Showing 6001 words to 9000 words out of 11148 words
Chapter 3 - DARASI Book 1 Complete Document by Miss Green .txt
taimakon gaggawa,sai dai mahaifin Fahima har yanzu bai farfaɗo ba amman Fahima ta farfaɗo.
Allah sai kun fara comments zan fara yin sa da yawa.
*Miss green ce*
*DARASI!!*
Free page 8/9
Rabiatu Bashir
(ummu maher)miss green.
*Ga masu buƙatar a tallata musu hajarsu ta online zasu biya 2k*
08/09
. . . . .har yanzu mahaifina bai farfaƊo daga suman da ya yi ba,sai dai yana numfashi,hankali na ya tashi sosai don likitoci sun faɗamin Mu biyu aka kawo mu ni da mahaifina,kuma tunda aka kawo mu ƴan sintirin da suka kawo mu sune suke biyan kuɗin.
Amma tana gidan goggo mahaifiyarta sai faɗa ta ke mata na rashin mutuncin da ke yi,gashi yanzu daga ni har mahaifina babu mu babu labarinmu,sharce hawaye ta yi da majina ta ce"wallahi Goggo ni fa ban san yadda a kayi yarinyar na neme ta na rasa ba,daga tura ta talla tun jiya bata dawo ba,idan zubarda kuɗin tallan ta yi ta dawo mana,shi kuma Malam da karan baninsa ya tafi nemo ta,gashi yanzu babu labarinsu su duka".sai ta cigaba da kukanta.
Tun da ta fara maganar Goggo ke yi mata wani banzan kallo,sai da ta gama sannan ta ce"wai ni kuwa Amaturrahman kina da kirki kuwa?"cewa fa ki ka yi wai mahaifinta ya yi karanbani?shi da ƴarsa sai yaƙi fita nemanta saboda sakaci da kuma rashin hankali?,ke irin wannan riƙon na yi miki a rayuwarki?tambayar ki na ke yi?".kamar za ta daki Amma ranar ta yi suna cikin wannan halin ne a kayi sallama a ƙofar gida.
Kallon banza Goggo ta yiwa Amma sannan ta ce"w/kslm waye?".ta ɗauki mayafinta ta leƙa.
Salati ta fara yi tana kiran sunan Allah tana cewa"to shikken Mlm Bashir yanzu zamu taho insha Allah",da sauri ta dawo tana faɗawa Amma wai ƴan sintiri ne jiya suka kai su Fahima da mahaifinta asibiti,kuma tunda safe akaje cen gidan Amma ba a sameta ba,shine Bashir ya ce yasan kina nan gidan.
Bakin Amma bai mutu ba da abinda ya faru da mijinta da ƴar ta ba sai cewa ta yi"Hmm su Bashir an riƙa wajen iya gulma yanzu har yasan nan na taho?".
lokacin har Goggo ta saka hijabi ta ɗakko kuɗi ta ɗaure a bakin zaninta"ta ce to maras tunani idan kin gama gulmar mutane ki tashi mu tafi?wa wiya kawai mara tunani,har a wannan halin da ake ciki bakin ki bai mutu ba".
*** *** ***
abin mamaki Sakinat tana fara kuka hankalin Ammar ya tashi,ya kalli Khalisat da ke jikin Mahaifiyarsa tana kuka ya daka mata wata uwar tsawa ya ce"shut up!ki yiwa mutane shiru munafuka wato daman bakya son matata ko?to wallahi ko waye zai ƙi matata ko waye wallahi tallahi saina rabu dashi".ya faɗi hakan cikin yaran fillanci ya riƙe hannun Sakinat suka yi wuce warsu,Sakinat harda wani la fewa ajikin Mijinta tana yiwa su Ammi gwalo.
Ni kuwa na ce oh Sakinat kamar abin arziƙi haɗa ɗa da uwa,Duniya ina zaki damu😭.ya Allah ka haɗa mu da surukan arziƙi Amin.
Sororo Ammi ta yi tana kallon bayan ɗanta Ammar,shi kuma tasa ƙaddarar kenan mace,jiya i yanzu yana tare da ƙanwarsa suna hira kamar abin arziƙi,amman yau daga zuwan matarsa har komai ya watse.
Wasu zafafan hawaye ne ya fara zubowa Ammi a ƙwarmin idanunta, bata san sanda Khalisat ta saka hannu ta fara share mata hawaye ba,ita ma Khalisat ɗin kuka ta ke na tausayin kansu"Ammi ki yi haƙuri don Allah kinji,komai ya yi farko yana da ƙarshe kada ki saka wannan abin a ranki kinji?".rungume junansu sukayi suna tausayin kansu dana Ammar.
Har sun manta da tsayuwar Amir sai da sukaji yana cewa"haƙiƙa Sakinat ba ƙaramar butulu ba ce da ta manta,da duk abin arziƙin da ki ka yi mata ta butulce miki,ta zaɓi taci miki mutunci ta kassara miki rayuwaɓ,ta zaɓi hanyar musguna miki ta hanyar mallake miki ɗanki,amman babu komai aƙwai Allah."
Matar Amir ma har kuka ta yi don ganin abinda ya faru,tana yawan ji a littafin hausa da sauran kafofi yadda ƴaƴa suke wulaƙanta iyayensu, amman bata taɓa gani da idanun ta ba sai yau.
a ranar Sakinat ta saka mijinta a gaba kamar mayya suka tafi Abuja,shi kuwa Amir saboda haushi daman alokacin ya tafi gida,saboda takaicin hali irin na Ammar ace ka rasa wanda zaka ƙunta tawa a rayuwarka sai mahaifiyarka wacce tasha wahala a rayuwarta don rayuwarka ta ginu?gaskiya abin aƙwai lauje cikin naɗi.
Ranar gidan Ammi kamar ana zaman makoki,gidan shiru don ɗan wannan zuwan da Ammar ya yi komai sun ƙara shaƙuwa sosai,ranar kusan raba dare Ammi da Khaisat sukayi suna kaiwa Allah kukansu ta hanyar yin nafilfilu.
Abin mamaki ranar Amma ta saka rigima wai mu koma gida alhalin har yanzu mahaifina bai farfaɗo ba,aranar na sake tabbatar da rashin tausayin Amma,Goggo ce tace mata idan ta gaji a yini ɗayan da ta yi,to ta tafi gida ita za tayi jinyar sa tunda shima ɗanta ne,jin wannan da Amma ta yi yasa ta zauna amman ba don ranta yaso ba don biyunnan da ta yi bata yi sana'a ba abin yana matuƙar damun ta sosai.
Hmm kuji fa rashin tausayi irin na wasu matan,mijinki yana ƙwance bashi da lafiya,mijin da ki ke saka ran samun aljanna ta ƙarƙashinsa amman ace kina nuna masa rashin tausayi haka?😭.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.
A ranar likitoci sukayi bincike wai mahaifina ya. . . .
Yasin idan kuna comments da yawa zan ƙara yawan tyiping oh.
*Miss green ce
*DARASI!!*
Free page 10/11
Rabiatu Bashir
(ummu maher)miss green.
*Ga masu buƙatar a tallata musu hajarsu ta online zasu biya 2k*
10/11
A ranar likitoci suka yi bin cike suka gano mahaifina ya kamu da ciwon ɓarin jiki,kuma suka rubuta magani da allurai masu tsada wai saboda idan aka yi mishi zai samu reliep kuma idan yana samin kulawa zai warke baki ɗaya,magani da allura shine ya tashi dubu sittin da biyar,kai tsaye Amma ta ce wai mu tafi gida ba sai anyi masa ba,wataran idan Allah ya kawo ayi aikin.
Hankali na dana Inna ya tashi sosa ta fashe da kuka tana cewa"oh Allah sarki Abu kin bani amanar Ɗanki yanzu gashi na kasa riƘewa",,sai ta fashe da wani kuka mai cin rai.
Fahima tana gefe itama tana wani irin kuka wanda harda amai sai da tayi kamar ance mahaifin ta ya rasu ne.
Ƙwanci tashi asarar mai rai yanzu watan Baba na huɗu da samun matsalar ɓarin jiki wataran ma har yamma baya samun abincin da zai ci,ya rame ya zama wani kamar tsoho ɗan shekara sittin abin dai gwanin ban tausayi.
Rannan na fita talla ina tafiya ina hawaye bana ganin gaba na ballan tana baya na,kawai sai ga wata mota ta yi saurin yin ribas don ashe ina tsakiyar hanya kuma motar tana ta yimin horn amman ban sani ba.
A hankali na cikin motar ya fito yana cewa"haba beauty ya zaki fito kan hanya kina tafiya bakya kallon hanya,me ya yi zafi haka shi ba wuta ba?".
a hankali nima na kallesa hawaye yana zuba a idanuna nace"yi haƙuri ban gani ba ne".na faɗi hakan cikin ƙaguwa don na matsu in siyar in koma in ga Baba na.
Handcachep ya ɗakko sai naji kawai hannayensa yana gogemin idanuna,cikin sanyayyar murya na ce"na gode".
"Dont mentioned beauty".
kallonsa na yi don ban san me yace ba,ya fuskanci hakan don haka ya ce"nan gaba ki dinga kula da hanya kinji don ke haryanzu girl ce".
da ɗan sauri na wuce ina ƴan dariya don rabon da inyi dariya har na manta,amman ban san abinda ya sakani dariya yau ba,ammn ni dai nasan tunda na kallesa naji wani abu ya tsaya azuciyata ko meye hakan oho".
Biyoni ya yi ya ajjemin kuɗi da yawa akan farantin sanman yace"idan kinje gida ki yiwa almajirai sadaka".kamar bazan amsa ba ammn dai na daure na amsa don tuno da masifar Amma idan na koma gida.
Abuja
Sai da Ammar ya ƙarasa hutunsa a Abuja sannan ya koma Tunesia don ƙarasa aikinsa,Sakinat kuwa kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha don tsabar farin cikin ta raba ɗa da uwa,Sakin duniyar nawa ma take baki ɗaya wataran mutuwa zamuyi.
Tana zaune tana waya tana cewa"am gaskiya yakamata kazo don tun jiya general ya koma,kuma kasanshi Ɗan ra'ayi ne ba ko da yaushe muke kasan cewa ba,don ɗan ra'ayi ne kuma gaskiya ina buƙatar zuwanka,ta faɗi hakan cikin shagwaɓa,a ɗaya ɓangaren kome aka oho?tace oky sai na jika ta kashe wayar tana ƴar dariya.
Sai kuma ta gimtse fuska tana cewa"aikin banza ko ta yaya ma mutum zai samu ciki oho".
duk abinda ta ke faɗa Raliya tana jin ta mai yi mata aikin sashenta tace"Hajiya na gama aikin nawa in tafi gida ne"?.
Ai wata Uwar ashar Sakinat ta ƙundu mawa Raliya ta ce"gidan uwarki zakije da zakizo ki tsayamin akaina munafuka shegiya ƴar talakawa,kuma wallahi ina fatan ko kinji me nake cewa kika nemi tona min asiri wallahi sai na saka an ɓatar ɓin dake".
tana faɗar hakan ta yi gaba abinta,Raliya ta bita da idanu,tasha kama Sakinat tana kawo maza amman har yau bata taɓa ganin fuskar wanda ya ke zuwa ɗin ba ballan tana ma ta bada shaida.
Ko wadda ta turo ta don ta ɗaukar mata rahoto amman har yau bata fara ɗauka ba don Sakinat ta iya takun ta sosai.
Kuyi haƙuri bani da lfy ne👏🏻.
*miss green ce*
*DARASI!!*
Free page 20/21
Rabiatu Bashir
(ummu maher)miss green.
*Ga masu buƙatar a tallata musu hajarsu ta online zasu biya 2k*
12/13
. . . .Ina zuwa gida na miƙawa Amma cinikin duka harda ɗoriyar kuɗin da wannan bawan Allah n ya bani,murna harda rawa Amma ta farayi ni kuwa kallonta kawai na ke yi ta ɗoramin talla na ɗari biyar,na kawo mata kusan dubu uku amman bata nemi ba asi ba,sai nice na ce"Amma wannan kuɗin baki tambayeni inda na samo shi ba?".
sai a sannan ta ɗan ɓata rai ta zauna kan turmi tana yimin kallon tuhuma ta ce"ikon Allah ke kuwa a ina kika samo wannan kuɗin me yawa haka?gaskiya kasuwar yau ta yi ƙyau sosai."
ɗan yatsina fuska na yi sannan na ce"wani mutumine ya haɗu dani a hanya shine ya bani kuɗin sannan kuma ya ce inyi sadaka da sauran".
na faɗi hakan ina kallon ɓangaren da mahaifina ya ke,idanunsa a rufe kamar me bacci,na lumshe idanuwa na inajin wani irin raɗaɗi a cikin zuciyata,ban sanda hawaye ya shiga sakkomin ba,sai ji na yi Amma na cewa.
"Ai wannan cinikin yanzu kasuwa zanje in saro kayan koli don mu ƙara jari,idan wannan ya tashi ki gyara mishi jikinsa ni ns tafi,ta nuna mahaifina da hannu a ya yinda ta ke saka mayafinta don fita,babu neman izini babu komai haka Amma ta saka mayafinta ta yi tafiyarta kuma tana bani sallahun wai idan ya ɓata jikinsa in gyara masa.
Kuka na shigayi babu ji babu gani don yadda zuciyata ta ke ta faman raɗaɗi sosai,ina Allah wadai da hali irin na mahaifiyata Amma.
Ko babu komai ai bai kamata ta ce in kula dashi ba saboda zai iya fitsari a zaune har ma da kashi,kenan ni ya kamata in ga tsaraicin mahaifina a wannan shekarun nawa da basu gaza sha huɗu ba,duk da a nahiyarmu ta ruwan kanya,da wuri a ke yiwa yara aure saboda mu fulani ne na usul.
Ni kaɗai na ke ta maganganu na babu mai bani amsa a haka na tashi na fara gyaran gidanmu ina cikinyi,na ga kamar alamar mahaifina ya buɗe idanunsa ƙwalla ta cika ƙwarmin idanuwansa tana ta sakkowa.
Jiki na a sanyaye na ƙarasa kusa dashi ina sharemai hawayen nasa,ya juyo ya kalleni yna son yimin magana amman bakin baya fitowa sosai,don bakin ya yi gefe gaba ki Ɗaya,kuka na fashe dashi kamar raina zai fita a tsugunnan da nake,da Ƙer ya ce"mama na ki daina kuka kinji insha Allah Zanji sauƙi kinji Inna woru na".
Ƴar dariya na yi na sunkuyar da kaina zara zaran gashin idona ya jiƙe da hawaye,ya tambayeni ina Amma na ce mishi bata nan,sai naga yana kiciniyar tashi alamun ya yi wani abu yana son a wanke mishi.
Ganin hakan da na yi na taimaka mishi na ɗebo ruwan na zuba mishi na rufe mishi suturarsa ya saka ɗayan hannun yana wankewa abin tausayi.
Tunda Amma ta ce ta tafi kasuwa bata dawo ba sai bayan isha'i bata bi takan mahaifina ba ta ɗora girkin dare babu ko magi a ciki ta zuba mana ni da ƙannai na muka fara ci,ita kuwa daman tazo da tsire da kuma gurasa na kasuwa ta cinye abinta,mahaifina ma wannan abincin yaci mara magi.
Kash!duniya kenan mata muji tsoron Allah mijin da ka ke saka ran zama dashi har a gidan aljanna kuma ka ke neman aljanna a wajensa amman kuma ka ga gara kyauta ta masa,Allah ka bamu ikon kyauta tawa mazajenmu Amin.
Amir yana zaune yana cin abinci amman hankalinsa baya kan abincin saboda tsananin tunanin wannan yarinyar da ya gani ɗazu gashi bai tambaye ta gidansu ba?yanzu ya ya zaiyi tunda ya ke bai taɓa jin son wata ƴa mace irin son da ya kewa wannan yarinyar da ya gani a ƙauyen Ruwan kanya,amman insha Allah kafin ya tafi zai nemi wannan yarinyar don yana ji a jikinsa matuƙar bai aure taba komai zai iya faruwa,yana cikin wannan tunanin Amira ta kirawo sa matarsa.
Yana ɗauka ta fara kuka tana cewa"Abban safna tun jiya muna asibiti safna bata da lafiya numfashinta ya ƙi saituwa har yanzu don Allah kadawo Kadawo".
da sauri ya ajje wayar hankalinsa ya yi matuƙar tashi a ranar Amir ya koma duk ya rame saboda tashin hankali.
A ranar Safna ta ce ga garunka nan Bayan Amir ya koma😭.. . .
*miss green ce*
DARASI!!*
Free page 14/15
Rabiatu Bashir
(ummu maher)miss green.
*Ga masu buƙatar a tallata musu hajarsu ta online zasu biya 2k*
14/15
"Ammi don Allah ki daina kukan nan, da saka damuwa aranki abinda yaya Ammar ya ke buƙata a wajenki kawai addu'a ya kamata ki dinga yi masa,damuwarki za ta haifarwa da Yaya matsala sosai aruyuwarsa,don haka ki share hawayenki ki yi masa addu'a insha Allah Sakinat sai ta girbi abinda ta aikata miki,don raba ɗa da uwa ba ƙaramin abu ba ne."
"insha Allah auta na daina kukan nan daga yanzu".
dariya Khalisat ta yi sannan ta ce"Ammi a kullum idan na tuno wacece Sakinat a cen baya abin har mamaki ya ke bani,kamar ba ita ce ƴar aikin ki a baya ba,kucaka ƙazama."
dariya Ammi ta yi wanda ya fi kuka ciwo tana tuno wacece Sakinat a ba ya.
*Asalin labarin Sakinat*
kamar yadda Khalisat ta faɗa Sakinat mai aiki ce a gidansu tun zamanin mahaifinsu yana nan kafin daga bisani kuma ya yi hatsari ya rasu.
Sakinar ƴar asalin maiduguri ce a cen aka haifeta ita kaɗai ce awajen mahaifinta tun tana ƙarama mahaifiyarta ta rasu,bayan mahaifiyarta ta rasu ne suka koma garin adamawa anan kuma riƙonta ya koma gun yayar mahaifinta.
Yayar mahaifinta ita ce ta kai Sakinat wajen aiki da kanta don ta ce tunda taƙi talla dole ne ta yi aiki,gidan farko da aka kaita yaron gidan ya yi mata fyaɗe daga nan kuma suka jo ne da yaron gidan don kullum Sakinat tana ɗakinsa,duk sanda
Za suyi mu'amala sai ya bata wata ƙwaya ta hana ɗaukar juna biyu,sakinat kuwa bata san ko na me ye ba don ba tada ilimin da za ta gane.
Kwatsa rannan mahaifiyar yaron ta gansu ta yiwa Sakinat korar kare,daga nan ta koma gidan yayar mahaifinta mai suna Abuwalle.
Abuwalle mace ce mai shegen son kuɗi da son duniya don haka babu daɗewa ta samo wa Sakinat aiki a gidansu Ammar.
Tun ranar da Sakinat ta fara aiki a gisansu Khalisat Ammar ya dawo daga tafiya daga ƙasar germany,Tun da Sakinat taga Ammar hankalinta ya tashi don kyaunsa da nutsuwarsa ba ƙaramin dagula mata lissafi ya yi ba.
Ta rasa yadda za ta yi da rayuwarta don ko kallo bata ishe sa,ko mopping ta ke idan ta hangosa ɓuya take saboda matuƙar ta gansa to fa zuciyarta ta yi ta bugawa kenan,har sai ya bar wajen da kusan awanni sannan za ta samu damar fitowa don cigaba da aiki.
Ammi ba macece mai takura ba saboda ba ta ɗaya daga cikin matan da ke wahalar da ƴan aikinsu ba,saboda macece mai mutunci da kuma karamci.
Ana cikin haka ne Sakinat ta fara wani irin ciwo,idan ciwon na ta ya tashi har aman jini ta ke,babu shiri Ammi da Alhaji Muhammad Lamiɗo wato mahaifin su Ammar suka kai Sakinat asibiti.
Tashin farko bayan likita ya gama gwaji ya ce ai Sakinat tana da ciwon zuciya,adinga yi mata duk abinda ta keso saboda idan ba haka ba ciwon ba zai warke ba.
Hankalinsu ya tashi sosai bayan sun dawo gida shima Ammar ya dawo ganin da Sakinat suke tare ya yi gaba zuwa cikin babban farlon gidansu,yana zama sai ga su Ammi sun shigo.
Suka saka Sakinat a gaba da tambayar abinda ya ke damunta kai tsaye ta ce ita Ammar ta ke so. . . ..
Kuyi haƙuri wani busy ne shiga ne👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻.
*Miss green ce*
*✨DARASI!!!✨*
(Topic)
*` _``a love&```_ destiny story*
By
Ummu Maher(Miss green)🍀💚
*Littafin na kuɗi ne ban yarda ki karanta mun baki biyani ba,Gamai buƙata n cigaban labarin zai biya ₦300 normal* group...Vip group
₦500... Special₦1k....zaku iya Turo da katin MTN ta wannan number 07068606171
ko kuma ku tura ta wannan account number 2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith Bank.
*Free page*
16/17
. . .Wani Mugun kallo Ammar ya wurgawa Sakinat da ke lafe a jikin Ammi,sannan ya kalleta cikin wata muguwar tsawa yace"i hate u!i said i hate u!"shin ana soyayya dole ne,me zanyi dake kucaka ƙazama mara class,ni kuma in rasa wacce zan aura sai ke? Stupid girl kawai mssttttt".
Ya buga wani uban tsaki ya haye upstair don gani ya ke idan ya cigaba da kallon wannan mumu girl ɗin komai zai iya faruwa dashi,ƙarshe power ɗinsa na soldier ya motsa ya shiga jibgarta.
A hankaki Alhaji Muhammad Lamiɗo ya zauna ya