Header Ads
Showing 3001 words to 6000 words out of 13347 words

Chapter 2 - INUWATA DA TA GABATA Book Complete by Mrs Sadauki.txt

Ads the beginning of article before Image

23 Jun 2024

278

Ads at the middle of Article

su dinga kula da ke ne fa ,motsin su ne kika ji”
Ta ja ajiyar zuciya ta ce “ to ai ba ka faɗa min ba saura ƙiris fa cikin jikina...” ba ta kai ga idawa ba wani ɗan kofi mai ɗauke da flowers ya faɗo daga kan table ya fashe.
Ta yi sauri ta riƙe ni ta ce “ ka gani ko? ”
“ To mine ne kuma yanzu? ”
“Ka na gani fa shi ya faɗo da kansa babu wanda ya je ko kusa da shi” na laƙace hancinta na ce “lokacinsa ne yayi” na sumbaci goshinta “sai na dawo” na furta ba tare da na bai wa lamarin da ya faru muhimmanci ba.




Maryam na daga tsaye ta na kallon Ja'afar har ya fice sai ta dinga jin motsi,a hankali ta sauke idonta sai ta ga abin saka flowers ɗin na haɗe kansa da kansa tamkar ba shi ne ya fashe ba.Da mugun sauri ta kai hannu za ta dafe mararta da ke murɗawa sai dai kuma ta ji kamar wani hannun ya rige ta.
Ta fasa wani uban ihu ta na kiran sunan Ja'afar,ma'aikatan ne suka shigo da sauri su na tambayarta lafiya ganin ta kasa yin magana sai suka kira ogansu amma bai ɗaga ba.






JA'AFAR


Cike da ƙwarewa nake tuƙin har na isa babban hotel ɗin da za mu haɗu da shi.A hanya ina ganin kira na ta shigowa amma ban ɗauka ba saboda muhimmancin abin da zan yi,sai bayan mun gama meeting ne na duba waya sai na ci karo da saƙon wai an kai Ryam asibiti.Hannuna na rawa na kira lambar na tambayi asibitin da suke,a tsiyace nake gudu har na isa.Da taimakon Dr asibitin na je ɗakin da aka shimfiɗe Ryam,ta na kwance ta na bacci .Wani irin tausayi ta bani,na je na zauna kusa da ita tsawon lokaci kafin ta farka ta na ganina ta fara yi min kuka haɗi da yi min bayanin abin da ya faru.
“Yanzu dai alhamdullah tun da cikin jikin ki bai samu komai ba” na furta bayan na tayar da ita zaune.Likita ya shigo ya duba ta,na je na biya kuɗin magani kafin mu dawo gida ina ɗora ƙafata cikin falo idona ya sauka kan abin saka flowers ɗin ya na tsaye ƙyam babu alamar ma ya taɓa fashewa amma ko kafin na ƙyabta ido sai kuma na gansa a tarwatse zube akan capet kamar yadda na bar shi ɗazu.Na jawo Ryam na rungume ƙyam zuciyata na ɗan harbawa,duk da ba gwani ba ne wurin yarda da maganar aljanu sai na ji sam zuciyata ba ta aminta da gidan ba.....
[13/06 à 17:56] MRS SADAUKI 👑: 🦔🦔🦔
*INUWATA DA TA GABATA*🕸️
🦔🦔🦔
```(the shadow of my past/l'ombre de mon passé)```









MRS SADAUKI💫✍️




FCWA ☀️




Dedicated to Saadiya Abdulrazak (Mai Zafafa)




_____________________________________________________________________________________________




*Akwai sashen da ya faru a gaske,wani kuma ƙirƙiraren labari ne,ban yarda a juya shi ta kowacce irin siga ba haka ban lamunce a saka shi a wata kafar ba youtube ko kuma a mayar da shi audio har sai da izinina*




3




Na so tsagaita tashinmu daga wannan gidan mu canza wani,sai dai sam Ryam ta ƙi yarda duk inda na yi ta na maƙale da ni ta na kukan tsoro take ji gidan aljanu ke yi mata gizau.Da ta yi waya da mahaifiyarta kuwa cewa ta yi kar ta jinkirta kawai ta dawo ko da kuwa ni ban yarda ba.
“Shalele don Allah mu koma Kamaru,wallahi tsoro nake ji duk a takure nake ji nake ana kallona ” Ryam ta faɗa ta na kuka.




Na ce “to ba gani a kusa ba? Wa ke kallon ki kuma? Za mu tashi”
“A'a ba za ka fahimta ba,irin kallon da nake ji a jikina tamkar ana son cinye nama na”
“Ya isa haka yi shiru bari kukan,za mu je hotel daga nan sai mu wuce filin jirgi” na faɗa cikin rarrashi kafin na haɗa kayan da muka zo da su na kai mota,sai da na yi wa ma'aikatan da na ɗauko alheri kafin mu bar gidan.Wannan karon direba ne ke jan mu,muna daga baya zaune sai aikin rarrashi nake har muka isa wata haɗaɗiyar hotel.
Ko kayanmu ban cire ba daga bot Ryam ta fara girgiza kai “ban son wannan hotel ɗin ,mu tafi Shalele” sai ta riƙe ni gam ta na cusa kanta a ƙirjina kamar mai gudawa daga wani abin tsoron,na kuma fi tunanin hakan.




“Ya Rabb ! Mi kuma kike gani yanzu?”
“Tsohuwar hotel ce fa,dubi yadda gininta duk ya tsage ya tsufa” ta bani amsa ba tare da ta ɗago ba.
Cike da kulawa na riƙe kanta na soma yi mata karatu,a sannu ta fara sauke ajiyar zuciya har ta tsagaita kukan da take.
“Ryam kin ga kaf ƙasar nan babu hotel ɗin da ta fi wannan haɗuwa,kawai tunanin ki ne ke baki tsohuwar hotel ce amma dubi fa komai nata sabo ne”
“Ni dai kawai mu je can filin jirgi ɗin mu jira” ta furta ta na mai ƙoƙarin komawa mota,na dafe kai amma babu yadda na iya haka muka shiga direba ya kai mu can.




Inda aka tanadi kujerun zama na ja ta muka zauna,muna nan ne aka yi kiran sallar azahar na miƙe ina mai ce mata “zan je na yi sallah kar ki gusa daga nan” ta jinjina kai,na tafi can Toilet na yi ɗahara sannan na yi alwala na shiga masjid.






Maryam na zaune wata tsohuwa ta zo ta zauna a kujerar da Ja'afar ya tashi ,ba ta ganin fuskarta sai dai hannuwanta uwanda suke fari sol kamar na zabaya.“Sannu ƴata” ta faɗa cikin muryar tsofi,Ryam ta yi mamaki don yadda ta ganta jawur ɗin nan sam ba ta yi tunanin ta iya Hausa ba “yawwa babah ina wuni?”
“Lafiya lau!” ta amsa ta na fiddo wasu awarwaro da zabba masu bala'in kyawu da ƙyalli, duk na ƴan yara ne.Yadda walwalinsu suka shiga idon Maryam har ba ta san lokacin da ta kai hannunta gare su ba ta ce “babah na sayarwa ne?”
“Eh ƴata ga su nan ki zaɓa na yara ne” har wannan lokacin ba ta buɗe fuskarta ba,Maryam ta ruɗe ta rasa wane za ta ɗauka ma can ta zaɓi masu duwatsu jajaye haɗi da wani zobe na farar dalma.
Tsohuwar ta karɓi sauran, Maryam ta ce “nawa ne kuɗin?”
“Duk abin da kika bayar ƴata”
Maryam ta soma laluben jakar Ja'afar da ya bari can ta ciro 10mill ,ta ce “ungo!” ta karɓa ta na juya takardar kuɗin ta ce “nawa zan cire?”
Cike da jin daɗi take kallon awarwaron ta na juya shi ta ce “Ki ɗauka duka na gode sosai”




“Da wa kike magana ne haka?” na furta daidai lokacin da na dawo daga sallah na tarar da Ryam na magana ita ɗaya.Ta ɗago da sauri ta fara waige-waige,kafin ta dube ni ta ce “yanzu na sayi wannan ga wata mata fa nan take zaune ” sai kuma ta ci gaba da dubawa ko za ta ganta ai kuwa ta hange ta can nesa,sosai ta yi mamakin yadda aka yi har ta kai can ɗin cikin daƙiƙun da ba su wuce goma ba.




“Mu je ki yi sallah kar lokaci ya shige” na karɓi awarwaron da niyyar saka shi a jaka ta amma abun mamaki sai na ji wani irin contact kamar ina da alaƙa da shi amma sai na yi watsi daga wani tunani na ja Ryam har toilet na yi mata rakiya muka kuma fito tare ta yi alwala.Ta na nan zaune kan tapis muka fara jin sanarwa jirgin da zai tafi Kamaru zai tashi nan ba da jimawa ba.




Cike da kulawa nake riƙe da hannunta muka zo na ja trollyn kayanmu muka isa can inda za a shiga jirgin.Babu jimawa kuwa duk muka shiga ciki,da kaina na ɗaura mata belt ina mai yi mata raɗa a kunne “ki nutsu don Allah” ta saki murmushi kawai,bayan komai ya kammala jirginmu ya cira a sararin samaniya.




Yadda na ji ta wani damƙo hannuna yasa na yi saurin kallonta,“ya dai?”
“Dubi yadda samaniya take kam...kamar ana bin bayanmu”
“Da zarar kin ji wani abu ki ce Hasbunallahu wani'imal wakil! ”


Ba tare da tace komai ba ta jingina da kafaɗata ,ni kuma na riƙe mata hannu .
Lokacin da muka isa sai da na tashe ta daga bacci,muna fitowa ƴan jarida ne suka yo mana caaa kowa da kalar tambayarsa.Ban amsa ko ɗaya ba na ja matata muka wuce mota a can inda direba ke jiranmu,“a kai ni gidanmu please ” Ryam ta faɗa ta na kallona cikin ido.Na girgiza mata kai na ce “a'a kin san ba zan juri rashin ki kusa da ni ba”
Ta ce “umarnin Mama ne fa! Ba za mu jima ba akwai maganin da zan yi wanka da shi”
“Hum!” kawai na iya cewa don ba tun yau na fahimci mahaifiyar Ryam na son harakar malamai ba.




Babu yadda na iya haka muka je gidan nasu,sai da masu tsaron gidan suka bincika motar tawa sannan muka shiga duk da kuwa sun yi min farin sani.
Tarba mai kyau muka samu daga Mamar,sai da muka yi sallar la'asar da ba mu samu mun yi ba ajirgi sannan muka ci abincin da aka gabar mana.Kafin kuma Mama ta janye Ryam domin gudanar da wankan,ina nan zaune har aka yi sallar magrib na je na yi na dawo muka haɗu da mahaifinta wanda shi ne minista.
Hira sosai muke da shi ya na ƙara jajanta min game da haihuwar da aka yi min irin ta ko da yaushe kafin ya soma yi min tallar malamansa da kuma bani shawarar doli sai da malamai in ka taka wani matsayin.




“In sha Allah zan duba na gani yalaɓai ” na furta ina karanta saƙon Dr Hannah da ta yi min na barka da zuwa,ban yi mata reply ba don ban son irin rawar kan da take nuna wa a kaina.
Lokacin da Maryam ta fito ƙarfe goma na dare ta gota don har sai da na gaji da jira,har mota Mama ta yi mana rakiya bayan ta bata wata ƙatuwar leda.


“Baby sai wani irin ƙamshi kike irin na aljanu” na faɗa bayan mun ɗauki hanyar zuwa gidanmu.Ta yi ƴar dariya ta ce “ka san halin Mama game da bin ƙa'idar magani ni kaina sai da na gaji wanka da turare-turaren nan kuma fa wai a haka zan kwanta bacci ”
Na yi sauri na ce “da wannan ƙamshin kamar ƴar bori?”
Wata dariyar ta ƙara yi kafin ta ce “ai kuwa dai gwara ka so ƙamshin nan don haka zan dinga yin wanka da maganin har sai na haihu Mama ta ce ƙalau zan haifi babyna kuma rayayye ”






Na girgiza kai kawai amma ni sam ban yarda da zancen nan ba,muna isa gida Ryam ta fiddo wani magani ta shiga yayafa wa ko ina na gidan tun daga bakin ƙofa ta ce “sheɗanu ba sa son wannan ƙamshi” sai kuma ta kira ma'aikata ta sa su idasa aikin da ta soma.




Kan salon muka zube,Dr Hannah ta zo ta fara duba lafiyarta ta tabbatar min komai normal.Har zan tafi can bedroom ta ce “bani awarwaro da zoben nan Shalele ”
Na buɗe jaka na bata sannan na haye can sama.
Haka kawai Maryam ta zauna ta na juya awarwaron shi kuma ya na fitar da wani sauti da haske sosai abin ke yi mata daɗi,da ace ta aje hankalinta to tabbas da ta lura wani jan haske mai kamar an saita fitilar hannu haka yake dalle saitin cikinta yayin da kuma hoton dunƙulen tsokar wacce ta kasance fœtus ne tsaf za a iya ganinsa ta jikin dutsen da ya fita daban a cikin duwatsun....
[18/06 à 18:38] MRS SADAUKI 👑: 🦔🦔🦔
*INUWATA DA TA GABATA*🕸️
🦔🦔🦔
```(the shadow of my past/l'ombre de mon passé)```









MRS SADAUKI💫✍️




FCWA ☀️




Dedicated to Saadiya Abdulrazak (Mai Zafafa)




_____________________________________________________________________________________________




*Akwai sashen da ya faru a gaske,wani kuma ƙirƙiraren labari ne,ban yarda a juya shi ta kowacce irin siga ba haka ban lamunce a saka shi a wata kafar ba youtube ko kuma a mayar da shi audio har sai da izinina*






4




Cike da tsantsar so muke rainon cikin jikin Maryam,dukkan wata kulawa da miji ke bai wa matarsa ni tawa har ta kusan yin yawa.Kusan kullum ina tare da ita don yadda take barbaɗe gidanmu da magani duk safiyar Allah abin sai ya dinga bani tsoro sai na ji kamar in na yi nisa da ita gaske za a cutar da ita.Duk wasu ƙawayenta na datse alaƙarsu sai bayan ta haihu kuma,ɓangaren mahaifiyarta ta zage dantse wurin bin malamai da bokaye duk don bai wa ƴarta da abin da ke cikinta kariya ashe ƙara ƙaimi ne take wurin rogaza rayuwarmu ba tare da dukkanmu mun sani ba.






Aikin hajji ya matso kamar kowacce shekara ina ware kujeru sama da 50 na wanda nake biya ma su je su yi Hajj kyauta .Takarda na bai wa Maryam na ce “ki rubuta sunayen dangin ki uwanda kike son bai wa damar zuwa aikin hajj”


Da murna ta karɓa sunan mahaifiyarta ne farko da kuma na aminiyarta,kafin ta rubuta sunayen wasu goma can da ban san su ba .Bayan ta gama rubuta su sannan na karɓa na saka sunan Dr Hannah da sunan masu gadin gidana uwanda ban taɓa kai wa ba da aka zo ɓangren masu yin hidimar cikin gida kuwa ƴan aiki dukkansu na kira na ce “ a cikin ku zan biya kujerar Makka 5 kenan sai ku yi shawara su wane za su tafi a wannan shekarar su kuma za su yi haƙuri har wata shekarar?”
Kallon-kallon suka shiga yi kowacce da alamu ta na so,ganin haka yasa na guntsira takardu masu yawa na yi rubutu na dunƙule na zuba a ƙasa“kowacce ta ɗauki ɗaya wadda ta ɗauko 0 to za ta zauna in kuma lamba ɗaya kika ɗauko to za ki je Hajj ”


Bayan sun gama zaɓa na fitar da uwanda za su je ɗin,a ranar duk wanda sunansa ke kan liste muka sanar masa sannan suka fara shiri.Tun daga gyaran takardu har abincin da mutum zai ci in ya je can ni na ɗauki nauyin komai,irin addu'o'in da nake sha kuwa Allah kaɗai ya san iyakarsu.




Duk da na so tafiya aikin Hajj kamar kowacce shekara amma haka na zauna domin kula da abincin ruhina.Duk wata sangarta Ryam ta iya ta da salon jan hankali,sosai muke more rayuwar aurenmu kasancewar sam cikin nata ba mai laulayi ba ne.Har aka yi aikin Hajj aka gama kullum sai sun yi waya da mahaifiyarta video call,abu guda ke ban mamaki yadda Mama ke da mugun son duniya sam ba ta yi duba da ƙasa mai tsarki ce za ta je kitson gashin doki aka yi mata.




Ina daga gefe ina aiki kan system ɗina na saka casque 🎧a kunnena,yayin da gefe na kuma Ryam ce ke aikin abin da ta saba wato video call.Kamar an ce na tsayar da abin da nake saurare sai ji na yi ta na cewa “Mama kin fi kowa sanin Ja'afar na sona babu buƙatar sai na yi wani abun don mallakarsa ”
“Duk da haka dai ba ki ji ƴan magana na cewa ko ka na da kyawu to ka haɗa da wanka ba? Duk wannan rawar ƙafar da yake yi a kan ki da zarar kin haihu dukkan soyayya zai ɗauke ya ɗora wa babyn” shi ne abin da Mamar ta faɗa.
Ina gani ta ƙasan ido lokacin da Ryam ta saci kallona kafin ta bai wa mahaifiyarta ta amsa da “ Mama in ma aikin ne bai wuce a yi min yadda Ja'afar zai bar ni na tuƙa mota da kaina ba,sam ban son direba kuma ina son zuwa na yi aiki ba wai don kuɗi ba a'a kawai ina ra'ayi”




Na lumshe ido jin abin da take faɗa zuciyata na dakan uku-uku,‘wato Ryam ke a tunanin ki na hana ki tuƙa mota ne don wata manufa ba ki san duk cikin kulawa ba ce da tsantsar kishin ki. Maganar aiki kuwa ba zan iya ba ” ban san ƙarshen maganar a fili na yi ta ba sai da na ji ta yi magana a ɗan tsorace “wayyo Allah dama ka na ji na? ” na dube ta muka haɗa ido ta yi saurin katse kiran ta soma yi min kuka ta na rantse-rantse duk ta bi ta rikice ta fita hayyacinta.






“Yi shiru mana!” na furta tare da jawo ta jikina, na ci gaba da cewa “ni na yi imanin ki na sona kuma ba za ki iya cutar da ni ba,Ryam na san da ba tun yanzu Mama ke son baki maganin da za ki zuba min a abinci amma kika ƙiya.Ki sani ina mugun son ki ke ce farin cikin da kika rage min a duniyar nan” ina gama faɗa haka na tallabo haɓarta na soma yi mata sumba mai tsaya wa a rai.
Sai jan ajiyar zuciya take,motsin da cikinta ke yi yasa na yi saurin tsayawa na ɗage rigarta ina kallo sai motsin yake har yanzu.Wani mugun daɗi ya ƙara luluɓe ni na soma shafarsa,“Daddy na son ka babyna..” Ryam ta yi saurin katse ni “a'a mace ce wannan karon don wallahi har mafarkinta na yi”


Na dube ta cike da so na ce “to Ammyn Abrar ” Ryam ta saki murmushi mai sauti ta na shafar gefe da gefen fuskata inda ke da saje “ina sonka Shalele” ƙuri na yi mata da ido ta hura min iska na lumshe ido da sauri.


“Shalele na ce ba in na mutu wurin haihuwa ya za ka yi?” furucinta ya yi mugun bala'in dakar min zuciya ban san lokacin da na zabura ba.“Ni za ki tonawa asiri Ryam? Innalillahi wa'inna ileyhi raji'un!” na furta tare da miƙewa tsaye dukkan jikina na rawa,kaina na bala'in sarawa yayin da zuciyata ke barazanar faso allon ƙirjina ta fito.




Ina jin lokacin da ta dafa bayana “Shalele...” cikin tsawa na ce “babu abin da za ki faɗa min Ryam! ” sai kuma na juyo muna facing juna kamar wani zararre na kamo dukkan tafukan hannunta na ce “faɗa min duk rintsi ba za ki tafi ki bar ni ba”
Idonta tab ƙwalla ta ce “na yi maka alƙawari za mu rayu

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads