Showing 9001 words to 11711 words out of 11711 words
Chapter 4 - KANGIN BAUTA Littafin Yaki Complete by Mansur Usman Sufi .txt
ya cakuɗa da ƙasa suka ɓace ɓat tamkar basu taɓa wanzuwa ba,
Nan take filin ya rikiɗa izuwa wata ƙasaitacciyar faɗa,
Da aka kawata ta da nau'ikan kayan ƙawa da alatun jin daɗin rayuwar duniya,
Bisa wani zagayayyan tudu da aka shimfiɗe sa da wata irin Koriyar Darduma anan aka ajiye wata ƙasaitacciyar sanda wace akayi ta zallar zinare kuma aka yi mariƙin ta da zubardaju,
Sandar tana canza launi lokaci zuwa lokaci
Kai da gani kasan aiki ne na sihiri.
Koda Husnat tayi arba da sandar sai ta dubi Bawa hilwas tace"sai kayi hanzari ka ɗauko mana waccan sandar sihiri domin mu tafi izuwa dajin kushuful-fannar domin ɗauko ƙoƙon kan boka Manaf.
Ko da jin wannan umarni daga bakin Husnat
Sai hilwas ya taka da kafafun sa har izuwa wannan gayayyen tudu yake ya dauki sandar sannan ya dawo izuwa inda su Kahzib ke tsaye.
Kawai ya shige gaba ya durfafi kofar fita daga gidan,
Sharwas, Kahzib na biye dashi jaruma Husnat ce a karshe,
Lokacin da suka fita sai suka hango dawakan su acan gefe suna cin ciyayi,
A sannanne Husnat ta lura cewa lokacin sallar la'asar ya giya,
Don haka sai tayi istigfari sannan ta cire salkar ruwan ta ta ɗaura alwala,
Bayan ta kammala ne ta fuskanci gabas ta tayar da sallah,
Sa'adda Hilwas, Kahzib da Sharwas suka ga yadda jaruma Husnat ke gudanar da ibadar ta nan take suka ji addinin musulunci ya kayatar dasu,
Domin ba su taɓa ganin addini mai tsafta da nutsu tamkar addinin Husnat ba,
Nan take Sharwas yaji soyayyar Husnat ta daɗa mamaye zuciyar sa,
Da yake yamma tayi liƙis duhun magariba ya fara kawo kai sai hilwas ya bayar da shawarar a kwana a dajin idan ya so da safe sai a durfafi dajin Kushuful-fannar,
Mu haɗu a KANGIN BAUTA Littafi na 12 domin jin cigaban wannan kasaitaccen labari,
Daga mai ɗebe muku kewa a kullum da ko yaushe
Marubuci
MANSUR USMAN SUFI
Wthapp number &;call
08137237071
KANGIN BAUTA
Marubuci
MANSUR USMAN SUFI
Wthapp&call
08137237071
Kamar yadda jarumi Hilwas ya bayar da shawara haka al'amarin yakasance,
In da aka kwana a wajen da duku-dukun safiya bayan jaruma Husnat tayi sallar asuba anyi kalaci kowa ya kimtsa cikin sa,
Sai kowa ya kama dokin sa ya hau ya sakaasa linzami aka cigaba da tafiya,
Hilwas, Kahzib da Sharwas suna tafiya a jere kusa da juna,
Husnat na biye dasu har a wannan lokaci fuskar ta rufe take da rawani idanuwan ta kaɗai ake gani,
Nan fa aka wanzu ana ratsa duwatsu, koramu tsaunuka haɗe kwazazzabai gami da sarƙaƙiya, cikin matsanancin gudu ma keta sa'a ,
Wasa-wasa saka gashi an shafe tsawon Sa'a uku ana wannan tafiya,amma ba'a haɗu da wani abu mai cutar wa ba,
Koda kuwa miyagun yan fashi da dakarun sumame,
Lokacin da Sa'a huɗu ta cika a dai dai lokacin aka shigo dajin kushuful-fannar,
Nan fa kowa yasha jinin jikin sa bisa ganin yadda dajin yaksance dole ne a samu miyagun halittu a cikin sa,
Kuma yakasance cikin shirin ko ta kwana
Tsawon tafiyar Sa'a aka yi sannan aka hango wata rijiya a can nesa,
Don haka sai aka ƙara azama domin isa, lokacin da aka isa sai kowa yaja linzamin dokin sa ya kama ya sauka ƙasa,
Ita dai rijiyar an gina ta ne da zallar dawatsun wuta masu kwarin gaske,
Tana ɗauke da murfi guda ɗaya jal, da aka yi shi da zallar mulmulallan karfe,
In da za'a sanya karti majiya karfi mutun sattin ba zasu iya buɗe murfin ba,
Nan fa aka yi cirko-cirko aka rasa wanda zai buɗe murfin rijiyar.
Daga can Kahzib ya matsa izuwa bakin Rijiyar ya sanya hannun sa ɗaya domin ya buɗe murfin amma sai yaji tamkar Dutse ya rike, sai da ya tara gumi ya jiƙe sharkab amma murfin ko gezau bai yi ba,
Amma sai da hilwas, sa Sharwas suka gwada tasu dubarar amma murfin bai buɗe ba,
Duk wannan abu dake da wakana jaruma Husnat na tsaye a gefe guda tana gani bata ce ƙala ba.
Koda taga kowa ya kasa buɗe wa sai ta matsa daf da rijiyar ta karanta ayatul-kursiyyu tare da yiwa Annabi s'a'w salati.
Ta sanya hannun ta ɗaya ta buɗe murfin tamkar ta yaye tufafi,
Hilwas, Kahzib da Sharwas basu san sa'adda su ka dunga dalalar da yawu daga bakunan su ba saboda matukar al'ajabi.
Koda murfin ya buɗe sai akaji wani irin mahaukacin gurnani na fitowa daga cikin rijiya,
Daga can sai aka ga wani ɗan wadan aljani yayo fitar burgu daga cikin rijiyar tamkar an janyo shi da ƙugiya.
Aljanin yakasance baƙi mummuna yana ɗauke da fuka -fukai irin na jemage, Du du du tsawon sa bai huce kamu biyu ba,
A hannu ɗaya ana rike da wani ƙoƙon kai, ɗayan kuwa yana ɗauke da wani zabgeegen Gatari na zinare yana sheƙi da walwali,
Aljanin ya bushe da dariyar mugunta tamkar bazai daina ba
Daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da wasikar mutuwa ya ce"
Kaicon ku yaku waɗannan bil'adama ma'abota taurin kai da GAJEREN KWANA,
kuyi sani cewa haƙiƙa kun tafka babban kuskure da kuka kuke tsammanin cewa zaku iya ɗaukar ƙoƙon kan mai girma Mannaf kuma har ku fita a raye,
Ina mai tabbatar muku dacewa dayan ku bazai fita a raye ba,
Kafin aljanin ya gama rufe bakin sa Husnat ta tari numfashin sa tana mai daka masa tsawa tace
"Kai tsohon maketaci kuma azzalumi la'anannan Allah kayi sani cewa,
Ka sani cewa ai babu mai kashe wa face Ubangijin musulunci,
Da yardar sa zamu ga bayan ka sannan samu abinda muka fito nema.
