Showing 6001 words to 9000 words out of 13485 words
Chapter 3 - MULKI BOOK COMPLETE BY ASHANTY LOVE.txt
karb'o min mankuli zuryan, sai ki biya gurin Hamisu ki karbo wa Bilkisu d'inkin ta"
Kaman nace ita Bilkisun fa nadai fasa na amsa mata da toh. Takarmi na kawai masa na fito . Kasuwan na fara zuwa na siyo mai har zan karya hanya na biyo ta lungu nace kai bari kawai nabi titin abuna yafi sauri. Ina gabda k'ara sawa shagon Hamisu telar wani irin mahaukacin horn ya rudani na kwasa a guje na koma gefe duk da a gefen nake tafiya ashe nayi kusa da kwata sai jina nayi chab'al cikin ta. Wata irin motace mai shegen girma kaman jirgi bak'a wuluk da ita ta wuce a guje babu alamun duk wanda ke tukata zai tsaya ya bani haƙurin ya tsorata ni na fad'a kwata. A fusace na miƙe na rarimi dutse dake kusa dani katan gaske na saita motar da iya karfi na na jefa. Ina jin yanda gurin ya dauka da "ke, ke kul" ai ina tuni aikin gama ya gama cikin ikon Allah kuwa na samu glass d'in motar ta baya. Ji kake tasss
Wani irin mugun birki motar taci ta tsaya chak bata motsa ba kan titi. Wani dake gefe ne ya ce
"Innalilllahi kinsan abunda ki ka yi kuwa kinsan waye cikin motar nan?"
A fusace nace "koma uban waye, bashi da hankali zai dinga yiwa mutane irin wannan horn yana tsorata su?,yanzu dubi yanda yasa na fad'a cikin kwata da kuma asara da nayi"
Har yanzu motar na tsaye tsakiyar titi. Ita bata tafi ba,ita bata dawo ba. A fusace nayi motar ina masifa mutane na hanani.
"Kowane d'an iska ne ya fito. Saboda kuna cikin mota mai tsada ne ku ka fi karfi ku bada hakuri?. Kuɗin banza da wofi. In Allah ya yarda kafin kaje gida sai tayar motar ta lalace bama tayar kad'ai ba harda motar ita kanta sai inga ta isa da tunkaho".
Gaban motar na tsaya ina bugata da iya karfina da naga dai ba fitowa mai motar zaiyi ba na dawo bangaren direba na hau dukan glass d'inta da karfi kaman zan fasa motar dan raina ba k'aramin baci ya yi ba. Jikina gaba d'aya tun daga kuguna zuwa kafata kwata ce har diga nake. Duk wannan bai dameni ba akan man Baba Lantana da ya ke laye cikin kwatar. Babu irin kashedin da bata yimin ba akan kuɗin mannan dubu hud'u da dari bakwai cif ta bani na kwalba biyu.
K'ok'arin bode motar da naga ana yi naja baya kad'an ina jijjiga jikina. Da wani irin slow kofar ta buɗe sai kafa ta biyo baya sanye cikin wani farin cambas mai kyan gaske. Kafar kawai ya fito da ita ya ajiye waje wajen minti biyu kafin ya janyo jiki ya fito. Wani irin ingarman namiji ne ya fito ya tsaya gabana sanye cikin wasu kananan kaya rigar kaman ta sanyi mai hulan mai mad'auri ruwan toka sai wando na jeans light blue mai haske. Duk yanda naci burin d'ud'd'ura masa zagi sai na tsinci kaina da rawar jiki wani irin mugun tsoran sa ya shige ni amma na boye hakan a fuskata. Jingina ya yi da motar ya zubamin wasu tsumanmun idansa masu girman gaske da suke gasu nan su ba fari ba baki ba(grey eye's). Ikon Allah shi kuma har kala yake sawa a ido?. Ko da yake alamu sun nuna kaman bature ne. A zafafe nace
"kai wane irin mutum ne zaka tsorata mutane haka. A gefen titi nake tafiya ka yiwa mutane wani shegen horn ka tsorata su. Duk kan titin bai isheka tafiya ba sai ka had'a da gefen titi? Wlh sai ka biyani asarar da kasa nayi bazan hak'ura ba"
Maimakon ya bani haƙurin sai ya ciro wata irin taba daga aljihun wandon sa ya dora ta gefen bakin sa ya fito da wata lighter ya kyesta. Dago kai ya yi yana wani iran zukar ta na fara tari dan dad'in ta sam babu dad'i. Hannu nasa na toshe hanci ina karkade hayakin dake yowa inda nake.
"Malam ka biyani dubu hud'u da dari biyar d'ita dan walh baza kasaci bulus ba"
Motar ce ta bud'e wajen mai zaman banza wani hadedden saurayi ya fito sanye cikin manya kayan. Doguwar riga ta shadda fara da wando ta. Yana fitowa ya fad'a kalman data hausana min ciki
"AJ, what did she wants?"
Au Allah. Toh badai uwata ba walh. Nace a zuciyata. AJ. Ido na zare bayan sunan ya kara dawowa kunyar kai na nayi saurin maida hankali kan sa. Take na fara zikiri cikin zuciyata Wainnahu min suleimanu wainnahu bismillah rahmanun rahim, kalu Innalilllahi,hasbunnallahu wa ni'imal wakil.A tsorace na ja baya ganin shi gab dani . Kai wannan mutum badai tsayi ba. Kawai sai ji nayi ya fesamin tabarnan a fuska ta. Tari ya mugun sarke ni tuni tsoron nasa ya bace na hau masifa
"Allah ya isa wlh bazan yafe ba. Mugu Azzulumi "
"Ke baki da hankali kinsan dawa ki ke magana kuwa?"
"Koma waye shi ai ba Allah bane. D'an Adam duk inda yake dajara ce dashi shi kuma bai isa ya wulaƙantani ba na kyale"
Baki d'an uwan nasa ya hangame yana kallo na cikin matsanancin mamaki da Alama yaune rana ta farko da aka yi musu haka. Sai kuma ya kwashe dariya na kara tunzura zan kwaba masa bakar magana kawai naji hannunsa kan fuskata ya cafki lebena da iya karfinsa. Ji nayi kaman na saki fitsari saboda azaba dagewa nayi na gartsa masa mugun cizo da har saida na huda hannun nasa. Da sauri kuwa ya sakarmin baki yana yarfe hannu da wata irin kaukausar murya tamkar a shake (deep voice) ya yi magana.
"Fuck"
Tsabar bakin ciki hawaye suka biyo kuncina amma bakina bai mutu ba.
"Allah ya isa daka tab'a ni dan iska kawai ,kedarin banza,kedarin wofi. Ka d'auka kowama irin kane dan iska da zaka dinga tab'a mutane. Allah sai ya sakamin wlh "
yawu na tofa masa na juya fuu ina sharar hawayen bakin ciki. Har waye shi dazai tab'a ni cikin mutane salon yaja ace nima y'ar iskace irin sa. Duk inda na wuce sai an tambayeni me ya faru bani da bakin magana sai kuka har naje gida.
Da ace Sahla zata juya taga irin kallon da ya bita dashi to dah tabbas sai taji kaman ta ruga a guje tana fitsari. Kallo d'aya ya yiwa gungun jama'ar dake gurin suka fara tseren gudu tamkar wanda suka yi gamo. Zuka d'aya yawa tabar ya shanye ta ya jefar a k'asa ya take ta yana kallon bayanta tana tafiya kaman zata kifa tsabar sauri duk inda tayi ruwan kwata na binta kaman zuba mata ake. Harshen sa ya taune cikin bakin sa idansa ya yi wani irin ja ya kalli hannunsa dake digar jini.
"I will destroy you"
Ya juya a zuciye ya shige mota. D'an uwan nasa da suke tare ya yi saurin shiga motar shima dan yanda yake a fusacen nan tsaf zai iya tafiya ya barsa a gurin. Gaskiya yaga k'ok'arin yarinyar da alama bata tab'a jin labarin AJ ba tunda har tayi jarumtar cizon sa bata tsaya a nan ba harda tofa masa yawu? Gaskiya yaga k'ok'arin ta. Gashi ta janyowa kanta masifar da babu ranan karewar ta.
♥︎♥︎♥︎
"Uwata, subhanallahi me ya same ki haka?"
Ai ina jin muryar Baffa na k'ara rushewa da kuka nayi inda yake tsaye da wani. Saboda yanda bana cikin nutsuwa ta ban kula da Malam Halliru bane. Cikin damuwa ya k'ara jefamin wata tambayar.
"Me ya faru jikin ki duk kwata haka? "
Ina kuka na kwashe duk abunda ya faru na gaya masa amma ban fad'a masa ko waye ba dan nasan fad'a zansha idan yaji wancan tantirin yaron ne. Ajiyar zuciya ya sauke mai karfi.
"Shiga gida ki gyara jikin ki, zan shigo na samu Lantana "
Shigewa nayi ina sharar hawaye. Ai tana ganin shigowa ta ta rafka salati tana tafa hannu.
"Ni dama nasan sai anyi haka. Wlh wannan yarinyar da mugun hali ki ke. yanzu dan tsabar bakin ciki saida kika salwantar min da kuɗi. To ahir d'inki sai kin biyani wlh "
Ban kula taba tana ta banbami kaman zata dokeni nasan muryar Baffa da taji a kofar gida ya hanata.
"Da Allah ki matsa a kan mu mana haba, kinzo kin tsaya mana a ka da warin kwata wa ya sani ma ko kina sane kika jefa kan ki tunda ba kece da asara ba. Ai wlh Baba karki raga mata sai ta fito miki da kuɗin ki"
Ji nayi kaman na rufe su da duka gaba d'ayan su. Tana kwance kan cinyar ta tana yi mata susar kai. Wuce su nayi na shige banɗaki na barsu tana ta masifa. Har na fito bata daina banbami ba na shige d'aki. Ina sallah naji Baffa ya shigo yana mata bayanin abunda ya faru yasan halin Lantana da rashin hak'uri sai daya lale kuɗin nan ciff ya biya ta dan kafewa ta yi kuɗin sana'a ne kuma gaba d'aya dan jarin ta tattare ta bani na suyo mai dashi. Makarantar da banje ba kenan ranan na kwanta ko tsakar gidan ban fito ba sai da aka yi sallan la'asar na fito nayi alwala na d'auki abinci na dake cikin kwano na shige d'aki. Haka na wuni sungun -sungun da fargabar abunda zaije ya dawo.
[13/12, 10:25 am] Ashanty 💞🌙: 💎𝐌𝐔𝐋𝐊𝐈💎
👑
By
Ashanty Love.
(M Afnan)
ASHANTY©AREWABOOKS.COM
✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟✯
P 9/10.
Yau tsawon kwana biyu kenan da zuwan Halliru da sakon soyayyar daya kawo. Malam Hallirun ma na daina cewa sai Halliru dan yasan bazai samu damar da yake buri ba. Harta islamiya a kwana biyun nan Kin zuwa na yi da niya nake janyo wani aike da lokacin makarantar ya yi saboda kawai kar naje. Ita kanta Baba mamaki take yanda nake rawar jiki idan ta aike ni. Baffa kuwa bai tab'a tambaya ba dan yasan bana fashin makaranta dole sai da kwakkwaran dalili, shi yasa yanzun ma ya sawa ransa haka ne.
Yau da kaina nakai markad'en awara can bayan layin mu sabida almajirin da yake kaiwa ya tafi garin su noma dan muna cikin lokacin rani ne. Bansan me yasa ba amma tunda na fito sai nake ji kaman ana kallo na. Na juya gabas,kudu,arewa amma banga alamun hakan ba kowa sabgar gabansa yake. Yo ma ina abun kallan ni dai nasan ba wani kyau ne da ni ba sannan abun da ke jan hankalin mazan ma suke kallan matan ni bani dashi. Har naje nakai markad'en na dawo jikina bai daina bani haka haba. Gabda zan shiga gida naji sallamar Halliru kusa dani. Chak na tsaya ina kallan sa gefe na sanye cikin shadda fara yau babu hula a kansa gashin kan nasa yana ta zuba shek'i yasha gyara. Babu laifi ya yi kyau kam dan baza ka kirashi da mummunan ba yana da kyau daidai misali. Baki ne shi dan na fishi haske ga wani gemu daya tara yasha gyara. Sannan bashi da tsayi sosai kusan zan iya cewa da kad'an ya fini.
"Sahla, slma nayi sallama baki amsa ba"
Sanin darajar sallama yasa na amsa masa a cunkushe na cigaba da tafiya yana bina.
"Markad'e ki kai ne?,kawo na riƙe miƙi mana"
"A'a ka barshi na gode"
"Sahla, don Allah kar mu tsaya muna ja-inja a kan titi ki kawo na riƙe, ai ni nace ki kawo"
Badan naso ba na miƙa masa dan nima bana san maganan tayi tsayi tsakanin mu. Har muka k'arasa kofar gida magana yake cikin Jan hankalin da nutsuwa duk da ba bashi amsa nake ba sai naji yau haushin nasa da bnke ji ya ragu. A kofar gida naja tunga na miƙa hannu zan karb'i markad'en ya riƙe.
"Baki bani Amsa taba Sahla, kin amince min na fito? "
Rasa abunda zance masa nayi kawai na d'aga masa kai dan na kagu ya bani kayan na shige gida. Dan in muka cigaba da tsayuwa anan tsaf zan kwarfe shi wlh. Wani irin murmushi ya sakarmin ya miƙo min bokitin na karb'a na shige gida da sauri.
"Ke da waye nake jin maganan ku a kofar gida"
"Malam Halliru ne"
"Waye kuma wani malam Halliru? Halliru ne ko jafaru? Wato kin fara jaye-jayen maza ko?,bari ma..."
Bilkisu ta yi saurin katse ta "Baba shi ne fa Malamin nasu da naji Baffa yana miki magana ranan "
"La'ilaha illallahu Muhammadu rasulullahi (S.A.W), wato labe ki ke mana kenan idan muna magana ko?"
"Nifa Baba ba labe nayi ba kin manta a tsakar gida ya yi maganan ranan "
Tayi maganan tana kunkuni alamun taji haushin kalman da Baban ta furta.
"Au toh yi hak'uri y'ar lele na manta ne ai shi yasa daina fushi "
Kai kawai na girgiza na shige d'aki na barsu nan tana ta faman lallashi. Tun ranan da Baffa ya yi magana kan saurayin Bilkisun ya fito wata sabuwar tarairaya ta tashi. Wani irin kulawa Baban ke bawa Bilkisu saboda burin ta ya cika Bilkisun ta ta samo attajirin mai kuɗi dake yi musu b'arin dukiya ba kad'an ba. Kullum da irin abunda Bilkisun ke shigowa dasu. Da Baffa ya gani ranshi ya masifar b'aci ya dinga fad'a ta inda ya shiga bata nan yake fita ba. Sai ya zama yanzu duk abunda ya bata sai a shigo dashi a boye ba'a barin Baffa ya gani a yanzu haka ma ya chanza mata Babbar waya babu abinda bata yi cikin ta. Ni dama basa bi ta kaina tunda sunsan ba fad'a zanyi ba.
♥︎♥︎♥︎
K'aramar motace kirar BMW fake chan gefen titi bak'a mai bak'in titi. Amin dake zaune mazaunin direba ya juya yana kallan AJ dake kwance bayar motar ya zuba mata ido yana zukar had'addiyar walking stick dake hannunsa gold colour (taba).
"What are we doing here ne AJ?, Akwai wanda za ka gani ne? Almost 1hr kenan munanan baka cemin komai ba"
"I need to know"
Shi ne kawai kalma da ya furta masa. Kan Amin ya k'ara d'aurewa da wannan maganan tashi. Juyawa ya yi shima inda yaga ya maida hankali. Ido ya d'an zare yana kallan yarinyar nan data musu rashin kunya kwana ki. Tabbas ita ce. Tafiya take amma sai waige-waige take kafin ta shige wani lungu riƙe da katon bokiti. K'are mata kallo ya yi bata da wani abu da zata ja hankalin AJ kanta ya .yaga irin y'an matan da suke bibiyar AJ kaf dinsu mata ne da suka amsa sunan Mace. Mata ne da suke so Booby da Assy amma ita wannan gatanan baiga alamun tana dasu ba duk da cewa ta zurma wani uban hijabi ne dake Jan k'asa. Yes a fuska kam tabarakalla dan tana da kyau zaice yasha ganin mata kyawawa na bibiyar AJ da har kyan nasu da ya yi yawa yasa duk kyan ki yake ganin ki saffa-saffa.
Abun tambayar anan shi ne me yasa AJ yau da kansa ya d'auko sa suka zo nan ba tare da matakan tsaron sa ba?. Sunzo kuma sun b'uge da kallon wata yarinya? . Shi yasan tun ranan data yiwa AJ wannan rashin kunyar bai d'auki mata ki a kanta ba akwai lauje cikin nad'i ,tabbas kuma zai gano koma mene. Sunanan zaune sai gata ta dawo still dai riƙe da bokitin kafin ta kauracewa idan su kuma wani ya tare ta suka jera suka tafi tare.
Wani irin mugun smirk AJ ya yi yana zuk'ar tabar sa idanshi a kanta har ta shige gida.
"Let's go"
Amin bai musa ba ya tada motar suka bar gurin ba tare da yace komai ba.
♥︎♥︎♥︎
Ni kaina ina mamakin yanda duk na zubar da maka maina a kan Halliru. Yanda naci burin wulaƙan tashi sai abun ya juye yanzu ina matuƙar ganin girmsa da jin kunyar sa. Bazan iya cewa ga takamaiman abunda nake ji akan sa ba amma nasan kasancewa ta dashi yana sani farin ciki. Ya iya kalamai ne ga kulawa bansan ta yarda zan kwatanta ba. Ana cewa malamai basu soyayya, ni kuma sai nake ganin sunfi samarin ma iya zuba kalamai na love dan gashi cikin dan k'ank'anin lokaci ya chanza min tunani. A yanzu maganan mu tayi nisa dan har iyaye sun shiga ciki sati mai zuwa nake tunanin za'a kawo kayan sa rana da lefe. Bilkisu ita saurayin nata wai ya fita amruka sai ya dawo Baffa yaso a had'a amma daya ga sunfi so s𝐮yi nata bidirin daban sai ya kyale su kawai.
Hira muke nida Sahiba bayan mun taso daga makaranta. Babu irin tsokanan da basuyi min ba bayan sunji labarin soyayya ta da malam Halliru gashi abu ya yi nisa. Tun ina fushi muna fad'a har na hak'ura. Daidai layin su muka yi sallama ta wuce gida nima sai na karya hanya nabi ta lungu ina ganin zanfi sauri ina kuma da suyar awara. Dankareriyar motace bak'a wuluk tasha gabana kaman zata bugeni. Da sauri na matsa gefe na d'ura uban ashar.kam bala'i ai kuwa da an tab'a ni da yau anga bala'i wlh. Bud'e motar a kayi gabana ya yanke ya fad'i. Wannan face d'in da har sallan dare nake Allah karya k'ara had'a ni da ita yau gashi a gabana sanye cikin kananan kaya gajeren wando da riga mai yankakken hannu. Wani salo har ta gashin kansa a tufke yake a tsakiyar kansa dama maza na tufke gashi ne?. Zikiri na fara ina kallansa tsoron sa fal cikin zuciyata amma fuska ta tamke. Ya kara wani irin girma kaman wani bijimi .rigar ita kanta duk da ba mai kamawa bace amma ta kamashi dam kaman kirjinsa zai yaga ta. Da wata irin tafiyar izza ya tako gabana sai dana d'aga kai na kall𝐞 sa. Kai MashaAllah ubangiji ya yi haliitta a nan.
🙆♀️ANYA KUWA AJ?ME KAKE SHIRYAWA NE?
[13/12, 10:25 am] Ashanty 💞🌙: 💎𝐌𝐔𝐋𝐊𝐈💎
👑
By
Ashanty Love.
(M Afnan)
ASHANTY©AREWABOOKS.COM
✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟✯
P 7/8.
Sati d'aya kenan da haɗuwa ta da AJ. Tun ina fargaba da tunani har na sake na cigaba da