Header Ads
Showing 9001 words to 12000 words out of 13939 words

Chapter 4 - KANWAR UWA CE KO KISHIYA UWA New Hausa Novels Complete by .txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

murmushi, sai dai tabasa tausayi baiso ya aikata haka garetaba, bayaso ta d'aukeshi masifaffe, ya bud'e mata murfin motar to fita muje ko.
Cikin sanyin jiki tafita lokacin har anfara yayyafi, yad'auki d'an kwandon da kulolin abincin suke ciki da wata leda, ganin ta tsaya kallonsa sai kawai yaja hannunta, batare da yayi maganaba, yabud'e kofar palon suka shiga, kai jama'a palonnan fa ya had'u aradu kuwa.


Ya zauna ad'aya daga cikin kujerun yana fad'in wash ALLAH, itakam Zuwaira k'asa ta zauna ad'arare, da sauri yace haba Juwairiyya keda gidanki ki zauna k'asa maxa tashi ki hau kujera, dayake atsorace take dashi saita tashi da sauri ta hau kujerar dake kusada k'ofa.
""Ya kalleta ya girgiza kai lallai yanada aiki agabnsa, dankuwa ya lura saiyayi Raino, saiya tuna ikeeram adarensu na farko itace ma ta taimaka burinsa ya cika, amma daga baya saita gujeshi alokacin dayafi buk'atar taima konta, harta jashi dayin aure biyu, abinda baya cikin tsarinsa, lallai yayi dana sanin d'aukar Zuciyarsa yabama Ikeeram.
Wata tsawa da akayi tadawo dashi hayyacinsa, ya mik'e ya nufi kichin, itadai Zuwaira batasan wainar dayake toyawaba ma, dan tuna ninta yana kusada.
"Ya fito hannunsa rik'e da filed da kofuna, ya zauna ya zuba abincin da abinsha, zuwa yay yakamo hannunta batare dayayi mata maganaba, ya zaunar da ita, abinci yad'ebo acokali ya nufi bakinta dashi da sauri ta matsa baya.
Yace" yaya dai ??
Cikin rawar murya tace inna karima tace mana kar mu yarda namiji yabamu abu abaki, iskanci ne.
""Tofa Sultan yafad'a yana gyad'a kai, lallai da sauran aiki, a fili sai yace to d'auka kici da kanki, amma banda wasa, inba hakaba kuma toh ya cije leb'ensa na k'asa.
Ta d'anci abincin saboda tsoronsa datakeji, jama'a bafa tsoro da amare sukeyiba, dan ita Zuwaira bama tasan wannanba.
Shima yaci yace " to tashi narakaki d'akinki ki kwanta ko ??
Tamik'e yarakata wani d'aki dayaji kayan gado na alfarma, to kinga ga d'akinki nan, ni bari naje nakwanta saida safe, tace "ALLAH ya kaimu.
Har ya fita yadawo kinga na manta na nuna miki bayi, ya nunnuna mata duk abinda ya kamata, yace bak'ya jin dai tsoro ko?? Tace"eh.
""To shikenan saida safe yafad'a yana fita.
Bayan fitarsa ta sake ganin ko ina, wai yau itace awannan d'aki wai kuma nata, ta tuna gidansu akan wata tsohuwar karaunin tabarma take kwana, ko abin lullub'a babu, ita kam ba abinda xatace da ALLAH sai godiya, saidai abinda yake bata mamaki ance tanada kishiya amma har yanxu tunda aka kawota bataga kishiyarba, kotana ina ?? Haka dai ta kwanta batare data cire kayan jikintaba, barci yay awon gaba da'Ita.


Shikam Sultan yana d'akinsa ya kasa barcin sai sak'a da warwar yakeyi, yasan dolene yay hak'uri da yarinyar nan sai xuwa wani lokaci, ga matsalar ikeeram, dan yasan bala'inta da k'in da takema kishiya, tunkan suyi aure ko hira suke yay maganar kishiya to saitayi sati bata fito wajansaba koda yaje gidansu, to bare yanxu ace ammata, kuma bata saniba lallai da cakwakiya kam....................✍🏻




🎯Bily🎯
🍀Mrs Abdus'salam🍀
I💓U MY FAN's
[10/25, 2:57 PM] ‪+234 809 777 0370‬: 29~ july~2016
💎2⃣8⃣💎
💎💎💎
💎💎
💎2⃣9⃣💎
💎💎💎
💎💎


🎯K'ANWAR UWACE🎯
ko
🎯KISHIYAR UWA🎯


💚NA BILLKISA IBRAHIM📝




»« KUSADA :- inna Asabe antashi, sai dai saboda bak'in cikin da zuciyarta take ciki takasa magana, wannan yasa bikin Atika baiyi wani arbashiba sosai, bayan 'yankai Zuwaira sun koma gida labari yacika gari akan gidan Zuwaira da mijin data aura, wannan lamari yak'ara gigitar da inna Asabe, takuma d'au alk'awarin tar watsa auren Zuwaira, tofa ashe dasauran cakwakiya kudai biyoni.


🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Katsina kuwa yau kwanan Zuwaira hud'u da angon nata, sai dai tak'i sakin jiki dashi ko kad'an, hasalima tsoronsa takeji, idan yana palo tana d'aki sai dai shi yashiga d'akin yasata taci abincin da ummy ta aiko musu, to gashi hutun da akabasa a office gobe zai k'are, yashafa sumar kansa yana mai fidda huci, yakamata yanemo hanyar dazata ringa kusantashi da yarin yarnan, dan bayaso taci gaba dajin tsoronsa, ya kalli wayarsa datake ta faman ruri yaja tsaki, ikeeram ce keta faman kiransa amma yak'i ya d'aga, dan yasan matsalarta bata wuce ta atura mata kud'iba, mai makon yad'auki wayar sai kawai yaxari mukullin mota da wayar yafice abinsa.


Gidan ummy yanufa bayan sun gaisa damai gadi yay masa alkairi kamar yanda yasaba yanufi cikin gidan ummy na zaune dawata dattijuwa suna kama da ummy sosai, sunata hira abinsu, yay sallama suka amsa, ummy tace ango kasha k'amshi yay d'an murmushi yana sosa gefen kansa da key d'in mota.
"Ya kalli dattijuwar nan yace" wlhy gwaggo dama kinyi zamanki anan kyaringa d'ebema ummy kewa tunda acand'imma babu abinda kikeyi.
Ummy tace wlhy nima auta haka nace tunjiya nake rok'onta amma tak'i, yace " kai gwaggo dan ALLAH ki zauna damu mana, gwaggo tai dariya to shikenan karkai kuka xan zauna, cikin farinciki yaje ya rungume gwaggo, suna masa dariya.
"""Bayan sun lafa da dariyar yace " ummy gobe idan ALLAH yakaimu xan koma wajen aiki, gashi inada fasinja zuwa GERMANY, bansan yanda zanyi fa Juwairiyya ba"""
Ummy tace"nima tuni wannan tunanin yana raina, dole sai dai anemo wata tsohuwa daxasu xauna dan ta rink'a d'ebe mata kewa.
" ummy asamo mai d'an k'arfi wadda zata taimaka da koya mata wasu abubuwan.
"Gwaggo tace"wannan kuma aikinane akwai wata hajja Rabi a saudiyya suka zauna da mijinta to bayan rasuwarsa saita dawo gida, to nakula xaman k'auyen bata jindad'insa tunda bata sababa, ita kawai yakamata ad'akko nasan zaku k'aru da ita sosai"
Ai gwaggo duk yanda kikace dai dai ne kinga kawai saiki shirya yanxu muje mu d'akkota kema ki had'o kayanki.
ummy tace wannan shawara tayi, saikuje d'in Salamatu, to shike nan yaya bari naje na shirya.


Sun isa garin matazu, garinda gwaggo take kenan, kuma sun sami nasar d'akko hajja Rabi, ana kiran magriba suka shigo cikin garin katsina, gidansu ummy suka nufa, ummy tayi farincikin ganinsu da hajja Rabi, anan yabarta yatafi gida sai gobe in ALLAH yakaimu xa'a kaita gidan Sultan.
"Yashiga palon da sallama, Zuwaira na xaune tsakanin kujeru ta mak'ure guri d'aya, jikinta sai rawa yakeyi, da sauri Sultan yak'arasa gareta yana fad'in Juwairiyya lafiya?? Yasa hannu ya d'ago fuskarta duk ta b'aci da hawaye, miya sameki ?? Yasake tambaya akaro na biyu, cikin sark'ewar murya tace tsoro nakeji."
Ya d'agota ya zaunar saman kujera shima ya zauna kusa da ita, Juwairiyya kinga wani abin tsorone??, ta girgixa kai, kawaidai inajin tsorone, yasa hankacif yana goge mata hawayen to ya isa haka kukan yi hak'uri kiji, naje samomiki wadda zaku zaunane, in sha ALLAH daga yau baxaki sake jin tsoroba kinji, ta d'aga kai cikin sanyinta.
"Kinyi SALLAH dai ko?? Ta girgixa kai alamar A'a, ya mik'ar da ita to tashi muje kiyi SALLAH ko"
Har d'akinta yarakata tashiga bayi tayo alwala tafito yana zaune abakin gado yana kallonta, yanda tayi sallar ya birgeshi dankuwa gyara kad'an za aimata aciki, insha ALLAH zai nemamata school tafara zuwa, kwananan.


Bayan ta idar, yace"Juwairiyya?? cikin sanyinta tace na'am, ya gyara zama, gobe idan ALLAH yakaimu wadda zaku xauna xataxo sunanta hajja Rabi, saboda yanayin aikina, yau inacan gobe inacan, gakuma binda ban tab'a sanar dakeba shine inada mata, sunanta ikeeram, yanxu bata k'asarnan tana Egypt jiyyar kakarta dabata da lfy, tokinga wataran ina gidan ta dan ba gidanku d'ayaba, kinga bazai yuwwuba nabarki ke kad'ai nasan ke yarinya ce tagari mai hak'uri, dankuwa tun aranar dana kusan tureki damota, harkikai asarar Awararki nakuma baki kud'i kika k'i karb'a sai iyana awarar shima dan bak'yaso ran innarki ya b'aci, ba k'aramin burgeni kikaiba gsky, wannan ya k'ara k'arfafamini son aurenki, gashi kuma ALLAH yabani yafad'a yana murmuhi.
""Yanzu nayanke sha warar nema miki makaranta dankema kisami ilmi na addini dana zamani, cikin tsananin farinciki ta dubeshi dan ALLAH dagaske ?? Yaune rana tafarko daya fara ganin fara'arta, ranar daya fara ganinta bata cikin natsuwarta, tunda kuma aka kawota gidansa tana cikin damuwa, cikin murmushi yace in sha ALLAH my Juwairiyy.
Gabansa taxo ta tsugunna tana masa godiya, yace"miyasa kike murna haka ?? Tace" inason karatu amma ban samuba dama inna karima tace in ALLAH yayar da wataran sainayi karatu, gashi kuwa ALLAH ya yarda, nagode ALLAH yajik'an mahaifa, ALLAH yak'ara bud'i.
Yaji dad'in addu"arta, dakuma mamakinta gata k'aramar yarinya sai wayo..................✍🏻




🎯Bily🎯
🍀Mrs Abdus'salam🍀
I💓U MY FAN's
[10/25, 2:57 PM] ‪+234 809 777 0370‬: 29~ july~2016
💎3⃣0⃣💎
💎💎💎
💎💎




🎯K'ANWAR UWACE🎯
ko
🎯KISHIYAR UWA❓🎯


💚NA BILLKISA IBRAHIM📝




»« washe gari dawuri yatashi yay shirin tafiya wajan aiki, yanufi d'akin Zuwaira tana bayi tana wankewa yay sallama yashiga, jin motsinta abayi yasa shi xaman jiran fitowarta, bayan kamar minti uku tafito, ta tsugunna ta gaidashi, ya amsa cikin sakin fuska, kiyi hak'uri 'yar aikinki tana nan zuwa munyi magana da ummy xa'a samomiki mai aiki, kanta ak'asa tace ai dama anbarsa zan iya, A'a ai aikin gidannan yay miki yawa, yafad'a yana mik'ewa bari natafi dan dawuri zamu tafi, sai gobe in sha ALLAH xan dawo.
To ALLAH ya tsare ya kiyaye hanya, amin Juwairiyya yashafi gefen fuskarta, bari naje su gwaggo su na nan zuwa inagama harda ummy, ya mik'a mata kwalin waya mai k'yau ga wannan in hajja tazo xata koya miki yanda akeyi, zan Runga kira muna gaisawa kinji, ta d'aga kai ido taf da hawaye, shima yakula da hawayen amma saiya basar dan baya son sata kuka, yabata key d'in d'akinsa gashinan idan kina buk'atar kud'i kije d'akina ki d'auka kinji, yay gaba batare dayajira ce wartaba, ta Window ta rink'a lek'ensa har yaja mota yabar gidan.
"Tadawo ta xauna tana hawaye, lallai rayuwa mai sauyi, idan ta tuna rayuwarta ada saitayita kuka, inda wani yace xata tsinci kanta awannan halin saita k'aryatashi, tabud'e kwalin wayar tana kallo, wayace mai kyau da tsada, ALLAH nagodemaka tafad'a tana hawaye, yanzu k'awarta Safare tanacan da innarta lallai tayi missing d'insu sosai, har inna Asabe datake bata wahala da k'annanta tayi kewarsu, jitake kamar tayi tsuntsuwa taje garesu, tanuna musu irin cigaban data samu.


Sai wajan k'afe 11:15AM su gwaggo sukaxo, amma ba ummy, taji dad'in zuwansu dan harta fara jin tsoro, takawo musu ruwa da lemo, ta tsugunna har k'asa ta gaishesu, bayan sun gama gaisawa gwaggo tai mata bayanin hajja Rabi, sannan tatafi tabar hajja Rabi anan.


++++++++++++++++++
Shikam Sultan yana filin jirgi, inda abokansa sukaita masa murnanar auren nasa, bayan sun koma gefe da Nazir, Nazir yace kai mutumina angwancin ya karb'eka kaganka kuwa har wani sharyning kakeyi saboda hutu.
Sultan ya hararesa kai dai wlhy d'an iskane Nazir, toni wlhy yarinyar nan ko d'aki d'aya bamu tab'a kwanaba bare gado d'aya.
""Nazir yasaki baki yana kallonsa kai wai dagaske kake??
Oh tunda muke dakai natab'a maka k'arya, aii da tausayi yarinyace k'arama yanxufa tashiga 15years.
Hummm kai dai kabarta ne kawai nikam in nine wlhy bawani d'aga k'afa.
Sultan yay dariya to kai dama aii sai dai addu'a ba tausayi kacikaba, kaga muje masinja sun gama shiga................✍🏻






🎯Bily🎯
🍀Mrs Abdus'salam🍀
I💓U MY FAN's
[10/25, 3:00 PM] ‪+234 809 777 0370‬: 2~August~2016
💎3⃣1⃣💎
💎💎💎
💎💎




🎯K'ANWAR UWACE🎯
ko
🎯KISHIYAR UWA🎯


💚NA BILLKISA IBRAHIM📝






»« Hummm Zuwaira ansamu abokiyar hira,, yau daka ganta zakasan tana cikin walwala,, hajja Rabi tsohuwar macece wadda tasan duniya,, dakuma saurin fahimtar matsalar mutane,, ko a saudiyya tana koyama mata yanda xasu zauna da miji,, dan tanada ilimin addini sosai,, yau d'aya data rayu da Zuwaira ta fuskanci abubuwa dayawa atare da ita,, yarinyar k'yak'yk'yawa ce,, lafiyayya rashin gatane kawai ya dakushe rayuwarta,, amma in sha ALLAH zata taimaka mata dan ganin taci ribar zaman aure.


@@@@@@@@@@@
Bari mu waiwayi inna asabe,, inna asabe an baxama bin malamai da bokaye,, dan ganin ta tsige Zuwaira agidan miji,, sai asarar kud'inta take,, duk kud'in data samu a wajan bikin sai mik'ama bokaye da malama tsubbu takeyi,, humm asara yawun barci🤑.


KIRA :- 'yan uwana mata yakamata ku gane wani abu,, boka ko malamin tsubbu babu abinda zasu iya yimiki,, hasalima saidai ki b'ata kiyi asarar kud'inki da imaninki,, domin babu masanin gaibu sai ALLAH,, shikan aikata asanda yaso akuma lokacin dayaso,, wanda kikaje gurinsa babu abinda zai iya tsinanma kansa bare ke yay miki,, asiri yana tasirine da ixinin ALLAH subahanahu wata'ala,, ALLAH yasa mugane,, akwai asirin dazakima duk wani d'an adam ki mallakesa,, mijine ko dangin miji ko danginki kai koma waye,, kubiyoni xan baku wanna asirin agaba,, ALLAH ya yafe mana ameen🙏🏻.


+++++++++++++
Zuwaira kwance akan gado tanata faman kuka da juyi,, ga hajja Rabi tafita kasuwa dan tasiyo wasu abubuwan daxata fara gyara Zuwaira,, tun tana juyi agado harta fad'o k'asa saboda azaba,, ALLAH mai hikima saiga Sultan kamar anjeho shi,, saukarsu kenan ikeeram takirashi tace gobe zasu taho kakarta tasamu lfy,, shine yayo gida dan fara d'aukar matakin tarbarta da rikicinta.
"" da sauri yak'arasa gareta, Juwairiyya lfy ?? Ina Zuwaira bata iya magana,, shima baijira amsaba ya sungumeta gaba d'aya yay waje,, sai asibiti.
Asibiti ankarb'eta da gaggawa dan ganin halin datake ciki,, sun bata tai makon gaggawa,, bayan kamar 30minutes likita ya buk'aci ganin Sultan.
Sun shiga office d'in likitan bayan sun zauna likita yace,, Sultan ka kwantar da hankalinka matsalarta mai sauk'ice in sha ALLAH nan bada dad'ewaba komai zaiyyi dai dai.
"" cikin sanyin jiki Sultan yace"haba Dr musa yaxakace na kwantar da hankalina kana ganin yarinyar mutane rai ahannun ALLAH."
Cool down my brother, kasan bana maka k'arya,, amma tashi muje ka ganta,, dan hankalinka ya kwanta,, zumbur ya mik'e tunkafin Dr musa yatashi,, har ya fice.
Hankalinsa yad'an kwanta ganin ansa mata k'arin ruwa tana barci, Dr musa yace"Sultan kaje gida kaxo mata da wasu kayan dan inta farka zata buk'aci haka,, cikin sanyin jiki yace zaku kwantar damu kenan ?? Eh to in yuwwuwar hakan tazo,, xamu kwantar daku zuwa gobe in ALLAH ya kaimu,, baice komaiba ya nufi gida.


Da sauri hajja Rabi ta mik'e tana tanbayarsa ina Zuwaira,, ba b'ata lokaci yay mata bayanin yanda ya risketa,, yace"" ta shirya sutafi asibitin,, yashiga d'akin Zuwaira ya d'akko mata kaya marasa nauyi kala biyu,, suka tafi.


Bayan kamar awa2 Zuwaira ta farfad'o,, Sultan yana zaune kusa da ita akan gadon,, hajja Rabi na zaune akan kujerar roba,, jinta cikin lema yasata saurin kai hannu ta tab'a k'asanta,, ta tashi da saurai, hankalin su Sultan yadawo kanta,, cikin kuka tace na shiga uku jini ajikina,, Sultan yarik'e hannun nata yana fad'in jini kuma?? Hajja tayi k'arfin halin fita kiran likita............✍🏻


Kuyi hakuri masoya wlhy 2days banida lfy shiyyasa bakuga typ ba.


🎯Bily🎯
🍀Mrs Abdus'salam🍀
I💓U MU FAN's
[10/25, 3:08 PM] ‪+234 809 777 0370‬: 2~ August~2016
💎3⃣2⃣💎
💎💎💎
💎💎




🎯K'ANWAR UWACE🎯
ko
🎯KISHIYAR UWA❓🎯




💚NA BILLKISA IBRAHIM📝




»« hajja suka shigo tare da da likita,, Dr musa yakama hannun Sultan kaga zomuje office namaka bayani,, Sultan yakalli Dr musa da idanunsa dasukai jaa, yaxakace naxo muje office batare daka duba min mataba ??
Kaga karka damu xanmaka bayanine, ita kuma ta gyayara mata jikinta, yajuya yakalli Zuwaira dake ta faman kuka tana kallon hannunta dakeda jini, hajja tace" kayi hak'uri Alhaji kaje.
Baice komaiba yabi bayan Dr musa suka tafi.




Bayan sun isa office d'in Dr musa yacika kofi da ruwa yamik'ama Sultan, kaga malam fara shan wannan kafin namaka bayani.
Ba musu Sultan yakar b'a ya shanye tas, Dr musa yay dariya kai mutumin kace dama k'ishi kakeji ?? Humm kaga ajiye wannan kamin bayanin matsalata.
""To shikenan Dr musa yafad'a yana gyara xama""
Bawani abubane yake damun matarka illa lokacin period d'in tane yayi, kuma wannan shine farkon yinta, danhaka saika kwantar da hankalinka.
""Wata wawuyar ajiyar zuciya yasaki, Dr dama haka nafaruwa??
So saima kuwa, kuma in sha ALLAH komai zaiyyi dai dai, sai kayi k'ok'arin kwantar mata da hankali itama, ga wad'annan magungunan kaje abata amma kud'an bata wani abu taci sannan.
""To d'an uwa ngd

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads