Showing 6001 words to 9000 words out of 11711 words
Chapter 3 - KANGIN BAUTA Littafin Yaki Complete by Mansur Usman Sufi .txt
tsananin tausayinsu
Sa'adda Hilwas, Kahzib da Sharwas suka yi. Arba da su a sannan ne mahaifin Kahzib da Sharwas da ke zaune a cikin wannan kejin suka fara zubar da hawaye.
duk da mahaifin Hilwas idanuwansa a makance suke baya gan abin abin da ke faruwa, amma da ya ji kukan ɗan sa Hilwas da abokanan Rauzil da Hasham sai shi ma ya fashe da kukan.
Sai da suka shafe wani lokacı a cikin wannan hali yarima Kinzaru na yi musu dariyar mugunta.
sannan sarki Shardasu ya sake nuna bangon a karo na biyu hoton bat! Kuma ya sanya wani duhu tsakanin su da su Rauzil ya zamana ba sa iya ganin 'ya'yansu.
Sarki Shardasu ya saki guntun murmushi ga su Hilwas da har yanzu hawaye ke zuba daga idanuwan su Sannan bushe da dariyar mugunta, kana ya murtuke fuska kamar an aiko masa da WASIKAR MUTUWA, ya ce, "Ya ku wadannan ZARATAN MAYAKA ma'abota karfin damtse ku yi saji cewa idan har kun ɗaukae mini Alkawarin da za ku samo mini abin da nake ji Bukata to zan 'yantaku tare da iyayenku ba za ku kara bauta a gare ni ba. Idan kuwa ku ka bijirewa buƙata ta ku da mahaifan ku za ku kasance a cikın KANGIN BAUTA har ajali ya riske ku,
Yanzu dai shawara ta rage ga mai shiga rijiya. Koda jin wannan batun daga bakın sarki Shardasu sa hankalın Hilwas, Kahzib da Sharwas ya dugunzuma ainun,
kuma su duka ukun suka faɗa kogin tunani don samun mafita.
Abin da ya faɗo musu a rai shi ne shin wace irin bukata ce za su biyawa sarkı Shardasu? An ya kuwa ba yaudararsu zai yı ba?
To yanzu kuma idan ba mu amince mun biya masa bukatarsa ba za mu ci gaba da zama a cikın kuncin rayuwa, tare da mahaifanmu? Amsar tambayoyın da suka kasa bawa kansu ke nan take hankulansu suka sake dugunzuma fiye da ko yaushe.
Hilwas ne ya katse shirun da ya wanzu a tsakanınsu ta hanyar buɗar bakı ya sanya hannu ya share hawayen sa sannan ya ce "Mun amince za mu bıya maka buƙatar matsawar za ka ba mu FANSAR RAYUKAN mahaifanmu.
Shin mece ce ake buƙatar taka?" Sarkı Shardasu ya yi murmushi a karo na biyu ya ce, "Abın da kawai nake buƙata shi ne za ku tafi izuwa gidan boka Kimraz domin ɗauko mini SANDAR SARAUTAR shi
Kafin ku isa gidan za ku tarar da miyagun dazuzzuka guda huɗu masu matukar haɗari.
Daji na farko ya kasance mallakin wani gawurtaccen matsafin dodo da ake yi masa masa laƙabi da suna Zamzaru.
Dodo Zamzaru ya kasance gwarzon mayaki, kaifi da tsini ba ya tasiri a kansa,
A wannan ƙarni ba ki ɗaya, domin saboda hatsabibancinsa ne ya zamana sarakunan da ke makwabtaka da dajin suka yi kaura suka bar yanayin.
Kuma an ce shi kadai ne yake rayuwa a dajin. Daji na biyu ya kasance na waɗansu irin tsuntsaye ne masu kama da tsuntsun batoyi, babu wani nau'in makami da yake tasiri a kansu face tsagwaran KARFIN DAMTSE da basirar mutum.
Masana da bokaye sun tabbatar da cewa adadin tsuntsayen ba zai kidayu ba,
Domin kullum kara yawa suke yi.
Daji na uku na waɗansu fatalwoyi ne na haske, mutum ba zai taba samun nasara a kansu ba face ya kashe shugabansu kuma dukkanninsu suna da kamanni iri daya sak!.
Babu yadda za a yi mutum ya iya gane wane ne shugabansu.
tsakanin zafin namansu kuwa ba zai musaltu ba sai dai abin da ido ya gani.
Na karshe kuwa ya kasance daji ne na waɗansu zakunan sihiri da wani shu'umin boka ya ƙirƙira mai suna Sultan ibn Hammar. Bayan kun samu nasara shiga gidan boka Kimraz kun dauko mını sandar tsafinsa sai kuma ku huce izuwa wanı daji da ke ıyaka da gidan ku ɗauko mini ƙoƙon kan boka Mannaf da ke ajiye a cikin wata tsohuwar rijiya dake fadar Sarkin bokaye na duniya,
Sa'adda sarki Shardasu yazo nan a zancen sa sai hankalinsu Hilwas ya dugunzuma ainun, Sharwas dubi sarki ya ce, "Ya shugabana a wace nahiya dazuzzukan suke?" Sarki ya ce, "Me ku ke ci ne na baka na zuba? Ai zan haɗa ku ne da wani hadimin aljanina ya yi muku jagora."
Koda gama fadin haka sai sarki Shardasu ya rintse idanunsa ya kırawo sunan aljaninsa, wata irin kakkarfar iska ta mamaye wurin wacce ta haddasa gashin kansu bawa Hilwas da rigunan jikinsu kaɗawa.
Daga can sai ga wani narkeken aljani ya bayyana tsum! Tamkar an jefoshi daga sararin samaniya.
Aljanin ya kasance mai matuƙar tsaho, muni, girma gami da kwarjini.
Domin duk dakewar zuciya irin ta su jarumi Hilwas sai suka firgita da ganin aljanın
Shi kansa sarkin yaki Hatyal da yarima Kinzaru sun razana matuka.
sarki Shardasu ne kadai bai tsorata ba. Aljanin ya faɗi ƙasa ya kwashi gaisuwa ga sarki Shardasu.
Sarki ya dube sa ya ce, "Ya kai Kubuzul Haiman ka yi sani cewa ban kirawo ka nan ba sai domin ina sai ka yiwa waɗannan jarumai rakıya izuwa dajin Darul Hashawar. Wannan shi ne abin da nake bukata."
Koda jin wannan batun sai aljani Kubuzul Haiman ya risina ya ce, "An gama ya shugabana. Ba tare da wani ɓata lokaci ba Hukubul Haiman rankwafa gadon bayansa bawa Hilwas, Sharwas da Kahzib suka hau kan kansu suka zauna tare da dawakansu sannan Kubuzul Haiman ya yunkura ya tashi izuwa sararin samaniya.
Kafin kiftawar ido ya ɓace ɓat a cikin gajimare, nan take sarki Shardasu, yarima Kinzaru da sarkin yaki Hatyal suka bushe da dariyar mugunta.
Wannan shi ne dalilin barowar jarumi Hilwas, Sharwas da Kahzib daga birninsu na Baitul Na'im, domin su ɗaukowa sarki Shardasu sandar sihiri da kokon kan boka Mannal.
SHIN WADANNE IRIN MIYAGUN MUSIBU SU HILWAS ZASU FUSKANTA A WANNAN TAFIYA TASU SUNA SAMUN NASARAR KETARE MIYAGUN DAZUZZUKA HUDU HAR SU ISA GIDAN BOKA KIMRAZ?
KUMA SUNA SAMUN NASARAR DAUKOWA SARKI SHARDASU SANDAR TSAFI DA KOKON KAN BOKA MANNAF DOMIN FANSAR RAYUKAN MAHAIFANSU?
SHIN YA SHURAIMA 'YAR SARKI HUSUBUL DINAR DA GIMBIYA LASHMIRA ZA SU KASANCE NA KEWAR MASOYANSU HILWAS DA KAHZIB?
TSAKANIN YARIMA KINZARU DA GIMBIYA LASHMIRA WAYE ZAI GAJI KARAGAR MULKIN SARKI SHARDASU?
INA LABARIN SARKI BARSUS, Sarkin marubutan yaƙi ANSAB DA SARKI HULBARU DA KOWANNENSU YA SHIRYAWA SARKI SHARDASU BAKIN TUGGU DOMIN RABA SHI DA KARAGAR MULKINSA, AMMA YA TSIRA DAGA SHARRINSU?
SHIN A WANE HALI MAHAIFANSU JARUMI HILWAS YA ZA SU KASANCE NA RABUWA DA 'YA'YANSU?
Mu hadu a 10 KANGIN BAUTA domin jin ci gaban wannan labarin nayataccen labari.
Lokacin da su jarumi Hilwas suka yi cirko cirko a kofar shiga gidan boka kimraz
Cike da matukar damuwa bisa halin KANGIN BAUTA da suka baro mahaifin su a ciki.
Sai suka shafe tsawon daƙiƙa arba'in Batare da ɗayan su yace uffan ba.
Ana cikin wannan hali ne kwatsam bazato babu tsammani sai suka hango wani mahayi bisa ingarman doki fari.
Ya rataya wata sharbebiyar takobi a gadon bayan sa ya durfafo inda suke gadan gadan.
Sai dukkanin su suka ƙura wa mahayin idanu suna jiran ƙarasowar sa. Sannu a hankali mahayin ya ci gaba da kusanto su,
Har yazmana tazarar dake tsakanin su bata huce taku biyar sannan yaja linzamin dokin sa ya tsaya cak
Yayin da suka yi arba da mahayin sai suka cika da matukar mamaki.
Abu na farko da ya basu mamaki shine yadda mahayin ya yaksance ya mace ba namiji ba,
Sannan ya akayi ta iya ketare miyagun dazuzzukan dake baya
Wato dajin fatalwoyi na haske, dajin dodo zamzaru da kuma dajin zakunan sihiri masu ɗauke da fuka -fukai ,
Wanda su kansu sai da suka sha bakar wahala sannan suka samu nasarar ketare dazuzzukan.
Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kansu kenan
Shi kuwa Sharwas sam bai ma san da wannan zancen ba,
Domin tuni ya shagala da kallon kyakkyawar budurwar, domin lokacin da ya fara arba da ita sai yaji zuciyar sa ta buga wa karfi wani abu ya soki ya soki zuciyarsa a karo na farko yaji ya kamu da matukar kaunar ta a zuciyar sa,
Tsawon daƙiƙu ana wannan kallon kallo tsakanin su Sharwas da Mahayin,
Sannan daga bisani hilwas yayi karfin hali yayi gyaran murya ya dubi budurwar yayi gyaran murya yace" yake wannan budurwa shin wace ce ke ?
Kuma ya akayi kika ƙetare miyagun dazuzzukan dake baya har kika iso nan?.
Sannan mene ne ke tafe da ke izuwa gar mu.
Sa'adda budurwar taji wannan batu daga bakin hilwas dai tayi gyaran murya cikin tattausar murya mai daɗin sauraro tace" yakai hilwas ɗan makaho rukaisu kayi sani cewa da farko dai ni suna na Husnat bintu abu-husein
Na fito ne daga gabashin duniya a wani birni da ake yiwa lakabi da Darul--imfidal,
Game da amsar tambayar ka ta biyu kuwa shine,
Na samu nasarar ketare dazuzzukan dake baya ne bisa taimakon Ubangiji mahalicci,shine wanda ya halicci duniya da Abin da ke cikin ta,
Amsar tambayar ta karshe ita ce bakomai ne ke tafe dani izuwa gare ku sai domin na taimaka muku da izinin Ubangiji na domin ku samu nasarar abin da kuka fito nema.
Kuma na kuɓutar da mahaifan ku daga makircin azzalumin sarki sharadi,
Sa'adda Kahzib, hilwas da Sharwas suka ji wannan batu daga bakin Husnat sai suka cika da ɗumbin al'ajabi da mamaki,
Kahzib yace "yake wannan jaruma taya ya za ki iya taimaka mana wajen cimma burin mu bayan cewa mu ɗin Jarumai ne zamu iya nasara akan dukkan abinda muka sanya a gaba,
Sannan naji kin ambaci wani Ubangiji shin dama akwai wani abin bauta bayan namu?.
Husnat tayi ƙaytaccen murmushi da ya ƙarawa fuskar ta kwarjini sannan tace " na yar da cewa tabbas ku sadaukai ne kuka kuma zaku iya cimma nasara akan abinda kuka sanya a gaba
Amma ina so ku sani zan taimaka muku ne wajen mallakar abin da kuka fita nema cikin ruwan sanyi batare kun sha wata wahala ba,
Sannan ina so mu haɗa karfi da ƙarfe wajen rushe mulkin zalunci na sarki shardasu domin ku sani cewa koda mallaka sa abubuwan dake bukata sai ya ci amanar ku bazai taɓa baku fansar rayukan mahaifan ku ba,
Sannan zan roƙi Ubangiji na ya warkar da lalurar dake samun iyayen ku,
Amma sai idan kun ɗaukar mini alkawarin cewa zaki bayar da gaskiya ga Ubangiji na
Sa'adda Sharwas, Kahzib da hilwas su ka ji wannan batu daga bakin Husnat sai jikin su yayi sanyi,
Suna masu zurfafa izuwa cikin Kogin tunani
Daga bisani sai
Sharwas yace "Ɗan bamu Lokaci zamu tattauna da yan uwa na,
Koda gama faɗin hakan sai shaewas da yan uwansa suka koma gefe guda suka yi ƙusƙus a junan su sannan daga bisani suka dawo izuwa inda Husnat take,
Hilwas ya dube ta yace" yake Husnat haƙiƙa mun amince zamu zamu karbi addinin ki,
Matukar kika cika alkawarin da kika ɗauka na taimaka mana wajen mallakar abubuwan da muka fito nema,
Sannan idan har Ubangijin naki ya warkar da mahaifan mu,
Munyi miki alkawarin cewa zamu taimaka miki wajen yaɗa addinin ki a wannan nahiya baki ɗaya,
Koda jin wannan batu daga bakin hilwas sai jaruma Husnat ta cika da matukar farin ciki maral misaltuwa,
Kawai sai ta kama linzamin dokin ta ta sauko ta durfafo ƙofar gidan boka kimraz
Da isar ta sai kawai ta sanya hannun ta akan Mabudin kofar tayi bismillah ta tura ƙofar bisa mamaki sai gashi ta buɗe
Al'amarin da yayi matukar bawa su hilwas mamaki kenan kuma ya ɗaure musu kai,
Domin dai ko da a tarihi basu taɓa ganin jarumin da yayi wannan bajin ta ba.
Domin kofar tana da kaurin gaske wacce in da za'a sanya karti majiya karfi mutun sattin ba za su iya ture ta ba,
Batare da fargabar komai ba, Husnat ta zare sharbebiyar takobin dake gadon bayan ta ta kunna kai izuwa cikin gidan tana mai yafito su hilwas da hannunta tana nuna su biyo bayan ta,
Batare da gardamar komai ba hilwas ya zare takobin sa ya bi bayan ta da sauri,
Kahzib na rike da mashin sa mai baki biyu,
Sharwas na rike da kwari da bakan sa suka shige izuwa cikin gidan,
Wannan shi ne abinda ya faru da su bawa Hilwas akan hanyar ta zuwa gidan boka kimraz domin ɗauko wa sarki shardasu sandar sihiri.
Acan birnin baitul-na'im kuwa al'amarin gimbiya lshamira da gimbiya shuraima yar sarki Husubul-Dinar kuwa,
Tun sa'adda suka ji abinda ya da yafaru da masoyan su wato bawa Kahzib da hilwas,
Sai suka kasance cikin tsanin damuwa yana zamana cewa sun kamu da rashin lafiya domin ko abinci basa iya ci,
Koda sarki Husubul-Dinar yaga abin da ya samu yar sa sai ya yanke shawarar ya tafi izuwa Birnin sa domin yi mata magani,
Amma sai sarki shardasu yace yayi hakuri har zuwa lokacin da zasu samu lafiya ayi musu magani tare da gimbiya,
Al'amarin mahaifan su Kahzib maza da mata a cikin kurkuku kuwa sun kasance cikin kinci da damuwa dare da rana bisa tunanin halin da ya'yan su ke ciki.
Suka ji sun tsani sarki shardasu fiye da komai a rayuwar su .
Wannan shi ne abin da yafaru da su gimbiya lshamira da mahaifan su Kahzib.
Mu haɗu a KANGIN BAUTA Littafi na 11 domin jin cigaban wannan kasaitaccen labari.
Daga mai ɗebe muku kewa a kullum da ko yaushe
Lokacin da su jaruma Husnat dasu bawa Hilwas suka shiga izuwa gidan boka kimraz,
Sai suka tsinci kansu a wani makeken fili mai tarin rairayi,
Sai suka ci gaba da tafiya Husnat tana mai dawo bayan su,
Saboda ta lura yadda Sharwas ke satar kallon ta a fakai ce,
Yayin da taga hakan sai ta dube sa ta sakar masa tattausar murya a lokacin da ya waigo ya haɗa idanu da ita ɗin.
Koda yaga irin murmushin da Husnat ke yi masa sai yaji zuciyar sa ta buga da karfi,
Kawai ya mayar da duban sa zuwa kan hanya yana mai tambayar kansa a cikin ran sa yana mai cewa shin Mene ne ma'anar wannan murmushi da Husnat tayi mini shin ko ita ma ta kamu da soyayyata ne.
Amsar tambayar da Sharwas ya kasa bawa kansa kenan.
Haka dai aka cigaba da tafiya sai da aka shafe tsawon Sa'a ɗaya ana tafiya batare da an haɗu da wani abu mai cutar wa ba,
Ana cikin wannan hali ne kwatsam bazato babu tsammani sai aka ga waɗansu irin dakaru na taso wa daga cikin rairayin tamkar yadda danshi ke tsattsafowa daga cikin ƙasa,
Dakarun sun kasance girɗa-girda tamkar samudawan farko suna dauke da siffa guda biyu,
Tsagin jikin su na dama na karfe ne tsagin hagun kuwa na na haske ne
Suna dauke da miyagun makamai masu barazana ga rayuwar bil'adama,
Suna dauke da idanuwa jajur kwaya ɗaya jal a tsakiyar goshin su,
Hancin su da bakunan su irin na gwaggwan biri ne,
Haƙiƙa waɗannan dabaru sun kasance munana kuma ababan tsoro,
Babu wata halitta mai numfashi walau mutum ko aljan da zayi arba da miyagun dakarun face tayi nadamar wanzuwar ta a doran ƙasa,
Sa'adda su jarumi Hilwas sukayi arba da dakarun sai suka ɗimauce,
Tamkar ace kyat su zura da gudu,amma saboda juriya irin ta zaratan Jarumai sai suka dake,
Jaruma husnat ce kaɗai bata razana ba ita ma saboda tana karanta sunayen Ubangiji tsarkaka ne a cikin ran ta yasa hakan,
Yayin da dakarun suka kammala yiwa su hilwas ƙawanya sai aka fara kallon-kallo tsakanin su,
Daga can sai dakarun su ka zare makaman su suka yi ihu da kururuwa mai firgitar wa suka ruga izuwa kan su.
Ko da ganin hakan sai jaruma Husnat ta zare takobin ta ta kwala kabbara da karfi ta ruga izuwa kan dakarun,
Sharwas, Kahzib da hilwas sukayi koyi da ita ta hanyar zare makaman su,
Lokacin da aka haɗu sai aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matukar kwarjini muni daban tsaro,
Kowa ne ɓangare su ka wanzu suna kaiwa juna miyagun hare hare cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta tagaban kwatance,
Wohoho ana fara wannan artabu ne wani abun mamaki ya fara guda domin kuwa duk irin zafin nama na su jarumi Hilwas yazama abanza,
Domin kuwa duk sa'adda suka sari jikkunnan dakarun da makaman su sai suji tamkar dutse suka sara domin wani irin tartsatsin wuta ne yake tashi gami da kara marar daɗin sauraro.
Al'amarin da yayi matukar dugunzuma hankalin su kenan suka fahimci cewa idan aka Cigaba da wannan artabu a haka dakarun zasu iya samun nasarar hallaka su.
Abangaren jaruma Husnat kuwa tuni labari yasha bambam,
Domin kuwa Husnat ta zamo gagarabadau a tsakiyar dakarun,
Duk in da ta sanya a gaba sai dai kaga dakarun na zubewa ƙasa matattu tamkar tana sassabe a gonar auduga.
Tabbas jarumtaka baiwa ce daga Ubangijin halitta ba'a siyan ta kuɗi ko mulki,
Komai hassadar Mutum idan ya ga Yadda Husnat ke ragargazar dakarun doka ne ya jinjina mata ya tabbatar dacewa ta cika mace mai kamar maza kuma jarumar Asali,
Nanfa ƙarar karafniyar ƙarafa,ihun mazaje haɗe da kururuwar dakaru ta cika dodon kunne,
Sassan jikkunnan dakarun suka dinga shawagi a sararin samaniya suna zubowa ƙasa tamkar ana ruwan su ne daga saman,
Jini kuwa ya dinga kwaranya, tsartuwa gami da feshi yana zubar a ƙasa tamkar an balle Teku,
Sai da aka shafe tsawon Sa'a ɗaya ana wannan fafatawa babu sassauci,
A sannanne dakarun suka fahimci cewa Husnat tayi musu muguwar barna.
Domin ta kashe fiye da rabin su,
Nan fa hankalin su ya dugunzuma ainun,kuma suka fusata ainun zukatansu suka dunga tafarfasa tamkar zasu kone,
Kawai sai suka zage damtse suna cigaba da kaiwa Husnat hare hare ta ko ina,
Al'amarin su Bawa hilwas kuwa sa'adda su ka ga irin gagarumar bajintar da Husnat ke yi sai suka cika da matukar mamaki suka ce a cikin ransa anya kuwa Husnat bil'adama ce,
Taya ya za'ayi ce zaratan Jarumai kamar mu mun kasa samun damar hallaka koda badakare ɗaya amma Husnat ta kashe fiye da rabin su,
Lokacin da sa'a biyu ta shuɗe ana wannan fafatawa a dai dai wannan lokacin ne Husnat ta hallaka ba ki ɗaya dakarun dake gaban ta,
Kuma ta hango irin mawuyacin halin da su Bawa hilwas ke ciki,
Domin dakarun sun galabaitar dasu basa iya mayar da martani sai dai ƙoƙarin kare kansu.
Wasu lokutan idan dakarun suka kawo musu hari suka kare da makaman su sai kaga sun faɗi ƙasa magashiyan,
Amma saboda juriya irin ta zaratan Jarumai sai suka muƙe tsaye aci gaba da yaƙin,
Koda ganin hakan sai ta falfala da azababban gudu izuwa kan su
Tana mai kwala kabbara da ƙarfi tare da yiwa Annabi Sallallahu alaihi Wasallama salati,
Domin ta kai musu ɗauki,
Cikin daƙiƙa hamsin bisa taimakon Ubangiji mahalicci ta samu nasarar hallaka dakarun baki ɗaya,
Faruwar hakan ke da wuya sai gaba ɗaya gawarwakin dakarun da makaman yakin gami da jinin da