yin da k'arara Aunty Maryam ke nuna ba ta son alak'arsa da Nusrat saboda akwai wani buri da suka ci a kansa ita da mai gidanta._






Kwata² Shukhura tak'i yadda ta shiga ko gurinsu, ta na filin babban tsakar gida a zaune ta na dakon zaman jiran Baba ya dawo, don kada ma Mama ta hanata aikata abinda tai niya, ledar da RJ ma ya bata a bakin k'ofar d'aki ta ajiye ta fito don duk kada Mama ta ruguza mata shirinta, ta san dai duk tsiya Baba bazai wuce 12 na rana bai dawo ba saboda ba a gida ya kwana ba.
Har kusan k'arfe d'aya Baba bai shigo cikin gidan ba, har ta fara tunanin tashi ta jiyo takun tafiya don haka ta maida idanuwanta kan k'ofar shigowar, aikuwa Baban ne ya yi sallamar ta amsa masa ta nufeshi had'e da d'ora damuwa akan fuskarta, har da fara taro k'walla, gaban Baba ne ya yanke ya fad'i yace.
"Lafiya Shukhura me ya faru? “
"Baba.“
"Na'am fad'a mini me ya faru? “
"Dama kullum Mama ce ke hanani gaya maka.“
"Ina jinki.“
"Duk ranar girkin Umma ba ta bamu abinci ishashshe, da kai da Iya da su ta ciccika muku kwano, kuma har d'anye take ragewa ta b'oye, to yau da safe ba ta toya mana k'osai ba zallar kunu kawai ta dama, ta bawa Nimha ta sayo musu su da Iya. “
Ran Babane ya yi mugun b'aci, ya tabbata Shukhura ba za tai masa k'arya ba, shafa kanta ya yi yace.
"Jeki ciki zanwa tufkar hanci. “
Cike da murna ta shige ciki ta na jin kamar ta sauke abu me nauyi a zuciyarta ko kad'an ba ta damu da hararar da Mama ke ta zabga mata ba.


Sai da ya bari Umma ta gama girki ta raba kowa ta kai masa shima ta kawo masa nasa sannan ya k'wallowa Shukhura kira, ta amsa ta fito da saurinta.
"D'auko mini abincinku.“
"Toh."
Tace da hanzari ta juya ta d'auko.
"Jeki ki anso mini na Iya. “
"Ai yau Iya ba ita kad'ai bace su Aunty Maryam sun zo. “
"Af na sha'afa, da na shiga gurin Iyanma mun gaisa, bar na tan. “
Ya dubi Umma yace "D'auko mun naku, kuma bance ki rage komai ba, inma kin rage da kaina zanzo na duba.“
Tsuru² Umma ta yi da ganinta ka san ba ta gaskiya taje ta d'auko ta kawo masa duban Shukhura ya yi yace.
"Je ki d'aki, ki turo mini Mamanku. “


Shukhura na barin gurin Baba ya dubi Umma yace.
"Yanzu wannan adalci kenan? Kalli abincin da rai d'aya zai ci, ki dubi na rai biyu duk sun taka wanda rai hud'u zai ci kinwa kanki adalci? Ko iya Nimha kad'ai ai sai ta tashi da wannan abincin, idan ni ba na gani ai Allah ya na ganinki kuma hakk'insu bazai tab'a barinki ba. “
Fad'a sosai Baba ya shiga yiwa Umma kamar zai ari baki, ya shaida mata muddun ta kuma irin rabon nan to sai ta bar masa gidansa, Mama da tazo fad'an ya rufe ta da shi akan me za ta hana a gaya masa irin haka na faruwa a cikin gidansa ya d'au mataki tunda ita ba ta gaya masa ba, ita dai Mama hak'uri ta bashi don sosai Baba ransa ya b'aci, ranar huni ya yi ya na surfawa Umma fad'a, abincinma ya yi zuciya ya k'i ci ya juyewa su Shukhura akan nasu na su Umman ma ya datsi rabi ya k'ara musu akai ya kira Shukhura ta d'auka, Umma kuwa sai huci take kamar ta janyo Shukhura tai ta jibgarta.










