Showing 6001 words to 9000 words out of 25770 words
Chapter 3 - ARMAN - MALEEK BY (1) SALMA YAR LELE-1.txt
dadi kafin ya miƙe daga in da yake.
gefen bed ya zauna, tare da dan daura hannunshi akan cikinshi, ya lumshe idanunshu, fuskarshi ya dan yamutsa tare da dan shagwaɓeta, kaɗan irin na Shagwaɓaɓɓun da in suka samu wuri to zasu zuba shagwaɓa, a hankali ya miƙe ya nufi fridge din da ke kusa da bed din.
budewa yy , tare da fitar da peak milk mai sanyi sosai, tare da wata gorar zuma mai kyau, cup ya dauka ya daurayo, ya dawo tsakiyar carpet din da yake walale bakin bed din shi,zuba madarar yy ya sanya zuɓa, tare da sanya Spoon ya fara jujjuyawa sai da ya tabbatar ya haɗe jikinshi.
kafin ya dauka da Bissimillah..!, dauke a bakinshi ya kafa kanshi, sai da ya shanye tasss kafin ya ajiye cup din, sanyayyiyar gyatsa ya saki tare da lumshe idanunshi.
gefe ya mayar da cup din da gwangwanin ya, matsa ya jingina kanshi da jikin bed din yy shiru, idanunshi a lumshe kamar msi barci, a zahirin gaskiya kuwa ba barcin yake ba,tunanin rayuwa kawai yake..
A hankali guraren 1 ya miƙe daga zaunan da yake, ya nufi bathroom, alwala ya ƙara daurowa, yana fitowa ya sanya wata lafiyayyiyar Dubai Jallabiya mai masifar kyau black da tayi asalin fito jishi da tsantsae farin fatarshi.
gurin pray met dinshi ya matsa, tare da kabbara Sallah, cikin zazzaƙar muryarshi ya ringa rairo karatun Al-qur'ani, har guraren 4 sai da aka fara kiran Sallah Subhi kafin, ya tsagaita ya koma gefe yana karatu da Tasbihi 4:30am ya miƙe , Sabon Wanka da Alwala yy, tare da chanja kaya, ya nufo hanyar waje.
Shi daya ya fara takawa daga cikin Masarautar zuwa Masallaci , a hankali yake tafiya, bakinshi kuma har lokacin bai gushe da ambaton sunayen Allah ba da Addu'o'i tare da Tasbhi , haka har ya fita daga part dinshi, ya fara ratsawa ta cikin masarautar da bb kowa, bb motsin kowa, sai sanyayyiyar Iska Asuba da take kaɗawa, wadda take dauke da ni'imomi da wani yalwataccen nishaɗi, iska ce mai sanyaya zuciya, da sanya ruhi cikin natsuwa, iska ce mai dauke da iskar hadari wanda ya gangamu garin yy baƙiƙƙirin kamar za'a kece da ruwa.
haka yake tafiya cikin rashin tsoro, har ya ƙarasa Masallacin da bb kowa a ciki, A hankali ya ƙarasa cikin Masallacin, sai da ya dudduba komai kafin ya fito, tsayawa yy daga dan gaba cikin rumfar Masallacin, ya kauɗa kiran Sallah cikin sanyayyiyar muryarshi mai dadin gaske.
wadda tayi sanadiyar tashin kusan dukkan Al-ummar Masarautar tashi daga barcin da suke yi, gaba dayansu zuciyarsu tayi wani irin taushi jikimsu duk ya saki, kwaɗa kiran Sallarshi na biyu ne yy Sanadiyar tashin duk wani mai gigga-giggan masu Jinnun da suke cikin Masarautar, dan dama aje ne, duk lokacin da zai sauka masarautar, yy kiran Sallah to , duk wani mai gigga-giggan Aljannu da suke cikin Masarautar sun tashi.
cikin Azama gaba daya Ahlin Masarautar maza gaba dayansu suka yo Masallaci domin gabatar da Sallah Subhi , kafin kace Kwabo Masallacin da bb kowa ya cika damkam da Mutane, wanda cikarsu ma har tayi yawa, hakan zai shaida maka ba mutane ne kawai ba, cikin Nishaɗin da ya tsinci zuciyarshi a cikinshi, ya fara karatuh Al-qur'ani cikin Surarul Maryam, wanda gaba daya dadin Surar da Daddin Muryarsa yasa illahirin Aljannu , Mutane , Dabbobin da suke cikin gidan suka yi tsiiiittttt suna saurararshi, hatta da iskar Hadarin da take kadawa da karfi sai ta daina kaɗawa da karfin, sai sanyayyyiyae iska da take ratsa ko ina, har sai da ya idar da Sallah, gaba daya wata iriyar iska mai karfi ta fara kaɗawa.
kan kace wani abu ruwa ya fara dan sauka a hankali, duk da haka sai da yy musu karatu sosai kafin a tashi, shine last din fita daga Massalacin sai da ya rufe kafin, ya fara tafiya cikin natsuwa .
lokacin 6am tayi, a hankali yake tafiya yana sauke numfashi, sai da ya kusan shiga cikin part dinshi, kafin ruwan ya fara sauka sosai kamar da bakin kwarya, har sai da yasa Shehi ya dan kara takun tafiyarshi da yake yi, duk kuma da haka cikin natsuwa yake tafiya,har ya ƙarasa.
palon ƙasa ya zauna, yana zama wata Babbar mace da zata iya kai wa 60years fara ta fito daga wata hanya fuskarta washe da murmushi, cikin dan farin cikin da ya mamaye gaba daya fuskarta da zuciyarta tace "Assalamu alaika...!",a hankali ya bude idanunshi,jin muryar da ta daki dodon kunnenshi.
wani murmushi da ya kusa kasheni ya sakar mata, kafin ta mayar da kamilalliyae fuskarshi kamar yarda take yace "Wa'alaikissalama...!", ya fada cikin sanyayyiyar muryarshi, idanunshi yy ƙasa da su kafin ya dan murya zoben Zinarin da yake cikin hannunshi da yake fitar da wani kyalli na musamman.
cikin bada girma da rissinawa, tace "Barka da Asuba Shehi..!", a hankali ya furta "Uhmmm Coffee..!", ya fada a hankali ba tare da yace komai ba , miƙewa tayi tare da cewa "bari na haɗa maka" tana fada ta bar gurin shi kuwa ya lumshe idanunshi.
bata dauki wani lokaci mai yawa ba ya dawo hannunta daure da ƙaramin tray mai dauke da wani flask ƙarami, da cups da tea spoon sai sugar, dan tasan zalla ake haɗs mishi shi yake aa sugar da kanshi.
Stool ta jawo ta ajiye gabanshi, kafin ta dan rusunar da kanta tace "Shehi an gama", tana fada ta matsa chan ta zauna, kan kujera ta zauna, tana dan kallonshi,shi kuwa a hankali ya bude idanunshi, tare da dan rankwafawa, ya dauki cup din ya dan tsiyayi rabin cup ya zuba Sugar tea spoon huɗu, tare da fara dan gaurayaww har ta narke, kafin ya matsa gefe, da Bissimillah ya fara dan sipping dinshi har ya shanye tass, ya ajiye cup din.
A hankali ya dan kalleta da idanunshu, yace "Ngd ..."', ya fada yana dan mayar da kanshi akan kujerar, jinjina kai tayi ba tare da tayi magana ba.
Dan Jim sai ga wanu kyakyawan matashin Sarauyi ya shigo cikin palon, cikin dan murmushi yace ''Barka da safiya Shehi . barka da safiya Umma Jakadiya", murmushi tayi tare da cewa "barka Zayn-Maleek . fatan kun sauka lpy ?", dan shiru yy tare da cewa "Qlau Umma", jinjina kanta tayi.
kallon Shehi Arman_Maleeq , Zayn-Maleeq yy tare da cewa "Yaa Shehi komai fa ya gama kammala. kayan suna wajen Masarauta zuwa Anjima za'a shigo da su." shiru Arman_Maleeq yy bai cewa Zayn_Maleeq komai ba...
daga karshe ma miƙewa yy ya haye sama, duk binshi da kallo suka yi, kafin Zayn_maleeq ya koma inda ya tashi, tare fara haɗa Coffee sai da ya gama ya kallin Umma Jakadiya yace "Umma An jima Shehi zai raba kayan Azumi, dan wannan karon ba zamu jima ba zamu koma,na ji kuma kamar Ammie tace a taho da ke ", ya fada yana surɓar Coffeen, murmushu tayi tare da cewa "Zayn_Maleeq baki abin magana, Allah ya kai mu, " dariya yy tare da cewa "Su Umma za'a hau jirgi a tafi Madina", dariya itama tayi cikin sabo da irin rahar Zayn_maleeq tace "Oh Zayn_maleeq baka gajiya. abin da ba zuwana na farko bane wannan, bari na tashu na shige", ta fada tana miƙewa..
******
Gaba daya kusan Drs Biyar ne a kanta bayan Nurses dukkansu sun rufa a kanta, suna dubata, dan gaba daya numfashinta daukewa yy , yana sama da ƙasa, sai shasheƙa take, gaba daya jijiyoyin jikinta sun fito, jikinta ya dauki wani rawa.
Gaba daya Drs din su fara sarewa da lamarin Yarinyar, cikin lokaci dan kaɗan zata birkice , sai kuma jikin ya dai-daita, yanzu ne abun ya fi ko yaushe gaba daya, ta birkice sun kasa yarda zasuyi da ita.
Dr Aslam wanda ya fara daukarta , ya fito yana sharce zufa idanunshi sunyi jaaazir, hatta kayan jikinshi sun jiƙe da zufa, Office dinshi ya shiga, ya zauna ya dafe kanshi...
sai kuma ya ɗago kan tare, da daukar wayarshi. lallatsawa ya shiga yi kafin ya karata a kunnenshi.
sautin ring din Wayar Shehi ne ya fara tashi cikin bedroom din nashi, lokacin 9am ,a hankali ya dan mirgina da Addu'ar tashi daga barci cikin bakinshi, ya miƙa hannunshi, ya dauku wayar, sai da ya duba sunan mai kiran kafin yy picking call din ya ƙara a kunnenshi.
Zallar tashin hankalin da ya ji a cikin muryar Dr din ne yasa ya dan muskuta ya gyara zamanshi,cikin gaggawa yace "Shehi a gaggauta fitar da Yarinyar nan domin yi mata dashen nan,dan jikin gaba daya ya rikice bb sauƙi gaba daya, numfashinta ma baya fita, gaskiya tana cikin hali, in da hali ayi duk abun da za'ayi a yau din nan zuwa gobe a fitar da ita,"sauke numfashi yy .
kafin yace "akwai abokina da yake irin wannan .......
Wannan littafin na kuɗi ne , game buƙata zai iya tuntuɓata ta number na kamar haka.
07033371851
DAGA TASKAR ƳAR LELE🧚♂️🧚♂️🧚♂️
[2/22, 5:33 PM] ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚♀️🧚♀️: 🌼🌼ARMAN MALEEK🌼🌼
*DAGA ALƘALAMIN*
ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚♂️🧚♂️🧚♂️
SADAUKARWA GA AMINIYATA MASOYIYATA SADIYYA ABBAKAR MARU (ƳAR GATAN ROYAL STAR🌹🌹)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
PAGE 4.
Akwai wani Abokina da yake irin wanna Surgery din a chan garin Madina yake zaune, in kana so zan iya magana da shi sai ya shirya muku duk abun da ake baƙata", Ya fada yana dan sauke numfashi.
dan jaaan ajiyar Zuciya Shehi yy kafin yace "okay..!", yana fada ya kashe wayar, tare da yin baya ya koma in da ya tashi, barcinshi ya koma sai guraren 1pm kafin ya tashi, wanka da Alwala yy ya fito, yana ta baza kamshi, tare da ƙoƙarin sanya agogon Rolex diamond da yake tayi a hannunshi.
kamar kullum yana sanye ne da Turkey Jallabiya fara sol,sai takalminshi da ya kasance half cover, ya lulube gaba daya jikinshi da irin Alƙyabbar Manyan Malamai baƙa mai kwalliyar Golding , ga wani kamshin Huge Boss da yake tashi, yy wsni sihirtaccen kyau, kamar a boyeshu, ƙasumbarshi da sajenshi gaba daya sun kwanta luf,dogon Gemunshi kuwa sai motsawa yake a hankali kyawawan lips dinshi suma suke motsawa,tare da Ambaton Ubangijin Talikai.
Downstairs ya nufa, yana ƙara baza Alƙyabbarshi, da gyara Agogonshi. tun kafin su ƙaraso cikin palon, kamshin turarenshi ya shidawa su Zayn_maleeq da suke zaune cikin palon zuwanshi.
cikin ladabi duk suke kallonshi, har ya ƙaraso cikin palon, duk duƙar da kansu suka yi ƙasa cikin bafa girma suka zube tare da cewa "Barka da fitowa Yaa Shehi", tsantsar kauna da kulawa, ya shafa kawunansu . tare da lumshe ido kafin yace "kuna lpy ?", gaba dayansu suka Amsa da "Alhamdulillah", jinjina kanshi yy kafin ya zauna kujerar da ta kasance ta zamanshi, bayan shi bb mai hawanta sai Zayn_maleeq shima kuma ba ko yaushe ba.
Umma Jakadiya ce ta fito daga wata ƙofa, kallom Shehi tayi tare da dan rausayar da kanta tace "sannu da hutawa Shehi...!", a hankali ya bude jikirtattun idanunshu, akan Umma Jakadiya, kafin ya jinjina kanshi, yace "Alhamdulillah..!", cikim tsananin kula ya mata maganar, wanda yake nuni da Zallar kularshi a kanta.
kallonshi tayi , tare da cewa "Shehi a kawo Abin ci ne ?", dan tsura mata idanu yy na wasu seconds kafin ya jujjuya kanshi, yacr "ah'ah lokacin Sallah...!", yana fadar haka ya miƴe, gaba daya Ƙannenshu suka mara mishu baya izuwa Masallaci.
ko da suka je Shi yana gurin Liman su kuma suna Sahun bayanshi, haka har aka idar da Sallah, bayan an idar duka fito, yana jere da Lamurɗe suna dan tattaunawa Zayn_maleeq da Abdul_Maleeq tare da Sayyid_Maleeq na bayansu tare da Ayman Yaron Lamurɗe, suna tafiya suma suna fira,sai dai Zayn_maleeq duk ya fi zuba, sauran Triplet dinshi kuwa Abdul_Maleeq da Sayyid_Maleeq basu cika surutu ba, duk ya fisu labari, dan su kusan zubin tsarin halittarsu daya da Shehi basu damu da duniya ba ayi ko kar ayi bb ruwansu, su dai kawai suna rayuwarsu.
In da aka tsayar da Motocin Rarrabar Azumi suka nufa, motoci ne Dav guda Biyar, daya Sugar ne ciki,daya gyero, daya wake, daya shinkafa sai dayar Mai ne ciki.
ga kuma jerun mutanan da duk suka hau hali suna jiran Shehi, bude motocin aka yi, fiffito da kayayyakin aka fara yi, Zayn_maleeq na gefe kasantuwarshi na mai son jiki yasa duk wani aikin wahala baya ciki..
Sayyid_maleeq da Abdul_maleeq kuwa suna bayan Shehi suna taimaka mishi, su da kansu suke dauka su bawa Shehi shi kuma ya miƙawa mutanan, bayan an gama rarrabawa, sai kuma ya bi kuwa da 10k , wanda wannan kyauta ta tsoma gaba daya yan Masarautar Baihan cikin murya da jin dadi, dan in ba shu ba sai Babanshi sune kawai suke bautawa Masarautar, da jikimsu da kuɗinsu, basa gajiya da dukkan buƙatun mabiyansu.
duk halin da mutun yake yaje ya fada musu sube masu kafadar dauka, wanda tausayin da Allah ya daurawa Lamido Abdul-azeez Arman Maleeq na talakawan garin shine mussababbin ciwonshi, yanda Al_umma suke kaunarshi shine mafarin ciwonshi, yarda yake da zaratan Mazaje wanda suka kasance Yaranshi ha cikinshi shine ya zama tubalin ciwonshi, wanda shekara day-daya har shekara 20years cif yana kwance bashi da lpy.
rashin lpy mai muni, wadda kwata-kwata baya iya aiwatarwa da kanshi komai, konai sai dai a mishi.
sai guraren 3:30 o'clock suka gama rarrabar cikin gajiyawa, Zayn_Maleeq ya taso daga in da yake zaune ya nufosu, yana zuwa ya riƙe hannun Shehi da yake cikin Alƙyabbarshi , cikin kulawa ya dan kalleshi, da ido ya mishi mgn .
fuskarshi ya dan ɓata kafin yace ,"Yaa Shehi akwai gajiya", ya fada yama kallon sauram Yan uwanshi, Abdul_maleeq yace " wa mai gajiya ??", a hankali yace "Shehi Zayn yake da gajiya..!", ga fada yana dan yin luuuu da idanunshi..
kallonshin Shehi yy cikin dan nuna hukunci ya rike yatsun hannunshi, tare da matsewa, yar ƙara ya saki, cikin dan yana yi yace "Ayya Hamma Shehi na tuba na bi Allah na bika,ba ni da Uwa , Uba ba lafiya Adda na bata kusa Kai ne kawai Babana Mmna , Addana, ka gafarce ni", ya fada yana shagwaɓe fuska.
tuni raunin Shehi ya bayyana, triplets din da suke jere masu bala'in kama da juna ya kalla, numfashi mai karfi ya sauke, tare da dan shiga tsakaninsu gaba daya ya rungumesu . suma riƙeshi suka yi, dan sun san duk lokacin da yake kewar Mahaifiyarsu ne kawai yake musu haka.
sun dan jimaa a haka kafin ya sakesu, ya kama hannayensu , suka nufi masjid.
sai da ya tsayar da su bayanshi, kafin ya matsa gurin Liman ya zauna, Al-qur'ani ya dauka duk ya mimmiƴa musu, shma ya dauka, cikin ƙira'a mai dadin gaske suka fare karatu gaba dayansu. bama sa kallon Al-qur'anin saboda suna da haddarshi a kansu, dan sittin ta zauna musu daram a kansu.
sun san yi karatu mai yawa kafin lokacn Sallah yy, miƙewa yy ya ajiye Al-qur'anin, suma ajiyewa suka yi suka kiƙe, kabbara Sallah yy, duk mutame suna shishigo cikin Masjid din, bayan sun idar suka fito, yana jere da Ƙananshi dukkansu Ukkun dan Dsn Lamurɗe baya tare sa su tuni Lamurɗe yy mishi wata Uwar harara da tasa bb shiri ya barsu.
suna tafiya Zayn_maleeq ma duƙewa, sa boda tsananin yunwar da yake ji, sun kusa shiga part din Shehi ya dan yi yar ƙara tare da dafe cikimshi, da sauri suka jujjiyo gareshi, kafin suyi taku daya ya isa in da yake da sauri ya taroshi, karashi yy da jikinshi, tare da tsura mishi kyawawan idanunshi, yana kallonshi.
sai kuma ya kalli Abdul_maleeq da Sayyid_ Maleeq, kallon sa yy musu kawai ya fahintar da su mai yake nufi, da sauri suka tarairayi Dan Uwansu, suka kakkamashi zuwa part din su, har sun gilma part din Jadda, Zayn_maleeq yace su shiga da kyar, su sama mishi abun da zai ci.
ba suyi musu ba suka shiga, zaune suka samu Jadda ƙafa daya kan daya