Showing 6001 words to 9000 words out of 13347 words
Chapter 3 - INUWATA DA TA GABATA Book Complete by Mrs Sadauki.txt
tare kuma za mu mutu tare” na jawo ta na rungume ina furzar da huci duk da cewa na san mutuwa ba ta barin wani don wani amma haka kawai yadda furucinta ya tsorata ni na ji ina son jin tabbacin ba za ta tafi ta bar ni ba.
A wannan ranar ban san mi ya shigi Ryam ba sai ta bani kulawa fiye da ta kullum,feshin kalaman soyayya kam ba a magana.
A washegari ne kuma jirgin su Mama ya sauka a Kamaru,tun a cikin daren na kai Ryam gidansu a can ma ta kwana.Tun da safe bayan na je can ofis sai na wuce gidansu wuraren ƙarfe goma,na samu tarba mai kyau kamar yadda aka saba yi min.Ina cin abinci amma fuskar Ryam sam babu walwala,ina ankare kuma da Mama yadda take jifarta da muguwar harara.Gabana ya faɗi ‘kar dai ace muguwar uwar can magani ta zuba min cikin abinci?’ na tambayi kaina a zuci amma don son tabbatar wa kawai sai na ce “Ryam zo mana” jikinta na ɗan rawa ta taso ta zo gare ni,ba tare da jin kunyar komai ba na jawo ta na ɗora ta kan cinyata “kin wani tsare ni da ido halan ba ki ci komai ba?” na faɗa ina mai kai cokalin abinci bakinta,ta girgiza kai ta ce “na ƙoshi” na ɓata rai na ce “wallahi sai kin ci ko kuma mu ɓata”
Ta ɗaga ido ta kalli Mama ta buɗe baki da niyyar magana na saka mata abinci a doli ta ci ta na wani zaro ido.
Na yi murmushi na ce “abincin yayi daɗi fa har da wani ɗanɗano na musamman kamar yaji kamar citta”
Ryam ba ta ce komai ba ta dai sunne kanta,kafin kuma in ga ta dafe ciki “mine ne?” ba ta bani amsa ba sai ƙara da ta saki,hankalina ya tashi musamman da ta fara cewa “wayyo zan mutu ana halbi na”
Mama ma ta soma tambayarta amma ta ƙi bamu amsa,hannuna na rawa na kira Goggo Dije tare da sanar da ita su yi sauri su zo ita da masu kula da lafiyar Ryam.
Cikin mintinan da ba su wuce goma ba Ryam ta haɗa uban gumi sai zufa ke mata tsiyaya duk da kuwa akwai sanyin AC.Ina daga gefe na ƙurawa cikinta ido da nake ganin shatin yatsun ƙafa jariri kuma sai motsi yake kamar zai fasa cikin ya ɓullo.Ko da likitocin da goggo Dije suka iso suka fara duba ta “naƙuda ce ta soma ya kamata a mayar da ita keɓaɓen wuri” haka ina ji ina kallo aka shiga da Ryam cikin ɗaki,tsawon lokaci kafin na ji muryoyinsu ana cewa “ma sha Allah yarinyar tubarkallah kamar ba ƴar wata bakwai ba”
Ban ji kukan jaririyar ba kamar yadda duk in baby ya zo duniya yake yi ba,kawai sai na ɗauka ita ma ɗin a mace ta zo.Amma ga mamakina sai ganin Goggo Dije na yi ta fito fuskarta cike da annuri ta na cewa “ angon jego barka ” sai a lokacin Mama ta miƙe ta na tambayar mi aka samu.
Goggo Dije ta ce “a kawo zane an samu ƴa mace” ita ma murnar ta hau yi,ni kuwa har izuwa yanzu ina cikin tsaka tsaki ina nan har tsaye har sai da aka fito da babyn cikin zane fara sol da ita kamar baturiya.
Na karɓe ta ,haka kawai na ji gabana ya faɗi lokacin da idona ya sauka kan kyakkyawar fuskarta mai bala'in kyawu.Dukkanmu daga ni har Ryam baƙaƙe ne amma kuma ga baturiya mun haifa,kamar Goggo Dije ta shiga zuciyata sai ji na yi ta ce “babyn nan dai ina tsoron farin Gambo ta biyo” ta na nufin mahaifiyata wacce ta kasance albino ce an haifeta ne bayan ƴan biyu maza shi yasa ta ci sunan Gambo.
Na ja ajiyar zuciya ina jin son babyn na ratsa min zuciya,na kai baki na sumbaci goshinta sai na ji gau kamar wuta da sauri na janye ina mai ci gaba da kallon ta daidai nan ta buɗe idonta taram cikin nawa kai kace wata mai wayo har wani taɓe baki take yi amma sam ban kawo komai a raina ba na miƙa wa Mama ita sannan na wuce ɗakin da Ryam take.
Ina ganinta na san ta galabaita,na je na sambace ta na ce “sannu jarumata ” ta ce “ina Abrar ɗin?”
“Ta na wurin Mama” ban rufe bakina ba sai ga su kuwa sun shigo,Mama ta miƙa wa Ryam babyn ta karɓa ta na kasa ɓoye tsantsar farin cikinta ba tare da ta san farkon uƙubar rahuwarta ne zai soma......
[19/06 à 14:02] MRS SADAUKI 👑: 🦔🦔🦔
*INUWATA DA TA GABATA*🕸️
🦔🦔🦔
```(the shadow of my past/l'ombre de mon passé)```
MRS SADAUKI💫✍️
FCWA ☀️
Dedicated to Saadiya Abdulrazak (Mai Zafafa)
_____________________________________________________________________________________________
*Akwai sashen da ya faru a gaske,wani kuma ƙirƙiraren labari ne,ban yarda a juya shi ta kowacce irin siga ba haka ban lamunce a saka shi a wata kafar ba youtube ko kuma a mayar da shi audio har sai da izinina*
5
Cikin ƙanƙanen lokaci ƙaruwar da muka samu ta Abrar ta karaɗe garin Kamaru,tuni kuma muka koma can gidanmu da babynmu.Cikin zumuɗi Ryam ta ɗauko awarwaron da ta saya ta saka wa Abrar shi,a gaban idona babyn ta wani zabura ta na juya hannunta kafin ta fashe da kuka.
“Ryam ina ga awarwaron nan ya matse ta kawai a cire” na furta ina ƙoƙarin cire shi ɗin ,Ryam ta hana ni ta fara ririga Abrar “shuuut! Yi shiru mana yarinyata,ado ne na yi miki ba ki ga hannun ki har yayi kyau ” duk yadda take ririga babyn amma ta ƙi yin shiru,, Goggo Dije ta shigo ta na cewa “ oh yarinyar nan tun da aka haife ta yanzu kawai na ji kukanta har mitsikarta nurse ta yi amma ta ƙi kokawa ,ina cewa kishiyar tawa soja ce ashe ragguwa ce miƙo min ita na yi mata wanka ga ruwan zafin nan sun tafasa ”
Ryam ta miƙa ta babyn ta na cewa “ ai kuwa dai duk kukan nan saboda awarwaro take yinsa kamar wacce ake cire wa rai”
Goggo Dije ta zauna ta na son cire awarwaron amma abun mamaki ya ƙi fita ga Abrar sai kuka take kamar ranta zai fita, wannan kukan da take yi ni kuwa sosai yake taɓa min zuciya na ce “ƙila kuma yunwa ce take ji”
“To bari na yi sauri na yi mata wanka sai a bata ta sha” cewar Goggo Dije ta na mai tsoma ta cikin ruwa,tsit Abrar ta yi ta bar kukan sai ajiyar zuciya.Ni ma sai na ji raina yayi sanyi,ina kallo har aka yi mata wanka aka naɗe ta a towel aka miƙa wa Ryam ita ta soma bata bata nono.Ta na gama sha ta yi bacci sai wani jan numfashi take,a doli na fita saboda yadda ƴan Barka suka fara shigowa.
A farfajiyar gida na zauna na soma kiran abokaina ina shaida musu Madam ta sauka lafiya.Ina nan zaune sai ga Alhaji Hamza babban abokina wanda muke raba ɗan fara guda,da murna muka rungume juna ya na cewa “barka! Barka Alhaji Ja'afar lokaci yayi mai haƙuri mawadaci”
Bakina kamar gonar auduga na amsa “barka kade abokina,dama haka Allah ke al'amarin shi.Ya gida ya yara?”
“Duk lafiyarsu lau,in sha Allah zuwa gobe Madam za ta zo yanzu ma su na can gidan ƙanwarta su na shagalin suna”
“Bai komai Allah nuna mana,ya kasuwanci?”
Ya ce “komai na tafiya daidai,ya maganar Nera an ce ta faɗi warwas ”
Na ce masa “ai ni na fita sha'aninta kawai na maida hankali wurin saffarar kayan ƙasashen ƙetare ina son ƙara buɗe wani kamfanin zuwa Hajj da umara ”
Alhaji Hamza yayi ƴar dariya ya ce “abokina ka san mi na tuna ?”
Na ce masa “a'a sai ka faɗa”
Ya ce “lokacin da muna yawon ƙwadigo duk kayanmu a koɗe wasu ma sun cire yanzu kuwa dubi gizner da muke sakawa,ka ga gidan ka kamar filin idi tsabar girma ga motoci jibga-jibga ,lamarin Allah kenan ”
Shiru na yi ina tuna tsohuwar rayuwar tamu,wacce ta na ɗaya daga cikin abin da yasa sam ba na ƙyama ko gudun talaka na san zafin talauci.Shi yasa nake girmama masu aiki ƙasa da ni ban taɓa jin wannan girman kan irin na masu kuɗi ba,ci gaban maganar shi ne ya yanke min shirun da na yi.
“Ita rayuwa sadaukarwa ce muddin ka na son canji,abokina talauci bai yi ba .Arziki shi ke kankaro wa mutum rigar mutumci,dubi goggon ka Dije sai ka ce ba ita ce wacce take koro mu ba in mun je gidanta yanzu ga shi ta ɓararaje ta na cin arziki”
Murmushi kawai na yi,Alhaji Hamza ya ci gaba da cewa “ya kamata fa mu je can Asungula”
Murmushin da ke kan fuskata ne ya ɗauke ɗif raina yayi bala'in ɓacewa in akwai abin da na fi tsana shine dajin Asungula da duk wani abu da ya shafi can.
“Yi haƙuri mana dama wasa nake,zan tafi sai goben” Alhaji Hamza ya faɗa ƙila ya lura da yanayin da na shiga.
Har bakin motarsa na yi masa rakiya sannan na koma can ciki,direct ɗakina na shiga na kwanta kan bed ina tunanin *INUWATA DA TA GABATA* sam ban son tuna abubuwan da suka shuɗe,hasali ma a doli na mantar da kaina su amma yanzu Alhaji Hamza ya faman min ciwon da ya daɗe ya na murƙusa ruhina.Na lumshe ido ina yi wa Ubangiji hailala,da wannan tunanin bacci ya ɗauke ni na kuma tsunduma duniyar mafarki.
A tsaye take da fararen kayanta kamar yadda ta taɓa zuwar min lokacin da muna Dubai .Idonta fari ƙal da su babu ɗogon baƙi sai shatun busashen jini a kumatunta.
A hankali na fara takawa inda take har na iso dab da ita na kamo hannunta “Ummaaa!” na furta daidai nan kuma ta ɓace ɓat ta bar ni da awarwaron hannunta wanda yake ta ƙyalli cikin tafin hannuna.Ruwan sama suka fara sauka ,a sannu a hankali dattin da ke jikin awarwaron ya fara fita kyawawan duwatsun suka fara bayyana a gare ni.
Kukan Abrar ne ya tashe ni daga baccin,na zabura na tashi zaune na dafe zuciyata da ke bala'in bugawa videon mafarkina na dawo min a kai sai dai duk da haka ban mayar da hankali kan awarwaron da na gani a hannun Umma sak irinsa ne wanda Ryam ta saya.
Da sauri na fita zuwa falo ina tambayar “lafiya kukan mi take yi?”
Ryam na hawaye tace “Shalele zo ka ga zabura take kamar wacce aljanu suka taso wa”
“To mine ne na kukan kuma?” na faɗa tare da karɓar babyn ai kuwa ta yi shiru ta na jan numfashi .
“Sai kin dinga bi a hankali wurin ɗaukarta don jikinta bai da wani ƙwari sosai” na faɗa ina kallon Ryam wacce ke shafar ƙwalla ƙila ta ji tsoro ne kar ita ma ace wannan ɗin mutuwa za ta yi kamar sauran.
Sai da baby ta koma bacci sannan na aje ta na je na shiga toilet domin yin wanka sai dai abun mamaki ruwan sun ƙi zuwa.Har zan mayar da kayana sai kuma suka fara sauka a hankali,na ɗaga kai sama na kalli shower idan ba gizau idona ke yi ba kamar fata maciji nake gani daga cikin hudodin.Kamar wanda aka shuka haka na yi tsaye ina kallon ikon Allah har na soma jin “surururuuu!” alamun ana tafiya daga can cikin ƙarfen pampon sai kuma ruwa shaaaa.Da sauri na rufe ido,hancina ne ya shaƙo min wani ƙarni marar daɗi a nan take ya haifar min da amai na shiga kwarara shi kamar raina zai fita sam ban yi lura da irin halittun da ke fitowa bakina ba wasu ƙananun tsutsotsi ne.
Ko da aman ya tsaya sai na ji kamar na fitar da wata guba na ji sakau babu nauyi.Dakyar na yi wanka na fito na shirya cikin jallabiya na fita zuwa masjid saboda kiran sallar magrib da ake,ba ni na dawo ba sai kusan ƙarfe goman dare.A falo na tarar da su ana ta hira,inda Abrar ke kwance na nufa na je na ɗauke ta na ce “bacci ma take”
Ryam ta ce “tun fa na ɗazu ne lokacin da ka ɗauke ta har wankan da aka yi mata ba ta farka ba”
“Shi ne kuma ba ki tashe ta ba kika bata abincinta?” na faɗa a hassale cikin ɗaga murya tsit falon yayi yayin da Ryam ke ƙyafƙyaf da ido.
Na tamke fuska na ce “kin ga in kin san ba za ki iya kula min da ita ba na nemo mai raino ko madara ce sai a dinga bata,sama awa biyar yarinya na bacci ba za ki tashe ta ba in fa yunwa ta kama ta?”
Goggo Dije ta ce “haba Ja'afar ya za ka dinga yi mata magana haka ? Ita fa ta haife ta akwai wanda zai fita son ta ne? Dama can jarirai lokacin baccinsu ya fi yawa kan wanda suke ido biyu”
Na ce “duk da haka dai Goggo ai sai a tashe ta ,na san da Dr Hannah ta dawo duk hakan ba zai faru ba ita ma sai ta yi faɗa”
“To sai ka kai wa Dr Hannah ɗin ta shayar da ita” Ryam ta faɗa tare da direwa daga kan salon ta wuce ƙuuu ta shige ɗaki,na bi bayanta da kallo kafin na take mata baya ina rungume da Abrar.
“Ke mine ne haka wai? Daga na faɗa miki gaskiya shikenan sai fushi?” na faɗa cikin sigar rarrashi amma sam Ryam ba ta saurare ni ba ta ci gaba da danna wayar hannunta can na ji muryar mahaifiyarta na “Lafiya kike kira na cikin dare?” kuka ta fashe da shi kafin ta soma yi mata bayani a ƙarshe ta ce “wallahi Mama ashe kin yi gaskiya Ja'afar ya bar sona Abrar yake so a kanta fa yake ɗaga min murya abin da bai taɓa yi ba” wayar a hand free take hakan yasa ina jin duk abin da suke cewa.
“Jarrrr ubaaa! To ya kai wa uwar Dr Hannah ɗin ta shayar da ita ai na ga alamu wani tashen rashin mutumci yake ji haka fa ɗazu a gaban idona ya ɗora ki kan cinya shi ga ɗan iska don ya nuna min abin da kuke yi ko a gidan,to ai ba sai yayi hakan ba iya cikin jikin ki ma ya isa ya sanar da ni amma bar shi da ni yake zancen gani nan zuwa” ƙittt ta kashe kiran.
In raina yayi dubu to ya ɓace ,sam ban san Mama wacce irin uwa ba ce mai ɓata tarbiyyar ƴaƴanta.Har zan yi magana baby Abrar ta fashe da kuka sai inyaaa ! Inyaaa take,na ja wata ajiyar zuciya na ce “ki yi haƙuri Ryam na tuba ba zan sake ba ungo bata ta sha ƙila yunwar ce ta tashe ta”
Wani mugun kallo ta yi min ta na cewa “ai kai ma ka na da shi sai ka bata,ko kuma ka kira a kawo Dr Hannah ɗin a yau ai ka na da iko”
Ban kula ta ba na je na ɗora Baby kan cinyarta ,da ƙarfin tsiya na yaga rigar jikinta sannan na fara taimakawa Abrar ta soma shan abincinta baiwar Allah yunwar kuwa take ji.Tun Ryam na motsi har ta bari,a ƙarshe kuma ta tallabe ƴarta ta ci gaba da shayar da ita.
Na saki murmushi na ce “ai dama uwa da ɗa sai Allah,ga shi har kin haƙura”
Ryam ta yi saurin janye Abrar ta ce “na fasa shayar da ita ɗin kuma wanda na bata sai ka biya ni kiɗinsa”sai kawai ta fashe da kuka haka ma babyn kukan ta canyara,duk yadda na so ta ci gaba da shayar da ita ɗin abu ya faskara har Goggo Dije ta shigo ta yi lallaɓar amma ta ƙi a ƙarshe ta fita da ita ta soma bata ruwan ZamZam ta na sha.
Waya na yi akan a sayo madara da biberon babu jimawa kuwa aka kawo, Goggo Dije ta haɗa ta baiwa babyn ta sha ta ƙoshi sai bacci.
A yadda Mama ta shigo falon sam babu alamar rahama kan fuskarta sai da na ji tsoro,“Maryam? Maryam fito mu tafi” shi ne abin da ta faɗa cikin ɗaga murya kafin ta ɗauki Baby Abrar,ita kuwa Maryam tuni ta fito daga ni har Goggo Dije babu wanda ya ce musu kanzil har suka fice.
MARYAM
Duk abin nan da ya faru ta biye wa Mama ne don Ja'afar ya ji tsoro ya shiga hankalinsa amma sosai soyayyar ɗiyarta ke danƙare a zuciyarta.Bayan sun fito ita da Mama ta karɓi Abrar suka shiga mota,har suka isa gida Mama na ta faman yin masifa ita dai Maryam kawai saurarenta ne take amma ba ta niyyar cutar da Ja'afar ta hanyar yi masa asiri.
Sabon zanen gado Mama ta shimfiɗa sannan Maryam ta hau ta zauna ta na shafar gashin Abarar.
“Ki yi kwancin ki nan ba za ki koma ba sai ya zo ya baki haƙuri” Cewar Mama ta na aje kaskon turaren wuta.
Maryam ta ce “Mama tun gida fa sai da ya ban haƙuri”
“Ke ni dai kwanta sai da safe ”
“Mama ki kwanta nan tun da Abba bai gida”
“A'a akwai aikin da zan yi cikin daren nan,na ga alamun shegen mijin nan naki sai mun tashi tsaye a kansa” da ace Mama ta kalli Abrar to da ƙila ta ga irin mugun kallon da jaririyar ke yi mata mai cike da tsana sai dai har ta fice ba ta waigo ba.
Maryam ta ce “oh babyna kin tashi” sai kuma ta yi shiru ganin yadda Abrar ɗin ke juya ido wasa ta yi ta yi mata kafin bacci ya ɗauke ta.Ko minti biyu Maryam ba ta yi ba da fara yin bacci Abrar ta tashi zaune ta na raraba ido ko ina,kafin ta hango window.Kallo ɗaya ta yi wa ƙwan lantarki nan take ya fashe da shi da sauran duk ƙwayaƙwayin da ke gidan.Hayaƙin turaren wutar da ke tashi sama ta yi tsalle ta haye kansa kafin ta ja reshensa ta ja shi yayi tsayi ba ta sauka ko ina ba sai a ɗakin Mama.
Za ku iya fara yin payment ɗin ku tun yanzu,don a page 7 zan tsaya da free page.My book is only 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ki turo shaidar biya ta WhatsApp +22795045822
[20/06 à 18:18] MRS SADAUKI 👑: