Showing 12001 words to 13939 words out of 13939 words
Chapter 5 - KANWAR UWA CE KO KISHIYA UWA New Hausa Novels Complete by .txt
sosai,, karka damu aikinane""
D'akin da aka kwantar da Zuwaira ya nufa, har angama gyara ta tsaf, angyara gadon, tana zaune abakin gado sai faman hawaye takeyi, yajawo kujera ya zauna gabanta kinga ki kwantar da hankalinki babu wata matsala likita yace anjima kad'an xa asallamemu ma.
Hajja tace nima tun d'axu nake lallashinta Alhaji nafad'a mata babu wata matsala, yasa hannu yana share mata hawaye, kinga bari naje nasa momiki abinci.
Dadaddare aka sallamesu suka koma gida.
"Suna isa Sultan ya wuce d'akinsa yashiga wanka,, itama zuwaira wankan hajja Rabi tasata tayi,, Sultan yagama wanka ya shirya cikin k'aramar riga tashan iska da wando iya gwuywa, yad'au ledar daya shigo da ita yafita""
Zuwaira na zaune bakin gado ta rabga tagumi, Sultan ya shiga da sallama gefenta ya zauna, yana fad'in har yanxu tunaninne dai?? Ta juyo tana kallonsa, yaune karo nafarko arayuwarta data kalli Sultan sosai, ya hura idanunta tai saurin yin k'asa da kai, ya jawo ledar daya shigo da ita yafito da always da sababbin pants gawanna kiyi amfani dashi kamar yanda aka nuna miki a asibiti,, sannnan ki kwantar da hankalinki bawani ciwone yasamekiba, jinin haila ne yazomiki.
Tai shiru tana saurarensa, can kuma tace miye jinin haila ??
""Karki damu xaki sanshi nan bada dad'ewaba, amma saikin shiga islamiyya, yanxu dai tashi kije ki saka wannan kizo ki kwanta dare yayi..............✍🏻
🎯Bily🎯
🍀Mrs Abdus'salam🍀
I💓U MY FAN's
[10/25, 3:14 PM] +234 809 777 0370: 4~ August~2016
💎3⃣3⃣💎
💎💎💎
🎯K'ANWAR UWACE🎯
ko
🎯KISHIYAR UWA❓🎯
💚NA BILLKISA IBRAHIM📝
»« a yaune ikeerama zata dawo, Sultan kwance kan gado yana sak'a da warwara,, yasan ikeeram sarai akan kishi,, ga shi kuma kishiyar taxo mata alokacin datake tsananin gudunta, yajuya kwanciyarsa zuwa rigin gine, dolene yashirya matakan xama da ikeeram ayanzu, dan tagane da da yanzu akwai bam banci,, ya mik'e yashiga wanka,, gayu yaci cikin blue na wando, da farar riga mai gajeren hannu,, ya d'ora tafkekiyar rigar sanyi jaa, saboda yanayin garin, yayi k'yau sosai,, yafito yana k'amshin turare mai dad'i.
Bakowa a palon sai dai yasha gyara ga kamshi natashi,, yanufi d'akin Zuwaira, da sallama yashiga tana zaune a saman dirowan gefen gado tana game a wayarta, ta d'ago kai tana amsa masa sallamar,, yazauna gefen gadon yana fad'in lallai jiki yayai sauk'i harda su game.
"Ta sakko k'asa tana dariya, ta durkusa tana gaidashi cikin girmamawa."
Ya amsa yana tan bayarta lfyr ta?
Tace ta warke aii,, ince dai kinci abinci?? Ta girgixa kai nak'oshi sai anjima,, A'a ban yarda ba tashi muje kici abinci kisha maganinki,, dole tamik'e sukaje, bayan sun gama yabata magani tasha.
""Yace"Juwairiyya yau matata xata dawo kakarta ta warke,, a raxane tad'ago tana kallonsa, saikuma tamaida kanta k'asa idonta cike da hawaye, yasa hannu yad'ago hab'arta Juwairiyya miyasa kike kuka??
Cikin muryar kuka tace ina jin tsoro wlhy.
Ya kamo hannunta ya rik'e, kibar jin tsoro Juwairiyya in sha ALLAH babu abinda xai faru, tundama ba gidanku d'ayaba, ya share mata hawaye, kinga bari naje karfe 10:30 jirginsu zai sauka, gashi kuma goma ta yi,, ina hajja?? Cikin rawar murya tace tana d'akinta,, to idan tafito kice mata na wuce,, cikin sanyi jiki tace to saika dawo.
Bayan fitarsa, ta fashe da sabon kuka,, lallai maraici yasa tana ganin taskun rayuwa,, atunaninta sauk'i yazo mata ashe shagala tayi tamanta k'alubalen dake gabanta, itakam taga takanta.
Hajja dake fitowa daga d'aki, tai saurin cewa 'yarnan lfy dai ko ?? Ko jikin nakine ??
Cikin kuka tace hajja nashiga uku,, dan ALLAH kice ya maidani gida, ALLAH hajja tsoro nakeji.
"" hajja ta zauna kusa da ita kinga bar kuka kimin bayani,, fad'a kukayi ??
Ta girgixa kai, yace yau matarsa zata dawo, nikuma ALLAH hajja tsoro nakeji, kinga ita 'yar birnice, kuma tayi karatu irin na 'yan birni.
"" to kukan ya isa haka, ki kwantar da han kalinki,, kema mijinki yace min xai saki makaranta, kuma nayi alk'awarin koya miki duk abida baki iyaba, wlhy Zuwaira jinki nake tamkar d'iyar dana haifa acikina, nasan zafin kishi, domin kuwa adalilin kishiya narasa d'iyata d'aya tilo, ta share hawaye, karki damu tunda mijinki yana sonki in ALLAH ya yarda babu abinda zai faru, haka taita lallashinta har tai shiru................✍🏻
4~ August~2016
💎3⃣4⃣💎
💎💎💎
🎯K'ANWAR UWACE🎯
ko
🎯KISHIYAR UWA❓🎯
💚NA BILLKISA IBRAHIM📝
»« Shikam Sultan gidan ummy yanufa,, suna zaune apalo itada gwaggo suna hira, ya shiga da sallamarsa, suka amsa masa, ya russuna ya gaishesu, suka tanbayeshi iyali da hajja, yace sunan nan lfy.
""Ummy dama naxo nasanar daku yau ikeeram zata dawo,, ALLAH sarki to ALLAH ya saukesu lfy,, yace amin,, auta saidai wani hanzari ba guduba,, kasan matarka bata san da maganar auren kaba to ka nutsu ka lallasheta,, karkace zaka gwada mata k'arfi, dan kishi xafine dashi,, karki damu ummy xan kiyaye in sha ALLAH,, nan sukai ta masa nasiha, sannan ya nufi filin jirgi.
K'arfe 10:30Am dai dai jirgin su ikeeram ya sauka,, ko kunyar iyayenta bata jiba tazo ta rungume Sultan, ta sumbaceshi akumatu,, nayi missing d'inka my lovely Prince, yay murmushi ikeeram baki ganin su mom naki, ta kallesu sannan tadawo da kallonta kansa to aii su suka baka da hannunsu,, ko bakayi missing d'inaba ne ?? Yay murmushi nayi mana sosai, yafad'a yana matsa hannayenta, kin k'ara k'yau matata,, tai dariya kaima aii haka ka k'ara k'yau da k'iba, ummy tana kula min dakai sosai,, azuciyar sa, yace wannan kulawar My Sweet Juwairiyyace, bata ummy ba, tajasa zomuje ku gaisa dasu mom sai mu wuce gida,, yace" kai haba basai mun rakasu gidaba??
"" har k'asa ya durk'usa ya gaida su mom,, haj maryam, kakarsu tace me gida mika tanaxar minine,, dan nadawo da kwad'ayi,, Sultan yay dariya karki damu Hajiya sai abinda kika xab'a xakici,, tunda ALLAH yasomu baki gangara ba,, aii danafi kowa banuwa, na rashin uwargida,, gaba d'aya sukasa dariya,, dadyn ikeeram yace lallai Sultan maman nawa kakeso ta gangara, sai dai idan taku ta tafi, ya nuna mom,, A'a dady aii ita da sauranta,, hajiya kuwa ta more duniyar dayawa,, nanma dariya sukayi,, kafin dady yace kaga Sultan kuyi tafiyarku gida ku huta zuwa gobe kwazo ku k'ara ganinta,, dole suka hak'ura suka tafi bayan yabama hajiya manyan ledoji guda biyu na tarba.
Tunda suka iso yaga yanayin ikeeram kamar ba itaba, kamar ta canja halayenta,, kokuma ta lullub'e saboda missing d'inka datayi ba,, wata zuciya ce ke shaida masa haka.
"Yinin yau agida ya cinyesa tareda ikeeram,, tanata bashi labarin xamansu na Egypt, saida magriba ya tafi SALLAH, daganan ya sub'uto zuwa gidan Zuwaira.
Tana zaune a palo ita kad'ai tana kallon wani hausa film na ibro, amma tunaninta yana kan Sultan, tunda safe daya fita bai sake zuwa gidanba, ko wayarta bai kiraba duk yau,, ko lfy??
"K'amshin turarensa yadawo da hankalinta,, yana tsaye jikin k'ofa, ya rungume hannayensa ak'irji, k'afafunsa hard'e da juna, ya kafa mata manyan idanunsa farafe masu launin zaiba.
Da sauri tatashi xaune tana fad'in sannu da zuwa yaushe kadawo??
Yak'araso gareta yaxa ayi kisan dawowata kina duniyar tunani,, miye damuwarki ??
Tace"bakomai naga tun safe daka fita baka dawobane kawai,, ALLAH yasa dai lfy??
Lfy lao,, kawai dai ina tare da yayarkine.
Batace komaiba,, yace ina hajja?? Hajja tafito tana fad'in ganinan Alhaji kadawo??
Eh hajja, ya gaisheta,, ta tanbayesa ikeeram yace"tadawo lfy, tana gida,, yace " hajja ga Juwairiyya nan dan ALLAH ki k'ara kula min da ita,, dan yau acan gidan zan kwana,, dan ALLAH karki barta tashiga damuwa,, inason dai daita al amurane.
To Alhaji karka damu, in sha ALLAH babu abinda zai faru.
""To nagode hajja,, yabata kud'i ga wannan ki ajiye ahannunki hajja saboda gudun matsala, hannu biyu tasa ta karb'a tai godiya, sannan tatashi tanufi d'akinta.
Yadawo da kallonsa kan Zuwaira,, kiyi hak'uri Juwairiyya,, in sha ALLAH komai zai dai daita, nibari natafi, dare nayi ga wannan ki ajiye ahannunki kema.
Ta girgixa kai kabarsa kawai nawajen hajja sun ishemu, A'a na wajan hajja da ban wannan daban, tashi muje narakaki d'akinki.
Har d'aki yarakata yakuma lallashinta sannan ya tafi, itafa ba kishi takeba dan batasan ma miye kishinba,, tanajin tsoron shan wahalane kawai..............✍🏻
4~ August~2016
💎3⃣5⃣💎
💎💎💎
🎯K'ANWAR UWACE🎯
ko
🎯KISHIYAR UWA❓🎯
💚NA BILLKISA IBRAHIM📝
»« Yaukam ba k'arya Sultan da ikeeram ansha soyayya, ya yarda tayi missing nashi dagaske, shikam dama ayunwace yake,, dan haka bai zauna jiran ya huceba,, bare rabon wani ya gifta.
Da safe dole yaje yasiyo musu abinci,,dankuwa gimbiyar tasa barcinta take kwasa,, saishi tadamesa da k'orafin yunwa takeji,, shikam kunyar zuwa sayen abinci yakeyi,, bakuma zai iya zuwagidan ummy neman abinciba, sai kawai yanufi gidan Zuwaira,, kamar yanda suka saba yauma gidan tsaf yanata tashin k'amshi ya shak'a ya lumshe ido,, hajja ta fito daga kichin hannunta rik'e da kula,, yace "sannu hajjarmu.
Tai dariya yauwa sannu Alhaji kaine da safe haka,, wlhy kuwa hajja nine kun tashi lfy??
Lfy lao, ya iyali??
"Lfy lao wlhy,, ina mutuniyar??
Tana d'aki yanxu taje tayi wanka,, to, babu wata matsala dai ko??
Wlhy bakomai lfy muka kwana.
""To Alhmdllh""
Ya shiga d'akin tana zaune bakin gado tana shafa mai ajiki,, tai saurin xamowa k'asa tana gaisheshi ya amsa cikin sakin fuska, yatan bayi jikinta, tace ai tawarke,, ringing d'in wayarsa yadawo dashi hankalinsa,, ikeeram ce, ya d'auka, Sultan kaifa nake jira wlhy yunwa nakeji,, to yi hak'uri ganinan zuwa.
"Ya kalli Zuwaira zamu sami abincin mutum biyu agidannan,, zuwaira ta amsa da eh xa'a samu,, to bani.
Taje ta kawo masa kayan abincin acikin wani d'an kwando,, rufe da k'yalle.
Yauwa 'yar albarka nagode miki, bari naje anjima zan dawo.
Ita batace komaiba tadai bishi da kallo kawai.
A palo yatarar da gimbiyar tasa tana jiransa,, kayan barcine ajikinta,, ya ajiye kwandon yana fad'in kin tashi?? eh mana kace haka, tunda katafi kabarni da yunawa.
""Humm waike randa yara sukaxo yaxakiyi ne?? Haka xan ringa bin gidajen sayen abinci"
Ta ya mutse fuska,, to kai an gayama zan haihune yanxu,, duk nabi na tsufa,, abi adameka da kiran momy momy,, kasa aranka sainan da shekara 6 xuwa7 zan haihu.
" kai haba wasa dai kike,kinsan kuwa yanda nakeson yara,, aiko dai sai karage,, dan kuwa nidai ayanxu baxan haihuba,, natsufa abanxa awofi,, tafad'a tana mik'ewa,, sai ina kuma,, gara naje d'aki dan nakula nema sani surutu kakeyi.
Ya tab'e baki matsalarkice 'yammata nanbada dad'ewaba xan gayyaceki sunan d'ana ko d'iyata,, kimace har duniya tatashi baxaki haihuba, banida matsala da hakan...............✍🏻
🎯Bily🎯
🍀Mrs Abdus'salam🍀
I💓 U MY FAN's
?