Showing 6001 words to 9000 words out of 41026 words
Chapter 3 - BABU SO Book Complete writing by Billy Abdul
school ɗinsa. Abie yay masa shirin wucewa jami'a a ƙasar Indonesia. Ya shiga damuwar rabuwa da ƴar ƙanwarsa, dan kuka sosai ya dingayi duk da lokacin yanada shekaru sha takwas a duniya dan ya zama ɗan saurayi abinsa. Haka dai babu yanda ya iya ya tattara ya tafi badan yaso ba. Yasha matuƙar wahalar kewar Anam a ƙasar Indonesia, dan da ƙyar ya haƙura ya maida hankali ga karatunsa kodan faranta ran Mamie da Abie ɗinsa. Fara karatun Shareff a ƙasar Indonesia ya ƙara bama Gwaggo da Mommy ƙwarin gwiwar cigaba da shiga da fita domin ganin hankalinsa ya dawo garesu, su kuma nisantashi dasu Mamie. Zuwa lokacin gidan nasu ya ƙara haɓaka da ƴaƴa. ALLAH kuwa ya amsa musu, dan kuwa dai a hankali rayuwar Shareff da hankalinsa suka fara dawowa Nigeria, ko hutu ya samu da yaje Malaysia dake kusa da shi gara ya wuto Nigeria. Takai yakan ma jima bai je inda su Abie suke ba. Sai dai abinka ga ikon UBANGIJI har lokacin soyayyar bayin ALLAHn nan na'a ransa babu abinda ya canja. Kawai dai baya son zuwa inda suke ne batare da yasan dalili ba, sai kuma Anam da sam a yanzu bayama ko san tunata dan babu dalili ya tsani yarinyar. ko Malaysia yaje babu abinda ya damesa da ita, wani lokacin ma kafin ya taho sai ya bugeta. Itako dama tama manta da shi tuni, rashin sakewar da yake da ita yasa basa shan inuwa ɗaya, ko inda yake bata kusanta balle ta nuna tama sanshi, idan kuma tsautsayi ya haɗasu ko hararta yay sai ta rama saboda tsiwarta.
A haka rayuwa ta cigaba da shuɗawa Shareff ya kammala karatunsa ya zama cikakken *_Architect Al-Mustapha Muhammad Shareff_*. Maimakon ya nufi Malaysia kodan nuna godiyarsa ga ALLAH ga waɗanda suke tsaye kan ɗawainiyar karatun nasa sai kawai ya nufo Nigeria. Hakan ya matuƙar bata ran su Daddynsa, yayinda Gwaggo da mahaifiyarsa Mommy suka bashi goyon baya da kariya. Sosai ran Daddy ya ɓaci har suka sami saɓani tsakaninsa da Mommy irin wanda basu taɓa samu ba. Ya kuma fito fili ya nunama Gwaggo kuskurenta. Aiko saita zauna ta dinga kuka wai su Daddy sun nuna mata ba itace ta haifesu ba. Shareta sukai, harta haɗa kayanta tabar gidan, ganin abin zaiyi tsamari Mom ta sanarma Mamie, itako ta sanarma Abie. Daga ƙarshe dai Abie ne yazo Nigeria ya kwantar da tarzomar tare da nuna shi bai ɗauka abinda Shareff ɗin yayi da wani ɓacin rai ba, abin birgewama sai yay zaman bashi shawarar mizai hana ya buɗe company kawai basai ya zauna neman aiki ba.
Sosai Shareff yaji kunya, ya dinga bama Abie haƙuri akan shima wani lokacin yana rasa gane kansane akan nisantarsu. Murmushi kawai Abie yay dan ya jima da fahimtar komai akan farraƙa yaron akai da su, bai kuma taɓa yunƙurin nuna ya sani ba tunda yasan dai Mommy akan abinda yake nata take hanƙoro mizaisa ya damu tunda shima ALLAH ya bashi tashi. Shareff bashi da kuɗin buɗe company, amma sai Abie ya bashi shawarar su haɗa gwiwa kawai.....
A haɗin gwaiwar ma Shareff baida ko kwatar kuɗin da zata gina company ɗin, amma sai Abie bai damuba shi ya bada duk kuɗin da ake buƙata aka kammala aikin cikin ƙanƙanin lokaci, ya kuma gargaɗi Shareff akan baya son Gwaggo da Mommy su sani, kawai suci gaba da tafiya akan shine ya gina abunsa. Sai dai sun zauna da lauyoyinsu an ajiye komai a rubuce tare da su Daddy matsayin shaida.
Ginin wannan company yasa Mommy fara hura hanci, a ganinta karan ɗanta yakai tsaiko shima. Har habaici takema su Mom da su Mamie ko kunya babu. Mamie ce kawai tasan gaskiyar lamarin, su Mom kam da aunty amarya suma duk tasu ɗaukar Shareff ɗinne ya gina da kuɗinsa. Gwaggo ma ta ɗau abun da zafi, dan ita taita tunzura Mommy akan su ƙara tashi tsaye su nisanta Shareff da su Abie wai kar wataran Abie yay tunanin haɗa Shareff da Anam aure tunda sunga ya kuɗance har yama fisa arziƙi. Wannan fanfi kuwa yay tasiri ga Mommy, dan tuni suka bazama shige-shige saboda ko'a mafarki bata fatar haɗa zuri'arta dasu Abie a duniya.....
Abubuwa da yawa sun faru bayan wannan, ciki harda karatun Anam da ko Nigeria ɗin ma sai jefi-jefi ake kawota, dan idan har suka zo ta dinga kuka kenan zafi-zafi. Anam yarinyace ƙyaƙyƙyawa black beauty, tana tsananin kama da mahaifinta a komai, sai dai akwai kamannin Mamie tattare da ita ta wasu wajajen. Yarinyace mai ƙiriniya da rashin ji, ga tsiwa. Sam ƴar babu ragice, dan ko cikin yaran da suka girmeta bata bari a cuceta balle sa'aninta, tanada baki sosai. A ɓangaren karatu kuwa sam bata da wani ƙoƙari saboda kasancewar ta yarinya mai son wasa, sai da su Abie suka miƙe kanta sosai sannan ta fara fahimtar karatu. Shekaru na karuwa gareta rauni daga idanunta na sake bayyana, dan takai idan abuna'a nesa da ita bata ganinsa, hakama da daddare idan waje babu haske mai ƙarfi bata ganin abu har saida lalube. Lokacin da su abie suka fahimci wannan matsala hankalinsu ya tashi, sai dai babu ɓata lokaci suka dangana ga likita, ya tabbatar musu idanunta nada raunin gani, amma zai ɗaurata akan magani da gilashi dazai taimaka mata. Wannan shine dalilin kasancewar eyeglasess a idon Anam koda yaushe. Abin mamaki kuma sam basa shan inuwa guda da Yaya Shareff. Hasalima haduwarsu tayi matukar wahala, idan ya fisge yaje Malaysia ma bata barin su haɗu sam, hakama idan tazo Nigeria baifi su haɗu sau biyu uku ba shikenan, a kuma duk haɗuwar tasu sai ya mata muguntar datake jin ƙarin tsanarsa a ranta kamar yanda shima haka kawai bai son yarinyar saboda tsiwarta da rashin kunya ido fiƙi-fiki injisa. Idan ma tana waje ya dinga ɗaure-ɗauren fuska kenan kamar an aiko masa da mutuwa, ko gaishesa tai sai ya gadama ya amsa shiyyasa tama daina gaidashi take nuna bama tasan ƙurar data kwasosa a duniya ba. Tuni company ya fara aiki cikin lumana da nuna ƙwazon shugaba kwata-kwatansa wato Architect Al-Mustapha Muhammad Shareff. Da mafi yawan mutane sukafi sani da *_MM Shareff_* a taƙaice. Company ne da aka haɗa masu ƙwazo kuma ƙuraye, dan Ya Shareff bai yarda ya ɗauka ma'aikatan banza ba sannan sam baya wasa da aikinsa bai bama ma'aikatansa damar yin wasan kuma.
Jajircewar tasa tai matuƙar birge Abie, ya kuma ƙara tsayawa tsayin daka ta bayan fage yana bama Shareff ɗin gudunmawa dan yana matuƙar kaunar yaron har cikin ransa tamkar Anam ɗinsa ƴa ɗaya tilo.
To ayanzu dai ga Anam ta dawo Nigeria da shirin zaman shekara guda domin yin saves da su Mamie suka takura mata. Ga kuma ɓeranta da tuni yayi nauyi a Nigeria kodan hidimar kamfanin da mahaifinta keda kamasho mai ƙarfi a cikinsa da shares batare da Mommy da Gwaggo dake hura hanci sun sani ba.........✍
_Ko yaya wasan zai kasance🤔? Kudai kawai ku zamto tare da littafin *_BABU SO...! MIYA KAWO KISHI? dan jin yaya cakwakiyar zata kasance. Littafine da yazo da wani irin sabon salo na musamman da nake tabbacin ni Bilyn Abdull ban taɓa zuwa muku da kalarsa ba sai yanzu. Domin kuwa ya taɓo zahirin rayuwa ne da zamanin da muke ciki a yanzu da rawar da tarbiyyar ƴaƴanmu ke takawa a social media batare da saninmu ba ko da sanin namu. Kar dai na cikaku da magana my guys, kumuje zuwa kawai dan duk wanda akai babu shi lallai ruwa tasha da shi kawai, saboda Zafafa biyar da gaske da zafinsu suke😉🥰🥰😘🚶🏻._
KU DAI KU GARZAYO A DAMA DAKU A CIKIN WANNAN ZAZZAFAR TAFIYAR CIKIN SALON NA ZAFAFA BIYAR MASU ZAFIN GASKE.
DUKKA LITTAFAN AKAN NAIRA DUBU DAYA (1k) KACHAL
IDAN KUMA DAYA KIKE SO (300)
BIYU (400)
UKU (500)
HUDU (700)
KARKU BARI A BAKU LABARI, DAN WANNAN SALON NA DABAN NE KUMA TAFIYAR MA TA DABAN CE!
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
HAFSAT UMAR KABIR
ZENITH BANK
2270637070
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
07040727902
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09134848107
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
SAI MUN JIKU MUTANEN AMANA!💃🏼💃🏼💃🏼
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏽
[10/3, 10:44 AM] Zeenaran🫶🏻: *_Typing📲_*
*_❤🔥BABU SO....!!❤🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_03_*
..........Tuni sun tattare kansu a sashen aunty amarya idan ka cire ƴan manya-manyan yaran gidan samari da basu gama dawowa da ga wajen aiki ba da kuma masu shiga school lectures ɗin yamma. Zagaye suke da Anam suna kwasar dariyar hausarta da bata nuna da ƙyau ba. Dan cike take gwamutse da yaren malay da turanci, wai a hakanma Abie na matuƙar ƙoƙarin mata hausar ne shi da aunty Mimi dan Mamie ma ba wani iyawa tai sosai ba harma gara Anam ɗin, tunda dama acan itama ta tashi, ko Nigeria tazo tafi yin turanci da jama'ar gidan. Aysha dake naniƙe da Anam ɗin da suke sa'annin juna dan dama idan tazo bata da ƙawar data wuceta a Nigeria, cike da kulawa take tambayarta dalilin matsar ciki da take famanyi.
A yatsine Anam ta sanar mata tana jin yunwa ne, dan ta kasa cin duk abincin da aka shirya musu a gidan. Dama can idan sunzo Mamie ce ke musu girki shiyyasa Anam bata da matsala tunda abinda ta saba ci ne, a yanzu ko babu Mamie dole sai abincin Nigeria da har yanzu ta kasa iya ci, ƴan abubuwan da take iya cin ƙalilanne kuma babu su.
Idanu Aysha ta ɗan waro, cikin harshen turanci take cemata miyasa zata zauna da yunwa bayan abinci da akai domin su tunda sun iske tarin kwanika a sashen Daddy lokacin da sukaje gaida Abie. Sunada tabbacin kuma an shiryasune dan zuwan su Anam ɗin. Fuska a marairaice ta sanarma Ayshan ita bata iyacin duk abincin ba ai. Ba Aysha kaɗaiba duk yaran sai da suka dara, dan sosai ragwantakar Anam ke basu dariya, kodan tana ganinta da ƙaramin jiki ƴar ficika da ita yasa a kullum bata sanin ta girma? Sosai Aysha ta fita girman jiki, sai ma ta saɓeta ta goya dan ita ta kwaso tsayi da garin jikin Mommy mahaifiyarsu.
Sake ɓata fuska Anam tai kamarzatai kuka, sai faman matse ciki take da cizar lips dan da gaske yunwar takeji, shi kansa Abie yana canne amma hankalinsa na kanta dan yasan bazata iyacin kowanne abinciba da ya gani an tara masa.
“Am so sorry sweetheart. Kar kiyi kuka faɗi abinda kike so sai a samo miki, ko a kira Yaya ya sayo miki tunda shi yasan inda yake samo abincin naku, dan shima dai ya jima yana wahala kafin ya saba da abincin Nigeria, ko yanzu ma ba komai yake iya ci ba”.
Fahintar wa Aysha ke nufin za'ama magana ya samo mata abinci ya sakata girgiza kanta, a langwaɓe ta kamo hanun Ayshan cikin nata. “No don't worry rakani wajen Abie na nidai kawai”.
Batama bari Aysha tace wani abuba ta miƙe har lokacin hanunsu cikin na juna, ɗayan hanunta kuma nakan cikinta. Wando da rigane a jikinta marasa nauyi, wandon irin mai faɗin nan sosai da ƴan Nigeria ke kira a fantama😂, sai fingilar top da tabi jikinta ɗas kamar dan ita aka halicceta, sai siririn veil data sakaya gashinta a ciki sai dai hakan bai hanashi bayyana ta gaba ba saboda veil ɗin daya zama baya.
Itace ta farayin sallama a hankali cikin sassanyar muryarta, ta dora da faɗin, “Daddy mu shigo?”.
Murmushi Daddy da Abbah keyi idonsu akan ƙofar. Abba ne ya amsa da “Shigo mana Mamanmu”. Hanun Aysha taja zuwa ciki, sai dai taku uku kacal tai ta tsaya turus fararen idanunta da sukai laushi saboda yunwa tsaye ƙyam akan wanda ke zaune bisa lallausan carpet ɗin falon gab da ƙafafun Abie ɗinta, yayinda hankalin Abie kacokan ke akansa da alama ma bai san da shigowarta ba.
Sosai ƙirjinta ya harba dan ko kusa batai zaton ganinsa anan ɗin ba, tunma data duro gidan addu'arta shine karma su haɗu kwata-kwata. Zancen Aysha na ɗazun ya tabbatar mata yana ƙasar, hakan kuma na nufin dole su haɗu koda ba yau ba. Amma batai tsammanin yanzu ba. Kamar yanda tai masa kallo ɗaya ta ɓata fuska da gyara yanayinta haka shima yay mata kallo guda duk murmushin fuskarsa ya ɓace, har wani yamutse fuska yay tamkar yaci karo da tutun safiya na cikin sanyi......
“Mamanmu ƙaraso mana”.
Daddy ya katsesu a tare dan duk yaga irin kallon tsanar da sukaima juna. Shikam ya rasa wannan ƙiyayya ta Anam da Shareff bayan kowa yasan irin dunbin son daya nuna mata tana jinjira har zuwa sanda ya wuce Indonesia, amma a yanzu baka ganin komai sai ƙin juna a tsakaninsu tamkar basu taɓa sanin juna ba. Yitai kamar bata gansa ba taje ta zauna kusa da ƙafafun Daddy, cikin marairaice fuska tace, “Daddy ina jin yunwa sosai”.
“Ya salam mamana garin yaya haka? duk abincin dake gidan nan ga wasuma ko taɓawa ba'ai ba kuma dan k kawai aka shirya su”.
Kanta ta girgiza kamar zatai kuka. “Daddy bana son su ban iya ci ba ai”.
“Sai ki fara koya yanzu ai”.
Abie ya faɗa kafinma su Abba suce wani abu yana hararar Anam duk da kuwa bai kai zuci ba, dan ransa cike yake da damuwar zamanta da yunwar tunda yasan da gasken ba iya cin tai ba.
Daddy yace, “A'a ba'ayi hakaba ai. Tunda tace bata iyaba da gaske bata iya ɗinba kuma bataso. A bita a sannu zata koya ci insha ALLAH tunda tana nan. Shareff ka ɗauketa kuje a sama mata abinci dan kaine kafi kowa sanin inda kake ciyo abinda ta iya ci”.
Tamkar saukar aradu haka Shareff yaji saukar zancen Daddy a kansa. Ya ɗago da sauri yana duban mahaifin nasa tamkar a razane. Harara Daddy ya zuba masa. “Lafiya ka tsareni da idanu halan?”.
Ƙasa ya risinar da idanunsa batare da yace komai ba. Sai dai fuskar ta sake rinewa tamkar an aiko masa da saƙon mutuwa.
“Daddy ni dai nama ƙoshi kawai zansha ko tea to”. Anam da itama ta haɗe fuska tana hararsa ƙasa-ƙasa ta faɗa baki a tunzure”.
Maimakon Daddy ya amsa mata sai ya kira sunansa a tsawace. “Shareff Are you daft?”. Kansa ya girgiza kawai yana miƙewa, idonsa a ƙasa yace, “Zanje na sayo kawai.....”
“Da ita zakaje ta zaɓa abinda take so”.
Dady yay saurin faɗa cikin katse masa hanzari. Wani irin rumtse ido yay da ƙarfi da cije lip ɗinsa na ƙasa uwa zai huda shi. Sai dai baice komai ba ya kama hanyar fita. “Basai kaje ɗakko key ɗin mota ba zo ka dauka wannan”. Abbah ya katsesa dan ya tabbatar Mommy ta gansa zata hana itama. Nanma baice komai ba ya dawo ya amshi key ɗin hanun Abban.
“Maza bishi mamana kuje, ki kuma zaɓo duk abinda kike so kinji”.
Kanta ta ɗagama Daddy tana murmushi, dan ganin yanda Shareff ɗin keyi yasata jin zama ta bisa kodan ta baƙanta ransa...
Kasancewar ya fita zafin nama sanda ta iso harabar gidan harya tada motar yana reverse, maimakon ya faka saitin inda take ya ɗauketa sai ya harba motar har bakin gate. Anam tai ƙwafa da taɓe baki, cikin kunƙuni da gurɓatacciyar hausarta tace, “Duk baƙin halin da kake sai naje saika mace idan kasha zuciyanka mugu mai baƙin rai”.
Oho baima san tanai ba. Cike da wani takun isa tazo ta buɗe murfin ta shiga kanta a gefe. Bawani duban kirki yay mataba a ciki, dan haka bai gama tantance kayan jikinta ba. Tana shiga ya fisga motar da ƙarfi har yanayi kamar zai taka mai-gadi ma, sai da yay tsalle gefe ya bashi hanya cike da mamakin mike damunsa. Dan shi shaidane Shareff mutum ne daya san mutuncin mutane, ko yaya kake a ƙasansa bai yarda ya ƙasƙantaka ba balle wulaƙantaka. Yayi imani da ALLAH ransa a ɓace yake bada son rai yay masa haka ba.
★ Sosai gidan abincin ya haɗu, ya samu waje yay parking batare da yace da ita komai ba ya fice a motar. Baki taɗan taɓe kaɗan da yima ƙeyyarsa gwalo, sai kuma ta zabura ta buɗe motar tamkar wadda ta tuna wani abu. Yana gab da shiga ta cimmasa saboda da ɗan gudu-gudu take tafiya. Cak ya tsaya, dan haka itama ta tsaya kanta a ƙasa dan duk fitsararta a bayan idone kawai dama.
“Idan kika bari ƙafarki ta shiga wajen nan sai na ɓallata”. Da yaren malay yay maganar, dan haka komai ya shiga kunnenta tsaf. Baki ta tura fuska a kumbure idonta na tara ƙwalla harya shige tana kallon bayansa ta ƙasan ido. Maimakon ta koma mota sai ta nema waje a gefe tai tsaye tana kallon mutanen dake. a ciki ta cikin glass da aka ƙawata wajen.....
“Hallo....”
Aka faɗa a bayanta cikin wani irin sallon daya tilastata ɗago idanunta masu haske, matashin saurayine ƙyaƙyƙyawa fari tas. Sanye yake cikin ƙananun kaya da sukai matuƙar karɓarsa ga wani ƙamshi na musamman a tare da shi. A hankali ta janye idanun nata ganin yanda ya tsareta da idanunsa birkitattu. Gefen data maida fuskar ya sake dawowa yana gyaran murya, ta sake ɗauke kanta gefe....
“Dan ALLAH ki kulani ƙyaƙyƙyawa ”. Ya faɗa cikin marairaicewa da haɗe hannayensa waje guda alamar roƙo. Baki taɗan taɓe gefe tana yamutsa fuska da kai hannu ta gyara glass ɗin idonta dake ƙara fiddo ƙyawunta duk da tana sakawane badan gayu ba, kamar bazatace komaiba sai kuma dai ta