Showing 1 words to 3000 words out of 13347 words
Chapter 1 - INUWATA DA TA GABATA Book Complete by Mrs Sadauki.txt
[11/06 à 20:13] MRS SADAUKI 👑: 🦔🦔🦔
*INUWATA DA TA GABATA*🕸️
🦔🦔🦔
```(the shadow of my past/l'ombre de mon passé)```
MRS SADAUKI💫✍️
FCWA ☀️
Dedicated to Saadiya Abdulrazak (Mai Zafafa)
_____________________________________________________________________________________________
*Wani sashen ya faru a gaske,wani kuma ƙirƙiraren labari ne,ban yarda a juya shi ta kowacce irin siga ba haka ban lamunce a saka shi a wata kafar ba youtube ko kuma a mayar da shi audio har sai da izinina*
Page 1
“Inyaaa! Inyaaa” kukan jinjiri ya karaɗe ɗakin,na ja wata wahaltaciyar ajiyar zuciya tare da sakin murmushin da ko second biyu ba a yi ba wani mummunan furicin da kunnuwana suka jiye min ya maye gurbinsa da ƙunci.
“Wannan ɗin ma ya koma ! Allah ya karɓi abinsa! Maryam ke kam ƙaddara ta aure ki”
Wacce ta yi furicin goggo Dije ce ƙanwar mahaifiyata,ko minti biyu ba a yi ba ta fito hannunta riƙe da jinjirin jikinsa da kumfan jini ta miƙo min shi ta na cewa “Ungo je ka rufe shi Ja'afar ” hannuna na rawa na karɓe shi,ban damu da farar gizner ce a jikina ba kawai na manna yaron a ƙirjina wanda yayi bala'in kama da ni.
Wasu zafafan hawaye masu ɗumi suka zubo min,babu yadda na iya haka na je na yi masa wanka na kira abokaina da ba su wuce biyar ba aka yi masa sallah aka rufe shi.
Jikina duk babu ƙwari na isa ɗakin matata Maryam,a kwance na tarar da ita ta na kuka.Ta na ganina ta ƙara ƙaimi,kukanta ya fi komai tarwatsa min zuciya don wani irin sihirtacen so da ƙauna nake yi mata jarumi ne ni a ko wane fage amma akanta ina da nakasau.Da sauri na ƙarasa na je na rungumo ta,wani kalar sautin kukan ta sake saki kafin ta soma magana cikin shaƙaƙar murya.
“Ja'afar don mi ni ? Duk abokaina su na da ƴaƴa ,in sun ɗauki ciki normal suke haihuwa amma ni kamar wacce ta yi wa Allah laifi kullum a mace suke zuwa wannan ɗin da ya ɗan koka har na sa rai shi ma ɗin ya bi sauran ƴan uwansa”
“Yi shiru mana Riam,ki yi wa Allah godiya a duk halin da kika tsinci kan ki shi ɗin ya fi mu sanin dai....” ta katse ni da “ na gaji! Ni dai kam na gaji wallahi ba zan sake ɗaukar wani cikin ba ƙarshe a je a binne shi cikin ƙasa ba”
“Ya Salam!” na furta da sauri ina jin kaina kamar zai tsage gida biyu tsabar yadda yake sara min,ina kallon Maryam ta tashi ta fara haɗa kayan ta cikin trolly.
“Wai ina za ki je ne?” na yi mata tambayar ganin ta na shirin jan akwatin kayan nata ta fice.
“Gidanmu zan je Ja'afar! Wallahi a yadda nake jin zuciyata na min ƙuncin nan komai zai iya faruwa in ina ganin ka a gabana”
“Wane irin zance ne kuma wannan Riam? Ni ɗin ne kuma yau a ba ki son gani?” na yi furta ina shirin kamo hannunta amma ta wani ja da baya,ta buɗe baki za ta yi magana kenan na ga ta yi luuu za ta faɗi na yi saurin taro ta sai kawai ta faɗa ƙirjina.Jijigata na soma amma idonta na ga su na birkicewa yayin da kuma halshenta ke zalzalowa.
“Goggo! ” na furta da mugun ƙarfi ina ciciɓo Maryam na fito da ita daga ɗakin,step ɗin ma bibbiyu nake taka shi.Kan kujera na sauke ta,likitocin da na ɗauka domin kula da lafiyata da ta iyalina suka fara bata taimako an ci wuya sosai kafin ta koma normal.
Na yi baya ina dafe goshi kafin na zube gwiwaina ƙasa ,daidai saitin kanta na zauna ina shafar fuskarta wacce ta ƙara yin haske fayau.
“Ta na buƙatar hutu,sannan kamar jininta ya so wuce ƙa'ida ya kamata a bata kulawa ta musamman a guji abin da zai ƙara mata wata damuwar kan wacce take ciki” Dr ta faɗa wacce ita ɗin ƙwararriya ce sosai wacce ta yi fice.
Idona har wani zugi suke min ina kallon Maryam abar ƙaunata wacce nake jin da dai ta suɓuce min gwara ace na rasa komai da na mallaka.
“Goggo a shirya mana tafiya zuwa Dubai”
“An gama” ta faɗa kafin ta soma shiri,kamar abun wasa tuni komai ya tafi cikin tsari .Ni da Maryam ne sai likitarta Dr Hannah wacce ke kula da duk wani motsin ta muddin ya shafi lafiyarta ne,maƙudan kuɗi muraren na zuba don ɗaukar ta aiki.
Kasancewa ta agent jirgi ,ɗan kasuwa fitacce babu ɓata lokaci komai ya kammala muka ɗau hanya.
Har lokacin da muka isa Dubai Maryam na bacci,da kaina na yi mata wanka da ruwan ɗumi na kimtsa ta sannan na saka mata wasu riga da wando masu taushi da sulɓi masu kamar jikin mage.Kan lafiyayen gadon na shimfiɗeta wanda ya sha shimfiɗa ta alfarma,sai yanzu ma na tuna da ban yi wa PA ɗina zancen ya soke duk wani zaman da zan yi da mutane da kuma taron da na tsara zan je.Text na tura masa bayan na yi wanka na shirya iya cikin gajeren wando kawai ko riga ban saka ba,na je na yi tsaye ina kallon beautiful fuskarta.Hawayen tausayinta ne suka zubo min,duk da ni ma ɗin ba baya ba wurin mugun son yara amma Maryam ta fi ni sannan a ƴaƴa ukun da duk ta haifa suka mutu ta fi sa rai a wannan na huɗun sai dai shi ma ashe ba zai tsaya ba.
Duniyar tunani na tsunduma ina mai lumshe idona,‘ Allah ni ɗin bawan ka ne mai yawan bautar ka,na rabu da iyayena lafiya,ina sada zumunci,ina kyautata wa maƙwabta da marayu da maras ƙarfi.Allah ban san abin da yasa kake jarabtata ta wannan fannin ba,sai dai kai masani ne akan komai ba zan tuhumeka ba .Ya Rabb in akwai wani laifi da na yi maka ka yafe min ka bani haihuwa mai albarka,Allah ba don halina ba sai don RahamarKa na da yawa’ duk a zuci nake yin wannan jawabin,wanda ba kowa nake yi wa shi ba sai maƙagina wanda ya hallice ni.Sam kasa samun nutsuwa na yi na miƙe na je na ɗauro alwala na soma jero nafiloli a nan bacci ya ɗauke ni mai ɗauke da mafarkin da ya kamata na tsaya na yi nazari don zai taimaka min wurin warware matsalolin gobena,amma kasancewar kukan Maryam ne ya tashe ni sam ban wani maida hankali akai ba.Na zabura na miƙe na je gare ta ,“Ja'afar ka kai ni gida wurin Mama”
“Ba mu fa Kamaru muna Dubai,ki ƙara haƙuri na san da ciwo rasa abin da ka haifa”
Ta soma waige-waige ta na ƙarewa ɗakin kallo,ban san mi ya ja ra'ayinta ba ta bar rigirmar kawai dai ta yi lamo a ƙirjina.
“A kawo miki Lipton ki sha?” na tambaye ta shiru ba ta amsa ba,na ɗago haɓarta na ce “ki daure ki sha kin ji?” ta lumshe ido kawai hawaye na yi mata shatata,na kai bakina a hankali ina shanye ruwan hawayen kafin na fake da sumbatarta.Ba wai don shauƙi ko sha'awa ba sai don kawai ya na ɗaya daga cikin abin da nake cin nasara wurin rarrashinta.Ban bar abin da nake yi ba sai da na ji yanayin bugun zuciyarta ya fara gudu,ya kuma koma normal.Na gyara pilow na kwantar da ita kafin na fita zuwa kitchen na haɗo mata tea,sai da na yi da gaske sannan ta sha rabi ni kuma na shanye sauran.
“Ina jin kamar pad ɗina ya cika” ta faɗa cikin sanyin murya,ba wai wannan ne karon farko da nake taimaka mata wurin kimtsa wa ba.Sau tari in ta na period ina yi mata wannan gatan don ta na mugun son haka,sannan na yarda kuma ya na ƙara danƙon soyayya.
Na sure ta ina cewa “mu je to na gani in ya ɓace sai na canza miki ” ta ɗan saki fuska kaɗan amma ba ta yi murmushi ba.Bayan mun fito daga toilet ne take cewa “Ja'afar ina jin daɗin yadda sam ba ka tsantsani na”
Na shafi gefen fuskarta na ce “to miye don na yi wa matata hidima ? Ni fa komai naki ina so kuma ban jin ƙyamar ki a kowanne irin hali”
“Na gode! Na ɗan ji sauƙi amma har yanzu ina jin ciwon rasa babyna” sai kuma idonta ya cika da ƙwalla.
Na ce “Haka Allah ya tsara ƙaddararmu ki ƙara haƙuri in da rabo za mu dace”
Ta girgiza ta ce “yaushe kenan? Haihuwa huɗu a jere amma babu ko ɗaya a gabana,yayin da mata dayawa ga su nan da ƴaƴansu...”
Na yi saurin katse ta da cewa “kin manta abin da Allah subhanahu wata'ala yake cewa a cikin Suratul Zhukur ? أَهُمۡ يَقۡسِمُونَ رَحۡمَتَ رَبِّكَۚ نَحۡنُ قَسَمۡنَا بَيۡنَهُم مَّعِيشَتَهُمۡ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۚ وَرَفَعۡنَا بَعۡضَهُمۡ فَوۡقَ بَعۡضٖ دَرَجَٰتٖ لِّيَتَّخِذَ بَعۡضُهُم بَعۡضٗا سُخۡرِيّٗاۗ ```Shin ku kuka bawa kan ku wannan ni'imar da kuke ciki ? Mu su Allah mu muke raba wa kowa kason shi mu tsara wa kowa irin rayuwar da zai yi,sannan ita kanta ni'imar da hawa-hawa ce ta wani ta fi ta wani daraja.....” yadda ta wani faɗo jikina irin da ƙarfin nan yasa na yi shiru .
Cikin kuka take cewa “na ji Baby J na ji na ɗauka,amma ka yi min alƙawari ba za mu bar nan ba sai na samu wani cikin”.........
[13/06 à 05:46] MRS SADAUKI 👑: 🦔🦔🦔
*INUWATA DA TA GABATA*🕸️
🦔🦔🦔
```(the shadow of my past/l'ombre de mon passé)```
MRS SADAUKI💫✍️
FCWA ☀️
Dedicated to Saadiya Abdulrazak (Mai Zafafa)
_____________________________________________________________________________________________
*Akwai sashen da ya faru a gaske,wani kuma ƙirƙiraren labari ne,ban yarda a juya shi ta kowacce irin siga ba haka ban lamunce a saka shi a wata kafar ba youtube ko kuma a mayar da shi audio har sai da izinina*
2
Na jinjina wa Maryam na ce “na yi miki alƙawari my Ryam in sha Allah sai kin samu wani cikin za mu koma Kameru,amma ya zancen zuwan ki aikin hajjin za ki fasa ne?”
“Ina matar Ejan jirgi guda? Kar fa ka manta kamfanin zuwa Makkar naka ne” ta furta a wani yanayin taƙama,zan iya cewa a kaf halayen matata wannan ne na fi tsana ta na da mugun alfahari.
“Za mu duba mu gani dai,kar ku gaji ke da abin ƙauna mai zuwa” na furta ina mai shafar mararta.Ta saki murmushi mai ɗan sauti ta ce “ni kam Shalele ƙarfe nawa yanzu?”
“Kusan ɗaya na dare fa”
“Ina son yin magana da Mama,zan sanar da ita halin da ake ciki kafin labarin ya karaɗe duniya”
“Ok babu matsala bari na haɗa ki da ita ” na faɗa ina mai shirin tashi amma ta riƙe min hannu ta na aiko min wani irin mayen kallo “Ryam zan ɗauko waya ne” sai ta yi saurin sakin hannun nawa ,na je na ɗauko waya na kira mata mahaifiyarta amma ba a ɗaga ba har sau uku.Ta yi wani zuru da ido alamun damuwa kafin ta ce “ka jaraba kiran wayar gida”
Na ce “Ryam irin wayoyin da ake ajiye wa a falo wani sa'in duk kiran da za a yi ana tsare da shi ko kin manta Baban ki shi ne Ministan Kamaru?”
“Don Allah Shalele ka kira ko ba ta nan ba doli mutane sai sun san da labarin nan,dama idon kowa na kanmu”
Babu yadda na iya haka na kira wayar,tsawon lokaci kafin ƙanwarta ta ɗauka na yi saurin miƙa mata.
“Allo Marfuwa ina Mama take?”
“Ta na ɗakinta mana, tun da safe ta ce ba ta jin daɗin jikinta ”
“Ayya! Je ki sanar da ita ina son yin magana da ita”
“Ga ta nan ma ta fito,Mama karɓa Maryam ce”
“Allo ƴata fatan dai ki na lafiya?” cewar Mamar cikin wani irin yanayi.
“Eh lafiya! Mama...”
“Lafiya mine ne?” Mamar ta tambaya,sai Ryam ta kalle ni duk da ba a hand free take ba ina jin duk tattaunawar tasu.
“Mine ne ya faru?” Mama ta sake tambaya .
Ryam ta fashe da kuka ta ce “wannan ɗin ma ya mutu Mama! Yanzu haka muna Dubai ni da Daddyn Abrar”
Salati kawai Mamar ke yi kafin ta yi furicin da ya fizgi ruhina “ Maryam ni fa na fara jin tsoro kar dai ace maganar da mutane ke yi kan mijin ki gaskiya ce”
Ban tsaya ida jin ƙarshen hirar tasu ba na bar wurin na dawo falo na zauna ina nazari.Maimakon na ɗauki mafarkin da na yi kan Mahaifiyata na auna shi da maganar da Mamar Ryam ta yi sai na shashance kamar kullum can ƙasan zuciyata na raya min ‘ita ma hassadar ka take yi kamar sauran mutanen garin shi yasa ta zargi haka’
Tsawon lokaci ina saƙa da warwara kafin in jin an lanƙamo hannuwa ta wuyana an rungume ni,“Akhee!” na ɗan lumshe ido game da sunan da ta kira ni,Ryam na mugun sona ita ma yanayin da take ciki to da irinsa take zaɓar sunan da za ta kira ni da shi.Kamar dai yanzu da ta kira ni da Akhee ta na son yi min nuni ne ita duk rintsi ta na tare da ni don ba a sauya ɗan uwa,in kuma ta kira ni da Shalele to irin ta na cikin farin ciki ne,faɗar sunan Ja'afar kuma in ranta a ɓace yake ne kawai.
Na kamo dogayen yatsunta na riƙe na ce “ƙanwata ya jikin naki?”
“Yunwa nake ji”
Da sauri na miƙe jin dai ta yarda za ta ci abinci, kitchen na shiga na ɗauko mata abin da ba a rasa ba a frigo.
Kan cinyata na ɗora ta na soma bata a baki,bayan ta ƙoshi ita ma ta ciyar da ni.Wannan romantic moments da muka yi mai cike da tattali da kallon bege yasa raina yayi sanyi ,sai da muka yi brush kafin mu hau bed.Tsam a ƙirjina na manna ta a haka muka yi bacci,kiran sallar farko na farka na je na yi wanka haɗi da alwala na bar Ryam ta na sharar bacci ba tare da na san hakan shi ne mafarin muguwar rayuwar da za mu fuskanta a gaba ba.
Maryam na bacci ,ƙofar ɗakin da Ja'afar ne ya rufe ta kafin ya fita amma ƙiiii ta buɗe kanta ƙarar ba ta taka kara ta karya ba amma abun mamaki ita ta tayar da Maryam ɗin.Idonta dishi-dishi take gani saboda nauyin baccin,a sannu a hankali ta ga kamar shigowar wani haske mai silki da iska ya shigo ta ƴar hanyar da ta buɗe.
Numfashinta ya soma canzawa,haka ma yanayin jikinta ya ɗauki wata irin muguwar kasala.Ba ta san mi ya ja ragamar jikinta ba izuwa toilet ta yi wanka abun mamaki jinin haihuwar ya ɗauke cak.Ruwan ɗumi ta tara ta gasa kanta,ta yi wankan tsarki ta zo ta soma yin sallah cike da rabkanuwa saboda wani mugun desir da ke bijiro mata.Ta na gama salamce sallah ko istigfar ba ta yi ba ballantana aje da zancen Azkhar kawai sai ta cire hijab ta je ta wani kwanta kan bed a haka nan .
Bayan mun gama sallah cikin sauri na taso sanin na bar Ryam cikin halin da take da buƙatar kulawa.A kan hanya na soma jan casbi da niyyar in na zo gida duk sauran Azkhar zan yi ,sai dai ina kutso kai na tarar da Ryam cikin halin da duk wani namiji mai lafiya in ya ga matarsa doli ya je gare ta.
Na saki casbin na isa inda take ido rufe, wannan ya na ɗaya daga cikin raunina ban da haƙuri ta fannin kwanciya zan iya cewa ma shi ke daɗa min ƙaunar Ryam a rai don ban taɓa zuwa da buƙatata ba ta hana ni.
Duk da ƙololuwar sha'awar da nake ciki bai hana ni tambayar Ryam ba gudun kar na faɗa hallaka na saɓa wa Ubangijina.
“Ryam jinin ya tsaya ne?”
Ba ta bani amsa ba saboda na lura kamar ta fi ni shiga yanayi,da taimakonta muka samu nutsuwa.
“Yau na ji wani mugun daɗi sosai” ta furta idonta a rufe,cike da mamaki nake ƙara dubanta karon farko kenan da Ryam ta taɓa faɗa min ta ji daɗin kasancewar da muka yi.A kullum ni ne ke faɗa har in tsaya yi mata comments daki-daki,abun mamaki yau ita ce ta ɗauki place ɗina ta soma zuba kamar kanya.Zantukan da take faɗa uwanda sam kunnen da ba na babba ba to ba zai iya ɗaukarsu ba,su suka rinjaye ni suka sa na ƙara janta birnin ma'aurata.
Ta na dariya na sure ta zuwa toilet muka soma wanka,“baby J please mu shiga cikin bahon wanka” ta furta min cikin kunne.Wannan duk ya na cikin abubuwan da nake so nake kuma roƙonta mu yi,sai ga shi yanzu ita ce ke yin duk wannan.Da muka shiga bahon nan Allah ne kawai ya san irin yanayin da muka tsinci kamu,dakyar muka iya bai wa kanmu haƙuri muka fita muka shirya tsab kafin mu je falo mu ci abinci.
Yadda Ryam ke nuna min soyayya da ƙauna da tattali ko farkon auren mu albarka,dama babu abin da namiji ke so irin haka wannan yasa na ƙara sakin jiki ina kwasar romon love.
A satin biyun farko Maryam ta zama ƴar gari,da kanta ta sallami Dr Hannah kan ta koma Kameru duk da ita ɗin ba ta ji daɗi ba amma haka ta tafi.Rayuwa mai cike da jin daɗi da farin ciki muke gudana,a kullum ina haɗa Ryam da Mamarta don kusan ita ce ƙawarta.Farkon wata na biyun mu a Dubai Ryam ta soma laulayi,da zuwanmu asibiti aka tabbatar mana da shigar ciki ne.Ra'ayinta shine mu ɓoye labarin cikin kar kowa ya sani sai bayan ta haihu.
“Ryam ciki bai ɓoyuwa fa ko yaya ne sai ya fito” shine abin da na ce mata.
“Zan zauna a nan na raini cikina hatta Dr Hannah ban so ta sani”
“Babu damuwa yadda kike so haka za a yi,yanzu dai kwanta ki huta zan fita na dawo”
Da sauri ta tambaye ni “ ina za ka je?”
“Na yi baƙo Ba'amurike ne,za mu tattauna kan harkar kasuwanci ” na bata amsa.
“To ”
“Ya na ga yanayin tsoro a tattare da ke?”
Sai da ta ɗan waiga ko ina kafin ta ce “ wallahi Shalele ji nake kamar ana kallonmu,yadda ka san ba iya mu biyu ne a nan ɗin ba”
Na saki murmushi mai ɗan sauti na ce “uwanda za