Sa'adda ɗan wadan aljanin yaji wannan batu daga bakin Husnat sai ya fusata ainun idanun shi su ka kaɗa su ka yi jawur, gashin jikin shi ya mimmiƙe ya dubi Husnat yace "Na rantse da gemun mai gidana boka Mannaf sai nayi gunduwa-gunduwa da sassan jikin ki ta yadda ƙananan tsuntsaye zasu ji daɗin tsatstsagar naman ki,
Domin hakan ya zamo darasi ga bil'adama masu tsarin idanu irin ki,
Kafin Husnat ta sake cewa wani abu Aljanin ya ɗaga gatarin sa izuwa sama ya falfala da azababban gudu izuwa kan ta yana ihu da kururuwa mai firgita DANDAZON MAYAKA
Komai tsakanin yawan su,
Koda ganin hakan sai Husnat ta kwala kabbara da ƙarfi tare da zare takobin ta ta ruga izuwa gare shi,
Su na haɗuwa suka ruguntsume da azababban yaƙi mai matukar kwarjini daban sha'awa,
Su duka biyun suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta tagaban kwatance,
Wohoho haƙiƙa masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce idan gwani ya haɗu da tsohon ƙashi , juriya da jarumtaka suka game a waje guda dola ne artabu ya zamo tashin hankali,
Gaskiyar masu iya magana da suka ce fadan da yafi karfin sai ka koma ɗan kallo,
Hakan ne yafaru da hilwas, Kahzib da Sharwas domin koda suka ga cewa Manyan GWARAZAN JIYA sun kacame da azababban yaƙi sai suka koma izuwa inda dawakan su suke suna hangen abinda ke wakana,
Sai da aka shafe tsawon Sa'a ɗaya ana wannan fafatawa amma aljanin bai samu nasarar taɓa jikin Husnat ba,
A zahiri ga wnada yake kallon yadda artabun ke wakana sai tabbatar da cewa aljanin ya nuna ka Husnat a karfin damtse,
Sai dai ita ta fi shi salon kwarewar yaƙi,
Al'amarin da ya fusata shi kenan ya kaiwa Husnat wani bahagon sara da gatarin sa sa nufin tsarga ta gida biyu,
Cikin wani irin baƙin zafin nama Husnat ta wurkila tare da zamewa,
Gatarin aljain ya sari iska, koda aljanin yaga cewa yakasa samun nasarar hallaka ta sai ya shiga aika mata miyagun sihiri kamar ,kibbau, duwatsu,mashi da sauran su,
Amma Dazarar sun doshi inda take sai su narke su zama ruwa su ɗige a ƙasa,
saboda addu'o'in da take karantawa na neman tsari a a gare sa,
Da kyar da siɗin goshi ta samu ta hallaka aljanin ta hanyar soka masa takobi a ƙahon zuciyar sa.
Kuma ta ƙone shi ƙurmusa ta hanyar karanta masa ayatul-kursiyyu,
Haƙiƙa su Bawa hilwas sun ga iko da ƙidira ta Ubangijin talikai bisa ganin yadda Husnat tayi masara akan aljanin,
Bayan an fito da abin guzuri an yi kalacin rana. Sai kowa ya sake kama linzamin dokin sa ya hau ya sakar masa linzmai a ka cigaba da tafiya domin fi cewa daga dajin kushuful-fannar.
Mu haɗu a Littafi na 12 don cigaban wannan labari
Marubuci
MANSUR USMAN SUFI
mansurusmansufi@gmail.com
Kangin Bauta 14
Rubuta labari
MANSUR USMAN SUFI
08137237071
A wannan karon da aka fara wannan tafiya sai fira ta ɓarke tsakanin su jarumi Hilwas,
Domin a wannan karon sun samu nutsuwa a zukatan su cewa jaruma Husnat za ta cika musu dukkan burikan su bisa taimakon Ubangijin ta,
Gaskiyar masu iya magana da su ka ce sannu sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba'a je ba, sai gashi an shafe tsawon kwanaki ashirin da uku ana wannan tafiya,
A ranar kwana na ashirin da huɗu ne da la'asar aka iso birnin Baitul-na'im,
Tun daga nesa aka hango kofar birnin cike da miyagun dakaru ɗauke da miyagun makamai, Al'amarin da ya sanya su hilwas su ka sha jinin jikin su kenan,
Domin da gani ruwa baya tsami banza, don haka sai hilwas ya ɗauki sandar sihiri ya sanya ta a kirjin sa ta yadda babu komai wanda zai iya gane ta,
Kuma ya ɗauki ƙoƙon kan boka Manaf ya sanya shi a cikin wata jaka ya rataya a gadon bayan sa, Sannan ya zare takobin sa. Da ganin hakan sai Kahzib ya zare kwari da bakan sa,
Sharwas ya ciro mashin sa ya rike a hannu, Husnat riƙe da takobin ta aka durfafi kofar birnin Baitul-na'im,
Yayin da ya rage saura taku talatin tsakanin su da kofar birnin. Sai kawai aka ji wani ƙara daga cikin birnin sai kofar ta buɗe, Sai ga sarki shardasu, yarima kinzaru da sarkin yaƙi hatyal, Waɗansu irin girɗa -girɗan dakaru na take musu baya,
Bisa tsakiyar dakarun mahaifan su hilwas me maza da mata sanye cikin sararin baƙin ƙarfe hannu da ƙafa,
Koda ganin hakan sai su hilwas suka ja linzamin dawakan su suka sauko ƙasa, Suka durfafi in da su sarki shardasu suke domin tarar juna,
Sa'adda sarki shardasu yarima da sarkin yaƙi suka yi arba da jaruma Husnat sai hantar cikin su ta kaɗa da karfi tsoro ya ka masu.
Sarki shardasu ya tambayi kansa a cikin ran sa shin wace ce wannan bakuwar jaruma?
Shin ya akayi halarar tsafi na bata bayyana mini ita ba a lokacin da na gudanar da bincike akan su hilwas ɗin,
Amsar tambayar da sarki shardasu ya kasa bawa kanshi kenan, Amma saboda kada yarima da sarkin yaƙi su fahimci wani abu sai
Kawai ya shiga sakar wa su hilwas murmushi mai taushi,
Amma har a lokacin zuciyar shi bugawa take da karfi tamkar zata faso cikin kirjin shi ta fito waje,
Abin da bai sani ba shine kamar yadda ya kamu da tsoron haka yarima da sarkin yaƙi su ka kamu dashi,
Yayin da ya zamana an iso daf da juna sai sarki shardasu ya dubi su hilwas cikin annurin fuska tamkar wanda aka bawa SARAUTAR DUNIYA ya buɗi baki yace "lale marhaban da zuwan JARUMAN DUNIYA sai a yau ne na tabbatar da cewa kun cika MAZAJENI DUNIYA kuma GWARAZAN JIYA da babu kamar ku a wannan KARSHEN ƘARNI,
yaku waɗannan jarumai kuyi sani cewa a yau ne zan cika muku alqawarin da na ɗaukar muku na baku yanci da mahaifan ku daga KANGIN BAUTA a karkashin iko na,
Don haka yanzu sai ku danƙamin sandar sihiri da ƙoƙon kan boka Mannaf,
Koda jin wannan batu daga bakin sarki shardasu sai hilwas ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da wasikar mutuwa ya dubi Sarki yace " ya shugabana ni da yan uwa mun amince zamu damƙa maka abubuwan da ka buƙata amma bisa sharaɗin cewa bazaki yaudare mu ba,
Idan kuwa har ka saɓa alkawarin zamu bar ka tare da wannan jaruma ta yanke maka hukunci dai dai laifin da ka aikata,
Kuma sai mun rushe mulkin zaluncin ka daga doran ƙasa,
Koda jin hakan sai sarki shardasu yace na amince da sharaɗin ku,
Da jin haka sai hilwas ya ciro sandar sihirin boka kimraz tare da ƙoƙon kan boka Mannaf ya miƙa wa sarki shardasu ya sa hannu ya karɓa zuciyar cike da matukar farin ciki,
Kawai sai ya nuna dakarun dake bayan sa da ɗan yatsan shi na hagu take su ka ɓace ɓat kuma sasarin ɗaya daure mahaifan su hilwas ya ɓace a daga jikin su,
Cikin matukar farin ciki maral misaltuwa hilwas, Kahzib da Sharwas, suka ruga izuwa in da mahaifan su suke domin tarar juna.
Yayin da ya rage saura kamar taku goma sha biyu a tsakanin su sai sarki shardasu ya yi nuni da hannun sa izuwa wajen take wata ƙarama ta tafasasshiyar darma ta bayyana a tsakanin su ta yadda babu damar su haɗu da juna,
Sannan sarki shardasu ya ɗauki ƙoƙon kan boka Mannaf ya sanya kansa take ya ya zauna a kan tamkar ya saka hular ƙarfe.
Ya riƙe sandar sihirin a hannun sa gami da bushewa da dariyar mugunta, Yarima kinzaru da sarkin yaƙi su ka yi koyi dashi,
Daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da wasikar mutuwa ya dubi su hilwas a lokacin da hawayen takaici ke zuba daga idanuwan su,
"Haƙika yaro man kaza ne bai san wuta ba sai ta nar ka shi, kuma tabbatar duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka,
Yanzu kuna tsammanin cewa zan barku a raye ne,
Ku sani cewa a halin ku da mahaifan ku baku da wani amfani a waje na,
Yanzu batare da ɓata lokaci zan hallaka waccan jarumar da kuke takama da ita,
Koda Gama faɗin hakan sai sarki shardasu ya daga sandar sihiri izuwa sama ya kwarara wawan ihu sannan ya falfala da azababban gudu izuwa kan jaruma Husnat,
Koda ganin hakan sai bawa hilwas ya riga izuwa kan yarima kinzaru, Kahzib da Sharwas kuwa suka tari sarkin yaƙi hatyal, rike da makaman su,
Lokacin da aka haɗu da juna sai aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matukar kwarjini daban sha'awa.
Ɓangarorin uku suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta tagaban kwatance,
Wohoho haƙiƙa masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce idan gwani da gwani suka haɗu a yaƙi juriya da bajinta suka game waje guda dola ne yaƙi ya zamo tashin hankali daban tsoro.
Sai da aka shafe tsawon Sa'a ɗaya cur ana wannan artabu,
Tabbas a wannan rana Allah ya nuna ikon sa domin Husnat ta samu nasarar hallaka sarki shardasu ta hanyar karya masa waya,
Amma ita ma tasha matuƙar wahalar gaske,
Hilwas da Kahzib suma sun kashe abokan gabar su,
Amma sai da Husnat ta kai musu ɗauki bisa taimakon Ubangiji,
Tabbas inda ace mutum yana tsaye a wannan waje zai ga yadda gawar sarki shardasu ke kawance a ƙasa cikin ƙaskanci da wulakanci dole ne ya gode wa Allah bisa ganin yadda ya kawo KARSHEN ZALUNCI da azzalumai.
Koda samun wannan gagarumar nasara sai wannan ƙorama da ta raba tsakanin su hilwas da mahaifan su ta ɓace ɓat tamkar bata taɓa wanzuwa ba.
A sannanne su hilwas suka ruga izuwa inda mahaifan su suke suka rungume juna suna masu zubar da hawayen farin cikin.
Al'amarin da ya sanya Husnat dake tsaye a gefe guda ta kamu da matukar tausayin su kenan har kwalla ta zubo mata,
Daga can sai ta taka da kafafun ta har zuwa inda suke ta durƙusa kasa bisa gwiwar ta ta dube su cikin tausaya tace "yaku waɗannan jarumai kuyi sani cewa a yanzu ne zan cika alkawarin da na ɗaukar muku na warkar da mahaifan ku bisa taimakon Ubangiji na,
Koda Gama faɗin hakan sai Husnat ta fito salkar ruwan ta ta kofa ayatul-kursiyyu da falaƙi da nasi,
Ta umarci mahaifan su Kahzib maza su shanye ruwan. Haƙiƙa tsarki ya tabbata ga Ubangiji maɗaukakin sarki,
Faruwar hakan ke da wuya sai idanun mahaifin hilwas suka buɗe garau yana iya ganin komai, Mahaifin kahzib kuwa bakin ya buɗe ya dawo yana iya magana tar-tar.
Sharwas kuwa duk kuturtar dake jikin mahaifin shi ya warke jikin sa yayi kyau sumul,
Batare da bata lokaci ba su hilwas da mahaifan su suka karɓi kalmar shahada a wajen Husnat
Sannan aka dunguma izuwa cikin birnin Baitul-na'im aka musuluntar da kowa dama sun gaji da mulkin sarki shardasu,
Bayin dake kurku kuwa aka fito dasu aka basu yanci. Nan fa gari ya kaure da shewa da murna,
Kashe gari tun da duku-dukun safiya aka shiga shagalin nadin sarautar bawa hilwas a matsayin sabon sarkin birnin Baitul-na'im,tare da auren sa da gimbiya lashmira,
Kahzib a matsayin waziri, hilwas a matsayin sarkin yaƙi tare da daura auren su, Kahzib da gimbiya shuraima yar sarki Husubul-Dinar,
Sharwas da jaruma Husnat, daga wannan rana aka rushe KANGIN BAUTA kowa ya samu 'yanci gaba ɗaya jama'ar birnin suka kasance cikin matukar farin ciki maral misaltuwa,
Hasken musulmi ya mamaye ko ina a nahiyar baki ɗaya
Alhamdulillah
Ƙarshe
Daga mai ɗebe muku kewa a kullum da ko yaushe
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin marubutan Yaƙi
08137237071