Header Ads
Showing 15001 words to 18000 words out of 25770 words

Chapter 6 - ARMAN - MALEEK BY (1) SALMA YAR LELE-1.txt

Ads the beginning of article before Image

20 Jun 2024

334

Ads at the middle of Article

sauke numfashi, bata yi mgn ba har ya haye Upstairs.




A hankali ta miƙe, kitchen ta nufa, bata jima ba ta fito da madaidaicin flask , da Ƙananan Cups sai kwalin Sugar da Tea spoon, saman ta haye, ƙofar farko ta kwanlwasa tare da tura ƙofar , haɗaɗɗen palo mai kyau da tsari ya bayyana, sanyayyan kamshi tare da sanyi ACn cikin palon ne ya haɗu ya gauraye Palon tare da bada wani ni'imtaccen kamshi mai sanyaya zuciya, tare da sanya natsuwa.




kan daya daga cikin royal chair din palon ta zauna, tare da jaawo Center table ta daura tray mai dauke da flask da cups, jiranshi ta shiga yi, ganin an share 1 hour, bai fito ba yasa ta miƙe ta fita, tana fita ba da jimawa ba, ya turo ƙofar bedroom din ya fito, yana ta baza kamshi, yana sanye da Jallabiya fara tass da wando, kanshi yana luluɓe da hirami red da ɗigon fari, hannunshi zube cikin Aljihun Jallabiyar , sai zuba kamshi turaren huge boss yake, fuskarshi na fitar da wani Annuri da haske mai daukar hankali , yy wani fitinannen kyau , yana tafiya kanshi a ƙasa, yana tasbhi da baya rabuwa da bakinshi.






zama yy kan kujera yana fesar da numfashi, jinginar da kanshi yy , tare da zame lips dinshi na kasa ya zamana yana cikin bikinshi, a hankali ya fara tsotsa cikin wani salo na musamman, wanda za'a kiranshi da Sexy moment , shi kuwa zallar gajiya da yunwa ce ta sanyashi yin hakan, dan rabonshi da abin ci, tun jiya war haka.




Wayarshu ƙirar Iphone 13 pro, ya dauka a hankalin tare da daddana number, ring daya biyu a na ukku ta dauka cike da natsuwa tace "Assalamu alaika..!", "Wa'alaiki salam..!, Yunwa", ya furta da daddare.




Yana ajiye wayar ta shigo sanye da hijab dark Blue , ta ziro siraran hannunwanta ta cikin hannun hijabin, fara ce sosai, sai dai tana da dan jiki ba laifi a shekaru ba zata gaza 16 years ba, colour ba Hijab din shi ya fidda Asalin kyan fuskarta, zagayayiyyar fuskarta ta fito rass ta cikin dan wuyan hijab din, tana tafe tana fitar da kamshin humra mai masifar kamshi.




Sallama tayi,chan ciki ya amsa mata ba tare da ya bude idonshi ba, tana ƙarasowa tsakiyar palon ta cire zunbuleliyar hijab din jikinta, ta ajiye akan kujera 1 sitter, kyakyawar surar jikinta mai kyau da tsari da ta gama haɗewa cikin ɗamammum kayanta, masu kyau.
sanye take da riga fara body hug , sai black din wando skin tight ya bala'in dameta shima iya cinya.
gaba daya surar jikinta da ta kasance coca-cola a bayyane, jikinta sai glowing yake.




ƙarasawa tayi kusa da shi, tare da dan zama ta shige jikinshu, a hankali ta furta"Shehi..!", idanunshi ya dan matse a hankali ta daura yatsun hannunta da suka sha jaan lalle akan fuskarshi tana bin sajenshi da yatsunta, tare da jaa mishi gemunshi.




kyakyawan murmushi ya sakar mata tare da riƙe hannun yy kissing nashi .
yana bude idanunshi akam hannun, idanunshi ƙirrr akan yatsun na wasu mintuna, yana kallon jaan lallen da yy masifar yiwa hannun kyau sai sheƙi da ƙyalli yake, turo bakinta ta dan yi, tare da gyara zamanta sosai, gaba daya rabin jikinta ya zamana yana nashi, ta daura kanta akan kirjinshi, tana dan shagwaɓe mishi.




"Waya miki..?", ta tsinci maganarshi a sama, "Ayyana..!", ta fada kanta tsaye, bai ƙara cewa da ita komai ba sai sakin hannun nata da yy yana gyara mata hular kanta mai gashi, wadda take kamar ta sanyi.




zamowa yy da ita , tare da zama akan carpet, miƙewa tayi ta dawo gabanshi, tare da fara warware cups din da Ayyana ta haɗe gurin daya, daya ta ajiye, tare da bude flask , ta fara tsiyayo coffee sai tiriri yake, sai da tayi rafin cup din kafin ta barshi haka, sugar ta dauka kwara ukku ta zuba, tare da jujjuyawa.




sai da ta gama ta kalleshi, shima ita ya kalla, sai ta kyarkyace da dariya, taɓe bakinshi yy bai ce mata komai ba, sai jawowa da yy shima ya fara haɗawa, sugar daya tal kawai ya sanya ciki tare da jujjuyawa, a hankali yy Bissimillah tare da fara skipping coffee .
tana gefenshi tana shan nata itama




kafin ya gama sha tuni zufa ta wanke mishi fuskarshi, handkerchief ta dauka tare da fara goge mishi goshinshu, da yake fitar da zufa, sai da ya shanye tas kafin ya saki sanyayiyyar gyatsa, Hamdallah yy lokacin da ya tabbatar da cewar cikinshi ya cika .






Sannu ta mishi, gyara zamanshi yy a inda yake zaune, kanta ta daura akan kafadarshi tace "Boɗɗi am ba zamu je gurin Affa ba ?", ta fada tana wasa da gashin kanshi, da yake har bayanshi, shiru ya mata , jaan gemunshi tayi, wanda hakan yasa ya lumshe idonshi, tare ƙara buɗesu sa boda zafin jaaan da ta mishi.




Miƙewa yy, yana mikewa itama ta mike, da sauri ta nufi bedroom dinshi, bata tsaya ko ina ba sai gaban wardrobe dinshi, budewa tayi tare da zaɓo mishi wata baƙar Alƙyabba mai torch milk , fitowa tayi da ita a hannunta, tana zuwa ta rataya mishi, tana kallonshi, ƙarasa sawa yy , yana sauke numfashi bb karya ya gaji, amma idan bai wa wannan Yar rigimar tashi abun ya take so ba, baza ta bar shi kwanciyar hankali ba.




trayn ta dauka , sai da suka zo in da hijab ɗinta take, ta dauka ta sanya suka fito, a kitchen din sama ta ajiye kayan suka fito, suna fitowa suka tarar da Zayn - Maleeq , tsaye da alama shigowarshi kenan, "na rigaka ai", ta fada tana dariya, tana ƙarasowa gurinshi suka yi shaking hands, shiru Yaa Shehi yy yana kallonsu, kafin cikin faɗa yace "ban hana ku wannan ɗabi'ar ba..?", ya fads cikin kakkausar murya, shiru duk suka yi, "uhmmm ya fada tana wucewa , da sauri ta bi bayanshi suka fita yana baza Alƙyabbar jikinshi.




suna zuwa aka bude musu mota suka shiga, sai da aka fara tafiya, kafin ta zame daga in da take zaune ta koma kan jikinshi ta zauna, sai da suka dan yi nisa da gida yace ,"Ɗabi'ar banza ko.?, sau nawa ina miki gargaɗi akan hakan.? shi bake tuna cewar ke matar aure ce.? in ƙara ganin hakan zaki ga hukuncin da zan miki.", ya fada fuskar a kamile, "ba zamu ƙara ba, kuma gaskiya ni ba Matar Aure bace," ta fads cikin rigima.




yana kallon bakinta yace "wace ke..?", tura bakinta tayi kafin tace "Yarinya mana, sai na girma zan aure", ta fads cikin zallar Yarinta, "Allahu yahdiki",da sauri tace "Ameeen", tare da lafewa akan jikinshi tayi shiru, har suka ƙaraso. ROYAL INTERNATION HOSPITAL da yake cikin garin Makkah bata ƙata cewa komai ba, dan hannunta ma na baki tana tsotsa, tuni na tuna da Munkhair dan kusan, Attitude dinsu iri daya ne.






har mannewar konai kala daya, suna tsayawa ya zareta a jikinshi, tare da dan matsawa, ana buɗe mishi ya fito, cikin kamala da cikar zato, itama zagayawa akayi aka bude mata ta fito .




Zagayawa tayi gurinshi, suka fara tafiya a tare,bayan ta gyara hijab dinta, ta rufe idanunta da niƙaf din jikin hijab din, idanuwanta kawai akr iya hangowa,haka suka shiga cikin Asibitin.



bayan shigarsu cikin Reception din Asibitin suka nufi wani sashe na daban , sun dan yi tafiya , ƙafin su ƙaraso wani haɗaɗɗen sashe mai kyau, ƙofar Room 2, suka tura suka shiga bakinsu dauke da Sallama, Ayyana da bata jima da zuwa bace ta Amsa musu Sallama tasu, ƙarasa shiga suka yi cikin room din mai kama da gida , dan palo da bedroom ne , Zama Halimatu tayi kusa da ita tana mata magana, Yaa Shehi kuwa ciki ya wuce Abinshu ba tare da ya ko zauna anan din ba.




duk da yasan ko yy Sallamar bb wsnda zai Amsa mishi amma haka yy Sallamar, tare da shiga ciki, bed din ya nufa, tare da raɓawa gefe ya zauna, wani kyakyawan Tsohon mutum dan ba'a ƙirashu da matashi ba dan zai haura 70years na kwanxe akan bed din, fari ne sosai wanda kalli daya zaka mishi kawa Yaa Shehi kasan suna da dangantaka ya jini sosai.




ko dai Mahaifinshi ko kuma Yayanshi dan kamarsu har ta ɓaci, sai dai yana kwance ne , yadda kasan butun butumi, baya motsi, ban da idanunshi farare tar da suke jujjuyawa bb wata jijiya ta cikinshi da take harbawa, riƙe hannunshi Yaa Shehi yy, tare da mishi magana a hankali, duk da baya iya mgn Amma fuskarshi ta fallasa Asirin jin dadin ganin Yaaa Shehi da yy, dan sosai fuskar ta washe duk da va murmushi bane kan fuskar, kuma ya kafe guri daya da ido.




Ayyana da Haleematou ne suka shigo cikin bedroom din, Yaa Shehi ne ya kalli Ayyana , cikin girmama Yayar tashu yace "Zaytun", ya fada ya a rike hannun Affa, matsawa tayi kusa da Drawer din da kaya yakw jere, ta dauko kwalbar Zaytun ta miƙa mishi, ƙarɓa yy tare da budewa ya tsiyaya, ya fara shafa mishi a hannunshi da yake tubus bb gautsi bb komai .




kamar bayan kifi tsabar sulbi, na dauka hannun ne kawai, sai da naga har ƙafafunshi da yana shafa mishi haka yake taushi tuɓus, sai yanzun na gane dadewa ne a guri daya zaune, da tsabar gyaran da yake samu.






sai 10pm suka shirya wucewa, suna fitows su Zayn na zuwa dan sune suke kula da mahaifin nasu da daddare, har za suyi shaking hands shi da Haleematou sai kuma suka tuna da gargadin Yaa Shehi suna juyawa suka ga ya tsaresu da ido kuwa......






Kar ku manta wannan Book din na kuɗi ne, duk wanda yake so zai biya domin ya sha karatu.




07033371851


Don Allah duk wanda yasan ba siya zai yi ba kar ya min mgn, domin kar ma mu ɓata lokacinmu a banza please.






DAGA TASKAR ƳAR LELE🧚‍♂️🧚‍♂️🧚‍♂️
[2/22, 5:33 PM] ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️: 🌼🌼ARMAN MALEEK🌼🌼




*DAGA ALƘALAMIN*




SALMAJI ƳAR LELEN ROYAL STAR CE 🧚‍♂️🧚‍♂️🧚‍♂️






SADAUKARWA GA AMINIYATA MASOYIYATA, SADIYYA ABBAKAT MARU (ƳAR GATAN ROYAL STAR CE🌹🌹)




*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alk’alaminmu ‘yancinmu*






*P.8*




Tsaki yy A hankali dan ya lura Ɗabi'ar ta hi jikinsu, sai ya ci mutuncinsu zasu daina
, sum-sum ta dawo bayanshi ta tsaya, wani kallo ya makawa Zayn-maleeq kafin ya wuce, shi kuwa sosa kanshi yy dan yasan shirun na Yaaa Shehi mai yake nufi.




har suka Fito reception , tana maƙale a bayanshi tana binshi a baya, gefen hijab dinta a hannunta tana tafiya tana wasa da shi.
kai ka rantse yar 8 years ce , tsabar shiriritar ta, da wauta, wani ɓangarwn suka ƙara nufa, ita dai tana bayanshi, har suka isa wani ɓangare sak shigen na su Affa dan dai wannan word din Yara ne.




Wani Ɗaki ya tura ya shiga da Sallama a bakinshu,kamar yarda yy itama haka tayi da Sallamatar ta shiga ciki,bb kowa a ɗakin sai Yarinyar nan dai da take kwance akan bed, fuskaeta manne da Oxygen , babban yatsar hannunta an sa mata wani abu mai kama da kilif din matse shanya , hsnnunta daya na dauke da ledar drip .
gaba daya jikinta an yane mata shi da mayafi, gashin kanta kuwa an mata cover dinshi da wata kalar hula sharara blue.




har suka ƙarasa gurn gadon Haleematou bata ankare da Yarinyae da take kwance kan gadon ba, tsayawa tayi a gaban Yaa Shehi zata yi mgn, sai lokacin ne ta lura da Yarinyar da take kwance akan bed.




kafe Yarinyar tayi da ido na wani lokaci kafin tace "Yaa Shehi.!", bai kalleta ba haka kuma bai Amsa mata maganar tata ba, matsawa tayi ta rike hannun Yarinyar daya, tace "Yarinya mai kyau, ina sonta.!" ta fada tana kallonta, ganin ko matsowa bata yi ba, yasa tace "Yaa Shehi bata motsi fa ?. ka ganta kamar wadda ta mutu, ko dai bata da rai ne ?" ta jera mishi tambayoyin a jere, rasa wadda zai Amsa mata yy, hakan yasa yy tsut da dan bakinshi, yana kallon yana yin fitar numfashin Yarinyar.




basu jima a Ɗakin ba ya fice, ganin ya fita yasa itama da sauri ta bi bayanshi, har tana haɗawa da gudu-gudu, sai da ta cin masa kafin ta dai-daita tafiyarta, haka suka jera suna tafiya, har suka fito compound din Asibitin, inda jeren motocinsu suke, ganin motocin b wanda ta saba gani bane yasa tace "Shehi ina ka samu wannan motocin da yawa kuma ba naka bane.?", izuwa yanzu ya gama gajiya da tulin tambayoyinta da yasa fara sanya kanshi ciwo, cikin yana yin kama kai da kamala , yace "satosu nayi ", ya fada ba tare da ya ko kalli inda take ba.




tsayaww tayi ta riƙe bakinta , ganin ya kusa shiga mota yasa ta kara kwasa da gudu zuwa gurinshi, bai fi sauran taku biyu zuwa ukku ta ƙarasa gareshi ba, zunbulelen hijab dinta ta harɗe mata ƙafarta, tayi gaba zata kifu, cikin jadadda Sunan Allah da ya kama bakinta tace "Innalillahi wa'inna'ilaihi ra'un..!", ta furta da karfi,kafin ta kifu ya riƙe hannunta tare da jawota jikinshi ta kifu akan kirjinshi, al-amarin da yasa tayi gajeruwar Ajiyar zuciya kenan, lamarin kuma da ya haddasawa Yaa Shehi wani yana yin na, a lokacin da sam bai shiryawa lamarin ba, dan lokacin da ta tashi sauka gcikin jikinshi sai ta sauka a bahagon yana yi, gaba daya ta zuba hannayenta kan waist sunshi tare da rungumowa very tight .




zareta yy daga jikinshi ya fara yarfa mata ruwan faɗa cikin sanyayyiyar shi , wadda sam bb hayaniya a cikinta balle kuma fusata, "baƙya kula ko, ? bana hana ki gudu ba ? duk ranar da kika ƙara gudu har kika yi attempting faɗuwa bazan tarekii ba, sai dai ki faɗi ki karye", ya fada yana zareta daga jikinshi.


tura baki tayi tana magana ciki, duk da yaji abun da take cewa amma bai kulata ba, sai da ya shiga mota ya zauna kafin ta shiga itama, bata fasa hayewa kan jikinshi ba, shi kuwa lumshe idonshi yy yana kiran sunan Allah, ya yin da gaba daya sassan jikinshu suke saku, wani baƙon Al-amari na mamaye gaba daya yana yinshi na Asali .




zamar da ita yy daga jikinshi, ya matsa , yana kafeta da idanunshimasu firgitarwa, cuno mishi ƙaramin bakinta tayi, idanunta nayi narai-narai kamar wadda zata yi kuka, akan kafadarshi ta daura kanta.
zame mata kanta ya yi, tare da matsar da ita dan nesa da shi, shiru ta yi dan tasan wannan alama ce da take nuna cewar fushi yake da ita.




har suka ƙarasa gida bai ƙalli inda take ba, dama kuma shi ba mai yawan magana bane, hakan yasa bai ce Uffan ba, hasalima idanunshi na lumshe, bakinshi kuwa bai gushe da Ambaton Allah ba, wanda da dukan alamu jikinshi da haka ya gino har ya saba,shi yasa baya gushewa da hakan.




suna zuwa suka tarar da Yaran Ayyana su ukku daya Namiji sai Twins dinra dukansu mata , Namijin bazai wuce 8 years ba, matan kuwa dukka ba zasi wuce 3 years ba, yana fitowa daga mota suka rugo dukkansu, suna cewa "Oyoyo Uncle M ", suka fada suna fadawa jikinshi, fuskarshu ce ta faɗaɗa, a hankali haɓarshi ta shiga dan motsawa alamar murmushi, sai dai bai bayyana akan fuskarshi ba, shafa kan Yaran ya yi,cike da tsantsar kaunarsu.




A ranshi yake fatan Allah ya kare mishi su, ya Albarkacesu da tarin Albarkarsa, tambayoyi suka shiga jera mishi, kasantuwar sun kwana biyu basu ganshi ba, hakan yasa suke tambayar in da ya je, Haleematou ce ta matsa tare da riƙe hannuwansu tace "Uncle M ya gaji ku barshi ya shiga ciki ya huta" ta fada tana musu murmushi.




Amatul-azez ce tace "Anuty Sadiyya ki goya ni." ta fada tana

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads