Header Ads
Showing 36001 words to 39000 words out of 41026 words

Chapter 13 - BABU SO Book Complete writing by Billy Abdul

Ads the beginning of article before Image

29 May 2024

695

Ads at the middle of Article

na yammaci sai ga Shareff da Dr Jamal abokinsa ɗauke dasu a motocinsu ashe sune sukaje tarbosu. Cikin ƙanƙanin lokaci gida ya hautsine da murna dan harda aunty Mimi da yaranta itama. Duk da an share musu nasu gida an gyara komai tsaf anan suka fara sauka. Anam ta rungume iyayenta harda kukan daɗi su Mubarak na mata dariyar ta girma batasan ta girma ba. Duk wannan kaikawo da ihun yara da hayaniya Mommy da Gwaggo ko leƙe basu leƙo ba duk da kuwa sun san su Mamie sunzo ne domin bikin ɗansu. Hasalima duk wani ɗawainiyar biki Abie da Mami suka ɗauka. Acewarsu Shareff ɗansu ne, sune suka cancanci yimasa aure ba kowa ba. Hatta lefe da duk abinda aka kai gidansu Fadwa sai da Abie ya dawowa Daddy da Abba abunsu. Mommy taita masifa amma Daddy ya taka mata burki tun wancan lokacin dan a sanda Abie ya rako Anam ne. Sai da sukaci suka sha sannan suka shiga suka gaida Gwaggo. Mommy kuwa basu nuna sun san da zamanta a gidan ba Gwaggon ma dan uwa ce shiyyasa suka bata girmanta. Ai tuni Anam tabi su Mamie can gidan, dan taci alwashin bazatai zaman gidan nan ba dan bata ra'ayin ayi bikin nan da ita, duk da kuwa katanga ɗayace tasan wasuma zasu shigo gidansu a ƴan bikin, amma dai ko yayane bazai kai nan gidan ba ai. Sai dai kuma batasan tayi gudun gara bane ta faɗa gidan zago😚.

          ★★★

    Acan gidan su amarya Fadwa kam wannan rana itace ranar ƙunshi, suna can ita da taren ƙawayenta wayayyu da gayyar media an ware musu part guda sunata shagalinsu harda su shisha. Ga hotunan amarya sun baje media musamman tiktok da istagram da amaryar ta tara ɗunbin followers da suka sakata yin ƙaurin suna cikin jerin celebrities da akeji dasu. Amarya tasha ƙyau da gyara harta gaji, sai dai ba'ai mata nata ƙunshin bama sai gobe idan ALLAH ya kaimu alhamis.

      ★★★

    Bayan sallar isha'i Mom ta aiko kiran Anam data maƙale taƙi bin su Aysha can gidan yin ƙunshi. Amma hatta da Amrah ɗiyar Aunty Mimi dake kusan sa'anni dasu Anam ɗin tana can itama za'ai mata. Cewa tai bataso itakam, dan ko wankin kai da sukaje yau ita ƙin zuwa tayi. Sai da Mamie tamata jan ido ta biyo ƴar aikin Mom. Amma da ta langaɓe wai kanta ke ciwo. Koda tazo anan ɗin ma faɗa Mom tai mata akan batun ƙunshin. Amma saita hau hawaye wai ita bata da lafiya. Kowa kallonta kawai yake da mamaki a falon, dan kuwa dai ko awanni huɗu bata cikaba da gama murnar isowar su Mamie ai. Ganin yanda take kuka Mom tace mata taje ta kwanta ayi mata gobe idan ALLAH ya kaimu. Ai kafinma ta rufe baki tayo waje. Maimakon taje ta kwanta ɗin can ta samu inda babu wadataccen haske ta zauna taci kukanta da batasan daliliba itama sannan ta koma gidansu tai kwanciyarta.
       Washe gari wajen sha biyu yaran gidan kowa da ƙunshi abin sha'awa amma banda Anam dako wanke kai bataiba balle maganar kitso. Tana gani suka shirya suka fita hausa day itako tace bazataje ba. Sai faman baƙin rai takeyi na babu gaira babu sabar. Mamie dai tunda taimata tambaya ɗaya tace bakomai bata sakebi takanta ba. Sai aunty Mimi ce ke faman lallaɓata da lallashinta. Sai tace kawai ita bata da lafiya ne.
       A wannan lokacin Shareff dake gidan batare da Anam ta sani ba ya shigo. Gabantane yay masifar faɗuwa. Ta miƙe zaram da nufin guduwa aunty Mimi ta dakatar da ita cewar ta kawo masa breakfast ɗinsa dake kitchen wanda Mamie dakanta da girka abinta kuma irin abincin ƙasar Malaysia ne. Jitai kamar ta fashe da kuka dan takaici, koda ta kawo ta ajiye masa ƙoƙarin juya tai zata bar wajen ya watsa mata mugun kallo saboda ido da suka haɗa by mistake. Baki ta murguɗa masa itama ta haura sama da gudu.
      “Kai kaji shasha lafiyarki kuwa Mamana?”. Aunty Mimi da bata lura da abinda ya faru ba ta faɗa da mamaki tana kallon hanyar da Anam ɗin tabi. “Babana wai kaga mi yarinyarnan tayi kuwa? Sai kace mai tsoron wani anan?”. Murmushi kawai yay baice komaiba. Ta hararesa. “Kaifa tsiyarka kenan ai magana ka bama mutum amsa da murmushi”.
     “Oh ALLAH small Mom rigima. Ni yanzu mikike so nace anan kuma? Ina ruwana da shirmenta”.
         Hararsa ta ƙarayi ta ɗauke kai. Yay dariya da shafa kansa yana buɗe kwanikan. Ƙamshin ya sashi lumshe ido murmushinsa na ƙara faɗaɗa. “Lallai na shaida Mamie na kusa dani”.
     Dariya aunty Mimi ta sanya masa da faɗin, “Makwaɗaicin banza”. Dariyar yayi shima da faɗin “Naji ɗin”. Haka ya fara cin abincin cike da nishaɗi suna hirarsu har Mamie ma ta fito daga sashen Abie ta samesu. Zama tai itama suka ɗora, daka gansu kasan akwai shaƙuwa mai faɗi a tsakaninsa tun ba yanzu ba. Anam na jiyo dariyarsu daga sama taƙi sakkowa har saida ya wuce massalaci sallar azhur. Aunty Mimi kuma ta fita zuwa can cikin gida ita da Mamie.
     Ta idar da salla tana shirin sakkowa ƙasa ta samu abinda zataci suka kusa cin karo da Fawwaz.
    “A'a autan Mom daga ina haka da gudu?”.
         “Yaya ne yace na kiraki”.
Kafin tace da shi wane yaya ya kwasa da gudu ya fice. Ta girgiza kai tana murmushi. Ɗaki ta koma ta ɗauka abaya kasancewar kayan jikinta wando da rigane marasa nauyi. Duk zatonta Khaleel yake nufi, shiyyasa ta fito hankalinta kwance. Harta nufi gate ɗin shiga cikin gida motar dake fake a tsakanin gidansu da cikin gida tai mata horn. Kamar bazata juyaba sai kuma ta dubi motar ganin an sakeyi alamar da ita ake, tunanin ko Yah Khaleel ɗin ne a ciki ya sata nufar can duk da tasan ba motarsa bace, bama tasan motar ba dan kamar ma sabuwa.
       “Tofa, wai su Yah Khaleel sabuwar mota akayine halan?”. Tai maganar fuskarta ɗauke da murmushi tana shafa motar har side ɗin mazaunin driver. Kanta tsaye ta buɗe murfin. Duk abinda take dama idonsa a kanta, kuma yana jinta dan ya ɗanyi ƙasa da glass kaɗan. Da sauri ta saki murfin tana ambaton ALLAH tamkar wadda taga wani shaiɗan ko aljani. Ɗaga kafa tai da nufin juyawa ya dakatar da ita.
      “Idan kika bar wajen nan sai na mareki”.
   Tsayawar tayi, sai dai taƙi ta juyo. Hasali ma auna yanda zata arta da gudu takeyi.....
            “Zagaya ki shiga”
     Ta tsinkayi muryarsa a dake. Shiɗin ba abun wasanta bane, musamman a yanda yay maganar babu alamar wasa a cikinta. Ta haɗiye ƙwallar da suka taru mata a ido cikin cije lip tabi umarninsa. Sanyin ac da kamshi na musamman suka ratsata a cikin sabuwar motar da ko leda ba'a cirema kujerunta ba. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauke da lafewa cikin kujerar ranta fal tunanin ina zai kaita? Bata da mai bata amsa dan haka taja bakinta ta tsuke ta zubama sarautar UBANGIJI idanu..........✍

    
_🤣Tofa, su Shareffudden ango ko'an fara kidnapping ne bamu sani ba😣, to magana ta gaskiya ƴan team ɗinsa ku faɗa mana gaskiya mu fara rigakafin killace kammu kar'a sakamu a ruɗani😂😆?._


_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
0913484810_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107 ko



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[10/26, 7:15 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*




*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*




*_13_*


..........Gab da magrib aka kawo amarya Fadwa, kamar yanda Daddy ya bada umarni nan gidan aka kawota wajen Mamie. Hakan ba ƙaramin zafar Mommy da su Gwaggo Halima da aka kira aka sanarwa abun yayi ba. Gwaggo kuwa kasa shiru tai sai da ta tanka, Daddyn yace ya gama yanke hukunci, miye ma abin magana bayan gobe idan ALLAH ya kaimu za'a maidata gidanta. Badan rigimar ta kwantaba akai daiyi shiru kowa yaje ya fara shirin tafiya dinner.
     Bayan sallar isha'i aka fara kwasar mutane inda za'a gudanar da dinner, sai dai har aka gama kwashe kowa babu Anam babu alamarta. Hasalima tuni taje tai kwanciyarta a falon Abie batare da kowa ya sani ba. Wajen dinner ya ƙayatar matuƙa. Amarya da ango sunyi ƙyau har sun gaji. Anci ansha ƙawayen amarya sun sami yanda sukeso suda amarya wajen daukar hotuna da videos wasu har live suke ɗauka ana kaiwa tiktok. Nera tayi kuka kamar yanda aka zubar da mutunci galan-galan dan anci rawa casss da warrr ƙawayen amarya ta rashin mutunci, amaryar kanta ta cashe kamar babu gobe, sai dai rashin yin rawar ango ta jawo cece kuce sosai dan wasu na ganin amarya Fadwa ta zaƙe da yawa. (Komadai miye ni ina ganin ranar farin cikin tace a barta ta shana😜). Ƙarfe sha biyu taro ya tashi lafiya aka kwaso jama'a aka dawo gida.

    WASHE GARI aka gudanar da walima tare da yinin biki anan gidan, yini guda babu wanda zaice yaga Anam sai Mamie kawai da aunty Mimi, dan tana falon Abie kwance babu lafiya zazzaɓi ta kwana da shi har sai da doctor yazo ya dubata da safe ma, dan haka yau ko kwalliyar bikin ma batai ba abinta. Lokacin da taji sallamar Shareff zai shigo falon wajen Abie tashi tai ta gudu bedroom ɗin Abie ɗin, tanaji yana faɗama Abie baida kafiya shima da ciwon kai ya kwana kuma har yinin yau ɗin bai sakesa ba yana ganin hayaniyar nan ce. Baki ta taɓe cikin rashin damuwa tai kwanciyarta har sai da taji ya fita. Har dare bata sauka ƙasa ba dan bata buƙatar ganin Fadwa har tabar gidan. Hakan kuwa akayi, dan washeri lahadi akai buɗan kai bayan sallar azhar. Anayin la'asar aka ɗunguma raka amarya Fadwa gidanta, yayinda a bangaren ango yaketa ƙoƙarin sallamar abokansa na nesa da zasu wuce gida yau. Hakama baƙin nan gidan wasu daga rakkiyar amarya bazasu dawo nan ɗin ba...
       Gidan amarya kam sai sambarka. Komai yaji zam masha ALLAH. Har kusan bayan magrib sannan mutane suka gama watsewa aka barta ita da ƙawayenta kawai dake jiran abokan ango.....

      ★★

  “Wai nikam wane irin ango ne kai Al-Mustapha? A irin wannan ranar irinka ɗoki da zumuɗi baya barinsu amma kai tun ɗazun sai fama ake da kai ka shirya a rakaka kanata jamana aji”.
        Duk da sarai abinda Dr Jamil ɗin ke faɗa yana shiga kunnensa tunda a kusa da shi yake amma babu alamar zai motsa. Sai cigaba da danne-dannen tab ɗinsa yake hankali kwance. Fharhan dake faman musu dariya ya miƙe ya fige tab ɗin. Ɗagowa yay yana harararsa da miƙa hannu, Isma'il ya amshe tab ɗin daga hanun Fharhan shima yana dariya. “ALLAH baza'a baka ba. Garama ka tashi kaje ka shirya mu miƙaka muma muje musa haƙarƙarinmu a katifa matanmu na jiranmu.”
       Isma'il ɗin ya kafe da idanu kamar zaiyi magana sai kuma ya girgiza kai kawai. Dr jamil ya dafa shi, “Wai nikam Musty ko tsoron amaryar kake ne? Idan akwai matsala inada kayan gyara masu inganci wlhy da zaka baje kolinka babu ragi babu ragowa”.
      Naushi ya kaima Dr Jamil, da sauri ya duƙe yana dariya su Fharhan na tayasu. Hararsu yay da miƙewa ya shige bedroom. 

       Jin gidan ya rage hayaniya sosai ta sakko downstairs. Su Mamie ne kawai zaune da ƙannenta, gaishesu tai kowa na tambayarta ya ƙarfin jikinta. Tace da sauƙi tana zama gefen Mamie ta kwantar da kanta a kafaɗarta. Ko mintuna uku batai da zama ba suka shigo da sallama. Shine a gaba cikin ɗanyar shadda milk color sai ƙyalli take harda hula a kansa. Sai su Fharhan biye da shi. Jitai kusan su dukansu idanunsu akanta suke kamar ta tashi ta arta da gudu, sai dai ta dake dan bata fatan sake tafka abin kunyar datai a ranar ɗaurin aure😝.
       Sai da suka gama gaisawa da su Mamie Dr Jamil dake jin kamar ya haɗiyeta fuska ɗauke da murmushi yace, “A'a Anam banda ke a kai amaryar kenan?”.
      Kanta ta jinjina masa tana ɗan murmushi batare data kallesu ba. “Banda lafiya ne shiyyasa”. Ta faɗa a hankaki tana ƙara sinne kanta jikin Mamie.
          “Ayya ai ban sani ba dana kawo ɗauki. Yaya jikin yanzun?”.
  “Na samu sauƙi”. Ta faɗa a taƙaice tana ɗan ɗagowa. Cikin idonsa natan suka shige, tai saurin janyewa ƙirjinta na bugawa da ƙarfi....
      “My son kuje kar dare yayi an bar ɗiyata ita kaɗai, ALLAH yay muku albarka, ya bada zaman lafiya na har abada. Ayi haƙuri ayi haƙuri ayi haƙuri. Mu mata a duk inda muke haƙuri ake damu akan komai dan halittane masu wahalar sha'ani. Banda yanke hukunci cikin fushi, duk abinda aka gani ba dai-dai ba abu asannu a ruwan sanyi a kawo maslaha a cikinsa. Ayi ƙokurin sauke duk hakkin da ALLAH yace duk da bani da damuwa a kanka game da wannan. ALLAH ya azurtaku da zuri'a masu albarka”.
      Gaba ɗaya suka amsa da Amin. Anam dai ma ta maida hankalinta ga wayarta kamar bata jinsu. Ƴan uwan Mamie ma sun masa tasu nasihar suka sallamesu dan dare na ƙarayi. Dai-dai yana mikewa suka ƙara haɗa ido da Anam data ɗago itama. Wani kasalallen kallo suka sakarma juna. Ta kauda kanta tana taɓe baki zuciyarta na mata zafi. Shima iska ya ɗan furzar yana janye nasa a wani yanayi. Bata sake yarda ta ɗago ba har suka fice Dr Jamal na faɗa mata sai yazo dubiya ta musamman. Bata tankasa ba, sai Aunty Nasara dake kamar ƙanwar Mamie ta bashi amsa cikin dariya.
      Tsam ta mike tabar falon dan ji take wani ɗan zazzaɓi ma na neman rufeta, ta nufi ɗakinta da fatan su Aysha su kwana a cikin gida yau bata bukatar su anan......

*_MONDAY MORNING_*

          Tana tsaka da barcinta na safe mai daɗi kasancewar bata samu yin na dare ba sosai saboda zazzaɓi mai zafi data sake kwana da shi aunty Mimi ta tasheta akan ta tashi ta shirya za'a aiketa.
      “Wayyo aunty ina su Aysha ki aika a kira miki su suna cikin gida fa ALLAH bana jin daɗi”.
         Hararta Aunty Mimi tayi. “Ai nasan dasu Ayshan na tasheki. Maza tashi kina ɓatamin lokaci. Da ƙyar ta miƙe ta shiga bayi kamar zatai kuka. Wanka tai da ruwa mai ɗumi dan duk son sanyinta kuma bata wanka da ruwan sanyi. Gudun masifar aunty Mimi ya sata shiryawa a ɗan gurguje cikin shigar da tafi so a ko yaushe wando da riga ta ɗaura abaya pink a sama ta naɗa veil ɗin abayar. Tayi ƙyau sosai sai zuba kamshi take duk da bawani kwalliya tai mai yawa ba. A falon ƙasa ta sameta har su Mamie wanda suka makara nata breakfast. Gaishe dasu tai tana karasawa inda Aunty Mimi take.
      “Yauwa ɗiyar albarka. Ai jeki kawai waje ga Ikram can na jiranki a mota da driver ”.
    “To aunty saƙon fa?”.
“Yana wajensu a motar”.
Kai kawai ta jinjina taima su Mamie sallama ta fita. Baya ta buɗe ta shiga yayinda Ikram ke gaba tanata zubama driver surutu da hausanta da bata iyaba wai ita a dole koyan hausa takeyi. Itace autar aunty Mimi shekararta goma sha uku, kasancewarta girman turai sai take abu kamar wata yarinya ƙarama ga tabara ta autoci.
      “Good morning aunty Anam”.
Ta faɗa lokacin da Anam ke ƙoƙarin rufe murfi. “Morning dear how are you?”.
    “Am fine, sai ƙafana dake ciwo saboda rawan da mukai a wajen dinner ranar”.
         “Good for you”.
“Kai aunty maimakon kimin sorry”.
    “Tunda ni na aike ki”.
Dariya Ikram tayi. Sai kuma ta shiga bata labarin yanda shagalin dinner ya kasance. Shiru Anam tai mata, da taga zata isheta sai ta buɗe bag ta ɗakko bluetooth ta saka waƙa har suka iso gidan da bazata taɓa iya mantawa ba. Kasa motsi tai balle magana har driver yay horn maigadi ya buɗe masa gate suka shige. Jitai kanta na juyawa, ta dafesa tana ambaton sunan ALLAH. Da tasan nan aunty Mimi zata aikosu da duk ma yanda zatai taƙi zuwa ALLAH da sai tayi. Yanzu kuma tana ƙin shiga wannan akku sarkin zancen zataje ta bazata a fassarata a mai baƙin ciki. Siririn tsaki taja da buɗe motar a fusace ta fita dan Ikram tuni ta fice har driver ya buɗe mata booth suna fidda kayan breakfast da sukazo da shi. Ƙin daukar komai tai sai driver da ikram ɗinne suka kwasa.
        Daga can baya ta tsaya Ikram ta shiga yin knocking tana kiran sunan Yaya Shareff. Sun kai kusan mintuna goma sha sannan aka buɗe har ta gama yanke shawarar juyawa ta koma. Shine ya buɗe ƙofar Ikram ta riƙo hanunsa cike da shagwaɓa. (Wayyo Yaya ƙafafuna har zafi suke da hannuna”.
      Kanta ya dafa da rufe idonsa daya nuna alamar a barci ya tashi yana buɗewa. Ya matsa mata alamar ta shigo yana maida dubansa ga Anam datai tsaye tana kallon wani waje daban. Kusan minti ɗaya yana kallonta ko ƙyaftawa babu sannan yay magana.
    “Tsaiwar ta miye?”.
  Baki ta taɓe tana ƙara tsuke fuska. Batare da tace komai ba ta nufosa. Harta ƙaraso idonsa na kanta yanzu ma. Ya ɗan matsa mata alamar ta shiga itama. Ɗagowa tai suka haɗa ido, tai saurin janyewa da raɓashi

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads