Header Ads
Showing 6001 words to 9000 words out of 13639 words

Chapter 3 - JININ SARAUTA Romantic Novels By Oum Aphnan.txt

Ads the beginning of article before Image

15 Jun 2024

1004

Ads at the middle of Article

dan majalisa ,bayan dogayen karatun da yayi a kasar waje duk a bangaren agric ,yabude gidajen gona da sauran su


Yanzu haka Alhaji bilya ,yina cikin masu kudin da bazaa kirga mutane gomaba a kasan nan cikin masu kudiba,dole a saka shi.
Kuma shine kwarton Momy fareedah da kawarta Shahida ,wannan kenan


***

Hudubar tsiya da famfo iri iri Shahida ta ringa yiwa Fareedah,akan lallai in bata rabu daniba sai Nayimuta k'wacen miji


Haushinta ne ya kama farredah "Haba Shahida ,don na aminta dake na fada maki sirrina shine zaki watsa mun kasa a ido ta hanyar nunawa duniya ni juyace bazan iya haihuwa ba?"


Matsowa kusa da ita tayi ta dafa kafad'arta
"Cool down my friend, ai lokacine ke sawa a zagi d'an sarki, shakuruminki bazan sake miki xancenta ba ,amma na baku shekaru biyar zaki kawomun mintin gayyatar Aurenta da mijinki"


Dam gaban fareda ya fadi don Allah ya zuba mata azaban kishin mijinta ,kuma akansa zata iya yanke halak'a da koma waye.

A sanyaye tace "Yanzu kina ganin Yusuf da Baby zasu iya cin amanata?"


"Au zauna nan ,ashema ke qaramar er barikice ,yo kin ta6a ganin inda tsintacciyar mage tayi mage?
Wannan fa yarinyar shegiyace ,so har Abadan jinin Iskanci a jininsu yike ,baki lura da kwarkwasan da take ringa yiwa mijinki,ga kalamai da salo ,tun yanzu da take er mininiyarta? Lallai to kisani kina rainon makishiyarki CE......."


Shiru tayi sakamakon zuwan Su'adah da dadynta ,ya riko mata hannu

Tana karasowa tahau doka kafa tana tsalle da ciccila hannu sama

"Yeeh momy kinga kyaututtukan da na samu kuwa? Ban ta6a samun kyauta kamar wannan ba don ko dadyn besty (Tana nufin mai girma V.p) saida ya bani kyautar mota ,momy guess Wata kala....👂


Hankadata tayi da kirjinta " dallah leave me johhhh..... nonsense ,kina abu sai kace mai motsuwa a kwalwa"


Zaro ido dukkansu sukayi ,tsakanin Su'adah da dadynta


Zaraf Shahida ta mike "Bara inje in masu alhaji bilya sallama yanzu zasu wuce"


"Uhm ni jirani,Muje in masu godiya mah"
Suka wuce suka bar Su'adah da dadynta tsaye sagale da hannu cikin tsakanin mamaki


Tundaga ranar Tsana ,kyara gamida tsantsan kiyayya shi ya maye gurbin soyayyar da ke tsakanin Su'adah da Momynta.




**

*KHALEESAT INTERNATIONAL HOSPITAL*

Yau Asibitin a hargitse ma'aikatan cikin ta suke,kowa kagani akan aikinsa yike cleaners sun goge ko'ina k'al k'al ,dukda koda yaushe amma nayau ta dabam ce, hakan zai tabbatar maka da cewa zaayi gagaruman baki a asibitin ,ko kuma NHIS zasu zo bincikar asibitin kanta.

Asibitin benene hawa uku ,tafkeken gaske, ko'ina farin fenti da ratsin brown akayi sai glasses da suka daure ilahirin Asibitin,A zahiri kashiga bakada banbanci da wanda yaje turai.don haka kowa kawai kagani a Asibitin to babbahne
Don haka akwai tsaro sosai na sojoji da En sanda horarru ,tunda ga farkon get din sojojine da bindigogi suke gadin Asibitin ,ba irin gajiyayyun mazannan da ake sawa ba da er sanda abasu uniformba a sauran Asibitin .



Tunda dadyn Su'adah motarsu ta shigo ,basu tsaya a parking lot ba saida suka kai har gaban reception kafin ya kinkimota,ya shigo cikin da gudu yina kwalla kiran "Nurse!"




Da sauri Nurses suka gungurata akan Wata gado me taya aka shige da ita wani station da naga Ansa A/E, daga down floor .

Cikin gaggawa doctors suka rufa A kanta,da sauri suka manna wani na'ura a kirjinta da naga an rubuta Resuscitating machine, Suna jijiga kirjin ta,haka take sama da k'asa .........kafin taja wata Ajiyar zuciya tareda fashewa da wani gigitaccen k'ara.
Wanda hakan yasa dady burmowa dakin batareda ni takan likitocin da ke kokarin dakatar dashi ba


**
A daga wajen Asibtin kuma,wasu lafiyayyun motocine guda Hud'u suka shigo harabar asibitin ,dukda kasancewar Khalesat Hospital asibitin private ne,Amma kaf ,cikin garin Abuja babu mashahurin asibiti kamarsa da yikeda hororrun likitoci ,Wanda indai cuta ta gagara warkewa anan ,to saidai a bar dashi k'asar.

Don ko chief doctor dinsu ,medical doctor ne kuma surgeon,shine kuma mamallakin Asibitin,Yakasance JININ SARAUTAr masarautar Azrajat , Wanda Sam bama ya zama a garin Abuja ,kai kasar ma sai jifa jifa yike zama a cikin ta ,donshi SARAUTA bata cikin tsarin Dr KHALEED

Don, ko asibitin sa inkaga yazo to An kawo case d'in da yafi k'arfin kafatanin likitocin ne.

Kamar koda yaushe hakan ne ta kasance da Dr.Khaleed Bamalli,shine kuma dalilin zuwansa da tawagar mabiyarsa cikin wainnan motocin hudu,don duba wani Ambassador na kasar burtaniya da yazo wajen shugaban kasa,saikuma cuta ta samesa.
Ankira wayarsa da nufin yaje ya dubasa a gidan gomnati yace shi lalle saidai akaishi Asibitin sa inko ba haka ba ,a nemi wani likitan da zai dubasa ko a maisheshi kasarsu
Kaji babbar likita da gadarar izzah,and a youth averaging age 29

Don dole aka kawo ambassador din asibitin,shi kuma bai dauki wasu Awanniba yabiyo jirgi daga university of victoria na kasar Uganda inda yike a matsayin visit lecturer dake daukarsu Med.surge ya taho nan garin Abuja ,Guards dinsa suka daukosa a motocin da suka dace zuwa wannan Asibitin


Motocin tunda suka shigo suke sheka gudu akan kwaltan asibitin inda wani irin titi ya nade Asibitin kamar yanda matakalan bene ke nade bene ta wannan titin suka dinga gudu sukadai batareda ko da me keke ya biyo bayan su ba,har saida titin ta sada su da bene hawa na ukun ,


A take ukun suka dakata a dan wani fili ,yayinda aka shige da cikon dayar Wata varendarh maidaukeda flowers cikin tukwane da Acs kota ina ,da wasu irin kujerun silver

Hmmm nan ne inda bakin Dr KHALEED kezama kafin su samu damar isa ofishin sakatariyarsa dake cikin falon ,sannan kakai nasa office d'in


Motarsa na tsayawa ya6alle murfin kofar batareda ya tsaya jiran a bude masa ba ,cikeda kuzari da zafin nama yafito

_Tsarki ya tabbata ga allah mahaliccin kyau da kyawawa cikin mutane.......chinikeeee🤔 Lallene wannan kyakyawan giant saurayin ne,ya maida Kansa busy haka?,Sam yafi kamada masu zaman Ac suna bada umurnin,Ma'ana kowa Allah yina saka shine a gidan da ya dace dashi,saiga Khalid ya sa6a daga nasa suffar ,na gaisheda wannan horzillar💪_


Bai tsaya amsa gaisuwar kowaba face daga masu hannu daya ringa yi har ya dangana da office d'in sa
Sannan yina Shiga bai had'e minti biyarba ,ya fito cikin shigar kayan theater ,bayan office dinsa yabi ,sakatariyarsa na bayarsa rikeda files da laptop tana koro masa bayanin case din patient din,har suka Shiga wani karamun lifter room ,ya danna lifter zuwa floor dinda yikeson zuwa ,yiuuuu suka fara k'asa sakatariyarsa still tana masa bayanin cutar nasa ,filter din tana tafiya dasu


"He has the history of strock sir,Ya samu sauki bayan daukan shekaru biyu yina kar6an therapy, sannan ya cigaba da harkokinsa

A halin yanzu kuma ,mun samesa da signs and symptoms na gangrene, which wannan ne case na biyu da aka ta6a samu na cutar a kasar nan, yanzu kana ganin theater ne zaayi mai ko kuwa yaya,tunda sir likitoci dai sunyi ittifakin gangrene bayida magani tukuna."


Cikin muryarsa mai madarar izzah ,sassanya can kasa ya soma magana
Hakan yasa tai saurin kanga kunnenta saitin sa yanda zata iyaji

"Waya fada maku gangrene yake dashi,yet investigation on progress,amma ina mai tabbatar maki ba gangrene bane and zai warke inshaallah"


A daidai nan suka fito wajen level 0 daga level 3 d'in, baikuma bi takan sakatariyarsa ba,yasa taba wata nurse kayan files din ,sannan ya bada umurnin a shigo da Ambassador din


Daga nan direct operating theatre ya nufa ,da sauri ya wanke hannunsa yanda akeyi ,ya fito ma'aikatan na zura masa theater gown din akan kayan sa shi kuma yina tafiya ya zare normal takalminsa a kofar dakin theater yina Shiga dakin ya zura boot din d'akin da glass da komai.......



---------------------------------------------------
```Kardai Ku sha'afa 🤩 Wannan littafin Zazzafa ne daga cikin gwarazan zafafan Alheri writers....Wanda suka had'a da:```

_*K'WARYAR SAMA🙄* zazzafa daga Alk'alamin *Maman teddy🧸*_


_*JININ SARAUTA(the gorgeous royal blood)* zazzafa daga Alkalamar *Hassenart Bamalli(oum Aphnan)*_



_Idan kinason biyan *NORMAL PAYMENT* ne ,to kowanne littafi d'aya *#100* ne duka biyun ne *#300*_



_Idan kuma *VIP* ne kikeson biya toh,kowanne daya *#200* ne ,in kuma duka biyunne *#500*_


_Idan kuma *SPC* ne kikeso toh kowanne d'aya *#300* duka biyun kuma *#700*_


_Zaki iya biyan kudinki ta daya daga cikin wannan hanyoyin biyan:_


_*BANK PAYMENT*_

7782217014
Mohammed Hassana
Fcmb


_*VTU TRANSFER*_
09065990265


_*MTN CARD PAYMENT*_
08081202932


_*SAI KI TURA SHAIDAR BIYANKI TA HANYAR SCREEN SHOTTING EVIDENCE DINKI TANAN👇:*_

08081202932



_SAI MUN JIKU MASOYAN AMANA,KUYI ZUWA DAYA KU KAFCI RABONKU CIKIN SASSAUK'AR FARASHIN GASKE🤌_


_Maman teddy🧸_
_Oum Aphnan takuce_
[7/12, 2:02 AM] Bamalli✌️: _*🕊️JININ SARAUTA💍*_
_(The Gorgeous Royal blood)_



_With_



_(Pure love, sex and Romantic)_




_Page 7 & 8_
_*Alheri writers Asso* ._




Na...Oum Aphnan
*Marubuciyar:*
Qasaitattun Mata
*Rayuwar Afredarh*
Ramuwar Gayya
*Bagidajiya*
Laylerh
*Jarababben Namiji*
Namijin kishi....dss





*Gargadi*
Littafin matan Aurene in bakida aure karki karanta dangirman Allah,muna kokarin gyarawa ne ba 6atawa ba



*Continuation*
Koda Na farfad'o daga doguwar suman da nayi ,gashidai inajin muryoyin mutane, ciki kuwa harda muryar dadynah yina k'wallah kiran sunanah ,ammah idona bana iya ganin komai sai matsanancin duhu ,saiko muryar momy sanda take tabbatar ma dady da kasancewata shegiya da ke dawomun tar tar a kunne kamar yanzu Abun ke faruwa.da karfi na rik'e kaina.
"No momy ,no ! Kicemun ba gaskiya bane abunda naji momy ,kicemin mafarki nakeyi ba gaske bane ,innalillahi wa inna ilaihir rajiun"


Da sauri dady yazo ya kama hannuna
"Su'adah! Su'adah ,tashi ga dadynki a gefenki ,wasa momynki take muki kedin er muce ,er mu ta cikin mu"


Shiru nayi ba tareda na cema dadyn komai ba amma nasan for sure so yikeyi ya kwantar mun da hankali ,amma gaskiyar zance ba sune biological parents dina,ba .
Zazzafan hawaye tuni ya fara gangaromun a kwarmun idona .


A haka nurse tazo ta janye dady ,aka cigaba da gwargwadani aka sakamun drip da alluran da zasuyi calming nerves dina,ban dauki wani lokaciba barci ya sureni


**
Bayan an shigo da Ambassador ciki
Dr khaleed ,tareda En team dinsa a operating theatre ,samun waje yayi ya zauna yina observing patient din batareda yako ta6a jikinsa ba.
Daga bisani ya danna desktop din gefen marar lafiyar yina karanta duk wani bayanin ciwon nasa.

Jan Ajiyar numfashi yayi ,kafin ya dauki oxymetre ya duba oxygen saturation d'in sa,ya kuma ga yawan litres per mints dinda aka sa masa oxygen d'in.


Bada umuni yayi da a jona masa Na'urar gwaji a kirjin Ambassador zuwa wajen hakarkarinsa na 6arin hagu...saida ya dauki dogon lokaci yina bincikensa ,kafin daga bisani ya hau typing akan desktop mai daukeda bayanin cutar marar lafiyar .yina gamawa tsaf


Ya kama hanyar fita waje,mamakine ya kama sauran likitocin ,da sauri Nurse dinda zatai assisting dinsa wajan surgeryn tabi bayansa
"Dr .wannan mutumin yina bukatar taimakon gaggawa amma bakace komai ba zaka fita ba ayi aikinba"


"A fitarda wannan marar lafiyar bayi bukatar aiki,ya shaki iskane mai guba ,wacce a take taje ta toshe sassan hunhunsa na hagu,zuciyarsa daganan ta wuce babbar jijiyar jinin dake kaiwa kwalwa sako wato (aorta) ,wannan ne ya haifar masa da cuta mai kama qagewan gabbai (Stiffness) da kuma kasa nimfashi due to (hypoxia) sai kuma ya tafi zuwa comma ,wannan shine a takaice sauran bayani da sauran therapeutic abubuwan da zaayi masa are documented a cikin folder dinshi....so a wuce dashi medical ward ,special side,sannan a kira physiotherapists saboda stiffness dinsa "
Tunda ya fara bayanin tayi shiru tana jinjina kai ,muryarsa na saukar mata da kasala Wanda yasa ko fahimtar abunda ma yike cewa batayiba ,haka ta zuba ma jajayen le66an bakinsa na mujiya tana qissimasu a cikin bakinta,batai auneba saidai taji fitarsa cikin dakin.

A hankali taja qafa zuwa wajen sauran likitocin ba tareda ta iya furta masu komai ba.
Dariya suka saki ,don kowa ya kwana da sanin zazzafar kaunar da jamila ke gwadawa Dr Khalid.


**
Chanja shirinsa yayi zuwa suit masu duhuwa ,ya wuce gaba ilahirin manyan likitocin na take masa baya ,a haka yike duba d'aki d'aki na cikin Asibitin.
Har ya kawo emergency.


Yina shigowa ina Dada tsaga ihu ,tareda fara fizge fizge kamar mai Aljannu

Da Sauri yazo ya kama hannuna kafin ya saita bakinsa cikin kunnena ,saboda k'arana bai bari inji magana ko anyi mun.
"Sorry kinji ,sorry" ji nayi wani sassanyan sauti namun magana a kunne,a take ya haifarmin da faduwar gaba har kana iya ganin harbawar kirjina da karfi a fili

Da sauri yakai hannunsa kan kirjina ,kafin ya tambayi likitocin da suke kaina
"Meye sunan ta?"
"Su'adah Yusuf"
"Su'adah?"
Ya kira sunana cikin sassanyar muryarsa,shiru nayi batareda na dai tamka ba
"Su'adah nasan fa kinajina,bude idonki ki kalleni"
Instead in bude ido saina dad'a rumtsesu ,A take gabadaya likitocin suka saki dariya.

"Meye ke damunta?"
"Ankawota unconscious, daga baya kuma sai kwalwarta yayi kamar ya samu matsala,yanzuma muna tunanin wucewa da ita psychiatric ward ne"

Shiru yayi yina kallona
"Su'adahhhh ,bude idonki ki kalleni ,zan muki maganin ko meke damunki ,ni dan uwankine,kuma ina sonki kinji? Wainnan likitocin basu iya koman suba ,ko ke mahaukaciya ce ?"

Da Sauri na bud'e ido tareda furta "A'ah yayanah"

Mamakine ya cika likitocin ,sun shafe awanni suna Neman kanta sai gashi daga zuwar Dr cikin kalmomi kididdigaggu ya dawo da ita hayyacinta


Jan kujera yayi ya zauna ya daura hannu a kafadana yina matsawa a hankali ,kafin ya soma yimusu magana


"Batada wani cuta face psychological distress, wannan yina bukatar psychological reassurance ne ,ba magani ba....Kaja patient dinka a jikinka bayan ka yi kokarin fahimtar matsalarsa ,sai kasan yanda zakayi ma patient magana daidai da kalaman da ziciyarsa da kwalwarsa keso,wannan tabbas yafi magani saurin aiki

Kunga kowani mutum yanaso ya samu soyayya ,sannan yina bukatar self esteem (According to Abrahama's law of psycho s.) So dole wajen kulada Mara lafiya ka duba wannan ,hakan zaisa yaji dudduniya ba kamarka..."


Duk likitocin jinjina masa kai suka Shiga yi alamar gamsuwa ,kafin ya koma kaina


"Yanzu meke damunki Ammmm (yina kokarin tuno sunana) oh yes! Miss Su'adah?"
Murmushin jin dad'i nayi don ni A duniya inaso a bani girma ,so naji dad'i da ya kirani da (Miss)


"Bakomai saidai momynah ne ta daina sona ,she said she hate our relationship, banida kowa yanzu sai Allah saikuma kai da yanzu a sama kakirani da ur love,ka kuma ce ni kanwarkace..." Na dakata da maganar ina sharar kwallah


Sunkuyowa daidai kaina yayi kafin ya furta "Is Alryt OK?....bara zanje in gama duba marasa lafiya zan dawo muyi magana a nutse"

Zumbur na mike zaune tareda kamo yatsun hannunsa manya guda biyu na rik'e da duk hannayena ina wasa dasu .
Cikeda shagwa6a "in zo muje in rakaka yaya? Kaga nima inaso watarana in zama likita kamar kai " na fada ina nuna kirjinsa da dan yatsata


"A'ah ke bakida lafiya"
Kuka na fashe dashi
Baki na rawa yace "OK ,taso ,taso muje"
Da Sauri na dirko kasan na zura wani takalmi da ake masa laqabi da shaku shaku ,shi marasa lafiyar Asibiti ke basu,Jikina sanye cikin rigata blouse Rabin cinya sai hular asibitin da ya rufe turgujejen gashi na.


Katakam na rik'e hannunsa kafin muka kama tafiya.
Muna fitowa na had'e da dadynah
"Dady zamuje survey da yaya"
Dan tsuke fuska yayi ,"waye yaya?" Shima a take Dr ya had'e rai don yasan P.A Ahmed Ngwandu ,karma yayi tunanin don matsayin sa ne yasa yake kula diyarsa

"Gaba yinan ba"
Ta nuna Dr
"Oh Adawo lafiya ...still waiting ,buh speedy recovery ah wish"
Thumb up Nayi masa kafin na wuce muka tafi



**
Sauki Alhmdllh ya samu,saidai har yamma kafin yayana ya bani sallama ,zuwa wannan lokacin wani sahihin shakuwace ta tsirgu a tsakanin mu,ni a haukata kallon yayah Nike yiwa Khalid ,yayinda shi kuma ya afka kogin soyayyahta tareda yiwa kansa Alkawarin duk runtsi duk wuya bayida matar aure sai Su'adah musammn ma da yaji asalinta na matsayin marainiya,ya yarda zai jirata tsawon shekaru har ta girma.


Muna bayan mota ni da dady ,driver na tikamu ,a sanyaye na waigo na kalli dady
"Dady momy taki zuwa dubani ,Na fada maka gaskiya momy ta fada Kaine baka saniba"na kare maganar shesheqar kuka


"Shsshsh ya Isah ,ki bari muje gidan itace zata fada maki wasa takeyi da bakinta,kunyane ya hanata zuwar,amma duk En mintoci saita kirani

" shikenan dad I trust you "
**
"Barka da fitowa sarki mai dogon zamani ,Adali mai dubu na masoya ,gaba salamun baya salamun ,Inuwa sa gabanka inda kake so✊"

Waziri kenan ke duk'e yina zaro banbad'anci bayan dukkan hakimai sunzo sunkawo gaisuwa wajen mai martaba.


Zaro da fuska sarki yayi fuska ba yabo ba fallasa .Abun saida ya kad'a hantar cikin kowani mahaluki dake zaune a wannan fada.

Cikin muryarsa mai d'auke da Amon Mulki ya kira sunan sa "Waziri Muqaddis!"
Dam gabansa ya fad'i ,kafin bakinsa ya fara rawa jikinsa ya d'auki kyarma
"Na'am ran takawa ya dad'e"
"Meye hukuncin Wanda yaci amanar fada?"
Zirrr ! Wani gumin Azaba ya karyowa waziri ,kafin cikin dakushewar murya yace "kis...kis...kisa ranku shi dad'e"
Juyawa yayi ya kalli mutanen fadar d'aya bayan d'aya kafin ya tsaida idonsa a saitin gabas ba tareda ya kalli kowa ba ya furta
"Sarkin hukunci a qaddamar masa!!!"


Sai da ilahirin wurin gabansu ya bada sautin dumm!

Wanda aka kira da sarkin hukunci da Sauri yazo gaban sarki ya gofana akan gwuiwakunsa
"Allah taja da yawan rai,a gafarceni bansan waza'ai wa hukuncinba"

Jim yayi kafin yace "Muqaddis!!!"
A take sarkin hukunci yayi zaman En bori wukar hannunsa me suna gayawa jini na wuce ta fad'i kasa

Cikeda izzah ya mike tsaye tareda nuna waziri da manunin yatsa "kuy masa yankan rago" ya fada cikin mugun tsawa


Da Sauri suka ja waziri zasu bardashi fadar zuwa wajen yanke hukunci.
Sunkai daidai bakin kofa ya kuma kiran "Sarkin hukunci " tsam sukaja suka tsaya ,tareda sadda kai kasa

Cikin mugun fushi ya ciko bindiga cikin Alkyabbarsa ,baiyi wata wata ba ya saita waziri
Sai saitin "Tushhh!!!" Tareda tsartuwar jinine ya karade wajen.


A firgice kowa ya dago yina kallonsa,amma kowa ya kasa furta kalma d'aya banda waziri dake burgima cikin jini

"I make a hut and I burnt it...ku fada masu muna iya ganesu a kwarorin idonsu....ko kaima ka soma zama munafikin fadane eyeh sarkin hukunci???"

--------------------------------------------------
```Kardai Ku sha'afa 🤩 Wannan littafin Zazzafa ne daga cikin gwarazan zafafan Alheri writers....Wanda suka had'a da:```

_*K'WARYAR SAMA🙄* zazzafa daga Alk'alamin *Maman teddy🧸*_


_*JININ SARAUTA(the gorgeous royal blood)* zazzafa daga Alkalamar *Hassenart Bamalli(oum Aphnan)*_



_Idan kinason biyan *NORMAL PAYMENT* ne ,to kowanne littafi d'aya *#100* ne duka biyun ne *#300*_



_Idan kuma *VIP* ne kikeson biya toh,kowanne daya *#200* ne ,in kuma duka biyunne *#500*_


_Idan kuma *SPC* ne kikeso toh kowanne d'aya *#300* duka biyun kuma *#700*_


_Zaki iya biyan kudinki ta

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads