Showing 6001 words to 9000 words out of 9428 words
Chapter 3 - AUREN YARINTA By Khadija s dogarai (lipton girl) .docx
Amsa ya fara kora ma bakin shi yana hadewa bai ida hadiye sauran ba ya tuda shi
Kallon shi taki ye "lafiya meki damun ka meyasa ka tuda zobon baka sha ba"
Tashi yayi tsaye ya reki cikin shi sai kokarin ye amai yaki a dadafe ya hau sama yana taure ya reki cikin sa har ya kai dakin shi Amai yayi mai yawa sai da ya gama ya dawo kan gado yana mai da nunfashi
Wanan wani irin hauka ni abinci ko mutuwa......!!!!
Abun ba karamen bata mamaki yayi ba meyasa ya wuce yana kokarin Amai....?
Haura wa tayi sama ta shiga dakin shi,
Shikuwa yana kwance kan gadon shi sai mai da nunfashi yaki ye
Reki kugu tayi ta fara zazaga masa masifa
"Wanan wane irin iskan ce ni zan dafa maka abinci kazo nan ka kwanta duk uban wahalar da na sha oyah ka tashi muje kace ko na kawo maka shi nan"
Tashi yayi yana fuskan ta Ta
"How dare you... Waya baki izinin shiga man kitchen "
Sakin baki tayi tana kallon i kon Allah
"Kaji ka da wata magana ae ba maza aka sani da kitchen ba mata aka sani don haka nayi maka girki ka tashi muji ka karasa"
"No way. Bazan ce wanan kazamin abinci ba"
"Eh lalai Yaya Aziz ka rama mutani ni zaka ce ma haka"
Nuna ta yaki ye da yatsa
"Ki fita man daga daki idan ba haka ba zaki jiya a jikin ki"
Ita kuwa daman akwai ta da saurin fushi fita tayi daga dakin ta rufe masa kofa gam....
Dakin ta tashiga ta saka lock sai fada taki ye ita ka dai
Har dare yayi bata fito ba
Fridge inda ki cikin dakin ta. Bude ta dauki jus ta hada da biskit sallah tayi ta kwanta bacci mai dadi yayi awon gaba da ita
Washe gari..... A hankali taki bude idon ta saukowa tayi kan gadon ta sai meka taki ye gurin labude ta nufa ta bude ganin safiya ta waye yasa ta ji dadi lumshe idon ta tayi taja wani dogon nunfashi beautiful day ta furta
Nan ta shireri ce daman aikin ta kinan idan safiya ta waye tayi tsaye tana shakar iska mai dadi daga bisani ta watsa ruwa dakin Aziz ta shiga
Kallon shi taki ye yanda yaki baccin sa hankali kwance zugum tayi tana kallon shi wani abu ta tuna da shi tayi murmushi ta koma dakin ta da gudu banga abunda ta dauko ba ta koma dakin shi hawa tayi kan gado tana ye masa wani abu.. Dariya ta kamaye ta fita daga dakin
Nasan duk fushin ka idan ka tashi yanzu zaka dai na
Kwanan shi yaki ye cikin kwanciyar hankali.. Wayan shi ni tayi ringing reject yayi domin yana jin dadin baccin da yaki ye saki kira aka ye karamen tsoki ya ja wai wanan wanini ya ki kirana cikin daren nan
Dago fuskan shi yayi ganin haskin da ki cikin dakin shi yasan gari ya jima da waye wa
Dauka yayi yah ni
Banji abunda yace masa ba yace ya bashi 2mnt ga shinan saukowa
Sauka yayi kan gadon shi yana nishi guda guda.
Har zai shiga toilet ya watsa ruwa kuma sai ya fasa don baya son ya karya alkaware yace nan da 2mnt zai sauko kuma yasan idan ya tsaya wanka zai jima sosai haka ya fita dakin shi Tun a sama ya hango su sunkai su 15 waton abokan shi suna zauni kan kujera ko wanin su reki da cup in jus Nafisa kuwa sai murmushi taki ye masu
Kallon ta yayi "I hope bata lalata masu abun sha ba"
Abokinan da ya hango shi sama ya meki tsaye yana bugun na kusa da shi duba ango guda guda suka fara tashi sun ka saki baki suna kallon shi har ya karaso kusa da su kallon su yaki ye
"What happen meyasa kuki ye man wanan kallon kamar kun ga dodo"
Nafisa kuwa ba abunda taki ye sai dariya.
Kallo daya yayi mata ta saida dariyan ta.
Dukan su suka saka dariya. Aminu kuwa har kasa ya kai yana dariya..
Kallon shi yayi
"Meye abun dariya a ciki pls saje up"
Tashi yayi.
"Tell me what wrong with my face....!
Jan shi yayi har gurin dinner area gurin da aka laka mirrow ya kai shi ya nuna masa.
Wani ihu ya buga dukan su sai da suka razana dukan su sukaye shiru
Nafisa kuwa bata san lokacin da ta saki dariya ba
Karasawa yayi kusa da ita
"How dare you???
Murmushi tayi "Yaya Aziz kaga yanda kayi kyau kuwa kaga nayi maka gira na shafa maka eye shadow ji yanda bakin ga yayi kyau da na shafa maka jan baki ga blush so beautiful da mace kaki da kayi kyau sosai.. Shiyasa aki cewa soyaya dadi ae wanan duk cikin soyaya ni"
Bai san lokacin da ya daga hanu ya wanka mata mare ba sai da ta kai kasa
Aminu ya yo kan shi
"Aziz kana da hankali kuwa? Matar ka zaka mara"
"Enought Aminu bana son jin kome let me fresh up"
Haurawa yayi sama Nafisa kuwa ga kunya ga zafin mare da Aziz yayi mata kuka taki ye sosai dukan su sun tausaya mata tashi tayi ta dauko Hijab inta ta fita daga gida.......
*Tofa ko ina Nafisa zata ji muje zuwa*๐ถ๐ปโโ
Auren Yarinta
Writing by
*lipton girl*๐ฅค
[12/17, 3:13 PM] ๐lipton girl๐: *AUREN YARINTA*
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
*Daga Alkalamen*โ๐ป
*Khadija s dogarai (lipton girl)*๐ฅค
*A short story*๐น
*~โ๐ฝโ๐ฝGOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONโ๐ฝโ๐ฝ~*
*~We are bearer's of so golden pen๐~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden penโ,behold our words.~*
*~A product of our pen๐,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*Addu'a Idan Ya Sauka A wani masauki a Halin Tafiya ko waninta.*
ุฃ
ู
ุน
ู
ูุฐ
ู
ุจ
ู
ู
ู
ู
ู
ู
ู
ุงุช
ู
ุงูู
ูู
ู
ู
ุงูุช
ูู
ุงู
ูู
ุงุช
ู
ู
ู
ู
ู
ุด
ู
ุฑ
ูู
ู
ู
ุง
ุฎ
ู
ู
ู
ู
ู.
A'oothu bikalimatil-lahit-tammati min sharri ma khalaq.
Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga sharrin abin da Ya halitta.
*Dedication*
๐๐ป
*HK nayi missing in ki over*๐๐๐
๐คPage 12&13.... ๐น
ยฐยฐยฐยฐYa kusan awa daya yana bathroom, da kyar ya samu ya goge kwalliyan da tayi masa, ranshi ba karamin bace yayi ba, shi yasa auren yarinta ko hauka baiyi ba, yarinya zata mai dani mahaukaci wanda bai san abunda yake nufi ba, bazan dauki wannan iskan ci nata ba zan gyara mata zama.
Kaya ya saka ya sauka inda ya tarar da abokan shi suna zaune suna jiran sa sai firan su suki ye.
Guri ya samu ya zauna, Muktar ya kamayi masa dariya.
"Mijin Yarinya har an fito".
Watsa masa harara yayi.
"Sorry".
Cigaba da hira sukayi.
Daga bisani suka koma gidajen su.
Muktar ne ya tsaya suna magana da shi.
"Amm... Aziz abunda kayi sam bai kamata ba. Kasan me idan ni ni matata tayi man haka ba zan yi mata yanda kayi mata ba imagine, marin ta fa kayi kuma a gaban friends dinka idan kai baka ga mutuncin ta ba taya mu zamu ga nata??
"Pls bana son surutun banza kayi tafiyar ka".
Murmushin takaici yayi.
"Ni Babban abokin ka ne dole na gaya maka gaskiya meyasa ba zaka karbi destiny din ka ba she is your wife kama ta yayi ka bata kulla wa ka nuna mata soyaya i know she is too young but kai ya kamata ka koya mata wasu abubuwa pls try to understand me kaga yanzu bata nan and baka ma tambayi ina taje ba baka ganta ba kasan ta fita gidan nan kuwa tana kuka only God know inda taje pls ka kwantar da hankalin ka. Ka fahimci abunda nake nufi ka zauna ka ba matar ka kulawa ka daina banzan tunanin da kake yi na barka lafiya"
Tafiyan shi yayi Ya shiga mota bai tsaya ko ina ba ya tarar da mom din shi zaune tayi zugum.
Karasawa yayi kusa da ita ya zauna a kasa.
"Mummy lafiya? Ya naga kamar kina cikin damuwa meke damun ki pls tell me kin san bana son abunda ya taba ki"
Murmushin karfin Hali tayi.
"Allah yayi maka Albarka son ina son kayi aure ni".
Zaro ido yayi "Aure kuma mummy meyasa kika yi wannan tunanin ni fa bani da wace naki so i am alone so taya zanyi aure"??
"Nayi maka kamen mata".
Juyowa yayi don ko ba'a gaya masa ba ya san gwaggon shi ce tashi yayi ya karasa kusa da ita har kasa ya kai ya gaidata.
"Sannu da zuwa Gwaggo yaushe kika karaso?".
Fuskanta dauke da murmushi.
"Yauwa.. Banjima da iso wa ba".
Hanunta ya rike ya kai ta kan kujera ta zauna.
Gyaran murya yayi.
"Nayi maka kamen mata waton yar uwarka Suhaila ".
Kallon mamaki yake yi.
"Gwaggo Suhaila fa kika ce".
"Eh kuwa. Ina fatan bazaka bijire ma magana ta ba".
Mummyn shi kuwa kokarin magana take yi ta dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu.
A kasalance yake magana.
"Amma Gwaggo naga ai Suhaila yarinya ce ba zata wuce 14years ba kuma kike ce wa na aure ta?".
"Sosai kuwa to meye in yarinya ce Mace ce fa ko shekara 10 ana iya yi mata aure kuma lafiya lau ta haihu bale 14".
Yaji kunyar maganar da tayi.
"Tau gwaggo ba damuwa amalma ni ban shirya ma auren yanzu ba saboda akwai abubuwa da yawa da akeyi kafin akawo Amarya".
"Na riga da nayi magana da Daddy din ka kuma ya yarda kawai za'a kawo maka Amarya".
"Tau gwago Allah ya bamu zaman lafiya. Ki huta lafiya".
Ya tashi ya shiga dakin shi.
Mummynsa kuwa bata ji dadi ba don taga ana yi ma dan nata auren dole.
*****
Nafisa kuwa bata tsaya ko ina ba sai gidan su Aziz tun a bakin kofa ta kara bude muryar ta.
Falo ta tarar da Dad din Aziz yana ganin ta hankalin shi ya tashi.
"Nafisa lafiya meya same ki? Meyasa kike kuka?".
Karasawa tayi kusa da shi tana kuka tana shesheka.
Kwallawa mom Aziz kira yayi.
"Hajiya salamatu kina ina maza kiyi sauri ki karaso".
"Ina zuwa Alhaji".
Ajiye kayan da ta dauko tayi da sauri ta karasa falon.
Ganin Nafisa na kuka abun ya bata mamaki.
"Nafisa meya same ki haka? ".
"Nima dai tun dazu nake tambayar ta bata ce man kome ba ki tambaye ta ki jiya ko zata gaya maki".
Jawo hanunta tayi ta zauna da ita kan kujera ruwan da ke gefenta ta bata ta sha tana sha tana saukar da numfashi.
"Gaya man diyata meya same ki?".
"Nafisa meya same fuskan ki haka kamar kwanciyar mari...."!!
Fadan Daddyn sa.
Mom kuwa abun ya bata mamaki.
"Ki gaya mana kinga hankali mu ya tashi sosai pls gaya man".
Cikin muryar kuka tace.
"Yaya Aziz ne"
Tare suka ce.
"Aziz meyasa yayi maki haka?".
"Uhmm...Amm. Mari na yayi kuma a gaban Abokan shi".
Alj. Sanusi ya zauna kan kujera dafe kan shi yayi.
Hajiya salamatu kuwa ta rasa wa za tayi lallashin sa ka Nafisa kuma ga Alj.
"Alhj. Dan Allah kada ka tayar da hankalin ka kasan kana da hawan jini kamata yayi mu kira Aziz din yayi mana bayani da kan shi saboda ba zamu yanke hukunci ba akan abunda bamu sani ba na san Aziz ba zai mare ta ba bata re da tayi masa wani babban abu ba"
Wani irin kallo yayi mata.
"Salamatu me kike nufi da hakan? Yanzu fisibililahi don tayi masa wani abu sai ya dauki hannu ya mare ta duka-duka kwana nawa da auren da har zai fara dukan ta ban aura masa ita ba don ya mai data jaka ba Aziz ya bata min rai yau matuka muddun zai rinka taba Nafisa zai rinka fuskantar fushi na!".
"Kayi hakuri Alhj. Ka kira shi ya zo".
"Ba zan kira shi ba. Idan ke zaki iya sai ki kira shi".
Tashi tayi ta dauko wayan ta kiran shi tayi amma bai daga ba...
Shikuwa wayan shi tana kusa da shi amma bai ji lokacin da tayi ringing ba maganar Muktar kawai ya tuna da ita kawar da zancen yayi.
"Dole naje na nemo ta ko bana so domin in dad ya san bata nan nasan rai na zai bace. To ina zan nemo ta? Bari naje gidan su na san can taji"
Wayan shi ya dauka ya fara hanya wayan shi ni tayi kara ganin mom in shi gaban shi ya fadi.
Ko dai Nafisa tana can?
Daukan waya yayi ya kara a kunnen sa.
Tun bai yi magana ba tace masa.
"ka same ni a gida yanzu duk abunda ka ki ye ka ajiye shi ka zo".
Ta kashe waya.
Gaban shi yana faduwa uku uku ya shiga motar shi ya nufi hanyar gidan su....
*lipton girl*๐
[12/17, 3:13 PM] ๐lipton girl๐: *AUREN YARINTA*
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
*Daga Alkalamen*โ๐ป
*Khadija s dogarai (lipton girl)*๐ฅค
*A short story*๐น
*~We are bearer's of so golden pen๐~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden penโ,behold our words.~*
*~A product of our pen๐,savour our words, for it will cause you no pain.~*
Addu'a Idan Ya Sauka A wani masauki a Halin Tafiya ko waninta.
ุฃ
ู
ุน
ู
ูุฐ
ู
ุจ
ู
ู
ู
ู
ู
ู
ู
ุงุช
ู
ุงูู
ูู
ู
ู
ุงูุช
ูู
ุงู
ูู
ุงุช
ู
ู
ู
ู
ู
ุด
ู
ุฑ
ูู
ู
ู
ุง
ุฎ
ู
ู
ู
ู
ู.
A'oothu bikalimatil-lahit-tammati min sharri ma khalaq.
Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga sharrin abin da Ya halitta.
*Dedication*
๐๐ป
*HK nayi missing in ki over*๐๐๐
๐คPage 14&15.. ..๐น
ยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐGabanshi yana duka uku uku ya shiga motar shi ya nufi hanyar gidan su.
Yana zuwa yayi horn mai gadi ya wangale mishi gate,guri ya samu yayi parking ya fito a bude ya bar motar ya shiga cikin gidan a falo ya same su, ganin Nafisa yayi mom din shi sai lallashin ta take yi.
Guri ya samu ya zauna.
"Barka da wuni Dad".
"In ban wuni ba zaka ganni?".
Dagowa yayi ya kalli Dad din shi ko ba'ayi masa bayani ba ya san ranshi a bace yake.
"Allah ya huci zuciyar ka".
"Aziz bana son iskanci yanzu fisibilillahi haka kawai zaka dauki hannu ka mare diyar mutane!".
"Haba Alhj. Meyasa bazaka tambaye shi ba sai ka hau shi da fada, ehmm!".
"Hajiya wannan wane irin magani har sai an tambaye shi. Ai tunda ki ka ga ya mare ta to a cikin hankalin sa yayi amma tunda kince haka kayi mana bayani meyasa ka mare ta?".
Sunkuyar da kan shi yayi kasa yana sosa kan shi kamar wanda yayi karya.
"Uhmm.. Amm. Dad.. Daman.... "
Nuna shi yayi.
"kin gani daman nagaya maki ba abunda zai ji haka kawai don jin dadi ya mare ta".
"A'a Dad laifi tayi min".
"Don tayi maka laifi sai ka daga hannu ka mare ta? Shekara na nawa da Mamar ka ka taba ganin ko a mafarki na daga hannu na da sunan in buge ta??".
Girgiza masa kai yayi.
"To meyasa baza