Showing 9001 words to 12000 words out of 13347 words
Chapter 4 - INUWATA DA TA GABATA Book Complete by Mrs Sadauki.txt
🦔🦔🦔
*INUWATA DA TA GABATA*🕸️
🦔🦔🦔
```(the shadow of my past/l'ombre de mon passé)```
MRS SADAUKI💫✍️
FCWA ☀️
Dedicated to Saadiya Abdulrazak (Mai Zafafa)
_____________________________________________________________________________________________
*Akwai sashen da ya faru a gaske,wani kuma ƙirƙiraren labari ne,ban yarda a juya shi ta kowacce irin siga ba haka ban lamunce a saka shi a wata kafar ba youtube ko kuma a mayar da shi audio har sai da izinina*
6
Idon Abrar a birkice baƙi ƙirin ta yi saukar ungulu a ɗakin Mama wacce ta baje kayan da malamai da bokaye suka haɗa mata.
Sam idonta ba sa ganin Abrar sai hayaƙin turaren wuta wanda har yanzu da ƙamshinsa,cike da mamaki Mama ke kallon hayaƙin wanda duhun ɗakin sam bai ɓoye shi ba.
Motsi ta soma ji kamar ana wasar guje-guje,shuuu! Ta ji an bi ta gabanta da gudu haka ma ta bayanta.Da sauri ta juya kafin kuma ta fara laluban wayarta,hannunta ta tsinta tsamo-tsamo cikin jini jikinta na rawa take kallon yadda jinin ke ɗiga da ƙasa har wani ɗil! Yake yi .
“Mike faruwa da ni ne? Ya ban ganin komai sai hayaƙi da jinin?” ta tambayi kanta ta na mai kai hannunta kusan fuskarta don sake tantance wa sai kuma ta ji ƙuuu! Rudududuuu! An wuce da mugun ƙarfi a can saman rufin ɗaki kamar za a faɗo ciki.
Hankalin Mama bai ida tashi ba sai da ta soma jin ƙurmus! Ƙurmus ! Kamar ana cin ƙulli a ƙarƙashin gadonta.Da gudu ta nufi hanyar da za ta fitar da ita daga ɗakin,ta ci burki ta ja ta tsaya ganin handle ƙofar ya soma rikiɗa ya na fitar da wani kalolin haske ko kafin Mama ta ida tantance mine ne a gabanta ta ji wani irin cizo gefen wuyanta.Ta ƙwala uban ihu kafin ta zube nan ƙasa warwas,Abrar ta haye bindin macijiyar ita kuma ta mayar da ita can ɗaki kusa da Ryam wacce ke ta sharar bacci.
Washegari sai ga Mama da kumburaren wuya kamar wacce ta kwana ta na busa wuta.Har aka yi wa Maryam da ƴarta ruwan ɗumi suka yi wanka Mama ba ta leƙo su ba,Goggo Dije wacce tun asubar farin ta dira gidan ita ce ma ta yi ƙarfin halin tambayar Mamar mafarin ta fito kenan.
“Mine ne ya same ki Mama?” Ryam ta tambaya cike da tsoro.
Dakyar ta iya buɗe baki ta basu labarin irin uƙubar da ta gani daren jiya,nan fa tsoron Ryam ya ƙara hauhawa ita da take cewa sam ba za ta bi Goggo Dije ba har sai in Ja'afar ne ya zo da kansa .
“Ki na nufin fatalwa kika gani Mama?”
“A'a ya za ki ce haka? Ai sam shirme ne babu fatalwa a duniya ƙila ruɗewar da ta yi ne sakamakon cizon yasa idonta ba su gane mata daidai ba.Mu ga wuyan?” cewar Goggo Dije, Mama ta ɗan rage tsayi ta yadda za a ga wurin da kyau.
“Kin ga Maryam zo ki ga yadda sawun haƙora suka fito ras”
“Wannan ai haƙoran mutum ne ba maciji ba Goggo ” Ryam ɗin ta faɗa.
“Ya kamata dai a kai ta asibiti can su za su san abin da ya kamace ta”
“Yanzu nake cewa zan kiran exellency sai na shaida masa” Mama ta faɗa ta na matsar ƙwalla.
“Yanzu dai zan wuce da Maryam ta koma ɗakinta, wannan ba girman mu ba ne ace hakan ta faru” Goggo Dije ta faɗa.
Mama ta haɗe rai sai yanzu ma ne ta tuna sam ba ta ga kayan tsafinta ba duk an kwashe komai,sai dai kafin ta kai ga yin magana Ryam ɗin ta ce “eh Mama gaskiya Goggo Dije ta faɗa ya kamata na koma tun da ga Marfu'a nan sai ta kula da ke”
“To ” Mama ta faɗa.
Goggo Dije ta ɗauki baby Abrar wacce ke sharar bacci suka fice ita da Ryam direba ya kai su gida.
JA'AFAR
Sosai na ji baƙin cikin abin da Ryam da mahaifiyarta suka yi min.Ban taɓa jin takaicin zama da mace ɗaya ba sai yau,da wannan baƙin cikin na kwana kuma na tashi.Da na dawo daga sallar asubah kamar wani marar lafiya haka na zube kan salon ina tunanin mafita,a gaban idona Goggo Dije ta fita ko ba ta faɗa min ba na san biko za ta je kuma har ƙasan zuciyata addu'a nake yi Allah sa Ryam ta haƙura ta dawo.Don ba ƙaramin abin kunya ba ne abokaina su zo ganin baby na ce musu Madam na gidansu.Ganin kewar za ta yi min yawa yasa na ɗauki waya na fara shating,status ɗin Dr Hannah na gani ta ɗora video ta na sanye da farin hijabi a saman kanta kuma ta ɗora jan hirami na maza ta na yin magana cikin harshen larabci kai kace Yarenta ne tun asali.Ban yi wani dogon karatun Addini ba amma na ɗan tsinci wasu kalmomi da na fahimta,wato godiya take yi wa Allah da suka gama Hajji lafiya sannan ta sanar da cewa a yau za su dawo.Tamkar wani gara haka nake ta maido videon baya ina sake kallo,laɓanta irin baƙaƙen nan ne duk da fuskarta na fara .Ta saka hauren maka har guda biyu sosai suka ƙara mata kyau,dakyar na iya barin videon na ci gaba da kallon sauran hotunan da suka yi ita da ma'aikatan gidana.
WhatsApp ɗina ba GB ba ne ballantana na ɗauki video ɗin,sai kuma na ji nauyin in ce mata ta turo min ita.Na shafi gefen wuyana ina murmushi wanda ban san ko na mine ne ba,na shagala sosai wurin kalle status Dr Hannah su Goggo Dije suka shigo.Kukan Abrar ne ya fargar da ni,na ɗago kai na dubi Ryam wacce ta yi tsaye ƙiƙam kamar wata baƙuwa .
“Zauna ki shayar da ita,kin ga tun da na yi mata wanka take baccin nan” cewar Goggo Dije .
Ina kallon Ryam ta zauna a sanyayye kafin ta ɗora wa Abrar maman amma ta ƙi karɓa sai kukan take ci gaba da yi.
Na kawar da kai gefe ganin ta na kallona,karon farko da ban ji wannan shauƙin son nata ba .
“Goggo zo ki ga ta ƙi karɓa wanda nake ɗan matsa mata ma ga shi nan ta na maido shi” Ryam ta faɗa cikin rawar murya.
Duk yadda aka so Abrar ta sha maman ƙiya wa ta yi,a ƙarshe Goggo Dije ta kaɗa madara ta soma bata abin mamaki sai ta yi shiru ta na sha har wani tsutsutsu kake ji ta na kame kan biberon ɗin.
“Daga yau a dinga bata madarar Goggo ” na furta ina mai tashi na shige can ɗaki,jallabiyata na cire na shiga toilet.Na lumshe ido ruwa na dukan fuskata babu abin da nake gani sai murmushin Dr Hannah da kyawawan haƙoranta da suka sha adon hauren Makka .
Ƙiiii! Na ji ƙarar buɗewar ƙofa,ko motsi ban yi ba ballantana na juya har lokacin da ta yi hugging ɗina ta baya ban juyo ba.
“Ka yi haƙuri don Allah Shalele ” ta furta cikin shashekar kuka,sai a lokacin na juyo muna facing juna ni da ita.Ina mugun son Ryam amma abin da suka min ita da mahaifiyarta ina jin kaso biyar ya fita,ban ce mata komai ba sai na soma cire kayan jikinta.A tare muka yi wankan ta bani nutsuwa sosai wacce ta sa zuciyata ta ɗan wanke,da kanta ta shirya ni cikin manyan kaya har da ɗora min hulla.Na sumbaci goshinta kafin na fito falo,Abrar na ɗauka na tsura mata ido ita ma ɗin ni take kallo na saki murmushi na ce “love You babyna ”
Goggo Dije ta ce “Allah sa ta amsa ma,a to yaran yanzu ba ku da ta ido a gabana kake irin wannan zancen”
Na yi murmushi mai sauti na ce “haba dai Goggo in ba kula da Abrar ba na bata dukkan soyayyata wa zan bai wa? Ita kawai gare ni fa” sai kawai na miƙa mata ita.Ina kallon ta taɓe baki kawai amma ba ta ce komai ba,a harabar gidana na fita direba na ganina ya rugo da gudu ya na tambayar inda zan je.
Na ce “no yau da kaina zan yi tuƙi”
“To yalaɓai wacce motar za ka hau?”
“Fara”
“Wace daga ciki?”
“Kunna duk wacce ka ga za ta fi min kyau” ina faɗar haka na wuce cikin lambu,kira na yi aka tabbatar min lokacin da jirgin zai sauka.Na ɗan jima zaune kafin na je na ɗauki motar na wuce filin jirgi,na ɗauki kamar minti talatin sannan jirgin ya sauka sai a lokacin kuma na fara tambayar kaina ‘to wai mi ma na zo yi? Tarben ta? Mi zan ce mata?’ da ire-iren tunanin nan har mutanen ciki suka fara sauka.
“Assalamu aleykum !” Dr Hannah ta faɗa lokacin da ta iso wurina,na amsa mata cikin kula wa kafin na ce “Hajj Mabroor!”
“Na gode sosai”
“Ke ɗaya ce cikinsu?”
“Eh su jirgin su bai taso ba”
“Okay” na furta tare da yin shiru,ita kuma ina lura da ita sai satar kallona take.
“Zan tafi” ta faɗa ta na sunne kai.
“Ki jira mu tafi tare mana” na faɗa ina danna waya.
Ta ce “ina son fara zuwa gida ne kafin na je can”
Na ɗago na tsure ta da ido aka yi sa'a ta ɗago kai idonmu ya shiga cikin na juna,duk sai na ga ta ruɗe.
Na ɗan kawar da kai na ce “can ina?”
“Gidan ka mana Alhaji !”
Na saki murmushi ina mai miƙe wa tsaye,sai da muka je ta nuna ƴan kayan da ta zo da su ma'aikatan wurin suka kai mana su har mota cike da girmamawa.
Na buɗe mata mota ta shiga ta zauna,ni kuma na shiga daga can ciki na yi wasu ƴan dube-dube dangane da alhazzai uwanda suka tafi ta kamfanina.
“Na tsayar da ke ko?” na furta bayan na shiga na zauna, murmushi kawai ta yi.Sai da muka fita sannan na ce “ina za mu je?”
Unguwar da ta faɗa min ta talakawa ce,sosai na yi mamaki jin wai can ne take.Da taimakonta muka shigo layin mai cike da ruwa ko ta ina amma ko kaɗan ban nuna ƙyanƙyami ba,har muka isa ƙofar gidansu.
“Ka na nufin ba za ka shiga ciki ba?” ta tambaye ni a lokacin da na yi mata fatan a huta lafiya.
“Na ce zan zo karɓar tsaraba ta ai in an jima”
Ta washe baki ta ce “to sai ka zo,ina fa jiran ka” na jinjina kai.Sai da ta fitar da kayanta kafin na ja motata na wuce ina ta mamakin kaina shin mike faruwa da ni???????
My book is only 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA Ecobank,DM +22795045822
[22/06 à 10:36] MRS SADAUKI 👑: 🦔🦔🦔
*INUWATA DA TA GABATA*🕸️
🦔🦔🦔
```(the shadow of my past/l'ombre de mon passé)```
MRS SADAUKI💫✍️
FCWA ☀️
Dedicated to Saadiya Abdulrazak (Mai Zafafa)
_____________________________________________________________________________________________
*Akwai sashen da ya faru a gaske,wani kuma ƙirƙiraren labari ne,ban yarda a juya shi ta kowacce irin siga ba haka ban lamunce a saka shi a wata kafar ba youtube ko kuma a mayar da shi audio har sai da izinina*
7
Ina tuƙi ina tunanin Dr Hannah,ya aka yi duk uban kuɗin da take samu amma a ce a nan unguwar suke rayuwa? Sosai nake mamakin haka don iya albashin da nake biyanta da shi ya isa ta ɗauki gidan haya mai kyau kuma su ci abinci har na tsawon wata,banda ma asibitocin kuɗi da take aiki don ta na da ilimi sosai za a iya cewa ma kusan duk Kamaru ita ce lamba ɗaya a mata in dai fannin aikinta ne.A haka na nufi can kasuwa inda nake da manyan shaguna da ake kula min da su,lokaci zuwa lokaci kawai nake zuwa can don duba yadda komai ke tafiya.
DR HANNAH
Faɗin farin cikin da ta yi da Ja'afar ya ce ta shiga motarsa Allah kawai ya san wannan,har suka iso ta na mamaki gani take ma kamar mafarki ne take wai yau ita ce a motar shi ya na tuƙa ta domin faranta ma ba don saboda ta je duba lafiyar matarsa ba.
Ta na shiga gida aka hau murna tare da ƴan gaishe-gaishe,maƙobta ma duk sun shigo yi mata sannu da zuwa Umma ce ke raba musu dabino da kuma bagaruwar Makka .Haka suka yi ta shigowa har suka ɗan tsananta,wanda hakan ya baiwa uwa da ɗiya zantawa.
“Hannatu ya hanya fatan kin yi aikin Hajj lafiya? Allah sa karɓaɓiya ce” Umma ta tambaya.
“Lafiya lau Umma alhamdullah,Amen ya Rabb ” Dr Hannah ta amsa murmushi na kan fuskarta wanda shine ke ƙarawa ummar kwanciyar hankali.
“Umma Alhaji fa ya kawo ni ” ta ƙara faɗa ta na wasa da yatsunta.
Umma ta murmusa ta ce “ ki yi ta addu'a Hannatu in sha Allah za a dace ai Allah da kansa yayi alƙawarin cewa in ka roƙe shi zai baka”
“Umma tun da na dira a Makka babu wata addu'a da zan yi ba tare da na ce Allah ya mallaka min Alhaji ba,har kuka na yi fa na kusa da ni dai su na kallona.Umma kuma fa kamar Allah ya karɓi addu'a ta inda kin ga yadda yake kallona” ta yi furicin cikin tsantsar farin ciki,Umma ta karɓe zancen “ in ba abun ki ba Hannatu ka yi addu'a nan ya karɓa ballantana a ƙasa mai tsarki? Ke dai kawai ki ci gaba da riƙe Allah don in kin kama shi kin gama komai tashi ki yi wanka ki zo ki ci abinci”
Dr Hannah ta miƙe ta ce “to amma dai ban jin yunwa” sai da ta rage kayan jikinta sannan ta cika bokiti ta je ta yi wanka.Bayan ta fito ne ta shirya cikin baƙar abaya ta yane kanta da kallabi,ƴar ƙaramar jakar nan ta mahajjata ta ɗauko ta fiddo tsarabar da ta yi wa Umma ta bata turare ne mai shegen ƙamshi umma sai godiya take,“sai sauran kayan sun zo ma ki ga abubuwan da na sayo miki ”
“Ko wannan ma yayi na gode,ina na Alhajin?” Umma ta tambaya cikin zolaya,Dr Hannah ta shiga yin dariya ta na rufe fuska kafin ta ce “ wannan dai nake son kai wa matarsa tun da ta na jego kin san sai da turare”
“Eh kin kyauta kuwa” nan dai suka ci gaba da yin hirarsu.
★
Ana gama sallar magrib na koma gida na ƙara ɗaukar wanka sannan na nufi gidansu Dr Hannah.Tun a hanya na sanar da ita,ina isa na kira ta a waya ta na ɗauka ta ce min “ ka shigo daga ciki mana Alhaji”
Na ce “ki fito ki min iso dai” da “to ” ta amsa ni kuma ina zaune ina ta mamakin kaina don har yanzu ganin abin nake kamar wasar kwaikwayo.
Ina ganin ta fito na yi saurin buɗe mota,ta yi tsaye ta na gaishe ni ban amsa ba sai ƙare mata kallo nake cikin abayar da na ga ta mayar da ita kamar balarabiya.
“Mu je ko” ta sake faɗa,sai a lokacin na dawo hayyacina na ce “ok to” sai na fito ta na gaba ni kuma ina take mata baya muka shiga farfajiyar gidan wacce ke ɗauke da ƙaton icce ,ko ina fes da shi babu ƙazanta haka komai na wurin da ya dace.
Da na shiga falon kuwa ƙamshin turaren wuta ne ke tashi,tun daga kujerun ɗakin har labulayen dukkansu fes da su babu ƙazanta.
“Ka zauna ga wuri nan” cewar Dr Hannah lokacin da muke gaisawa da Ummarta.Na ɗan harare ta kafin na ce “nan fa ba asibiti ba ce ballantana ki ce ke ce shugaba ”
Umma ta yi dariya ta ce “in dai Hannatu ce akwai matsuwa,in banda lafiya haka take matsa min wurin shan magani”
Na ce “ai kuwa dai kuma ƙila ita ba ta son shan maganin”
“Ina sha allura dai a ban so” sai a lokacin ta yi magana kafin ta kawo min ruwa masu sanyi na sha,Umma ta miƙe ta koma can ƙurya ɗaki sai ya zamana daga ni sai ita a wurin.
A yadda na ga ta na wani sunne kai sai abin ya bani mamaki,ita da kullum cikin yi min kallon bege take yau kuma da na kawo kaina shine ta wani sunne kai.
Na yi gyaran murya na ce “ don Allah Dr Hannah nake nema ba Hannatu ba”
Da sauri ta ɗago kai muka haɗa ido,wani irin daram na ji yadda idonta suka sha baƙin kwalli suka ƙara haske sai na ji ya tafi da imanina ban sani ba ko don Ryam ba ma'abociyar saka shi ne ba? Ita kanta Dr Hannah ɗin na yau ya sha banban da na kullum.
“Ni dai don kar ka sake ce min Hannatu ” ta faɗa cikin wata yanga,na kuwa shagala da yadda take maganar kafin na yi dariya na ce “ au! Dama kwaskwarima ne kika yi wa sunan naki? To ni ma Hannatun zan dinga cewa”
“Ni kuma na ce Alhaji Jafaru ”
Yadda ta kira sunan sam kasa riƙe dariyata na yi sai da na dara,na ce “Allah sarki sai kika tuna min da Momah ”
“Wace ce haka?”
“Mamana mana wacce ta rasu”
“Wai dama ba Goggo Dije ce mahaifiyar ka ba?”
Na kalle ta cike da mamaki na ce “sai yau kika sani? Momah ta rasu fa shekaru wajen biyar yanzu”
“Allah ya jiƙanta yayi mata rahama”
Na ce “Amen!” sai kuma na ɗauki wayata na shiga gallery na nemo hoton Momah na ce “ kin ga hoton ta” ta taso daga inda take ta karɓi wayar ta tsure hoton da ido,kafin ta ce “ni kuwa kamar na san matar nan hoton bai fita da kyau ba sosai”
Na ce “ eh shi ma dakyar na same shi” ta bani wayata na dube ta na ce “ba za ki je ki ga Baby ba?”
Ta langaɓe kai ta ce “wai da sai gobe na je”
Na haɗe fuska na ce “ Dr Hannah ki ji tsoron Allah ke ce fa mai kula da ita haihuwar nan in ba don ta zo cikin wani yanayi ba ke ce za ki karɓe ta”
Ta turo baki ta ce “bari na tambayi Umma in za ta bar ni ” sai kuma ta wuce can ƙurya ɗaki ta ɗan jima kafin ta fito ta ce “ tashi mu je”
Umma ta fito muka yi ban kwana sannan muka fito,ina tsaka da tuƙi ta miƙo min wani ɗan ƙaramin akwati ta ce “ ga tsarabar ka” na karɓa ina murmushi na ce “na gode mine ne a ciki”
“In ka buɗe za