Header Ads
Showing 21001 words to 24000 words out of 25770 words

Chapter 8 - ARMAN - MALEEK BY (1) SALMA YAR LELE-1.txt

Ads the beginning of article before Image

20 Jun 2024

331

Ads at the middle of Article

a muslunci shine mu qara nunawa mutane masu hada Uwa da 'yan'uwa cikin gado cewa babban kuskure ne, domin matuqar akwai Uwa ko 'ya, to, 'yan'uwa ba su da kason komai cikin abinda dan'uwansu ya bari, sai dai suna yiwa Uwa babbar illa wacce ke hana mata cin kaso daya bisa uku (1/3) na danta, ta koma cin kaso daya bisa shida (1/6) na daga abinda dan nata ko 'yarta ta bari.


Bari dai mu kawo aqalla misalai uku cikin mas'alar mutuwar Ɗa ya bar magada tare da abinda za su gadan, domin idan ya zama babu abinda ya bari to, babu abinda zasu gada kenan. Abinda aka bari na daga cikin sharadin gado.








تفسير القمي‏ يُوصِيكُمُ اللَّهُ فِي أَوْلادِكُمْ لِلذَّكَرِ مِثْلُ حَظِّ الْأُنْثَيَيْنِ‏ قَالَ إِذَا مَاتَ الرَّجُلُ وَ تَرَكَ بَنِينَ وَ بَنَاتٍ- فَلِلذَّكَرِ مِثْلُ حَظِّ الْأُنْثَيَيْنِ‏- فَإِنْ كُنَّ نِساءً فَوْقَ اثْنَتَيْنِ فَلَهُنَّ ثُلُثا ما تَرَكَ‏ يَعْنِي إِذَا مَاتَ الرَّجُلُ وَ تَرَكَ أَبَوَيْنِ وَ ابْنَتَيْنِ فَلِلْأَبَوَيْنِ السُّدُسَانِ وَ لِلِابْنَتَيْنِ الثُّلُثَانِ وَ إِنْ كَانَتِ الِابْنَةُ وَاحِدَةً فَلَهَا النِّصْفُ وَ لِأَبَوَيْهِ لِكُلِ‏ وَاحِدٍ مِنْهُمَا السُّدُسُ وَ بَقِيَ سَهْمٌ يُقْسَمُ عَلَى خَمْسَةِ أَسْهُمٍ فَمَا أَصَابَ ثَلَاثَةَ أَسْهُمٍ فَلِلِابْنَةِ وَ مَا أَصَابَ اثْنَتَيْنِ فَلِلْأَبَوَيْنِ فَإِنْ كَانَ لِلْمَيِّتِ إِخْوَةٌ وَ أَخَوَاتٌ مِنْ قِبَلِ الْأَبِ وَ الْأُمِّ أَوْ مِنْ قِبَلِ الْأَبِ وَحْدَهُ فَلِأُمِّهِ السُّدُسُ وَ لِلْأَبِ خَمْسَةُ أَسْدَاسٍ فَإِنَّ الْإِخْوَةَ وَ الْأَخَوَاتِ مِنْ قِبَلِ الْأَبِ هُمْ فِي عِيَالِ الْأَبِ وَ تَلْزَمُهُ مَئُونَتُهُمْ فَهُمْ يَحْجُبُونَ الْأُمَّ عَنِ الثُّلُثِ وَ لَا يَرِثُونَ‏.


Ya zo cikin Tafsir na Qummy (R. A) game da inda Allah (T) ke cewa :


" ALLAH NA YI MUKU WASIYYAH CIKIN 'YA'YANKU, NAMIJI NA DA KASO BIYU NA 'YA MACE. " yace :


" Idan mutum ya rasu yabar 'ya'ya maza da 'ya'ya mata, to, namiji na da kaso biyu na 'ya mace. " IDAN KUMA 'YA'YA MATAN SUN FI BIYU, TO, SUNA DA BIYU BISA UKU (2/3) NA DAGA ABINDA AKA BARI. " Abin nufi shine idan ya rasu ya bar mahaifa biyu (Uwa da Uba) da 'ya'ya mata biyu, to, iyayen na da biyu bisa shida (wato kowanne daga cikinsu na da daya bisa shida kenan), su kuma 'ya'ya matan na da biyu bisa uku (2/3). Idan kuma ya kasance 'ya daya (1) to, tana da rabi 1/2, kowanne daga cikin mahaifan na da daya bisa shida (1/6), abinda ya rage (bayan kason) sai a kasa shi gida biyar, abinda aka samo kaso uku na 'ya ne, abinda aka samu na kaso biyun na iyaye ne.


Idan ya zama ga mamaci yana da 'yan'uwa maza da 'yan'uwa mata ta bangaren Uwa da Uba ko kuma ta bangaren Uba kadai, to, Uwa na da daya bisa shida (1/6), Uba kuma na da biyar bisa shida (5/6). Domin su 'yan'uwa maza da mata ta fuskar Uba suna cikin iyalan Uba, dawainiyarsu ta hau kansa. Su suna tsare Uwa daga (samun) daya bisa uku (1/3), amma ba za suyi gado ba. "


تفسير عليّ بن إبراهيم ج 1 ص 132- 133.


Ga misalan nan biye kamar haka :






(1)- Mutum ne ya rasu ya bar Uwa da Uba da kuma 'ya'ya mata 2 tare da dukiya #1,200,000.


YADDA KASON ZAI KASANCE


Uwa Uba 'Ya'ya
1 1 2
-------- ------ ---------
6 6 3
1 + 1 + 4 = 6
----------------------------
6


KASON UWA


1 #1,200,000
----- * -------------=#200,000
6 1




KASON UBA


1 #1,200,000
---- * -------------=#200,000
6 1


KASON 'YA'YA MATA


4 #1200,000
----- * -------------=#800,000
6 1


Idan muka hada jimlar za muga #1,200,000 ta fito, shi wannan kaso na 'ya'ya sai a kasa musu daidai-wa-daida, wato kowacce za ta sami #400,000 kenan.


(2)- Mutum ne ya rasu ya bar Uwa da Uba da kuma 'ya guda daya (1) tare da dukiya #2,000,000.


YADDA KASON ZAI KASANCE


Uwa Uba 'Ya
1 1 1
------ ------- -------
6 6 2
1 + 1 + 3=5
---------------------------
6


KASON UWA


1 #2,000,000
---- * --------------=#333,333
6 1




KASON UBA


1 #2,000,000
---- * ---------------=#333,333
6 1


KASON 'YA


3 #2,000,000
---- * ------------=#1,000,000
6 1


Idan muka hada jimlar abinda aka raba za muga an raba #1,666,666, abinda ya saura a qasa bayan kaso shine #333,334.


To, wannan sauran shine aka ce a raba shi kaso biyar, abinda aka samu na kaso uku sai a bawa 'yar, sauran kaso biyun kuma sai a bawa Iyayen, wato kowanne daga cikin mahaifa zai sami qarin #66,666 kenan, sai ya zama kowa ya tashi da #399,999 kenan, ita 'ya kuma ta sami qarin #200,000, sai ya zama ta tashi da #1,200,000.


Idan muka tara jimlar zai zama:


#1,200,000
+# 399,999
# 399,999
---------------------
#1,999,998


Abinda ya rage shine #2, wacce ba za ta rabu ba.


Saboda haka maimakon ayi wahala biyu bayan anyi kaso na farko azo ana qara kasa sauran abinda yayi saura sai a kasa shi kawai kashi kashi biyar, a bawa 'ya kaso uku, iyayen kuma kowa a bashi shi kaso daya daga cikin biyar din.


Ga shi kamar haka :


KASON UWA


1 #2,000,000
---- * --------------=#400,000
5 1




KASON UBA


1 #2,000,000
----- * --------------=#400,000
5 1




KASON 'YA


3 #2,000,000
---- * -------------=#1,200,000
5 1


Idan muka tara wadannan kaso za mu sami jimla kamar haka :


#1,200,000
# 400,000
# 400,000
--------------------
#2,000,000
--------------------
--------------------


(3)- Mutum ne ya rasu ya bar Uwa, Uba da kuma 'yan'uwa maza da mata tare da dukiya #900,000.


YADDA KASON NASU ZAI KASANCE


Uwa Uba 'Yan'uwa
1 5 ---------
----- ------
6 6
1 + 5=6
-------------------
6


KASON UWA


1 #900,000
---- * -----------=#150,000
6 1




KASON UBA


5 #900,000
----- * -------------=#750 000
6 1


'YAN'UWA


Su 'yan'uwa ba su da komai duk da cewa samuwarsu ya yiwa Uwa illa, domin illar kawai suka iya amma ba su da wani abu cikin kaso, domin matuqar akwai Uwa ko Uba ko kuma daya daga cikin 'ya'ya ba za suyi gado ba.


Idan muka tara jimlar kason Uwa da Uba za mu sami jimla kamar haka :


#150,000
+#750,000
-----------------
#900,000
-----------------




Shi kenan kaso ya fita", ya fada yana sauke nannauyar ajiyar zuciya, wanda yasa gaba dayansu suka ƙara natsuwa, cikin zallar gajiya, idanunshi akan Agogon da take daure A tsintsiyar hannunshi, tace "Idan Allah ya kai mu gobe zamu daura akan Cin Dukiyar Marayu", ya fada sautinshu chan ciki, godiya suka mishi tare da ficewarsu , sai da aka samu saukin hayaniya kafin ya bude idanunshi da ya rufe, a hankali ya ƙara tattara Alƙyabbar jikinshi ya miƙe,cikin gajiyawa yake taka ƙafarshi har ya fito inda motocinshi suke, har zai shiga ya dan tsaya, yana kallon gefe in da Yaga rabi da kwatar Limaman Massalacin sun tsaya.




jim yy kafin ya nufi in da suke, ganin cikin gayyar har da su Sarki, yana zuwa ya mimmiƙa musu hannu suka yi musabaha, "Yawwa Shehi game da batun ganih Wata muna sa ran Yau In sha Allahu a ganshi, dan haka za'a fito dubanshi da misalin karfe 3pm "', jinjina kai Yaa Shehi yy kafin ya musu sai An jima ya wuce, halinshi wanda da yawansu suka tsana, wanda basu san nature dinshi ne haka ba, bashu da hayaniya baya sonta kuma, Amma su kallon mai girman kai suke mishi.




A hankali ya shiga takawa daga parking Space zuwa cikin gidan, yana tafiya yana sauke sanyayyayen numfashi, idanunshi masu dauke da gajiya yake lumshewa a hankali , yana budewa, cikin kamilalliyar muryarsa yy sallama cikin palon gidan, Hayaniyyar Surutunsu Amatul-azeez da Amaturrahman da Haleematou ya jiyo cikin kitchen, sai kaya kayya suke, Umma Jakadiya na ta faman magana, Amma sun ƙi suyi shiru, daya daga cikin kujerun palon ya zauna, tare da ɗago Tsintsiyar hannunshi, 7:30am ya gani, lafiyayyen numfashu mai cike da zallar gajiya ya sauke.




A hankali cikin natsuwa , ya furta "Amah.! Amah!!", ya fada yana lumshe ido, a hankali hayaniyarsu ta fars yin ƙasa, kafin daga bisani Haleematou ta fito , tana sanye da riga da wando da suka ɗameta, rigae iya cibi fara sai wandon bakita yane kanta da bakin siririn mayafi, idanunshi da ya lumshe ya bude, gently cikin natsuwarshu da kamala ya miƙe yy sama, da sassarfa ta bi bayanshi da tray din coffeen da cups a sama.




ko da ta shiga nan ma a zaune ta sameshi kan kujera, bakinshi na Ambaton sunan Allah, da sauri ta ƙarasa tare da jaan center table gabanshi ta ajiye tray din , tsugunnawa tayi gabanshi tace "Sabahul khhair Yaaa Zauj!, ta fada idanunta na kan haɗa mishi coffeen da take cike da kwarewa, shi kuwa fuskarta ya tsurawa ido, ƙasa ya ringa yi da idanunshi har ya sauka akan kirjinta da suka cika masha Allah, lumshe idanunshi yy, yana jin wani chanji na daban wanda a iya tsawon rayuwarshi ya manta rabon da ya ji irin wannan chanji a jikinshi, wanda da har yake tunanin koma bashi da lafiya, "Zauj.!" , ta dawo dashi daga tunanin da yake, miƙa mishi cup din tayi, A hankali ya karɓa, hakan yasa ta miƙe, hips dinta da suke kamar zasu faso wandon jikinta su fito ya tsuraww ido, yana mamakin girman da Sadiyyerh tayi lokaci daya, ta cika ta ko ina, iskar da ya shaƙa ya fesar cikin wani yana yi, kallonta yy ganin tana shirin juyawa, "Yaa Subhanallah" ya furta lokacin da yy Arba da Mazaunanta da suke so masha Allah kawai, tuni zuciyarshi ta Ayyana mishi wani saƙo.






har ta juya yace "Sadiyyerh!." a hankali ta juyo tace "Zauj..!", har cikin ranshi yake jin sunan in ta faɗa dan tayi mugun iya sarrafa harshenta ta lankwasashi ta yarda in ta faɗi magana zata jaa hankali, "Zo!" ya furta ba tare da ya kalli fuskarta ba, a hankali ta tako zuww gareshu, jikinshi ta fara ƙoƙarin shigewa , ganin hakan yasa ya bubbuga gefenshi da hannunshi, gane abun da yake nufi yasa ta zauna a gefenshi, tare da daura kanta a kafaɗarsa, hannunta cikin gemunshi tace "Zauj Azumi gobe ko ?", ba tare da ya kallets ba yace "In sha Allah !", idanunta akan yatsun hannunshi da suke zara-zara farare tass suna dauke da kyawawan kumba, ga wani siririn duhu da ya zagayesu wanda ya ƙara ƙawata hannun, kumbarshu fatt , sai sheki take.




hannunshi yasa ya shafi wuyanta har zuwa gurin kirjinta, zabura tayi tare da kankame hannun, dan danan jikinta ya dauki rawa, kamar wadda aka haɗawa Electric current , idannunshi akan yatsunta, yace "me.?", cikin fisgo maganar daga ƙasan maƙoshi ta ce "Allah hannunka Current", kallonta ya danyi , ido cikin ido suka kalli juna, da sauri ta dauke idanubta tare da yin ƙasa da su, dan ba zata iya jurar kallon cikin idanunshi ba, shi kuwa abun da ya gani cikin idanunta ya sanyashi sauke ajiyar zuciya mai karfi , yana da ɗumbin ilimi sosai, ciki kuwa har da Ilimin nazartar halayen Dan Adam da ɗabi'unsu har ma da wasu sassan nasu, shi yasa cikin abin da ba zai wuce second biyu zuwa ukku ba ya gama fuskantar yana yinta, har ma da zubinta.




kafadarta ya rungume tare da lumshe idonshi, chan ciki tace "Zauj Coffee ", ta furta cikin sanyi da kasalar da suka risketa cikin lokaci ƙanƙani, matsawa tayi daga jikinshi, ta miƙa mishi tea din, a gurin karɓa hannunsu ya goge juna, da sauri ta saki, cikin zafin nama ya damki cup din, idanunta da suka fara chanja kala cikimsu yy jaa-jaa ga hawaye kwance ciki ya kalla, da sauri ta dauke idanunta , dan yau din in ya kalli cikin idanunta wani abu take ji cikin jikinta.




gefenshi ta koma ta kankame jikinta kamar mai tsoron a taɓata, wannan sauyin nata a yau ya matuƙar bashi mamaki, abun da ya gani cikin idanunta ya matuƙar gigitashi, bai taɓa tunanin har haka ba, bata taɓa abu makamancin haka ba. duk ya yarda take duduma akan jikinshi amma bata taba haka ba, ko yanzu girma ya fara kamata, da buƙatar mijinta?.
shin akanshi kawai abun yake faruwa ko kuwa hae ma akan kowa, ya zama dole kuwa ya mata hijabi da sauran maza , kuma dole ya tabbatar da ita a matsayin katangarsa,wadda zai ringa raɓa a duk sanda yake da bukatar hakan, a hankali ya fara shan coffeen yana kallonta har ya ƙarasa shanyewa tas, ƙafarta da gashi suka mimmiƙe ya tsurawa ido yana kallon yarda matsirar gashin tayi burɗum-burɗum.




Alƙyabbar jikinshi ya cire tare da yafa mata a jikinta dan yama fuskanci sanyi take ji, shigewa bedroom dinshi yy domin ya dan kwanta ya huta, yana shiga ya wuce bathroom sai da yy wanka kafin ya shirya ya fito, cikin Jallabiyarshi, bed ya nufa direct yana zuwa ya haye tare da jaaan blanket ya rufe jikinshi, idanunshu a lumshe har ya gama Addu'a kafin ya fara kiran sunnan Allah, dan-dan barci ya daukesa, barci mai dadi.....




iya kuwa cikin wasu yan mintuna gaba daya jikinta ya gauraye da zafin zazzaɓi zafi sosai , jikinta na ta rawa, tuni ta ƙara ƙudundunewa cikin Alƙyabbar da ya bata, sai guraren 12 pm kafin zazzaɓin ta zamu ya dan barta har barci ya dan dauketa, amma duk da haka da zafin zazzaɓin a jikinta.






12:30pm ƙamshin turaren Huge Boss ya karaɗe gaba daya palon har ma da kewayen palon, yarda kamshi yake ƙara shiga hancinka ne kawai zai ƙara jadadda maka cewar mamalakinshi yana kusa ko kuma yana doso gurin, takun takalminshi yasa na dagon da kai na, kamar kullum yana nzn dai cikin shigarshi ta kamala da ya saba yi,idanunshi a kanta har ya ƙaraso cikin palon har gurin da take, yana mai mamakin yarda aka yi har lokacin bata tashi daga in da take ba, ko wuyanta ba zai mata ciwo bane ?, ya tambayi kanshi , a hankali ya yaye kanta da yake cikin Alƙyabbar, gashun kanta ya fara tozali da shi wanda ya zubo kan fuskarta, wanda da alama wahala ce ta mayar da shi kan fuskarta, hannunshi mai ɗumi yasa ya fara tattare mata gashin kan nata, tare da gyara mata shi yy baya.




hannunshi ya daura kan wuyanta, numfashi ta jaaa , jin jikinta da zafin zazzaɓi yasa, ya ƙyaleta tayi barcin may be zai ƙarasa sauka duka in

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads