Header Ads
Showing 9001 words to 12000 words out of 14992 words

Chapter 4 - GWARZON SADAUKI book complete by abdul'aziz Sani Madakin Gini

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

tun tsawon shekaru bakwai baya amma mun kasa Gadaraz shine mutumin da zai tai maka mini na sami lagon sarki Marhat, na sata amarya Sulaisa daga hannun sarki Marhat shi kuma Gadaraz va saketa daga hannunsa na mayar da ita wajen marhat matar Gadaraz wato jaruma Ilaila itace kadai wadda tasan inda littafin sarki Marhat yake kuma itama ta manta inda yake, amma zata iya tunowa idan wani abu ya faru makanancin wanda ya bata labari inda aka ya boye littafin. Ya zama wajibi nayi gagarumin shirin yaki nabi bayan su Gadaraz ba tare da sun san da cewar ina biye da su ba har sai sun đanko wannan littafin daga nan naje na yaki sarki Marhat
na kasha shi na mallaki kasar sa, dukiyarsa dama amaryarsa sulaisa, matsala ta guda daya ce yanzu, gobe daura aurensa da Gimbiya Sulaisa lallai ina son na tsayar da wannan daurin auren domin bana son ya kwanta da ita kafin na gama dashi, lokacin da sarki Zamral yazo nan a jawabinsa sai fadar tayi tsit aka rasa wanda zai kala. Daga can sai wazirin sarki zamral yayi gyaran murya ya dube shi yace ran sarki ya dade ai wannan abu ne mai sauki, kawai rundunar yaki zaka tasa ta isa kofar birnin misra a gobe da sassafe a aikawa sarki Marhat takardar yaki, kaga kenan batun bikin aurensa ya rushe tunda tashin hankali va zo sannan kai da wasu dakarun daban sai kabi bayan su Gadaraz a sirrance. Koda jin wannar shawara sai sarki Zamral ya sake bushewa da dariyar farin ciki sannan ya dubi wazirin sa yace tabbas duk wanda yariga ka kwana dole ne ya riga ka tashi wannan shine amfanin zama da manya, ga shi a cikin kankanin lokaci ka bani shawarar da itace kadai mafita. Sarki zarmal ya dubi sarkin yakin sa dake tsaye a gefe guda yace ya kai dirka birnin kisira maza kaje ka shirya dakarun yaki kaso biyu, kaso na farko kaine zaka jagorance su izuwa kofar birnin misra ku vaki Sarki Marhat kaso na biyu kuma ni zan jagoran ce su Mubi sahun su Gadaraz sarkin yaki Darkis yace angama ya shugabana.
A can daji bayan su Gadaraz Sun gama yarjejeniya akan dayansu bazai ci amana ba sai Gadaraz ya dubi Ilaila yace lokacin da kina yarinya karama wane abu kika fiso, kuma wane abune yafi baki tsoro?
Koda jin wannan tambaya sai mamaki va kama Ilaila ta dube shi tace saboda me kayi min wannan tanbayar?
Gadaraz yace dole a cikin wannan abubuwan guda biyu zaki iya tuno labarin da mahaifin ki ya baki dangane da inda aka boye Iittafin sirrin sarki Marhat. Ilaila tayi shiru tana tunani har izuwa tsawon yan dakiku sannan tace a rayuwa ta ina son hawa tsauni da shiga cikin kogon duwatsu abin da yafi bani tsoro a cikin wannan duniya shine nayi arba da aljani ko dodo mummuna. Gadaraz yace da kyau mun sami mataki na farko na ga0e inda zamu sami wannan littafin, dole ne muje inda kogon duwatsu suke da kuma tsaunika mu shigesu mu kuma hau kansu, wannane kawai hanyar da zai sa ki tina inda aka ajiye littafin sirrin da muke nema, tabbas inda aka ajiye littafin aljanu
da ko dodanni ke gudinsa. Ku sani bamu da wani isashen lokaci don haka kuzo muyi sauri mutafi izuwa wannan wurare. Gama fadin hakan keda wuya sai Gadaraz ya mike tsaye ya kama dokinsa ya hau, cikin sauri sauran yarana masu shigar bakaken tufafi kimanin su dari suka yi koyi dashi, ai kuwa sai Insam, Barsad da Ilaila suka mike suka kamo nasu dawakan suka hau aka dunguma gaba daya aka nausa cikin daji. Gadaraz ne akan gaba yana yi masu jagora.
Al'amarin sarki Marhat na binin misira kuwa ashe kifi na gani ka mai jarkoma. Duk abubuwan da suka faru a fadar sarki Zamral da wanda suka faru a daji tsakaninsu Gadaraz sarki Marhat ya gani a madubin tsafinsa, don haka sai ya kyalkyale da dariyar farin ciki. Lokaci guda sai yace ai ni murucin kan dutsene ban fito ba sai da na shirya, tabbas sarki zarmal yayi kuskure da kake tunanin cewa zaka iya yaudarata da yaki sannan ka tafi izuwa inda littafin sirrina yake ka dauko shi, duk da cewa nima kaina bansan inda littafin yake ba amma ai gashi a saukake za'a kaini inda yake, naga ta yadda ko su Gadaraz zaku iya mallakarsa alhalin ina wajen. Koda gama wannan batu sai sarki Marhat ya tura aka kirawo sarkin yakin birni nasa mai suna sadauki Inzan ya dubeshi ya ce ya kai Inzam dama ka kwana biyu baka motsa jiki ba.

AlhamduLillahi naga addu'o'inku yan uwa, kuma ina godiya matuka Allah Ya saka maku da alheri ga karin kumallo nan.

Allah Ya cika mana burikanmu na alheri 🙏🙏🙏
GWARZON SADAUKI
Littafi Na Biyu (2)
Part E
Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini
Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey

To ka sani abokin hamayarka sadauki Darkin na birnin kisira ya đebo dakarun yaki sun taho izuwa nan birninmu domin su yake mu, so suke su iske mu has nan kofar gari, abinda nake so da kai shine kaima ka debi dakaru masu yawa kaje kutaresu a can daji kuma ku dana musu mugayen tarkuna da zasu hallaka kafin ku hada jiki dasu, ma'ana kuyi musu yakin sumame da mamayar bazato, koda jin wannan koda jn wannan batu sai farin ciki ya lullube sadauki Inzanu saboda damá ya dade yana so yayi ramuwar. akan sadauki Daskin na kisira bisa dan uwansa uwa daya uba daya daya kashe a wani yaki da akayi shekaru biyar baya, don haka ya dubi sarki cikin murna ya ce ya shugabana ina mai tabbatar maka da cewa zan shiryawa dakarun birnin kisira tuggun yakin da dayan su bazai tsira ba kuma wannan sine karo na karshe da zamu yi yaki dasu domin birnin nu ya zama namu. Koda jin haka sai sarki marhat ya bushe da dariyar farin ciki yace maza kaje ka fara shiri nima.yanzu Zanyi nawa domin bin bayan $arki Zamral izuwa inda littafinsa na sirri yake domin kawo karshensa gaba daya.
Sadauki Inzam ya risina yace angama ya shugabana, nan take ya juya da sauri ya fice daga cikit dakin. Sarki Marhat sai ya fara kira sunayen wadansu aljanu, kwatsam sai ga wasu zaratan matasan aljanu acikin shigar yaki dauke da makamai masu ban tsoro, suna ratsowa ta saman gini suna sauka a gaban sarki Marhat suna masu kwasar gaisuwa.

A can sai da su Insam suka shafe kwanaki biyu da yini guda sannan suka iso wannan daji mai dauke da manyan tsaunika da manyan kogunan duwatsu, da iso warsu wannan waje sai sai suka tsayar da dawakansu suka sauko suka daure su a jikin bishiyoyi, faruwar hakan keda wuya sai suka ga Ilaila ta kama kallon wani guri ta hanga can ta kalli nan, daga can kawai sai ta durfafi wani tsauni kai tsaye, koda ganin haka sai Gadaraz yabi bayanta da sauri ai kuwa sai Insam da Bushrad ma suka biyo su, yayin da Ilaila taci gaba da tunkarar tsaunin sai kuma ta kara sauri | daga bisani ma ta fita da gudu hart a isa kan tsaunin suma su Gadaraz suna biye da ita, koda isa kan tsaunin sai ta tsaya cak ta kura wa wasu duwatsu guda biyu idanu wadanda aka ajiye a wajen nan take sai hawaye ya zubo mata ta tsuguna bisa gwiwoyinta ta shafa dutse daya a cikin duwatsun, koda ganin haka sai Gadaraz ya tsugunna kusa da ita ya dubeta yace shin kin tino da wani abu ne?
Ilaila ta dubi Gadaraz lokacin da hawaye ya ci gaba da zubo mata tace ni da mahaifina mun ta6a hawa kan tsaunin nan har muka zauna a kan duwatsun nan guda biyu.
Cikin murna Gadaraz ya ce ina son to ki kurawa duwatsunan biyu idanu ki yi kokarin tino da duk abin da ya faru tsakaninki da mahaifinki lokacin da kuke zauna a wannan wuri.
Koda jin baka sai Ilaila ta dafa dutsen da mahaifinta ya zauna sannan ta rintse idanuwanta ai kuwa nan take tafada kogin tunani.
Suna zaune akan duwatsun biyu sai mahifinta ya dauko salkar ruwa ya samata a baki ta sha, sannan shima ya sha sakamakon kishit ruwal da kuma da gajiyar tafiya da suka sha, sa'adda idanunsa suka ciko da kwalla yace yake yata ki sani inda zamų yanzu wajene mai hatsarin gaske, zan iya rayuwa kuma zan iya mutuwa amma bamu da wani zabi wanda ya wuce muje wajen, in ba haka ba wanda ke biye da mu zai riskemu koma yakashe ni ko ya rabani da wannan littafin, nan take mahaifin Ilaila va sa hannu cikin aljihun rigarsa sai ya dauko wani dan karanin jan littafi ya nuna wa Ilaila inda sarki Marhat ya boye dukiyarsa mai tsananin yawan gaske kuma yana dauke da sirrin sa na tsafi wanda dole saida shi da shi ne kadai za'a iya hallaka shi, kuma duk wannan dukiya daya tara nine sanadinta Hakazalika duk sihirin daya samu nine sanadi kuma nine kadai na sani a fadin wannan duniya. Bisa wannan dalili ne yake so ya kasha ni kema kuma kama ki zaiyi yanzu daga nan zamu je kogon badarel anwar inda zan boye wannan litattafin a gaban idonki idan kin rayu zaki iya zuwa ki dauki littafin domin ki kawo.karshen sarki Marhat bisa cin amanata da yayi, idan kuma baki rayu ba shikenan shi ma har abada ba zai sake mallakar littafinsa ba kuma sai ya mallaki littafin a hannusa sannan zai iya samun nasara akan abokan gabarsa har ya cika burikansa. Lokacin da mahaifin Ilaila yazo nan jawabinsa sai ta dube shi tace,
Yakai Abbana to akan me kake fadamin cewar ba zaka rayu ba, alhalin gaka yanzu a raye ina tare da kai? Mahaifin Ilaila yace ka'idar wannan littafi shine duk wanda ya kai shi cikin kogon Hadara aswar ya ajiye shi indai ba mamallakasaba rmutuwa zai yi, kuma ba bu wanda zai iya sake daukoshi face jininsa. Amma ke zaki iya dauko shi nan gaba babu abi da zai sameki. Sa'adda mahaifin Ilaila yazo nan a jawabinsa sai Ilaila ta fashe da kuka kuma ta rungumeshi tana mai cewa ya kai Abbana saboda me zaka sallamar da rayuwarka don kawai kakai wannan littafi kogon Hadaru Aswar. Dajin wannan tambaya sai ya janye jikinsa daga ciki nata sannan ya dubeta cikin nutsuwa yace nayi hakane domin ceto rayuwar miliyoyin jama'ar da sarki Marhat yake zalunta. Idan ban rabashi da wannan littafi ba to nan gaba sai ya mallake nahiyarnan gaba dayanta, kuma mulkin zalunci zai yi ta dorarwa kema ba zakiyi rayuwa mai kyauba. Kafin Ilaila ta budi bakin ta kara cewa wani abu sai kawai suka hango sarki Marhat bisa doki tare da wasu dakarun yaki acan nesa kadan sun darfafo wannan tsauni da suke kai! Nan take Mahaifin Ilaila ya mike tsaye zumbur ya suri Ilaila ya goyata a bayansa yasa Mayafi va daureta ta tamau sannan va falfala da gudu yana mai sakkowa daga kan tsaunin ya nufi wata hanya da tanufi çikin kungurimin daji mai dauke da manyan duwatsu, koda su sarki Marhat suka hango mahaifin Ilaila goye da 'yar sa ya tunkari cikin wannan daji a guje sai suma sukal karawa dawakan su.kaimi domin su cin musa, amma sai suka kasa saboda gudun nasa na sihirine. Ai kuwal sai shima sarki Marhata ya fara amfani da na shi sihirin na tsatin ya zamana dawakansu na iya tsallake duwatsu da bishiyoyi tamkar kibiyoyi ake harbowa, $ai da aka shafe rabin sa'a ana wannan tseren gudun tsakanin mahaifin Ilaila da sarki Marhat amma basu riske shi ba, gashi suna harbo masa kibiyoyi sai dai sun kasa samunsa har suka isa bakin| kogon| Hadari Aswad. Da zuwa sai mahaifin laila ya kunna kai cikin kogon ba tare da tsoron komai ba yana goye da Ilaila.
Mutum na shiga wannan kogo zai ga wani katon rami a kasansa mai tsananin zurfin gaske dauke da wata gadace a saman ramin wacce aka yi ta da itatuwa, dole sai mutum yabi ta kan wannan gadar sannan ya wuce kana ya isa cikin wannan ainihin kogon dutsen inda aka ajiye kayayyaki na dukiya da sihiri marasa adadi, ba tare da shakkar komai ba mahaifin Ilaile ya wuce da gudu takan wannan gadar yana kallon kasa kuma yane tsalake wasu itatuwa wanda ba a takasu, domin idan mutum yayi kuskuren ta kasu zai subuto kasa gadar ya halaka saboda wata irin gagaruma wuta ce a kasan ramin take zabalbala har da narkeken dutse a cikin ta.
Mahaifin Ilaila na cikin yin gudu akan wannan gada sai yaga sarki da dakarunsa sun shigo a guje sai suka tsaya a bakin gadar wace aka yi tada itatuwa, kuma itatuwan sun tsufa ga dukkan alamu baza suyi kwari ba, sai hankalinsu ya dugunzuma jikinsų va kama kyarma kawai sai sarki Marhat ya ratse gefe guda ya dubi badakaren dake bayansa sai yace
maza ka ruga ka riske su ka kasheshi ka dauko min wannan yarinyar da littafin dake hannunsa, ciki tsoro bisa dole badakaren ya ruga kan gadar aikuwa taku na uku sai icen da ya taka ya karye ya sullubo kasan gadar yana mai kurma ihu. Koda ya isa can kasa cikin wutar nan sai suka ji kara soyewarsa tamkar anjefa nama a tafasashen man girki, nan fa saurar dakarur suka fisgita ainur suka fara Kokarin jada baya amma sai Sarki Marhat ya daka musu tsawa tare da cace duk wanda ya yi yunkurin guduwa zan kure masa kudunsa kuma in halakashi da hannuna, sajin haka sai dakarunsa suka tsaya kawai sarki Marhar ya ci gaba da umartarsu suna rugawa kan gadar har saida mutum tara suka hallak sannan ya tsayar da sauran ashe yana lurane da abinda yake sasu Hallaka, wani farin ice ne ba'a takawa daga cikin itace, idar kuwa mutum ya takashi take -zai sullulibo kasan ramin, nan take sarki ya sanar da sauran dakarunsa wannan matsalar sannan ya fara wuce wa da gudu ba tareda ya taka farin ice ba ya nufi inda su Ilaila suke, aikuwa suma sauran dakarun sukayi koyi dashi, koda mahaifin Ilaila ya hango su sarki Marhat sun biyo su sai yakara karfin gudun har ya įsa karshe gadar ya dira cikin kogon hadari Aswar. Yaci gaba da gudu a cikin kogon bai tsaya ba, ga tsubi tsubin dukiyoyi nan kamar su Zinare, luu u'u, jauhar da sauransu ko kallonsu bayi ba har $aida ya iso gaban wani teburi na karfe wanda a tsakiyar sa akwai wani dan karamin rami sannan ya
tsaya ya kwanto Ilaila daga bayansa ya ajiye ta a gabansa ya kalleta kallon karshe a lokacın da hawaye ya zubo masa yace yake 'yata anan nake miki ban kwana domin ni nazo inda mutuwa zata rabamu da zarar kin ga na sa wannan littafi a wannan raminki gudu ki nufi can kudu karshen sa akwai cibiyar ruwa ta kogi kawai ki yi tsalle ki fada ciki, nasan tun kina yar shekara hudu na fara koya miki iyo a ruwa kiyi iya yinki har ki isa gabar rowan idan kina da rabon rayuwa zaki rayu har ki dawo nan ki dauki wannan Iittafi idan kuma baki da rabon rayuwa to shi kenan koba komai mun hana sarki Marhat cika babban burinsa a rayuwa, yana gama fadin hakan sai ya zura wannan littafin cikin wannan ramin dake kan wannan tebur din adaidai wannan lokacin sarki Marhat suka įso ya zamana cewa tazarar dake tsakaninsu bata wuce taku hudu ba gama zura littafin a cikin ramin keda wuya sai mahafin Ilaila ya daskarc ya zama kamar kankara sannan ya dinga ruburbushewa yana zama gari. Koda ganin haka sai laila ta kurma uban ihu kuma ta fashe da kuka amma da taga Sarki Marhat ya nufota sai ta juya da gudu ta nufi inda mahaifinta ya umarceta saura taku daya ja!
Marhat ya cafkota da hannunsa sai ta daka tsalle ta fada cikin wannan ruwan daya kasance cibiyar wani kogi kuma daga inda tayi tsallen ta fada kasa çikin kogin ramine mai zurfin gaske wanda ya firgita sarki Marhat ya kasa yin kundunbalar ya bita.
Lokacin da llaila ta fada cikin wannan kogin tuni ta suma, cikin sa'a sai ta taso saman ruwa kuma igiyar ruwa ta nnga hankadota har ta isa bakin gaba indal wadandu masunta keyin su, anan sarkin masuntan kauye ya tsiceta inda yaga wata laya a wuyanta, koda ya bude layar sai vaga wata wasika a ciki, a cikin wasikar ne yaga wasiyyar da mahaifin Ilaila ya bari a gare shi daya ɗauki Ilaila sai ya kaita wajen wani mashahurin mayaki domin a bata horo ta jarumta da iya yaki
Koda Ilaila tazo nan a tunanin ta sai ta fashe da kuka. Cikin hanzari Gadaraz ya shiga rarrashinta kuma ya rungume akan kirjinsa, daga can sai ýa janye jikinsa ya dubeta yace nasan yanzu Kin gama tino komai kisani yanzu bamu da warni isasshen lokaci don haka kitashi mu hanzarta muje inda aka ajiye wannan littafin sirrin mu dauko shi saboda shi babban makamin da zai kaimu ga nasara. Koda jin wannan batu sai Ilaila ta mike tsaye zumbur ta্|juya da baya ta sauko daga kan wannan tsaunin da gudu ai kuwa sai Gadaraz, Insam da Barsad ma suka yi koyi da ita suna saukowa daga kan wannan tsaunin kowannan su ya kama dokinisa ya haye suma dakárun Gadaraz masu bakaken tufafi sai suka bisu a baya aka sukwani dawakai da guda aka nufi kogon hadaril Aswad, dayake Ilaila ce akan gaba suna isowa gaban kofar kogon sai ta tsayar da dokinta ta sauko kowa ma sai ya tsaida nasa dokin ya sauko kai tsaye ba tare da wata fargaba ba Ilaila ta kunna kai cikin kogon ta tsaya a bakin wannan gadar ta itace har sai da su Gadaraz suka žo suka risketa sannan tayi musu bayanin yadda za'a haye gadar ba tare da dayansu va fadđa kasa cikin wannan gagaruma wuta ya hallaka ba, tana gama yi musu bayani sai ta wuce da gudu ta kan gadar kamar yadd mahaifinta ya wuce da ita tana goye abayansa shekarun da suka gabata sa'adda tana yarinya karama, hatta gwarzon sadauki wato Insam saida

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads