Showing 12001 words to 13347 words out of 13347 words
Chapter 5 - INUWATA DA TA GABATA Book Complete by Mrs Sadauki.txt
ka gani” ta ban amsa daga nan ba mu sake magana ba har muka isa gidana.
A waje na tsaya ita kuma ta wuce ciki,Dr Hannah ta shiga da sallama duk aka amsa mata.
Fuskarta fal annuri ta soma yi wa Maryam Barka tare da tambayarta jikinta,sanin ita ɗin likitarta ce yasa take bata amsa daki-daki.
“Nurse Jamila miƙo min kayan aiki na duba ta” cewar Dr Hannah ta na gwale idon Ryam,nurse Jamila wacce ta na ɗaya daga cikin uwanda suke taya Dr Hannah aiki ta yi sauri ta je ta ɗauko kayan a ɗakin da Ja'afar ya ware matsayin ɗakin kula da Ryam.
Awon tension ta soma yi mata sannan duba bugun zuciyarta,“mike damun ki haka ne? Ki na cin abinci kuwa? Shayi fa bai yi miki a yanzu doli ki dinga ci ki na ƙoshi yadda baby za ta samu nono”
“Ruwan nonon ma sun tsaya sun bar zuba fa” Ryam ta bata amsa cikin wani yanayi.
Dr Hannah ta ce “ kamar ya sun bar zuba? Ku haɗo mata tea a saka garin hulba a ciki ta sha.A kawo babyn mu ga ta ɗora ta”
Goggo Dije ce ta ɗauko Abrar wacce ta lumshe ido kamar mai bacci ta ɗora kan ƙafafun Maryam,Dr Hannah kuwa maman Ryam take matsawa don tabbatar abin da aka ce ɗin sai kuwa ta ga ko ɗigo ɗaya bai zuba ba.
“Ɗorata a kai mu ga ƙila ta zuƙo...” ta faɗa ta na mai kallon fuskar Abrar,gaban Dr Hannah yayi mummunan faɗuwa har sai da ta ɗan ja baya kafin kuma ta ƙara gwale idonta sosai kan fuskar Abrar zuciyarta na ci gaba da buga wa yayin da kuma take addu'a Allah sa abin da take gani ba gaskiya ne ba.
Ta kai hannu da niyyar taɓa kumatunta,wuluk Abrar ta buɗe idonta suka sauka cikin na Dr Hannah.Muƙut ta haɗiye yawu kafin murya na rawa ta ce “Mar....y.am zan je na dawo kaina na min ciwo” ba ta jira abin da za ta ce ba ta nufi ƙofar fita.
Ina tsaye ina waya da abokina da ya kira ni na ga Dr Hannah ta fito kamar a firgice,gabana ya faɗi ina addu'ar Allah sa dai ba Ryam ta yi mata wani abun ba.
Har inda nake ta iso,ido cikin ido take kallona kafin ta jefo min wata tambayar rainin hankali “ wane ne kai?”
“Ke kin san abin da kike cewa kuwa?” na tambaye ta
“Wane ne kai tambayar ka nake kawai ka bani amsa ?” ta min magana cikin ɗaga murya kafin kuma ta fashe da kuka,ta na shirin tafiya na cabko hannunta na ja ta izuwa can baya na tsure ta da ido na ce “mine ne ke damun ki Hannah ?”
“Ka bani amsa ta wane ne kai? ”
“Ja'afar ne ko ba ki gane ni ba?”
Ta girgiza kai ta ce “ bari nuna kamar ba ka san mi nake nufi ba,duk wanda yake cikin ɓoyayyar duniya in aka masa tambayar nan zai amsa kai tsaye ne”
Na yi wata irin dariya na ce “ Dr Hannah wai lafiyar ki kuwa? Bayan wannan duniyar har akwai wata ɓoyayya wacce ni ban sani ba?”
Cak ta tsaya da kukan da take ta na wani kallona tsakiyar ido kafin ta faɗa min abin da har ƙasa ta naɗe ba zan taɓa manta abin ba,kuma tsanarsa ba za ta fita zuciyana ba.
“Za ka iya tuna rayuwar ka ta baya wacce kuka je ƙauyen Asungula ?”
Ban san lokacin da na saki hannunta ba ,na soma yi mata wani kallo ba tare da na ce komai ba.
Dr Hannah ta ci gaba da cewa “ *INUWAR DA NA GABATA* ce ta soma biyayata,na yi tunanin komai ya ida tun da har na dawo gidanmu amma yanzu abin da na gani a tattare da Abrar....” sai kuma ta tsaya cak kamar wata zararriya ta ce “ Alhaji mu ga hoton nan da ka nuna min na Momah ”
Ƙarfin hali kawai na yi na nemo mata shi,“ eh tabbas ita ce! Eh yanzu na tuna! Na tuna Ja'afar kai ne ta ban saƙo wurin ka shekaru biyu da suka wuce don Allah ka faɗa min ka bani labarin ka Momah na cikin matsala ta na neman taimakon mu”
Na riƙe kaina da dukkan hannuwana na cikin ƙaraji na ce “ Dr Hannah ya isa ! Mi kike so da ni ? Haukata ni kike son yi? Duk wannan banzan shirmen naki ban gane komai ki fito kai tsaye ki yi min magana ta yadda zan gane”
Sai da ta wani zo dab da ni ta min raɗa a kunne ta ce “ Kuɗin ka haramtattu ne,kuɗin ka same su ne ta hanyar sadaukar da jinin Momah ba tare da kai kanka ka sani ba za ka iya tuna ƙauyen Asungula?”
Ƙafafuwana ne suka soma yin rawa sam hankalina ba zai iya ɗaukar wannan al'amari ba jiri ya soma ɗiba ta ina shirin zubewa Dr Hannah ta riƙe ni gam.Amma duk da haka numfashina barazanar tsaya wa yake,dakyar ta zaunar da ni ta yi saurin fita daga wurin sai ga ta sun dawo da maza ma'aikatan gidana.
“Ku taimaka ku kai shi mota za mu wuce asibiti”
Haka suka kama ni aka sani mota aka kai ni babban asibitin da take aiki,ita ce da kanta ta shiga bani taimako.A sannu na fara jin zuciyata na ɗan samu rangwame Dr Hannah ta yi tsaye kai gare ni ta ce “ don Allah ka nutsu kar kasa zuciyar ka ta buga duk abin da ya faru Momah ta faɗa min ta ce ba da sanin ka ba ne ka bayar da ita”
Idona suka fara zubar da hawaye na ce “ kalaman ki Dr Hannah su ke ƙara tarwatsa ni Momah ta rasu kusan shekara biyar ki na kuma zancen kin ganta ba a fi shekara biyu ba”
Ta ce “ ƙwarai kuwa don ba ka san wace ce ni ba shi yasa ka yi mamaki,amma kafin nan ina so ka ban labarin ka mine ne dalilin da yasa ka sadaukar da Momah?”
Tsabar haushi da takaicin da suka rufe ni har bn san lokacin da na zabura na wanka mata mari ba,na ce “ ki tsarkake halshen ki,a duk duniya babu abin da na fi so sama da Momana ita ce komai nawa ta yaya kike tunanin zan bayar da jinin ta?”
Dr Hannah ta ce “ za ka iya tuna lokacin da za ka yanka baƙar agwagwar da bokan na ya ce ka yanka ka ji muryar mutum?” tambayar nan da ta jefo min tasa komai nawa da ya wuce ya dawo min a kai,da sauri na toshe kunnuwana saboda sautin abin da ya wuce da ya soma dawo min “ kar ka yanka niiii! Saboda kuɗi za ka kashe niii” ihu na ƙurma wanda yayi sanadiyar faɗuwar duk wani abu da ke wurin ƙwan lantarki ya fashe taratseeee,labulen da ke sarkaye ga window ya soma tashi sama ya na wuwilniya ɗakin ya ɗauki wani irin duhu mai tsanani wanda yayi bala'in bani tsoro.Ba a mafarki ba ido biyu na ga wani haske ya huɗo daga can ƙasa ya dalle idona wanda har ta kai da na sa hannu na kare fuskata.
Dr Hannah ta riƙo hannuna ta na cewa “ Ja'afar dubi ga Momah nan ta fito ta na roƙon ka” a hankali na soma ware idon nawa sai dai ban ganin komai sai wani dogon halshe da ke jan ƙasa kamar wani ƙaramin yaro na laɓe bayan Dr Hannah ina ce mata “ aljani! Aljani ne” amma abun mamaki sai na ji murya Momah raɗau a kunnena ta na cewa “Jafaru ka yi abin da ta ce ma”
Kamar ƙyabtawar ido kuma sai komai na ɗakin ya dawo normal,na dubi Dr Hannah kallo irin wai duk abin da ya faru gaske ne? Ta jinjina min kai ta ƙara jefo min tambayar nan “wane ne kai?”
Ƙarshen free page duk mai son ci gaba zai tura 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ki turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 ƴan Nijar kuma carte airtel ko Moov ta 500f ,na bar detail ki tura kawai ki turo evidence in kin san ba ki shirya biyan kuɗin karatun ki ba don Allah kar ki min magana na gode.