Header Ads
Showing 9001 words to 12000 words out of 13485 words

Chapter 4 - MULKI BOOK COMPLETE BY ASHANTY LOVE.txt

Ads the beginning of article before Image

05 Jun 2024

484

Ads at the middle of Article

sabgogi na. Labari dai ya bazu cikin unguwa tun ana fad'an sa daidai ya zama an k'ara masa sukari da wasulalluka. Harda masu cewa ai bashi da karfi dana riƙe wuyan rigars na dinga ta mule dashi ina zuba masa mari sai da ya bani haƙuri, wasu suce A'a ai shine ya dinga zabga min mari na tawo hanya ina kuka. Kuji min mutane da neman min masifa da bala'i?toh Ta Allah ba tasu ba hakan bazai faru ba. A rana idan ban maida zancen nan sau biyu ko uku ba to zanyi sau hud'u. Sosai nayi suna fa duk wanda ya sanni da wanda bai sanni ba yazo wai na gaya masa ya akayi me ya faru ne?. Naga AJ ido da ido?. Ya kamanni sa suke?da gaske yanda ake fad'a yafi haka a fili?. Bilkisu da ba shiri muke da ita ba sai naga mun kulla zumuncin karfi da yaji. D'an abu kad'an za kaji ta jehoni a ciki. ikon Allah. Yanda labarin ya bazu unguwa ya kai har kunnan Baffa ranan nasha fad'a ba kad'an ba rabon da Baffa ya yi min fad'a irin wannan na manta. Baffa shi laifi na ya gani wai da ban kula shi ba na kyale shi inzo shi in gaya masa zaisan yanda zaiyi da Baba Lantana.


Yau tun safe Baba Lantana ta fice ita da Bilkisu wai suna biki can dangin Baban ta. Kananin ta ke Aurar da yarinyar sa. Dana gama abunda na ke miƙewa nayi na kwanta sai barci. Sai wajen la'asar na tashi. Bayan nayi salla na fito ina k'ara kimtsa gidan ina wanke- wanke Baffa ya shigo.


"Uwata ajiye aikin nan ki wanke hannu kije maza kinyi bako a waje"


Da matsanancin mamaki nake kallan Baffa Bako kuma? Toh ni yaushe ma nayi saurayin da har zaizo gida zance?


"Tashi mana kina zaune"


Jiki a sanyaye na wanke hannu hijabi kawai na chanza na fito ina dube -dube. Saboda ya juyamin baya yasa ban gane shi ba na tsaya a bayan nasa ina k'are masa kallo. Shadda ce a jikinsa Ash data sha guga ya karya hula a kai. Gyaran murya nayi tare da yar sallama kad'an. Da sauri ya juyo kuwa na mugun haɗe fuska. Idan ba ido bane kemin gizo to tabbas malam Halliru ne sai wani murmushi yake.


"Kinyi mamakin ganina ko?"


Ido kawai na zuba masa ban bashi amsa ba. Ji nayi kaman na rufe shi da duka me yake nufi ne wai? Allah yasa ba maganan su Barira ce take shirin zama gaskiya ba?in kuwa haka ne toh wlh bai isa ba. Sai ya katse min tunani da cewa


"Nasan za kiyi mamaki da ganina a nan. Sahla ni ba yaro bane bazan tsaya ina b'oye- b'oye ba, tabbas abunda ki ke tunani haka ne. Ina sanki Sahla kuma ba wasa nazo yiba nazo ne da maganan aure dalilin da yasa na fara neman izni gurin Baffan ki. Amincewar ki kawai nake nema ki bani dama na nuna miki soyayya ta inshaAllahu sai kinfi kowa farin ciki zan kasance mai faran ta miki. Zan baki lokaci kiyi tunani amma ina rokon ki don Allah kar kice A'a "


Kutmelesi da alama dai yaci kai ne walh. In banda rainin hankali ya gama cin zalina yanzu ya kewayo wai sona yake?.


"Ki zauna kiyi tunani mai kyau don Allah. Zan dawo gobe danjin amsar ki na barki lafiya"


Da ido na bishi kaman na bishi na kwarfe da wani d'an gololon wando wai shi uztaz. Tsaki naja mai karfi na shige gida ina zagin sa cikin raina babu damar yin hakan a fili dan Baffa yana nan. Maza wlh Sam basu da kunya. Wane baisan irin karan tsanan daya d'oramin ba a makaranta. Bani da ikon yin wani d'an kuskure zai jibgeni kaman ya samu jaka shi ne yanzu dan rashin kunya zaice yana so na yazo da wata y'ar k'aramar murya yana roko? Kwafa nayi na cigaba da wanke- wanke Baffa na bina da kallo. Ina gamawa na d'ora mana wake da shinkafa. Zama nayi kan tabarmar da Baffa ke zaune na fara daka mana yaji.


"Uwata"


"Na'am Baffa"


"Na yaba da hankalin yaron nan. Dama duk wani d'a na kwarai kafin ya fara tare yarinya a waje sai ya fara neman izni gurin iyaye. Saboda haka na amince masa nace duk lokacin da kuka gama daidaita kanku ya turo iyayen sa kawai basai an tsaya ana Jan wani lokaci ba sai a had'a keda y'ar uwarki don itama Lantana ta dad'e da kawomin wani wai yana sonta kuma da gaske auran ta zaiyi"


Wani irin dum naji a kirjina. Abunda bazai tab'a yiwowa ba kenan babu zanchen dai-daita kai. Kai na sunkuyar bance komai ba shima Baffa bai k'aramin maganan ba muka hau zanchen Kaka muna dariya a haka su Baba Lantana suka riske mu.




♥︎♥︎♥︎




PG/18+


THE PALACE.


Katon d'aki ne da idan ka k'are masa kallo ya yi girman wani k'aramin gida guda. Wata irin chandler ce a saman falon da ta kusa cinye rabin silin saboda girma da tsayi. Chan gefe wata katuwar TV ce kaman glass bango gudu sai k'asan d'akin glass ne da wani irin blue ruwa ansa wasu irin kifaye masu masifar kyau suna yawo cikinsa kaman AQUARIUM. Hasken ruwan yasa gaba d'aya d'akin ya bada wani irin blue dim light mai masifar kyan gaske idan ka shiga kaman kar ka fita. (ALJANNAR duniya kenan) Ga wasu irin kujera kaman koshin farare da swing chair a chan gefe. Babu wani tarkace a falon hakan ya kara kawata shi sosai. Slow music ke tashi cikin d'akin dum-dum kaman d'akin zai ruguje. Chan kan wata kujera da tafi ko wacce girma kaman gado tana swinging a hankali yake kwance daga shi sai gajeren wando dake so tight a jikin sa. Wasu y'an mata ne guda biyu turawa d'aya kan cinyarsa d'aya gefen sa. Wani irin lap dance suke bashi suna striping kayan jikin su . Yanda d'ayar ke zaune kan kugun sa tana juya mazaunai kan mini d'in sa wadda ke gefen sa tana shafa kirjinsa da packs dinshi cikin wani irin salo yaci ace imma release ne ya yi sau uku ko biyu. Awa biyu kenan tun d'azu suna abu d'aya amma nothing babu wani reaction yana nan kwance kaman lawashi. Su kansu sun gaji basu isa kuma su furta hakan ba. Tabar dake bakinsa ya zuka ya buɗe manyan grey eye's dinshi dake rufe. kallan yarinyar dake kan cinyarsa ya yi da wata irin deep voice yace


"Leave "


Tun bai k'arasa furta leave din ba suka miƙe a guje suna tsince kayan su dake yashe a k'asa. Wasu rafars na dollars ya d'iba guda biyu ya watsa musu a guje suka kwashe sukayi waje basu da matsalar komawa gida. Private jet ya tura tun daga can London aka d'auko so, za kuma a mayar dasu. Ya jima a kwance bayan tafiyar su kaman wanda aka tsikara ya wani tashi a fusace ya yi tankamemin toilet nashi dake k'asa. Had'addiyar shower d'inshi ya shige da aka kewaye da glass. Komai na toilet din gold colour ne( waya sani ma ko gold dinne ba kala bace.haha). Ruwan sanyi ya sakarwa kanshi hannushi dafe jikin bango ruwa nabin kansa da bayan sa. Idansa dake rufe ya buɗe saboda jijiyarsa da yaji ta wani harba kaman wutan nefa. Dif ta kawo ta d'auke. Ba komai ya jawo hakan ba sai flash na wannan bak'ar yarinya data yi masa gizo lokacin da hannunsa ya tab'a ta. A 31 life nashi wannan shi ne karo na farko da ya samu wani reaction game da mace koma macen ma bak'ar fata da yake ganin su kazamai munana shi yasa takanas ya yi hayan turwa tun daga waje, kalar sa.ko matan da suke bibiyar sa babu bak'ar fata sai in bakin naki ya kasance mai haske kaman na yan Morocco ko Ethiopians or Black Americans, but wannan bak'a ce. She is black. Shi kanshi ya yi mamakin kansa da a wancan ranan bai chanza mata kamanni ba wannan feeling shi ya yi holding dinsa back. Ya tsani mace ko wace iri ce ta rab'e shi amma yau gashi da kanshi bayan wasu shekaru da suka shud'e ya hayo strippers tun daga London dan ya tabbatar da abunda yaji ranan. Yana so ya tabbatar wa kansa ba ita ce ta janyo masa wannan reaction ba ,baya yafiya he will soon destroy her.


Wani irin harbawa ta k'ara yi ya yi wuf ya damke ta cikin hannunsa ya matse ta da karfi. Sai kuma diff ta k'ara d'auke wa kaman an kashe wutan nefa ta koma kaman lagwani. Ajiyar zuciya ya sauke mai karfi ya kaiwa bango naushi.


"What the f*ck just happened? "


Ya yi tambayar da babu mai bashi amsa .
All this facade da yake sawa na Bad boy characters yasan cewa deep down his not A REAL MAN.
Ya yi hiding the Real AJ a wannan fuskar.




♥︎♥︎♥︎




Cikin matsanancin damuwa ya juya ya koma inda ya fito sakamakon karo da yaci da y'an matan da suka fito daga bangaren AJ. A Koda yaushe addu'ar sa guda d'aya ce duk sanda ya kai goshin sa k'asa. Allah ya shirya masa yaran sa su dawo kan hanya mai kyau. Hajiya Kilishi dake kishingid'e cikin kayatatcen falon ta bayi na kanta wasu na mata tausa da firfita wasu na bata labari dan nishaɗi. Yana shigowa duk suka miƙe cikin girmamawa suka fice daga d'akin. Guri ya samu ya zauna kusa da ita cike da damuwa. A duk masarautar nan ita kaɗai ce macen da yake samun nutsuwar zuciya a tare da ita saboda macece dake da nasibi da kuma hangen nesa.
Tasowa ta yi har inda yake zaune ta durkusa gaban sa tana murmushi mai k'ayatar wa.


"Wanene ya tab'a min Baban JABEER , mijina abin sona abin alfahari na. Bacin ranka babban tashin hankali ne a gari ni farin cikin ka tamkar ammin albishir ne da Aljanna. Gayamin waya tab'a min kai ka ke fushi yanzu nan na d'auki mataki a kansa"


Duk irin damuwar daya shigo da ita saida ya saki murmushi. A duk lokacin da yake cikin damuwa irin wannan tasan hikiman da zatayi ta mantar dashi damuwar da yake ciki shi yasa yake alfhari da ita.
Tafi mishi sauran matan shi da babu abunda suka sa gaba sau kishi.


"Kinsan maganan gizo bata wuce ta koki. Nida wancan yaron naki ne. Na rasa yanda zanyi da JABEER ya nutsu ya daina duk abinda yake. Lamarin sa kullum sai k'ara tabarbarewa yake. Yanzu na fito daga sashen sa naci karo da mata suna fitowa babu ko suturar arziki a jikinsu. Yanzu me ki ke tunani zai faru idan aka ji wannan babu cikin masarauta? Kullum da abinda za'ace Jabeer ya yi. Ni na gaji ina ganin zance masa ya moma gurin uwarsa kawai dama ai ita take d'aure musu gindi har suka zama abinda suka zama, da tabani su tun-tuni dana ce ta bani da duk hakan bata kasance ba"


Cikin matsananciyar damuwa ya k'ara maganan kaman zaiyi kuka. Kuss dashi ta zauna duk cewa girma ya kama su bai hana ta mayar dashi yaro karami ma a duk lokacin da suke tare. Janyosa tayi ta kwantar kan cinyar ta tana shafa masa kai a hankali kaman maiyi masa tausa.


"Addu'a zamu dage mu cigaba dayi masa inshaAllahu Jabeer na kan gab'ar shiriya.kar kace haka. Ita jarabawar Ubangiji tana kan kowa ne. Sai kaga suna hannun naka amma idan Allah ya yi da wannan hali shima bazasu fasa yinsa ba. Bana so kana ganin Laifin MaMa QUEEN akan haka. Tana K'ok'arin itama a kansu .Kasa a ranka kaman ya shiryu ne da yardar Allah zaka zama mai alfahari da haihuwar sa bama kai kad'ai ba harmu kanmu ,Ba'a yanke kauna da rahamar Ubangiji. Shi mai harama ne a koda yaushe. Mu dage dayawan Addu'a da kuma sadaka ka kuma kasance mai adalci ga al'ummanka ,ka kasance mai tausayi da duba na k'asa dakai. ALLAH bai baka mulkin nan ba dan kafi wani ne. A'a shima mulkin yana d'aya daga cikin kaddarar ka ne. Mu dage dakai masa kukan mu Allah zai amsa mana da yardar sa"


Bata yarda yabar sashen taba saida ta tabbatar damuwar daya shigo da ita ta ragu. A lokacin da yake bangaren nata kuwa tuni labari ya cika masarauta Yarima ya d'ebo karuwai daga kasar waje sarki da kanshi ya gansu amma ya kasa taɓuka komai a kai. Magana taita yad'uwa ana ta cece-kuce. Mak'iya suka samu abun fad'i wajen ganin sun kawo karshen Mulkin sarki Saif da D'ansa Yarima AJ ko nace King AJ.
[13/12, 10:25 am] Ashanty 💞🌙: 💎𝐌𝐔𝐋𝐊𝐈💎

👑
By


Ashanty Love.
(M Afnan)


ASHANTY©AREWABOOKS.COM


✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟✯



MMN MEENAL


WANNAN PAGE NAKI NE,KIYI DUK YANDA ZA KIYI DASHI😎






P 11/12.


Last free pages.






Cikin dakiya nace




"Lafiya dai malam?"


Sai da ya d'auki wajen minti biyu kafin ya fara magana da d'ai-d'ai. Har na kosa ina shirin juyawa a fusace na bar gurin.


"Did- you- think -you- will -get away -with -what you have done?"


La'ilaha illallahu Muhammadu rasulullahi (S.A.W). Shi kenan yau ya zage ni har tattaba kunne. Uwarki,ubanki,kakar ki? Har Baba Lantana bai kyale ba saida ya sata Babar ki Lantana?. Eh toh banji haushin zagin ta da ya yi ba ita .Aikuwa na d'ora hannu aka ina ihu


"ya zagarmin iyayi har tattab'a kunne, toh wlh badai uwata ba ta mutu sai dai ko in taka"


Wani irin kallo ya min ya k'ara matsowa gab dani sosai nayi saurin ja baya sai ji nayi na jingina da bango ginin wani kango d'aya sha gabana. Gaba d'aya ya saka hannu ya dafe saman kai na ya sani tsakiyar sa . Wani irn bugawa kirjina ya yi na fara wurga ido ko zan hango gilmawan wani shegen layi shima kaman anyi ruwa an d'auke babu kowa .


"Kaga ni ba yar iska bace ka matsamin na wuce"


Kaman ba bada mutum nake magana ba dan hankalinsa gaba d'aya ya kar kata kan wani abu daban. Da sauri nima na kai kallo na inda ya maida hankali. Gaba d'aya hankalin sa da nutsuwar sa na kan kirjina ne babu wani alamun damuwa ko shakku a tare da shi. Wani irin ihu na saki da kururuwa bansan sanda nakai masa mari ba na fashe da kuka. Da azama na durkusa na fita ta karkashin sa.


"Allah ya isa, dan iska arnan banza da wofi."


Fuu na wuce ina kuka harda d'an gudu na da share majina. Eh lallai na yarda shi din hatsabin dan iska ne. Yanzu duba yanda ya tsaya yana karewa kirjina kallo ba tare da wata damuwa tattare dashi ba abin haushi a titin Allah?. Allah ma ya taimake ni babu kowa yanzu idan an ganmu a haka me za'a ce? . Gabda zan shiga Layin mu na tsaya na saita fuskata kaman babu abunda ke damuna.




♥︎♥︎♥︎




Matsanancin mamaki yasa shi daskarewa a tsaye ya kasa motsi har ta b'acewa ganin sa . What the f*ck? Yau shi AJ wata k'aramar banzar yarinya ta mara? Shi AJ da a kewa inkiya da King? . Shine fa ko sunan sa aka ji yara da manya suke firgita .shi ne fa, shi ne fa..wai what the f*ck is happening ne da yake kasa reacting a kanta kaman wadda take saka abu ta d'aure .what kind of magic take amfani dashi a kansa da wani irin zuciya ya fisgi murfin motar zai bud'e tsabar yanda yasa kwanji gaba d'aya murfin ya baro daga jikin motar kai kace irin abu ne mai sauki da ana tab'a shi zai b'alle. Wurgi ya yi da murfin motar ya fad'a ciki haka a zuciye ya tada motar da wani bala'in gudu ya harba ta kan titi.


Ta baya ya shige inda yake ajiye motacin sa da sunfi gudu ashirin latest duka-na dukan wannan. Duk da cewa a sirrance ya shigo amma labari tuni ya baza masaurata yarima ya dawo rai bace ga motar da yafita da ita babu murfi. Tuni aka fara shiga taitayi da gujewa haɗuwa dashi. Maimartaba yana fada da wasu manya baki da suka zo daga zaria. Magana suke akan sarkin zazzau ya turo su dan k'ara karfin zumuncin dake tsakanin su ta hanyar had'a yaran nasu aure. Har suka gama jawabi sarki Saif bai iya cewa komai ba sai murmushi da ake cewa yafi kuka ciwo. Harga Allah zaifi kowa san wannan had'in amma bazai so ya zama mai san kansa ba. Kwata-kwata gimbiyar Juwairiya bata dace da wannan tak'a d'irin d'an nashi ba. Yana mamaki yanda yaran sarakai da suke mutunci suke nacewa JABEER dinsa duk da sunsan halin sa da kuma tarbiyar da yake da ita shi yasa idan sunzo yake fad'a musu gaskiya amma sai yasha mamaki da amsar da suke bashi sunsan halinsa sunsan wane shi a hakan kuma suke so a had'a. Bazai manta had'in da ya yi ba da yarinyar sarkin Abuja. Sai da ran kowa ya baci amma duk da haka basu saduda ba har yanzu suna bibiyar yaron nasa.


Kasa cewa komai sarki ya yi har suka gama jawabi. Waziri dake zaune ya karbe zancen


"In banda abun Gimbiya Juwairiya me za tayi da d'an iskan yaron da kowa yasan halinsa na bin mata da shaye-shaye. Ga yara nan masu hankali da nutsuwa ga Amin d'an gurina abunda ya yi Yarima ai shi ya yi amma tarbiyar ba d'aya bace tunda shi yana da hankali sai tafi kowa farin cikin samun sa a matsayin miji".


Wani irin abu ne mai daci ya daki kirjin Maimartaba. Bashi da wani abu dazai furta ko kare d'an nasa dan gaskiya ya fad'a. Duk da haka Murmushi ya yi mai ciwo yana kallan mijin yayar tashi dake kuma wazirin sa. Kaf fad'in masarautar nan su uku kawai Allah ya bawa margayin Sarki Baban su daya rasu shekaru da d'an dama. Khalisa ita ce babba sai shi Saifullahi sai kuma autar su Zeenat da suke kira Gimbiya. Ita tana can US da mijinta da yaran ta dan taki zaman nan. Tun kuruciya shida Khalisa sun taso ne masu banbancin ra'ayi. Tana da san mulki da

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads