Header Ads
Showing 6001 words to 9000 words out of 14992 words

Chapter 3 - GWARZON SADAUKI book complete by abdul'aziz Sani Madakin Gini

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

wannan al'amari da ya faru a baya sai Gadara ya dafa kafadarsa ya ce "Na san yanzu ka gama tuno komai. Shin ka san ko waye ya sace amarya Sulaisa kuwa?"
Insam ya ce, Ya za a yi na sani sai zargi da aka dora mani aka zalunce ni bada hakkina ba.
Gadaraz ya ce "Haka ne to ba wani ba ne ya sace ta face ni di nan, kuma na mayar da ita gidan sarautar Sarki Marhat nd babban abokin gabata domin na dawo masa da farin cikinsa sannan kuma yanzu daga baya a na same ku kai da Barsad
zan je na rushe dukkan farin cikinsa da arzikinsa kuma na cika burina a kansa. Hadin kanku kadai ya rage mani yanzu na cimma burina. Ku sani idan wannan buri nawa ya cika har abada kun tsira daga sharrin kowane $arki a wannan nahiya kuma zaku zama manyan Sarakai na manyan biranc a wannan nahiya ta mu."
Sa'adda Insam da Barsad suka ji wannan batu sai suka kamu da farin ciki amma sai Insam ya dubi Gadaraz ya ce, To yanzu ta ya ya zaka iya rushe farin cikin Sarki Marhat kuma ya zamu yi da barazanar Sarki Zamral tunda dole ne ya cigaba da farautarmu saboda ya san cewa kai ne ka taimaka mana muka sami nasarar guduwa daga kurkuku?"
Gadaraz ya yi ajiyar zuciya ya ce "Duk abubuwan da ka ga nayi yanzu a lissafe suke kuma a shirye tun shekaru uku baya da suka gabata. Sai da na auna komai na tanadi komai da sannan na fara aikina, hatta kai a Barsad kana cikin mutanen da na tanada don cika wannan burni nawa. Abin da na ke bukata da ku kawai ku daukar mini alkawarin cewar duk wuya duk tsanani kuna tare da ni ba za ku ci mini amana ba. Idan kun amince ga hannuna kowannenku ya dafa shida hannunsa na dama.
Sa'adda Insam da Barsad suka jii wannan batu sai suka dubi junansu sannan suka tsaya suna tunanin abin yi.
Insam ne ya fara dora hannunsa a kan na Gadaraz sannan shima Barsad ya dora nasa a kan na Insam. Koda ganin haka sai ita ma llaila ta.đora hannunta a kan na Barsad ta ce, Ni ma ina tare da ku dari bisa dari."
Wannan shi ne abin da ya faru ga su jarumi Insam bayan shugaban dakarun kürkukun birnin Kisira wato Gadaraz ya taimaka musu suka sami nasarar guduwa.
A can baya kuwa lokacin da Gadaraz ya sace Gimbiya Sulaisa, sai da ya kai ta har kusa da gidan sarautar birnin Misira amma ba ta san wane ne ya satota ba. Kawai ta san cewa ta kwanta ta yi barci a can birnin Kisira amma sai farkawa ta yi ta tsinci kanta a kan doki wani mutum na rike da ita a gaban dokin yana tsala gudu.
Ko da ta waigo sai ta ga fuskarsa a rufe take za ta yi magana ke nan sai ta ji ya ja linzami takc dokin ya yi turjiya gami da daga kafatuwansa na gaba sama yana haniniya sannan ya ajiye su kasa.
A sannan ne suka sauko daga kan dokin. Sulaisa ta dubi gabas da yamma, kudu da aewa kawai $ai ta hango gidan $arautar masoyinta wato $arki Marhat.
Nan take ta kamu da tsananin mamaki gami da dimbin farin ciki ta dubi mahayin ta de "Wane ne kai kuma saboda me ka sato ni daga wajen wancan azzalumin sarkin ka dawo dani hannun masoyima?"
Lokacin da mahayin ya ji wannan tambaya sai ya kwaye fuskarsa. Ko da ta yi arba da shi sai ta sake cika da mamaki saboda ba wani ba ne face Gadaraz.
Gadaraz ya yi murmushi ya ce, "'Na san za ki yi mamaki domin kin sanni a matsayin amintaccen hadimin sarki Zamral amma kuma ga Shi naci amanarsa, ki sani na yi haka ne domin na cika wani buri nawa. Ina so ki sani cewa shi ma wannan masoyin naki azzalumi ne ya cutar da rayuwar mutane da yawa amma ba ki sani ba Shawarar da zan ba ki ita ce ki yi bad-da kama ki.shiga gidan sarautar a matsayin.baiwa domin ki gano ainihin wane ne Sarki Marhat sannan ki yanke shawara a kan za ki iya ci gaba da rayuwa da shi ko a'a."
Gadaraz na gama fadin hakan sai ya kama dokinsa ya haye sannan ya dubi Sulaisa va ce "'Sai mun sake haduwa a wani karon. Yana gama fadin hakan sai ya juya da dokinsa baya ya zabure shi da gudu ya nufi hanyar da suka fito.
Ita kuwa Sulaisa hankalinta ne ya dugunzuma ta rasa abin dake mata dadi domin ta tsinci kanta acikin wasu-wasi ákan shawarar da Gadaraz ya bata.
Ga shi dai yanzu tana farin cikin rabuwa da Sarki Zalmat wanda yake kokarin aurenta bisa dole kuma gashi ta dawo garin masoyinta Sarki Marhat wanda ta ba wa amanar Zuciyarta da ámanar rayuwarta.
Idan abin da Gadaraz ya gaya mata gaskiya ne to ai kuwa ba ta ga amfanin zama da azzalumi ba gwara ta goge Sonsa daga cikin ranta har abada.
Gama ayyana hakan ke da wuya sai Sulaisa ta nufi wannan hanya wacce za ta kai ta gidan sarauta. Sai da ya rage bai fi tazarar tafiyar dakıka dari biyar ba sannan Sulaisa ta rabe bayan wata bishiya daidai mararraba hanya mai zuwa cikin gari.
Dama Sulaisa ta rufe kanta da mayafi da duk jikinta, kuma ta sunkuyar da kanta kása. Da vake Sulaisa ta san duk iri abubuwan dake faruwa a cikıa gidan sarautar Sarki Marhad a kowane lokaci sam ba ta da wata damuwa domin da ta dubi lokacin da ake ciki yanzu sai hankalinta va kwanta saboda nan ba da dadewa ba wata amintacciyar kuyangarta zata fito daga cikin gidan sarautar domin zuwa kasuva yin siyayya.
Haka dai Sulaisa ta ci gaba de jira |har tsawon yan dakiku, kwatsam sai ta hango baiwa ta fito daga cikin gidan sarautar kuma aka yi Sa'a ita kadai ta fito tana rike da wani kwando.
Sai da kuyanga Rasimat ta gifta wannan bishiya wacce Sulaisa ke rabe sannan Sulaisa ta kira sunanta.
Cikin firgita ta waigo har tana sakın kwandor dake hannunta ya fadi kasa. A zaton Rasimat gamo ta yi. Ko da ta vi arba da Gimbiya Sulaisa sai ta kamu da tsananin mamaki ta rugo da gudu izuwa gareta suka rungume juna.
Rasimat ta janye jikinta daga na Sulaisa tana murmushin cikin farin ciki ta ce "Ya $hugabata wai su waye suka sace ki, kuma ya ya aka yi kika dawo nan yanzu?
Sulaisa ta ce "Duk wannan wani abune mai tsawo sai na nutsu, abin da nake so da ke shi ne mu tafi kasuwar tare amma a can zan batar da kamannina na dawo a matsayin baiwa saboda ina son na gano wani al'amari a tare da sarkil Ina bukatar ki rufa nin asiri kuma kada ki bari Kowa ya gane ni.
Sa'adda Rasimat ta ji wannan batu sai ta yi nmurmushi a ce Ya shugabata ai wannan abu ne mai sauki a wajena tamkar cire silin gashi daga cikin tandun mai, A matsayina na shugaba kuyangin gidan nan zan iya yin abin da ya fi hakarn, muje kasuwa kawai."
Nan take Rasimat da Gimbiya sulaisa suka jera suka nufi kasuwa.suna hira abin su tamkar baiwa da ৮aiwa.
Bayan sun hattama duk siye-siyen da ya kamata ne sai Rasimat ta kai Sulaisa shagon wata mace inda take siyen kayan Sawa na bayi da kuma kayan shafe-shafe na mata. Anan ne aka zabowa Suiaisa kayan da suka yi mata daidai, sannan aka yimata wani irin gyaran gashi gami da shafe-shafen fuska wanda ya canja kamanninta gabadaya. Duk irinn sanin da mutum yai mata bai isa ya gane ta ba. Daga nan ne suka kama hanya suka koma gidan sarautar.
Ba su sami matsalar komai ba, tun daga kofar farko ta shiga gidan suka yi ta kutsawa suna wuce dakaru, bayi, fadawa da hadimai har suka iso bangaren da turakar Rasimal takc
Rasima ta sa mukulli ta bude kofar dakin har ta sa kafarta guda ciki Sulaisa na biye da ita kawai sa suka ji muryar Sarki Marhat a bayansu ya ce Yau kin dade a kasuwa tun dazu nake neman ki."

Kuyi hakuri wallaahi exam muke yi ne shiyasa kuka jini shiru kwana biyu, yanzu ma space na samu yi maku wannan posting din saboda yadda kuke a cikin zuciyata.

Daga karshe ina mai neman Addu'arku yan uwa na gode 🙏🙏🙏GWARZON SADAUKI
Littafi Na Biyu (2)
Part D
Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini
Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey

Take zuciyar Rasimat da ta Sulaisa suka buga da karfi Rasinat ta juyo ta dube shi tana murmushin karfin hali ita kuwa Sulaisa ba ta dago kanta ba Rasimat ta ce Ai ba ya kasuwa na je ba, na je dakin bauta ne."
Sarki Marhat ya dubi Sulaisa wadda ta rufe kanta da mayafi ya ce "Yau kuma kın siyo sabuwar kuyanga ne?"
Rasimat ta ce E yanzun nan na taho da ita daga kasuwa.
Marhat ya ce "To dama neman da nake miki kenan ina son a canja mani kuyangin dake kula da turakata saboda ba sa yin aikinsu yadda ya kamata, sai ki hado da wannan sabuwa a cikinsu don na ga kamar zata kasance mai nutsuwa da sanin ya kamata.
Rasimat ta risina ta ce "An gama Shugabana."
Da jin haka sai Sarki ya juya ya koma hanyar da zaa ta mai da shi turakarsa. Tafiyarsa ke da wuya sai Rasimat da Sulaisa juna suka dafe kirjinsu suka sauke ajiyar Zucıya, sannan suka shige cikin turakar suka kulle kofar.
Bayan sun zauna ne Rasimat ta kawowa Sulaisa abinci da abin sha ta ci ta koshi sannan ta dube ta ta ce "Tabbas idan kika kảl ni cikin kuyangin dake yi wa Sarki hidima da zarar ya kalli idanuwana zai shaida ni, ni kuma a ƙalla ina bukatar kwana bakwai kafin na gano abin da nake son na gano."
Sa'adda Rasimat ta ji wannan batu sai ta kyalkyale da dariya ta ce "Kwantar da hankalinki ya shugabata. Dabara ba ta karewa mai neman tsira. Na san yadda zan yi ke dai kawai ki zuba ido ki sha kallo."
Kafin sa'a guda ta cika Rasimat ta zabo kuyangi guda goma sha daya sai ta yi musu ado iri daya da na Sulaisa sak, sannan kafin ta fito da Sulaisa daya cikin furakarta sai da ta sauya mata launin gashin kanta na ainihi daga baki zuwa ruwan kasa yadda babu wanda zaigane cewa launi aka sauya masa, sannan ta bata wani abu ta sanya shi cikin kwayar idanunta.
Take kalar idanunta suka sauya Sulaisa ta fito daga cikin turakar Rasimat ta jero acikin kuyangi goma sha daya suka tsaya reras a sawu guda Rasimai ta zo ta tsaya á gabansu sannan ta sanar da su yadda za su tafiyar da ayyukansu a turakar Sarki daga nan ne ta wuce gaba suka bi ta abaya har cikin turakar sarki.
Sarki Marhat na zaune bisa wata shimfida ta alfarma a tsakivar turakarsa sai ga shi an shigo da kuyangi guda goma sha bivu suka jeru a gabansa suka risina suka kwashi gaisuwa sarki Marhat ya mike tsaye ya fara kalonsu daya bayan daya yana matsowa gaba a hankali har ya zo daf fa Sulaisa wacce ita ce ta biyun karshe a layi. Ya dubeta da kyau amma sai ya wuce gaba ya kurawa ta karshen idanu sannan ya juyo ya dubi Rasinat ya ce "Aikinki ya yi kyau su fara nasu aikin."
Ba tare da bata wani lokaci ba Rasimat ta raba kuyangin gida uku ta nuna musu irin ayyukan da za su gabatar. Shi kuwa Sarki Marhat sai ya koma kan shimfidarsa ya kishingida aka kawo masa kayan ciye-ciye da na shaye-shaye amma ko kallonsu bai yi ba sai ya daga kansa Säma yana kallon rufin falon. Ga dukkan alamu dai tunani yake yi, kuma yana cikin damuwa mara misaltuwa.
Ku da ganın haka sai Rasimat ta taho gareshi ta zauna a gefen hagunsa ta dube shi ta ce, Ya shugabana kamar kana cikin damuwa da rashin walwala, shin akwai wata matsala ne?"
Sa'adda Sarki Marnat ya ji wannan tambaya sai yayi murnushin yake ya ce 'Ya ke shugabar| kuyangi ki yi sani cewa tun daga ranar da aka nemi masoyiyata Sulaisa aka rasa a cikin gidan nan sai farin ciki da walwala suka kaurace mini. Na tura yan leke asiri izuwa duk biranen dake nahiyar nan su gano min ko wane ne ya Saceta amma ko duriyarta ba ajii ba. Nayi amfani da karfin sihirin tsafina don gano inda take duk a banza. Ni dai
zaton da nake yi wanda ya saceta ya kasance gawurtaccen matsafi kuma babban makiyina."
Lokacin da Rasimat taji wannan batu sai ta yi ajiyar numfashi ta ce Ya shugabana ga yadda soyayyarku ta kasance ta gaskiya kai da Gimbiya Sulaisa babu wani mahalukin da ya isa lya raba ku face mútuwa."
Da jin haka sai Sarki Marhat ya bushe da darıya al'amarin da ya yi matukat baiwa Rasimat mamaki kenan Kawai sai ta ga $arki Marhat va murtuke fuskarsa ya dubeta ya ce, "Ba ki san sharrin makiya ba.
Yanzu haka wanda ya saceta ya gaya mata gaskiya da karya kuma ya nuna mata hujjojin da zai sa ta gamsu cewar ni ba mutumin kirki ba ne, don haka za ta iya tsanata a rana kuma a lokaci guda."
Rasinat ta ce Haba ya shugabana ai ciki da gaskiya wuka ba ta huda shi, kuma so ba karva ba ne."
Cikin fushi sai Sarki Marhat ya mike tsayesayd zumbur ya dubi Rasima ya ce Tabbas So gaskiva ne amma yana |ya juycwa ya zama kıyayya. A halin vanzu Suiaisa ta daina sona tunda har ta amince da maganar da makiyi na Gadaraz wanda ke shirin daukar fansa a kaina ya fada mata.'
Ko da jin wannán batu sai zuciyar Rasimat ta buga da karfi jikinta ya kama tsuma. Ita ma Gimbiya Sulaisa da ke cikin bayi ta yi bad-da-kama tana ta aiki såi Zuciyarta ta kama daka. Kawai sai suka ga Sarki Marhat ya baro inda yake ya durfafo inda Suiaisa take, Yana zuwa sai ya cafkk kevarta ta baya da hannunsa, ta kurma ihu sannan ya dube ta kuma ya waigo ya dubi Rasimat ya ce, "Ke munafuka kina zaton za ku iya yaudarata ne? Na karfinku kuma na fi karfin makiyana. Tabbas ni azzalumi ne, na kashe talakawan da ba su da laifin komai, haka ma attajirai da masu mulki don kawai na mallake abin da suke da shi, ko kuma domin jin dadina da nishadina. Ke Sulaisa ki sani cewa Babanki ma yaudararsa na yi da batun neman aurenki ba shirya gasar dukiya ta hakan ne na sace dukkan dukiyar da aka tara a wajen gasar da kuma ta 'sa wacce ya boye a įnda ya ke zaton babu wanda ya sani. Yanzu na mai da shi matsiyacin Sarki bai sani ba.
Aurena da ke kuma ya zama wajibi gobe-goben nan za a sha shagalin bikinmu."
Yana gama fadin hakan sai ya tafa hannunsa sau biyu Nan take wasu dakaru guda biyu suka shigo Cikin falon, ya dube su ya ce, Ku kama munafuka Rasimat ku kai ta kurkuku, gobc bayan an gama shagalin bikina da Sulaisa za a yanke mata hukuncin rataya."
Ko da jin haka sai Rasimat ta kurma ihu, ai kuwa sai dakarun suka kamata da karfin tsiya suka fice da ita daga cikin falon, Ita kuwa Sulaisa sai ta doke hannun Sarki Marhat daga jikin keyarta ta waigo, ta dube $hi a fusace ta ce Tabbas abin da Gadaraz ya fada mini a kanka gaskiya ne. Ka tabbata azzalumi kuma butulu, ma ci amana To ka $ani zalunci baya dorewa kuma ina mai tabbatar maka da cewa sai dai ka zauna da gawata a gidan nan."
Sarki Marhat ya kyalkyale da dariya ya ce "Duk abin da na shiryawa rayuwata shi ke faruwa. Ba a sarrafa ni sa dai ni na sarrafa wanda na so."
Nan take Sulaisa ta yunkura cikin zafin nama ta ciro wata takobi da ke rataye a jikin bango ta daga sama da rufin ta caka a cikinta amma sai hannunta ya kame a saman ta kasa motsa shi.
Sarki Marhat ya kyalkyale da dariya sannan ya sa hannunsa va karbe takobin daga hannunta, ya dube ta ya ce "Ai jikinki namu ne sai dan haka babu wani abu zai same shi face da yardarmu.
Şhige ki tafi turakarki ki kwanta ki huta. Ba zan zo miki ba sai gobe đa daddare bayanan gama shagalin biki."
Ai kuwa sai Gimbiya Sulaisa ta juya ta fice daga falon Sarki ta nufi tata turakar kamar yadda ya umarca ta. Tabbas tsafi gaskiyar mai shi ne. Gabadayan kuyangi da hadirnan dake cikin wannan falo na Sarki Marhat sai da suka cika da tsananin mamakin karfin sihirinsa þisa yadda ya gano duk irin shirin da Rasimat da Sulaisa suka şhirya da kuma yadda vake sarrafa Sulaisa tamkar rakumi da akala.
Wannan Shi ne abin da va faru a birnin Misira bayan Gadaraz ya mayar da amarya Sulaisal ainihin ga masovinta Sarki Marhat wanda a halin yanzu ya babban makiyinta a duniya.
A can fadar Sarki Zarmal na birnin Kisira kuwa yana zaune ana tafiyar da harkokin fada cikin nishadi, wasu yan mata na rawa a gabansa ana buga wani kidan taushi sai ga Sadauki Bartus ya shigo da sauri fuskarsa cike da alamun damuwa Da zuwansa kusa da karagar Sarki sai va zube kasa bisa guiwarsa guda lokacin da masu kida suka dainab'yanmatan dake rawa suka tsaya cak, fadar ta yi tsit tamkar babu mai rai a cikinta.
Sadauki Bartus ya budi baki kansa na sunkuye ya ce Ya shugabana. Gadaraz yaci amanarka. Ya kashe dakarunmu kuma ya taimakawa insam Barsad sun sami nasarar guduwa daga kurkuku. Koda jin wannan batu sai sarki Zamral ya bushe da dariyar farin ciki al'amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan a fadar, sannan Zamral va murtuke fuska ya mike tsaye daga kan karagarsa ya dubi sadauki Bartus ya ce ai dama wannan ranar nake jira ya kai Bartus kasance wa wani lokaci yazo wanda zan mallaki birnin Misra. A duniyar nan kaf bani da makiyin da yafi sarki Marhat na binin misra ni da shi munyi kunnen doki a karfin mulki arziki da kuma karfin sihiri tsafi. Kowannan mu so yake ya kawar da daya domin va mallake komai nasa,

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads