Showing 18001 words to 21000 words out of 25770 words
Chapter 7 - ARMAN - MALEEK BY (1) SALMA YAR LELE-1.txt
dira ƙafa irin na Shagwaɓaɓun Yara, Duƙawa tayi ta haye bayanta , girgiza kai Yaa Shehi yy dan yasan bata rabuwa da shiriritar Yaran, yana ji bayan wucewarshi Amatulrahman na cewa ta dauketa, haka ta goya daya ta dauki daya, tana nishi da komai haka take takawa da su zuwa cikin gidan.
bata zauna a Downstairs ba sai tayi sama , palon Yaa Shehi ta tura ta shiga,baya palon hakan yasa ta tabbatar da yana bedroom, ajiye Yaran tayi ta kwanta kan carpet tayi ruf da ciki tana hutawa, idanunta na lumshe, dan mararta take mata ciwo, Amatul-azez ce ta dawo kan bayanta tace "Anuty ki min goyo - goyo." bb yarda ta iya miƙewa tayi da Amatul-azeez din a bayanta ta shiga zagaya palon da ita.
Daga chan ciki yana jin ƙarar hayaniyarsu da dariyarsu, Addu'ar shiriya ya fara karanto musu cikin ranshi, dan suna buƙatar shiriya, bayan gama shirinshi yy duk abun da ya dace, ya gama.
Amma har lokacin da hayaniyarsu cikin palon , Agogon da take manne da Bedside drowar ya kalla, idanunshi ya dan fitar kadan cikin ɗunmin mamaki, ganin lokacin 1 saura.
bedroom slippers dinshi masu taushi da tudu ya zura, tare da miƙewa ya fito palon, zaune ya tarar da Hakimar ta kunna musu MBC 3 suna kallon Cartoon sai kyarkyata dariya suke, suna maganganu a tsakaninsu, tsayawa yy kawai yana kallonsu, girgiza kai yy, tare da matsawa gurin kayan kallon, cable din TV ya zare, wanda hakan yasa da sauri suka kalleshi.
shanyanyun idanunshi ya watsa musu kafin yace "in ce ko gobe bb School.?" ya fada yana tsaresu da idanunshi, Haleematou ce ta sosa kasan gashin kanta da ya zubo baƙi siɗik, girgiza kai yy kafin yace "Allah yasa nazo tashin mutum da Asuba na tarar bai farka ba yaga yarda zan yi da shi", ya fada yana shigewa, da sauri Amatul-azeez suka miƙe.
dan sun san kashedin wa su aka bugawa, duk da Yara ne sosai, Amma an horesu da ibada, tare da karatu sosai, dan Sallah Asuba baya bari ta wucesu.
kullum da Asuba sai ya tashe su,bayan gama Sallah su daura da karatun Al-qur'ani da sauran litattafan Addini, sai da safe sukawa Haleematou kafin su wucewarsu part dinsu.
ta dan jima a gurin tana tunanin faɗan da Yaa Shehi zai mata, dan tasan tilas ne fadan nan sai ya mata shi, gashi ita a rayuwarta bb wanda take tsoro da fargaba irin ɓacin ranshi da faɗanshi,rashin samun madafarta yasa ta sauke nannauyan numfashi dan ta kasa samun wata gamsashiyar hujja, jiki a Saɓule ta nufi bedroom dinshi .
ko da ta shiga kwance ta tarar da shi kan bed dinshi kamar mai barci, a Zahirin gaskiya kuwa idanunshi biyu, itama kuma tun shigowarta ta ga alamun hakan, to amma bb yarda ta iya, Wata Wardrober ta bude, towels ne kala-kala suka bayyana, fari, pink, baƙi, blue, green , kala kala, pink din da yake sama ta zame, tare da daukar ƙarami ta nufi bathroom, Ruwan wanka mai zafi ta tarar a haɗe da turaren wanka mai kamshi sosai, ga flowers a ciki, murmushi tayi dan tasan wannan aikin Yaa Shehi ne, madamar yana gari to ruwan wankanta a haɗe take zuwa ta sameshishigewa ciki tayi tana lumshe idanunta, ta jima sosai kafin ta fito, towel ta daura a jikinta kafin ta daura wani akanta.
a hankali ta leƙo ta yar kafar key din ƙofar , numfashi ta sauke kafin ta fito, tana sanɗa ta ƙarasa gaban mirror, lotion din ta mai kamshi ta bude tare da fara murtsukawa jikinta bayan ta gama shafawa, ta shafa humra, turare ta mai matuƙar kamshi da daukar hankali, ga sanyin kamshi dauka ta fara fesawa, har sai da ta ji yana hawar mata kanta, kafin ta ajiye.
A hankali ta fara takawa zuwa gurinshi, har ta ƙarasa gurin bed din, tana tafiya a hankali ba tare da ta bari wani sautin taku ya fita ba, a hankali ta ƙara kunneta gurin hancinshi, domin tabbatar da cewar barcin yake, kafin ta ankare sai ta ji tayi, ya sakar mata lamuntaccen cizo a kunnen wanda yasa tayi zillo .
fisgota tayi ta faɗo jikinshi, bargo ya bude tare da sanyata ciki, ya haɗa hannayenshi ya rumtse , kallonshi tayi tana cuno baki......
07033371851
DAGA TASKAR ƳAR LELE🧚♂️🧚♂️🧚♂️
[2/22, 5:33 PM] ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚♀️🧚♀️: 🌼🌼ARMAN MALEEK🌼🌼
*DAGA ALƘALAMIN*
SALMAJI ƳAR LELEN ROYAL STAR CE 🧚♂️🧚♂️🧚♂️
SADAUKARWA GA AMINIYATA MASOYIYATA, SADIYYA ABBAKAT MARU (ƳAR GATAN ROYAL STAR CE🌹🌹)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*P.9*
miƙewa tayi tare da fara yunƙurin guduwa, Kanshi ya fara jujjuyawa yana mai miƙa hannunsa ya kashe wutan ɗakin.
A take duhun daren da ya tsala ya mamaye ɗakin gaba ɗaya.
Cike da tsoro ta fara kiciniyar sauƙowa daga kan gadon.
Tana sauƙowo, shi kuwa yana isa gab da ita, haka yasa bayanta ya manna da ƙirjinsa, da sauri yasa hannunsa duka biyu ya ruggume da ƙarfi jin yadda take mutsu-mutsun kwace kanta ne, yasa cikin cool voice dinshi yace "Sadiyyerh!", ya furta cikin sanyayyiyar murya mai nuna zallar fushi, wanda hakan ya tilasta mata zama kan kafarshu cike da fargaba.
sakinta yy ya koma kan bed din ya kwanta, da kanta ta gangara gareshi, tare da shigewa cikin jikinshi ,a hankali tace "Afwan Yaa Zauj.!", ta furta a hankali, banza yy da ita, tasan halinshi, dama ba lallai he ya mata mgn ba , amma ita da wannan shirun nashi gwara ma in dukanta zai yi ya duketa, dan ta tsani shirunshi, hannunta ta sanya cikin tattausan gemunshi ta dan shafa, tare da sanya yatsunta biyu tana dan jaaa a hankali, cikin sigar shagwaɓa tace "ina fa Zauj bana son shirunka , na gwamma ce in ma duka na ne kayi . da kayi shiru", ta fada tana cuno baki gaba.
banza ya kuma yi da ita, dan bai ma san ta in da zai fara ba, ace matar Malam gudu, Shehi, Alaramma, Sheikh amma tana abubuwan da basu dace ba, "don Allah..! " ta fada cikin marairaicewa.
Ajiyar zuciya ya jaa tare da cewa "Uhmmm..!", "Uhuum uhummmm", ta fada tana tirza kafafu a jikinshi, zameta yy daga jikinshi ya juya mata baya, riƙe bakinta tayi kafin tace "Laaaa'ilah Abun ya ƙaura har haka, innalillahi don Allah Yaa Shehi ko faɗa kamin in ta kama da duka, Allah kuwa bazan iya fuskantar fushin nan naka ba, domin ban san mai yake nufi ba, fushinka a gareni babban bala'i ne, don Allah ka sauko " ta fada tana haɗa hannayenta tare da komawa dayan side din da ya mayar da fuskarshi.
Numfashi ya ja kafin cikin harshen Fulatanci yaren da yasan zata fi fuskanta fiye da ko wame Yare a duniya, Yaren Uwa da Uba, yaren duk Ahlinta ya fara cewa " D'un wod'a gorko me ma debbo mo tegal nasti shaka ma66e e dow andal, bo d'un gotun e memuki don nanki beldun e bo memuki nontan.
Sai dai to wodi larura nyawu, a d'on gorko wa wai mema debbo to wodi koltan a shaka, ko b'awo waduki god'd'un iri ba majun.
Ko e d'un warti dole sai d'un wad'ama, ko ittiku d'er diyam, da dun watta gam non d'un mema 6andu ko d'un nyid'u ko dun nyid'a.
Ko yidaki tinaki, to wala wakkati te fuki koltal koo d'un hendirta shaka
bo to memuki kin warti na der shiri ko andal, ko majjuki heftiki dina, to wala god'd'un e dow do'o.....
Gam non, har joni memuki bandu na dow jawu dun wod'a, d'un dole bo d'un tubana dun, sannan dun hotana jomirawo tagud'o tagu .
(Haramun ne taɓa jikin juna a tsakanin mace da namijin da ba Muharraman juna ba bisa sani, kuma duk ɗaya ne taɓawar da nufin jin daɗi ne ko kuwa ba da wannan ƙudurin ne ba. Amman a cikin yanayin larura kamar Magani da Jiyya babu makawa sai ya zamo wannan taɓawar da tufafi a Tsakani, ko kuma bayan sanya safar hannu ta roba da ire-irenta, in banda a yanayin da yake keɓantacce idan ya kasance maganin ko jiyyar ko kuɓutar da wanda ya dulmiya a cikin ruwa ba zai taɓa yiwuwa baya tabbata ba sai an taba jikin kai tsaye, ko kuma ta lalurar gaggawa zuwa maganin ko kuɓutarwar ta fuskar gaggawa da rashin lokacin da za a sami safar hannun ta robar da ire-irenta nan kusa".
Hakanan idan ya kasance taɓawar ba cikin shiri ne ba kuma ba cikin sani ba, ko kuma ya kasance bisa jahiltar hukuncin shari'a ne to babu komai a cikin hakan. Duk da haka dai ita taɓawar juna bisa sani ba bisa lalura ba Haramun ce, kuma wajibe ne yin istigfari daga aikatawa da yin Tuba zuwa ga Allah Maɗaukakin Sarki.
cikin sanyin harshe ya kai karshen mgnr tashi, numfashi ya jaa dan ya manta rabon da yy mgn mai tsawo haka, ita kuwa shiru tayi tana saurararshi ,chan tace "Astagfiroullah wa atubu ilai..! ³ Astagfiroullah.!³", ta furta a hankali tana ƙara maƙaleshi, tare da sauke ajiyar zuciya mai sanyi , tana jin natsuwa na saukar mata cikin ruhi da gangar jikinta, tana Alfahari da samunshi a cikin rayuwarta dan a duk lokacin da ratuwarta zata shiga tangal² shi yake tarota.ya mayar da ita kan hanya mai-daiciya.
"Jazaqallahu bil khair Yaa Zaujilkhair", ta fada tana hug nashi very tight har sai da ya dan yi nishi kafin ta sassauta riƙon da ta mishi, a hankali ya fara biya mata karatun Al-qur'ani mai girma cikim zazzaka sanyayyiya lallausar muryarshi, haka ya ringa mata karatun a kunnenta, har sai da ya ga barci ya dauketa , dan yasan a irin wannan lokacin har idan ba haka ya mata ba, to haka zata yi ta surutu har lokaci yazo ya ƙure bata yi barci ba.
sai da ya tabbatar da yin nisan barcinta kafin ya zameta a jikinshi a hankali, sai da ya jaa mata blanket tare da sanya mata pillow a ganta ya runguma mata,kafin ta miƙe ya nufi bathroom,wanka ya yo kafin ya fito, da Jallabiyarshi Ash colour wadda tayi Asalin fito da kalar fatar jikinshi da take ta walƙiya , ya mannu a jikinshi ta lafe, sai hularshi wadda ta rufe mishi gaba daya kanshi, wanda hakan yy sanadiyar zubowar sumar kanshi da take ɗigar da ruwa, "Fa Tabaraqallahu Ahsanul khaliqin ", bb abun da za'ace da ya wuce wannan .
duk in da ake neman cikakken namiji mai haiba da kamala, kwarjini da kasaita , mulki da dukiya, to duk ya wuce yanan, ilimi Allah ya bashi both Arabi da Boko, duƙiya yana da ita wadda har bai san iyakarta ba, ƙarewae mulki shine kanshi Sarkin gobe wanda mulkin Yau din ma yake karkashin ikonshi, shi dai bb abun da zai ce da Allah sai godiya, dan irinsu ne ake cewa 1 in world ma town ba.
Lungun da kayan Ibadarshi suke ya nufa, yana zuwa ya dai-daita tsayuwarshi kan pray mat din gurin,tare da Kabbara Sallah, yy nafilfili kamar yarda ya saba, kafin ya fara karatun Al-qur'ani da Hailala tare da salati, a takaice dai haka ya gama raya wannan daren gangar jikinshi da ruhinshi basu samu wani hutu ba, sai bautar Allah da suka nitso a gurin yi,sai ƙarfe 4 saura kafin ya tashi daga gurin da yake, gurin da ake ijiye kayanshi ya nufa, bai wani jima ba ya fito sanye da Jallabiya sai kuma Babbar Alƙyabbarshi haƙa mai golden din zane , irin wadda yake yawan sawa, kafarshi sanye da takalmi Gucci baƙi da yy wa ƙafarshi gwanin kyau, kanshi na nannaɗe da hirami fari, sai siririn glasses din da ya sanyawa kyawawan idanunshi, wanda ya sanya ne sa boda ya tashu baya jin dadin idonshinshi sosai, yana jin kamar zai mishi kyau, amma ba ƙaramin kyau yy mishi ba dan sai ka rantse irin samarin nan ne yan 20 something, Al halin kuwa ya bawa 30 ma baya dan ya fara hararar 40, turarenshu na Huge Boss da ya zauna a jikinshi ya dauka tare da ƙara faffaseww yarda ba zai yi yawa ba, shi bai yi yawa ba shi bai yi kaɗan ba dai-dai misali, ya sanya, sai da ya gama shiryawa kafin ya kalli Haleematou da ta ƙara nannaɗewa cikin blanket sakamakon sanyin Subhi da ya fara busowa kamar za'ayi ruwan sama , dan da wasu ƙasashen ne da ake ruwan ƙanƙara to da ba makawa irin sanyin nan da ake zugawa da sun sa ran ko ruwan dusar kankarar za'ayi.
matsawa gefen bed din yy , yasan idanunta biyu dan a irin wannan lokacin yasan rabi da kwatar mutanan gidan nan idanunsu biyu, sai dai Yara haka suma kuma kiran Sallar fari zasu mafarka.
"tashi..!" yana fadar haka ya ficewarshi hankalinshi kwance bakinshi kuma na fitar da sautin Ambaton Allah, lokacin da zai fito gaba daya Driver din gidan da Escort idanunsu biyu, suna ganinshu suka fara gaisheshi, bai iya amsa musu ba sakamakon Abun da yake bakinshi, sai dai jinjina musu kai da yy ,
mota aka bude mishi da sauri, ganin lokaci na kurewa yasa ya shiga, A hankali Driver dinshi ya fara jaan motar , cike da kwarewa da sanin ya kamata.......
tafiyar da suka yi ba zata wuce ta 5 minutes ba suka ƙaraso Harami, Kofar shiga ta gaba nan motar Shehi ta tsaya, bude mishi aka yi, a hankali ya fito yana raira karatun Al-qur'ani cikin zuciyarshi, shiga yy cikin masallacin , lokacin da zai shiga lokacin Sallah ya cika, bayan saqala Microphone din a jikin rigarshi ya fara ƙwala kiran Sallah, wanda yasa Haleematou tashi zumbur dan, bayan fitarshi wani barci mai masifar dadi ta fara jin ya dauketa, Umma Jakadiya ma da ba barci take ba ta miƙe ta zauna, haka Ayyana da dukan sauran yan cikin gidan, ba cikin gidan kawai ba duka yan cikin garin in da sautin muryarshi zata iya ratsawa,cikin gaggawa maza har ma da wasu matan ƙwala kiran Sallah, wanda yasa Haleematou tashi zumbur dan, bayan fitarshi wani barci mai masifar dadi ta fara jin ya dauketa, Umma Jakadiya ma da ba barci take ba ta miƙe ta zauna, haka Ayyana da dukan sauran yan cikin gidan, ba cikin gidan kawai ba duka yan cikin garin in da sautin muryarshi zata iya ratsawa,cikin gaggawa maza har ma da wasu mataan,cikin natsuwa da kamala tare da tattausan harshe da karyashi yake rero karatun Al-qur'ani mai girma cikim bawa ko wane harafi haƙƙinsa.
gaba daya zuciyoyin masu sauraranshi sun tsumu, sun shiga bege da shauƙin karatun nasa, domin muryarshi na da taushi da dadi ga wani sarewa da yake cikinta, ba zaka karaa jin dadin muryar tashi ba sai ma ka ji yana rairo karatun Al-qur'ani kai girma, anan zaka ƙara sanin cewar Ehhh lallai Allah yy baiwa anan.
bayan idar da Sallah ne , ya fara gabatar da Tafsiri da hatahohi , sai misalin 6am, yy Sallama zai miƙe wani daga cikin Ɗakibzn gurin ne yace "Yaaah Shehi muna son ka kara mana gayani game da rabon gado , tare da cij duƙiyar marayu ma baki daya",shiru yy yana jin yarda lokaci daya mutumin ya ɓaro mishi gaggatumin jawabi mai girma, wanda baknshi sai ya kusa ciwo a kanshi, Amma zai taƙaice kusu bayanin kawai.
```NIMA ANAN NIKE CEWA BARI NA TAƘAICE MUKU KAWAI , SAI ZUWA GOBE IN SHA ALLAH```
```GAMAI BUKATAR BOOK DIN NAN ZAI BIYA KUƊI SAI NA SANYASHI CIKIN GROUP DIN DA ZAI RIGA SAMU KULLUM BAYAN GAMA FREE PAGES IN SHA ALLAHU ```
07033371851
```WANDA ZASU SIYA KAWAI DON ALLAH, IN KIN SAN BA ZAKI SIYA BA TO KAR KIYI MGN PLEASE```
DAGA TASKAR ƳAR LELE🧚♂️🧚♂️🧚♂️
[2/22, 5:33 PM] ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚♀️🧚♀️: 🌼🌼ARMAN MALEEK🌼🌼
*DAGA ALƘALAMIN*
SALMAJI ƳAR LELEN ROYAL STAR CE 🧚♂️🧚♂️🧚♂️
SADAUKARWA GA AMINIYATA MASOYIYATA, SADIYYA ABBAKAT MARU (ƳAR GATAN ROYAL STAR CE🌹🌹)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
Second to the Last Free page
*P.10*
Gyara zaman Alƙyabbar jikinshi yy, tare da fesar da numfashu cikin lankwasa harshe , ya fara cewa "Abinda muke son fitarwa cikin karatunmu na yau game da al'amarin rabon gado