Showing 9001 words to 9515 words out of 9515 words
Chapter 4 - YARON GIDANA Complete Romantic Novels By Oum Afnan.txt
na ajiye aikin!”
****
El’ameen hankalin sa in yayi dubu ya tashi ,da ya fito yaga Kausar ta fice da asussubahin nan ,amma hankalinsa bai ƙara tashiba saida yazo kwanciya barcin bayan asuba yaji yayi juyi a fitsarin da tayi ,zabura yayi ya miƙe ya dangwala yatsarsa ya shinshina tabbas ga zarni nan fitsari ne.
Sai falo ya koma yaje ya kwanta bai tashi ba sai tara saura ,a kiɗime ya miƙe yayi shirin office ya tafi ,sauri sauri. Yayi mamakin barcin da yayi.
Yina shiga Companyn office dinta ya fara shiga a rude amma bai ganta ba ,Sambatu ya farayi
“Ya Allah ina rokonka kasa yarinyar mutane ba ɓata tayi ba”
Motsi yaji ta bayansa yayi maza ya waiga Juliana ce tsaye ta riƙe ƙugu
“Lafiya ? Ina Kausar ? Tazo kuwa?”
“Kai zan tambaya ina Kausar,sarai na fahimci babu jituwa tsakanin kai da Kausar ,sannan jiya har yamma lis kuna wajen nan har saida ka ribace ta kuka fita tare ,yau kuma babu kai babu ita bayan munsan Kausar bata taɓa kin zuwa aiki ba koda da dalilin fashinta sai ta sanar da Awanni kafin lokacin aiki”
Hankalinsa a tashe yace “Me to kike nufi kina nufin na sace Kausar ko yaya?”
“Ko ma salwantar da ita kayi duk za kayi bayani ,malam have a look of your self ,ka shigo a furgice kana neman ta ,matar da baku shiri me ya fitar daku tare da yamma lis jiya?”
“Saboda ta sallameni a aikin kamfanin nan na koma yaron gida nta”
“To meyasa baka bita gidaba sai kazo nan office ɗin?”
“saboda bansan gidansu ba ”
“kaiii 🙄bakasan gidansu ba ?jiya da kuka fita ina ka kaita”
“Gaskiya na gaji da tambayoyinki,ki bari in Kausar din tazo kya tambayeta”
“kai abun tuhuma ne ,Amma bincike zata biyo ta kanka” ta ƙare magana tana nunasa da yatsa.
Kife kansa yayi da jikin ƙofa,baisan dalili ba yaji hawaye na gangaro masa a fuska
“Allah kasa ba yarinyar mutane wani abu ya sameta ba bayan ta fita daga gida na ba ...” wani wutar sonta a take yaji yina Daɗa ruruwa masa a birnin zuciya.
Office din nata ya koma ya zauna akan table dinta ya fara da ɗaukan wani ƙaramar album ɗin ta na hotuna ya soma buɗawa hotonta ne ya soma gani a sama ,ƙyam ya tsaida idonsa akai ya sa yatsa yina kewaye fuskarta yina mata sambatu kamar mahaukaci.
Tambaya?
_Shin Kausar da gaske ta ajiye aikin companyn ne ko zata koma?
_Yaya makomar soyayyar El’ameen da Kausar ,anya mai ɓillewa ne?
_Kausar dai tayi masa fitsarin kwance ya haduwarsu zata kasance a matsayinsa na direban ta? Wulakantasa zata cigaba dayi a matsayinta na ogansa ,ko kuwa sallamarsa zatayi bata bukatar aiki dashi kuma?
Wannan dama sauran bayanan da suke rufe sai mun hadu a littafi na biyu ,karku manta mundaiji Kausar harija ne,amma me yake sata fitsarin kwance? Kuma wani irin sadaukin miji zai iya mata a shimfida
Wannan da sauran tambayoyin duk amsoshinsu suna littafi na gaba
Ku biyo oum Aphnan ta hanyar biyan kudinku ta daya daga cikin wannan hanyoyin Katin mtn ta wannan Number 09065990265 ko a tura ta asusun banki na
7782217014 ,mohammmed Hassana ,fcmb
Oum Aphnan
09065990265