Showing 3001 words to 6000 words out of 14992 words
Chapter 2 - GWARZON SADAUKI book complete by abdul'aziz Sani Madakin Gini
riski inda su Insam suka bar wannan kwalc-kwale. Da fitowarsu daga cikin koramar sai suka bi sawur su Insam suna masu falfala uban gudu.
Al'amarin Insam da Barsad kuwa tun da suka iso gabar koramar $uka fito daga cikin kwale-kwalen sai suka ruga izuwa cikin daji. Sai da suka yi gudun sa'a guda ¢ur sannan suka zube kasa bisa guiwoyinsu suka kama haki da numfarfashi sakamakon tsananin gajiya da suka yi a kokarinsu na fitowa daga cikin kurkukun da kuma gumürzut da suka yi da dakaru.
Barsad ya dubi Insam ya ce, "Yanzu dai ga shi mun $ami nasarar fitowa daga cikin kurkukur nan amma daga yanzu zuwa kowane lokacin dakaru za su ya isowa nận su cimmana ka ga kenan duk wahalar da muka sha a baya ta zama ta banza, domin ba za mu iya tserewa ba.
Insam ya ce Kamar yadda na baka nmamakl na cire rodunan tagar dakin da aka kulle mu kurna na gaya maka ta hanyar da za mu bi mu ficc daga cikin kurkukun wacce kai baka taba tunaninta ba a zuciyarka haka ma yanzu zan shirya mana yadda zamu kubuta. Za mu gaba da yin gudu na tsawon rabin sa'a kacal sannan mu tsaya. Shi inda za mu tsaya din anan gaba bishiyoyi ne a wajen ko kuwa duwatsu ne? Ka fi ni sanin haka tun da kai mutumin daji ne".
Barsad ya jinjina kai ya ce, "Bishiyoyi za mu riska masu tsawo da duhowoyi".
Insam ya ce "Da kyau" faduwa ta zo dadai da zama. Lallai a iya Tsawon gudun abin sa'a ne dakarun kurkuku za su riske mu domin a kan dawakai zasu biyo mu. Yanzu dole ne mu hanzarta mu isa inda bishiyoyin nar suke kafin su rigamu zuwa domin mu hau kan bishiya mu
buya inda zamu dinga yi masu daukar daidai. Abin da nakc so ta kal ১hine da zarar mun isa wajen, duk abin da ka ga na yi kai ma ka vi shi.!
Gama fadin hakan ke da wuya sai Insam ya falfala da gudu izuwa cikin dajin, ai kuwa sai Barsad ya yi koyi da shı.
Haka dai suka gaba da gudun babu waiwaye babu tsawa har tsawon cikar rabin saa sai ga shi sun iso wannan wuri mai dauke da dogayen bishiyoyi wadanda suka haifar da duhuwoyil sakamakon fadin ganyayyensu da yawansu.
Da isowarsu wannan wuri sai lnsam ya yi trujiya shi ma Barsad sai ya tsaya cak lokacin da Insam ya kurawa dajin idanu yana kallon gabas da yamma kudu da arewa
sannan ya dubi kasa. Ko da ya daga kansa sama sai kawai ya hango raga ta taho kansu.
Kafin su yi wani yunkuri tuni ragar ta lullube su sai kawai suka ga dakarun Gadaraz suna firfitowa daga maboyansu rike da masu da takubba kimanin su dubu sun kewayesu.
Gashi raga ta kanannadesu kuma g6 shi babu makami a hannunsu ko guda daya Insam ya dubi Barsad cikin alamun takaicj da bakin ciki ya ce Mun yi latti tunda sun rigamu isowa nan.
A daida wannan lokacin ne mataimakin Gadaraz sadauki Bartus ya fito daga inda yake boye yana kyalkyala dariyar mugunta sannan ya murtuke fuskarsa ya dubi Insam da Barsa ya ce, Mene he amfanin gudun da ba tsira. Ku sani cewa hukuncin kisa ne a kan duk wani fursunan da ya yi kokarın guduwa. Yanzu za mu kasheku a nan don haka inda kuma da wata wasiyya ku fada kafin taku ta kare'
Ko da jin wannan batu sai Barsad ya dubi Insam ya ce Yanzu wace dabara ta rage mana?"
Insam ya ce "Ba ni da sauran dabara mutuwa za mu vi kawai tunda in dai muna cikin ragar nan ba mu da wani tasiri".
Barsad ya ce "Amma dai ka cuce ni. Ni ina da buri a duniya ka janyo min mnutuwa a lokacin da ba ta kamacc ni ba. "
"Ta ya ya za ka cika burin naka alhalin an yanke maka hukuncin daurin rai da rai?"
Barsad ya ce Kullum tunani nake yi a kan hanyar da zan bi na tsere cikin nasara amma kai naka wannan gajere ne mara nasara."
Kafin Insam ya kara fadin wani abu sai Bartus ya dubi dakarunsa ya ke "Ku zuba musu kibiyoyi mu ķwashe gawarsu mu kai gidan sarki.
Da jin haka sai dakaru suka zaro kibiyoyi suka dana a kan baka suka tabe da nufin sakin harbi.
|Kwatsan sai aka ga wasu wasu kibiyoyin a sama cikin iska suna fadowa kan dakarun suna zubewa kasa matattu. Ba shiri Bartus ya vi wuf ya đauki garkuwa ya rufe jikinsa, kibiyoyi suka ci gaba da zuba akan garkuwar tasa.
Sai da Bartus ya ji shiru alamar cewa kibiyoyin sun kare sannan ya mike saye Kawai sai ya ga gabadayan dakarunsa a kwance kasa sun zama gawarwaki. A sannan ne kuma ya hango wadansu dakarun yaki a cikin shigar bakaken tufafi sun rufe fuskokinsu da makamai sun durfafo lnda yake.
A guje Bartus ya nufi inda dokinsa yakc ya yi tsalle ya haye shi, ya zabure shi da gudu ya nufi hanyar da za ta mai da shi cikin birnin Kisra.
Su kuwa wadannan dakaru masu bakaken tufafi sai mutum daya daga cikinsu ya dana kibiya da nufin ya harbo Bartus amma sai shugabansu ya rike hannunsa ya yi masa nuni da ya kyale shi.
Insam da Barsad kuwa mamaki ya turnuke su kawai suka kurawa bakin dakarun idanu suna tambayar kansu a cikin zuciya suna cewa wadannan Kuma su waye kuma a kan wane daliii suka ceci rayuwarmu?"Amsar da ba su sani ba ke nan bar Dakarun suka iso daf da Su.
Danna shugabar dakarunne a kan gaba tare da mataimakinsa Da
isowarsu dafl da su insam sai shugaban dakarun da mataimakinsa suka kwance rawanin da ya rufe fuskokinsu koda su Insam suka yi arba da su sai suka kara kamuwa da tsananin mamaki. Ba wadansu ba ne wadannan mutane biyu face Gadaraz da matarsa Ilaila.
Gadaraz ya dubi Insam da Barsad cikin murmushi ya ce "Ni ne na taimaka muku har kuka sami nasarar isowa nan wajen domin ni ne na sa aka ajiye muku kwale -kwalen da kuka hau kuka ketarc wannan
babbar korama ta buyan kurkuku. Na kubutar da rayuwarku ne domin ku yi mini wani aiki. Ku sani yanzu ba mu da lokacin tattaunawa, dolene mu fice daga cikin yankin kasar nan kafin Sarkin Kisira ya turo mana dakarun da za su fikarfinmu. Kowa a hau doki mu bar nan wajen.
Yana gama fadin haka sai ya zaro wuka ya farke ragar da ta lullub su Insam. Cikin hanzari kuwa suka fito daga çikin ragar. Kafin cikar dakika dari da tamanin kowa ya kama doki daga cikin dawakan Dakarun kurkuku ya haye, nan da nan suka zabure su izuwal cikin daji.
Sai da su Gadaraz suka shafe sa'a shida suna gudu kan dawakai su ratsa wannan daji su fita wancan har dai suka samu suka ficc daga cikinnyankin kasar Kisira $annan suka yada zango a wani daji gaban wani katon tsauni.
A wannan lokaci rana ta fadi gari ya soma duhu. Nan take aka kafa tantuna Sannan aka kunna wuta kashi-kashi domin jin dumi sannan aka debo abinci aka fara bawa kowa ya sami nasa.
Insam Barsad! Gadaraz da Ilaila na zaune a wajc guda gaban wuta suna ji dumi kuma suna cin abinci, sai Gadaraz ya dubi Insam da Barsad ya kyalkyaie da dariya ya ce, Tabbas duniya juyi-juyi ce, dazu
kuna cikin kurkuku a tsare babu yanci amma yanzu ga ku a sake cikin walwala har kuna cin abinci mai kyau da dadi ba irin na kurkuku
ba.
Sa'adda Insam ya ji wannan batu $ai ya tsaya ga barin cin abincin ya
dubi Gadaraz cikin nutsuwa ya ce "Wace bukata ka kaso mu biya maka wacce har ta sa ka hakura da aikinka na shugaban dakarun kurkukun birnin Kisira kuma ka aikata laifi na kashe abokan aikinka wanda idan har aka kama ka hukuncinka kisa ne?"
Lokacin da Gadaraz ya ji wannan tambaya sai ya yi murmushi ya ce,
Ya kai Insam dan Hashman jikan Damrus na sani cewa kai bawa ne
kuma dan bawa a cikin gidan sarautar Sarki Zamral na birnin Kisira. Ảna zarginka da laifin yin alakar soyayya da matar Sarki, bisa wannan dalii ne aka yanke maka hukuncin dauri rai da rai. Tabbas wannan zalunci ne domin kai ba Sonta kake ba, ita ce take sonka saboda kana kama da masoyinta. Hakan ya samo asali ne a ranar da aka kawota gidan sarautar tana amarya a lokacin da kuka yi wasan nuna jarumta kai da 'yan'uwanka bayi don taya sarki murnar bikin aurensa.
Ko da jin wannan batu sai Insam ya fada kogin tunani.
Da yanmaci ne aka shigo da amarya Sulaisa a cikin wani keken doki na alfarma cikin gidan $arautar birnin Kisira. A wannan lokaci dakaru dubu ne suka rako Gimbiy Sulaisa wacce ta kasance| ya ga sarki Zarkam na birnin Sadyas A gaban tawagarta akwai kuyangi dari biyu
bisa dawakai dauke da kaskwayen furanni suna ta watsa furannin sama suna zubowa kasa a cikin harabar gidan sarautar. Har sai da aka iso.tsakiyar gidan sarautar sannan aka tsaya!
Sarki Zarkam na zaune bisa wata kujcra ta alfarma fadawansa da dakaru da hadimai sun kewaye shi. Tsayuwar keken dokin amarya Suiaisa ke da wuya sai Sarki ya mike tsaye fuskarsa cike da murmushi ya kasa rufe baki saboda doki gami da farin ciki.
A wannan lokaci su Bawa Insam na tsaye a gefe kimanin su goma sha shida sun yi shiga iri daya domin debewa amarya kewa.
Ko da aka bude keken doki amarya Sulaisa ta zuro kafafunta waje suka taba kasa sannan ta zuro kanta waje kowa ya yi arba da kyakkyawar fuskarta sai jama'a suka rude kuma suka dimauce saboda ganin tsananin kyawunta.
Sulaisa ta kasance matashiya budurwa yar shekara goma sha takwas. Doguwa ce kuma fara kal mai madaidaicin kaurın jiki. Tana da dogon hanci, dan karamin baki, manyan idanu gami da siririn wuya. Gashinta baki ne sidik yana sheki da walwali tamkar madubi kuma ya zubo har kasan kwankwasonta.
Tana sanye da wata doguwar farar riga mai tsadar gaske irin tasu ta sarakai. Tsayin bezar rigar ta daga baya va kai kamu sittin kuyangi ne ke rike da ita suna tattareta.
Kallo daya mutum zai yi wanwannan amarya ya gane cewa ba ta son wannan aure da aka yi mata saboda murmushin yake take yi kawai. Fitowarta ke da wuya daga cikin keken dokin sai sarki Zamral ya mike da sauri daga kan kujerar da yake zaune ya je ya taro ta, inda ya mika mata hannunsa ta kama sannan ya jawota suka zo inda yake zaune suka zauna.
Shi dai jarumi Insam tunda ya yi arba da Gimbiya Sulaisa sai ya ji zuciyarsa ta buga da karfi kuma wani irin tsoro ya shige shi wanda bai san dalilin faruwar hakan ba. AI kuwa sai Gimbiya ta waiwayo ta hada idanu da Insam ai kuwa sai ta kura masa do ta kasa kawar da kai har sai da Sarki ya lura da abin da ke faruwa ya kamo hannunta sannan ta daina kallon Insam.
A daidai wannan lokaci ne mai gabatar da taro ya mike tsaye ya yi dan jawabai sannan aka gabatar da bayi wadanda aka shirya musu gasar fada domin fitar da gwani.
Mutum na farko da aka fara kiran sunansa daga cikin bayin shi ne bawa Insam. Insam ya fito daga cikin yan'uwansa bayi yana sanye da dogon wando buje da kuma riga falmaran ya shiga cikin wata daira dake tsakiyar |wannan fili.
Kuyi hakuri kwana biyu shiru in sha Allahu ba zamu kara daukar long time irin haka ba fatan alheri gareku masoya masu bibiyar wannan littafin.
Ga masu son complete pdf zasu iya tuntubata ta Numberta har ma da wasu littattafan 08138873799GWARZON SADAUKI
Littafi Na Biyu (2)
Part C
Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini
Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey
Ita dai wannan da'irar an kewayeta ne da wasu karafa da kuma igiyovi akan wani gini mai tudu wanda duk jama'ar da ke wajen ke iya hangota. Bayan an budewa Insam da'irar ya shiga ya tsaya sai aka jcho masa sanda ya cafe sannan aka kirawo bawa na biyu wanda shi ne abokin gwaminsa mai suna Janas.
Janas wani katon Bawa ne dogo kuma kakkaura domin ya ninka Insam sau biyu 2 girma da kwarjini, kuma fuskarsa babu annuri ko kadan. Janas na shigowa cikin da'ira gasa sai shi ma áka jeho masa tasa sandar ya cafe sannan ya gyara tsayuwarsa suka fuskanci juna.
A wannan lokaci ne jamaa suka rude da shewa gami da tafi. Kawai $ai aka buga gangar fara wasa. Jana ya ruga da gudu i zuwa kan Insam ya kawo masa wawan bugu da sanda a kai, cikin zafin nama Insam ya kare dukan suka ruguntsume da azababben fada ya zamana cewa Şuna kai wa junansu duka ta sama da Kasa. Sai da suka shafe dakika dari da tamanin suna kai wa junansu hare-hare ba tare da dayan su ya $ami wata nasara ba, sannan suka ja da baya suka gyara tsayuwa suna tunanin irin sabon salon fadan da kowannensu ya kamata ya yi don ya samu nasara.
Lokaci guda suka ruga da gudu a karo ha biyu suka kacame da sabon masifafien fada. A wannan lokaci kowannensu ya zage damtse yana fadan ne da iyakar karfinsa da kuma kwarewarsa.
Tun a farkon fara wannan gumurzu tsakanin Insam da Janas sarki Zamrall na lura da Gimbiya Sulaisa Duk sa'adda ta ga an kai wa Insam wawan hari har yana neman faduwa sai hankalinta ya tashi alamar fargaba ta bayyana karara akan fuskarta amma da zarar ta ga cewa Insam ke da alamu nasara sai fuskarta kama annuri da murmushi. Ganin hakan ne kishi ya turnuke Sarki Zamral ya ji kamar ya bayar da umarnin nan take a kashe bawa lnsam.
Ba wani abu ba ne ya sa Gimbiya Sulaisa ta ji tana son bawa Insam anganin farko face yana tsananin kama da masoyinta wanda ta so ta aura akanhanata wato Sarki Marhat na birnin Misra.
Sai da aka yi gasa ta dukiya a tsakanin sarakuna goma sha daya sannan aka fitar da gwanin daya sami damar auren Gimbiya Sulaisa kuma ba wani ba ne ya lashe gasar face Sarki Marhat amma a ranar da za a kai amarya birnin Misra aka nemeta aka rasa ashe Sarki Zamral ne ya tura aljanu suka sato ta. Sai da aka shafe shekaru uku ana nemanta ba ganta ba har
masoyita Sarki Marhat da nahaifinta suka hakura suka rungumi kaddara,
Duk irin karfin tsafin Sarki Marhat na birnin Misra bai ya gano inda Sulaisa take ba. Bayan shekara.uku ne Sarki Zamral ya shirya bikin aurersa a Sirrance a gidan sarautarsa ba tare da ya gayyaci Sarki ko guda daya a Nahiyar ba. A ranar da amarya za ta tarc aka shirya wannan gasa ta jaruma tsakanin bayin gidan sarautar.
Ko da fara wannan artabu karo na biyu sai fadan ya sauya ya zamana cewa insam ne yake kai wa Janas mugayen hare-hare wadanda da kyar yake iya kare su kuma baya iya mayar da martani. Ana ciki haka ne lnsam ya shammaci Janas ya doki kafafunsa da sanda Janas ya sama kafin ya fado kasa lnsam ya sake doka masa sanda akan kirjinsa, take Janas ya fado kasa tim, bisa gadon bayan sa ya furzo da gudan jini daga cikin bakinsa kuma ya kasa mikewa tsaye.
Nan fa yan kallo suka rude da shewa gami da tafi Gimbiya Sulaisa kuwa ba ta san sa'adda ta mike tsaye ba, tana yi wa lnsam ta fi sai da Sarki Zamral ya riko hannunta sannan ta koma ta zauna.
Daya bayan daya sai da jarumi.Insarn ya yi fadan sanda da wadannan bayi guda goma sha shida kuma ya yi nasara a kansu, đayansu bai sami nasarar koda dukan jikinsa ba sau daya. Ana gama wannan gasa ne Sarki Zamral ya ja amaryarsa
suka shiga cikin gidan sarautar, taro ya watse kowa ya kama gabansa.
Lokacin da bayi da kuyangi suka raka amarya Sulaisa cikin turakarta suka fito suka bar ta ita kadai jal a zuane gefer gadonta na alfarma sai ta fashe da matsanancin kuka na bakin cikin wannan auren dole da ta yi. Ga shi an rabota da kasarta ta haihuwa iyayenta ma ba ta san ranar da za ta sake ganinsu ba, kuma ga shi an rabata da masoyinta Sarki Marhat
To wai shin jarumin da na gani yanzu mai kama da masoyina Marhat waye shi? Anya kuwa ba shi da wata nasaba da Sarki Marhat domin kamannin nasu ya yi yawa matuka.
Tana cikin yin wannan tunani ne da kuka Sarki Zamral ya shigo cikin turakar. Koda ta ga ya durfafota gadan-gadan sai ta sauko daga kan.gadon da gudu ta nufi kan tebur da aka ajiye ya'yan itatuwa da wuka Kawai sai ta dauki wukar ta đoral a kan wuyanta ta dube shi ta ce, Idan ka kara yin tafiya taku d'aya izuwa gareni na rantse da darajar iyayena sai na kashe kaina.'
Ko da in wannan batu sai hankali Sarki Zamralya.dugunzuma ya yi taku biyu sannan ya dubetal ya |ce, "Ni ma na rantse da darajar nawa.iyayen daga yau ba zan sake kusantariki ba har sai kin bukace ni da kanki Amma ki sani cewa wannan bawa da ya lashe gasar jarumta mai kama da tsohon masoyinki duk anar da kika kusance.shi ko kuka yi magana da juna ba ki sake ganinsa ba domin kurkuku zan kai shi a yanke masa hukuncu
daurin rai da rai."
Gama fadin hakar ke de wuya sai Sarki Zalmar ya juya da baya a fusace cikin bakin ciki ya fice daga cikin turakar.
Kashegari da safe kuwa aka nemi.amaryal Sulaisa sama da kasa aka rasa a cikin gidan sarautar. Al'amarin da ya dugunzuma hankalin Sarki Zalmar kenan ya baza dakarunsa a
nahiyar aka yi ta nemanta amma ko duriyarta ba a ji ba a tsawon kwanaki bakwai. Bisa wannan dalili ne Sarki Zalmar ya zargi Bawa Insam a kan cewar akwai sa hannunsa a batan Gimbiya Sulaisa don haka ya sa aka kama shi aka yi ta gana masa azaba iri-iril har tsawon kwanaki goma sha daya inda Sulaisa take.
Bayan an gano cewa babu sa hannunsa a 6atan Sulaisa sai kuma aka yanke masa hukuncin daurin rai da tai aka kai shi kurkuku. Sau uku yana guduwa ana kamo shi daga karshe aka kai shi babbar kurkuku inda Gadaraz ke shugabancin dakaru.
Lokacin da Insam ya gama tunanin