Header Ads
Showing 9001 words to 9428 words out of 9428 words

Chapter 4 - AUREN YARINTA By Khadija s dogarai (lipton girl) .docx

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

kayi hakuri ba. kasan da cewa dukan mace ba kyau ko?".

"Ayi hakuri Dad ba z'a sake ba".

"Alhj. Ni na so ka bariyayi bayani meyasa ya mare ta don da na san ba karamin abu bane".

"Bisimillah zaki iya tambayar shi".

"Son ka gaya min meya faru?".

"Amm... Mom ina bacci tayi min kwalliya yanda kin ka san aljani kuma ta san da cewa abokaina sun zo ta kyale ni suka tayi min dariya abun ya bata min rai shiyasa na mare ta".

"Ka gani ko wannan wane irin iskanci ne?".

Fadan Dad din shi.

"Shikenan don tayi maka kwalliya sai ka mare ta kuma a gaban abokan ka? Wai meke damun ka ne baka san soyayya ba, yarinya ce fa dole sai kayi hakuri da ita".

Dagowa yayi ya kalle ta ya saka mata wata harara murguda masa baki tayi ta cigaba da wasa da hanunta.

"Amma dad....".

"Yi min shiru bana son jin shirmen ka. Maza ka dauki matar ka ku bani waje!".

"Allah ya baka hakuri insha Allah zan kiyaye".

"Nafisa ki tashi ki bishi kinji kiyi hakuri".

Mikewa tayi tsaye tayi masu sai anjima suka nufa gurin motar shi.

Dad ya biyo bayan shi.

Shiga yayi ya rufe mota ita kuwa tayi tsaye.

Har zai tada mota yaga bata shiga ba.

Horn yayi mata alaman ta shigo su wuce, amma tayi kamar bata ji sa ba.

Ganin Dad din shi yayi ya daure fuska ba don ranshi ya so ba ya fito daga motar bude mata kofa yayi.

Ita kuwa ta shiga tana jin dadi. Da karfi ya rufe mota sai da ta razana. Zagayo wa yayi ya tada mota fuuuu......

******

Muktar kuwa tunda ya shiga dakin sa babu abunda yake tunawa sai abunda Nafisa tayi ma Aziz shima haka za'aye mai?

Kawar da zancen yayi ya san suhaila bazata yi yarinta irin ta Nafisa ba.

Ko ya za'ayi auren a ranshi ya nasa ba zai yi ma Suhaila yanda Aziz keyi ma Nafisa ba.

***

Tunda suka fara hanya ba wanda yace ma wani kala sai wasa take yi da Hannunta.

Shikuwa ranshi a bace don ta rame shi ta saka shi cikin kunya kuma tazo ta kawo karan shi??



~lipton girl~💙

Ads At the End of Article
2
3
4

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads