Showing 12001 words to 13485 words out of 13485 words
Chapter 5 - MULKI BOOK COMPLETE BY ASHANTY LOVE.txt
nuna isa da iko. Da ace ita da take babba Allah ya yi ta namiji toh da tabbas ita zata maye gurbin mahaifin su. Toh sai Allah yasa tazo a mace ya kasance shi ya gaji babansu. Wannan dalili yasa basu jituwa da ita sosai dan har yau bata fidda ran cewa d'an ta Amin zai gaji mulki ba tunda shi ya yi mulki toh itama dole ne wani nata ya yi mulki dalilin da yasa tasan duk yanda za tayi aka dora mijin ta (Shazali) a matsayin Waziri dan tace ba'a isa shi kaɗai ya yi mulki ba da nashi iyalan itama dole tana da hakki a kai.
"Allah yaja da ranka wannan sako ne daga sarkin zazzau, kafin muzo ma saida ya kara jadda cewar yasan halin sa yasan kuma halin ubansa. Saboda halin sa baza a kii had'a zuri'a ba mai inganci. InshaAllahu zai shiryu shi d'a ai nakowa ne babu wanda Allah baya jarabawa da irin su .Baban sa mutumin arziƙi laifin d'an sa bazai shafe saba tunda kowa yasan irin k'ok'arin da yake a kansa. Kasan ance aure ma yana gyara mutum inshaAllahu Juwairiya zata bada nata gudun mawar wajen jawo hankalinsa ya zama nutsutstsen yaro bacin haka ma ita da kanta tace taji ta gani tana san sa a haka. Mudai fatan mu ku bamu amincewar ku"
Kululun bakin cikine ya tsayawa Waziri ya kasa maida martani dan sun d'aure shi. K'aramin tsaki yaja da Maimartaba kad'ai dake zaune kusa dashi yaji ya saki murmushi yana mai jindaɗin wannan kalma da suka furta. Kama wanda aka jeho ya shigo fadar rai b'ace .tafiyar sa kad'ai ya isar musu da shigowar sa tun kafin ya bullo idon su. Tsakiyar fadar ya tsaya yana zuba uban huci ko kaɗan bai damu da mutanen dake cikin fadar ba bare su samu arziƙin sallama bare gaisuwa.
"Kunga abinda nake fad'a muku, baya ganin kowa da daraja. Yanzu fisabillahi me za'ayi da wannan a matsayin miji da baya ganin girma da darajar iyayen sa bare na gaba dashi."
Wani irin mugun kallo AJ ya wurga masa ya yi saurin d'auke kai koda wasa baya iya furta magana irin haka a gabansa sai dai bayan idansa ko gaban Sarki tunda yasan yanda Sarkin keda sanyi duk irin zagin da cin mutuncin da zaiyi bazai d'aga kai ya kalle sa ba. Wani lokacin shi ke k'ara hura wuta wajen ganin ya b'ata AJ cikin masarauta. Wato daga shi har Khalisa komai nasu iri d'aya ne shi yasa suke zaune har yanzu ba tare da anji kansu ba. Suyi ta had'a tuggu da munafurci.
Runtse ido Maimartaba ya yi zaciyarsa kaman zata buga ya buɗe su ya yi d'an murmushi na yake ya miƙe yana bawa bak'in hak'uri da inshaAllahu zasuji daga garesa nan bada jimawa ba. Wuce AJ ya yi dake tsaye har zuwa lokacin yana huci cikin kowa ya d'uri ruwa babu wani wanda ya k'ara motsi tunda ya shigo fadar.
Kaf dinsu ya bisu da shegen kallo kafi ya juya a zafafe ya bi bayan Maimartaba. A katon falon shi ya riske sa tsaye ya zubawa k'ofar da zai shigo ido yana ganin sa kuwa ya saki ajiyar zuciya ta taho gabansa ya kama hannunsa zuwa tsakiyar falon. Ido ya zubawa d'an nasa yana nazarin sa. Hakika Allah ya yi wa yaron nasa baiwa da ba kowa keda ita ba. Idan ka kuruwa idan nasan ido sai kaga kwayar har wani kyallin take kaman zaiba. Numfashi yaja mai karfi
"Jabeer, kana so ne zuciyata ta buga sabodan bak'in cikin ka ne, me yasa a koda yaushe kake son gani na cikin bacin rai?,kafi burin ka ganni ne a kwance na kwanta ciwo?"
Kai ya sunkuyar jikinsa ya yi sanyi amma fuskar nan tana nan cunkushe.
"Sorry Dad"
Dago fuskar tasa ya yi suna kallon juna.
"Mene ya samu fuskar ka naga alamun hannu"
Ai kuwa ya k'ara tunzura ya fara muzurai
³
"She slap me"
"Ita wa?" Cikin matsanancin mamaki Maimartaba ya kara jefa masa tambayar. Leb'ensa na k'asa ya cije kaman zai fasa leb'en. Da sauri ya kai hannu kan fuskar tasa yana girgiza masa kai.
"Wacece ta mare ka Jabeer?,what did you do"
Haushi ya kamashi wato ma bai damu da marin da wata banza tayi masa ba sai abunda shi ya yi mata?
"Me kayi mata Jabeer?, Allah yasa baka cutar da y'ar mutane ba"
A harzuƙe yace " I did nothing, ...I did nothing " fuu ya wuce shi yana zuba uban huci. "Am going back to mom right this moment" . Bam ya bugo k'ofar. Ya jima a tsaye yana k'ara maimaita kalman a zuciyar sa. Murmushi ne ya kubce masa a karo na farko a rayuwar Jabeer wani ya masa abu bai d'auki mataki ba? Wanin ma mace?. Wacece wannan YARINYAR?. dole ma a nemo masa yarinyar duk inda take.
♥︎♥︎♥︎
ANONYMOUS PERSON
Boyayyen Mutum.
D'aki ne k'aramin mai masifar duhu tamkar a karkashin k'asa. Sosai d'akin ya yi kama da perfect hiding spot da in ba wanda yasan dashi ba babu ta yanda za'ayi a sani. Dim light ne a d'akin red mara haske dan dole in kashiga sai ka kunna torch saboda rashin hasken fitilar. Y'ar igiya ce mai tsayi a d'aure lungu da sak'o da wasu hotona birjik a jikin ta kaman shanya. Can gefe yake tsaye jikin wani tebir kato yana duba wasu hotuna dake kai . Kofar aka buɗe a ka shigo bai juya ba tunda yasan mai shigowa. Daga shi sai wanda ya shigo suka san da wannan d'akin.
"Ya ya ake ciki ne?, ka samu wani news ne?"
"Kaman dai koda yaushe babu cigaba dan gane da wannan harkar sai yau nema muka samu wannan duk da nasan ba wani abu ne mai muhimmanci ba"
Wani hoto ya d'auko daga cikin ruwan wanki yana nuna masa. Murmushi ya yi mai k'ayatarwa.
"Wacece wannan d'in yake tare da ita haka a kan titi?ina so a binciko min ita ko wace kayi editing hoton nan sosai ta yarda babu yanda za'a gane ba gaskiya bane hoton. "
"Amma ita yarinyar fa?kana ganin baza'a a sata cikin matsala ba, alamu sun nuna batayi kama da irin karuwan da yake hurda dasu ba?"
"I dont care. Tunda har ta rab'i AJ tasan rayuwar data jefa kanta. So edit this pictures ka bani mu jira perfect opportunity da zamu sake so"
K'arasa maganan ya yi da wani mugun smirk ya juya ya fice a d'akin.
♥︎♥︎♥︎
Tun ranan da wannan abu ya faru tsakanina da AJ nake Allah ya isa da Allah wadai da masu hali irin nasa. Ko kaɗan ban bari damuwar da nake ciki an fuskanta ba a gida ina iya k'ok'arina wajen b'oye wa. Gobe ne nake tunanin zuwan y'an uwan Malam Halliru kaman yanda muka lissafa. Da wuri yau Baffa ya dawo da kayan cefane. Gaba d'aya yau wunin ranan aiki mukayi ta yi har Bilkisu sarkin san jiki ta dan tab'a wani abu babu laifi. Ana yin sallan isha kuwa na watsa ruwan zafi na kwanta sai barci. Washegari da safe da wuri na tashi nayi duk abunda zanyi karfe takwas na fice daga gidan zuwa gidan su Sahiba duk da nasan cewa ba lallai ne zasu zo da wuri ba amma gwanda nabar gidan da wuri.
Dariya Sahiba ta kwashe dashi tana kallo na. Tun zuwana take yimin wannan dariyar kaman mahaukaciya har ta bani haushi tun ina masifa na daina kula ta.
"Yanzu wai da gaske kin kusa zama ta Malam Halliru?, oh ni Sahiba inga idon wadda take cewa Allah ya kiyaye tayi soyayya da Malam Halliru ko maza sun k'are. Har na hango y'ay'anku wa yaga Sahla a gidan Halliru "
Sai ta kara kwashewa da wata dariya na kuwa cika nayi fam kaman zan fashe. Da nasan iskancin da zata sani gaba tanamin kenan da banzo ba nayi zamana a gida. Karar wayarta ne ya katse ta ta daina dariyar ta d'auki wayar tana dubawa. Sai naga ta miƙe zaune daga kwancen da take da sauri ido waje tana kallan fuskar wayar. Matsowa nima nayi dan naga abunda take kallo har ya raza nata haka. Mugun sarawa kaina ya yi take naji wata hajijiya ta kamani duk da a zaune nake saida na zube k'asa warwas. Innalilllahi wa Innailaihi raji'un. Wayyo ni Sahla meke shirin faruwa dani ne??
🙆♀️🙎♀️!
Me kuke tunanin ya faru ne??
Sarki zai sa a nemo masa SAHLAN KUWA?.
Idan ya nemota mu kuke tunanin zai faru?
Shin AJ Zai kyale Sahla bayan duk irin wannan rashin mutunci da tayi masa?
Mene AJ YAKE BOYEWA NE da babu wanda ya sani sai shi sai Allah daya haliccesa?.
Su waye waɗannan mutena da suke had'a wannan tuggu ta karkashin k'asa?.
Auren Sahla da Malam Halliru mai yiwuwa ne ko A'a?
Karku bari a barku a baya ku biyoni dan muyi tafiyar daku.
KAMAN YANDA NACE A K'ARSHEN LAST FREE PAGE ZAN K'ARA SAKA WANI NOTE. GASHI
👇
NAN MUKA KAWO KARSHEN FREE PAGES NA LITTAFIN 'MULKI'. DUK MAI BUKATAR CIGABA ZAI BIYA NAIRA 400 KACAL TA WANNAN ACCOUNT NUMBER D'IN.
👇
3078293374
AISH SANI DANJUMA
FIRSTBANK
A TURO SHEDAR BIYA TA WANNAN NUMBER.
👇
08140754777