_____________
Bayan sati guda Baffa Shamsu yazo garin zariya, a lokacin su Aunty Maryam sun koma kwana uku sukai suka tafi.
Transfer yake nema zai dawo zariya gaba d'aya hakanne yasa yazo don neman gidan da zasu samu su zauna, duk da nan kusa da gidansu an masa tallansa to dai ya na son siya amman dai ba su gama cininki ba, tun zuwansa Iya tace.
"Nidai yau aradu shinkafar gwamnati zanci, don wallahi na gaji da cin shinkafar hausa ina karo da tsakuwa ta na farfasa mini hak'ori, kalli nan kaga yadda duk hak'orina ya farfashe, don haka ma ni wallahi in za ka tafi binka zan, don na gaji da cin tuwon masara kullum da daddare na kwanta, gara a dinga dafa mini taliyar nan ta gwamnati me dad'in gaske.“
Murmushi kawai Baffa Shamsu ya yi yace.
"Haba Iya ba na son kina irin wa'yan nan
magan ganun kema dai kinsan Yaya yana matuk'ar k'ok'ari, idan yaji abinda kike cewa bazai tab'a jin dad'i ba.“
"To kar ya ji dad'in mana ni ina ruwana, wani k'ok'ari yake banda son 'yarsa da ya fifita a kaina. “
Ko me ta tuna kuma sai tai shiru kana tace.
"Mubar ma maganar d'an arzik'i maza je ka siyo mana shinkafar, ka kuma siyo mana kaji don yau mu d'an wasa bakinmu, don rabona da ci nikam ina jin tun kan rasuwar Malam. “
Girgiza kai kawai Baffa Shamsu ya yi ya na mamakin halin mahaifiyar tasu sam ba ta da godiyar Ubangiji, duk zuwan da zaiyi sai sunci kaji a gidan, haka zalika Baba ma idan ya ji aljihunsa da nauyi ya na siyo musu su ci amma wai kunji rabonta da ci tun kan rasuwar Malam.


Buhun shinkafa biyu da katan na taliya da macaroni biyu Baffa Shamsu ya siyo musu ya ajiye su a d'akin Mama, ya siyo musu kaji guda biyar manya ² gashi kuma aka taki sa'a girkin Umma ne, don haka Shukhura ta na da 1000 tace bari taje titi ta siyo don ta san 'yar kad'an za'a sanmusu, Nusrat ma na da 1000 sai ta bata ta siyo musu guda biyu kuma manya da su.
Ilai kuwa cinya d'aya fukafiki aya sai wuya aya aka saka musu, ko kad'an ba su damu ba Shukhura ta wanke nasu ta tafasa ta fara suya.
K'amshin suyar naman Iya ta ji a ranta tace kaddai matar nan ragewa ta yi take soyawa da hanzari ta fito don ta ganewa idonta, ganin Shukhura ce me suyar ta kai hannu za ta d'auka a cikin wa'yanda ta kwashe, Shukhura ta yi saurin d'auke robar hannun Iya ya sauka a k'asa har sai da ya yi k'ara tace.
"Auchhhhh“
Don ta ji zafi sosai, Shukhura kuwa ko a jikinta ta murgud'a baki tace.
"Ai ba taku bace, wannan tamu ce naje na siyo, da za ki d'auko yamutsats tsan hannunki ki saka mini a ro....“
Ba ta k'arasa ba taji saukar mari a kuncinta, dafe kuncin ta yi ta tsaya ta na kallon Mama da ta fusge robar naman a hannunta ta d'auki cinya manya² guda biyu ta bawa Iyan, sai da Iyan ta ansa kana ta tab'e baki.
"Ai da ba ki daketa ba ai na san duk makirci ne irin naki, ke kitsa mata dukkan abinda takeyi a gidan nan, amma ai Shamsu yazo zai mini maganinta. “
Ta na kawowa nan ta fice daga gurin Shukhura ta bita da d'an iskan kallo, Mama ba ta iya cewa komai ba ta koma d'aki Shukhura ta k'wallowa Nusrat kira.
"Yayarmu zo ki kama mini na shiga band'aki. “
Nimha tace.
"Kawo na miki kan ki dawo. “
"Don aji dad'in d'iba akai d'aki ba, a'a basshi na gode ga Yayarmu nan za ta ansa. “
Umma ta gallawa Nimha harara.
"Maganin shishshiginki kenan

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads