Showing 3001 words to 6000 words out of 19859 words
Chapter 2 - RAYUWA SAI DA KE Complet by Mimi queen.txt
shagalin koda aka kirasu suyi rawa basuyi rawaba amma sunsha manni domin duk Wanda ya kallesu se yace sun dace da juna, sunyima Amarya da Ango manni domin duk kudaden da Sabrina tazo dasu seda suka kare a manni, Se wuraren 6pm sannan taro ya watse suka koma gida.
11/13/20, 10:29 AM - Mimi:
*RAYUWA SEDA KEE!!*
By
*Ummu Ramlat @2020*
?? *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*????�
```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da aiki da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.
____________________
Page 5&6
Washe gare ne daurin auran Feenah tunda safe da bobby ze wuce gurin aiki ya ajiye ta a agidansu Feenah Inda suketa shan biki wuraren shida na yamma takirashi akan yazo ya dauketa yace yana kan news ne amma tajira inya gama zezo ya dauketa (kasancewar shi ma'akacin gidan tv ne) dan haka da akazo daukan Amarya se ta bisu suka kai Amarya unguwan rigasa. Misalin karfe takwas da kwata Sabrina ce tsaye tana duban hanya tanata faman tsaki gefe guda kuma wani saurayine me suna mudassir ya takura mata daga can gefe kuma yan matan Amarya ne keta shiga motan samarinsu, motar Amjad ce ta kunno kai hakan yasata saurin cewa."malam dan Allah nagode nika kyaleka." Tana fadin haka tayi gaba parking Amjad yayi tareda zuge glass din motan yana kallanta tareda fadin."meya hadaki da mudassir."? Tsaki taja ta zagaya ta bude motar ta shiga tana bashi labari dariya ya hauyi yana fadin."meyesa baki yarje Mishi ba? Kinga da shikenan kin zama Amaryar mudan." hararshi tayi cikin wasa yana dariya yace."sorry Amaryar mudan." Juyawa tayi ta daure fuska yayinda yafara driving, sunkusa gida ya juya ya kalleta yana fadin."lafiya Amaryar mudan."? Kuluwa ta karayi kaman zatai kuka da haka suka karisa gida yanayin parking tafice Jakarta ya dauka ya nufi bangaren su dashi, Abbane da Ammi zaune se Sabrina a tsaye da alama shigowarta kenan gaidasu Ammi yayi tareda fadin."Amaryar mudan kin manta da jakarki." bubbuga kafa tayi cikin shagwaba tafada jikin Abbah tana fadin."Abba kaji shi ko? yana cemin Amaryar mudan." Murmushi kawai Abba yayi Amjad yana dariya yace."Abba wani sabon saurayi tayi yau waishi mudan." A shagwabe tace."to nidai kadaina cemin Amaryar mudan suna kaman zanyi amai." yace."to sedai nace miki Amaryar me? Samarin nakine duk bamasu suna me dadi daga Audu se bilya mudan dinne ma dan gwamma gwamma." Tashi tayi daga jikin Abba tace."Ai gwara ni wani ko saboda bakin jini ko budurwar babu..........." rugawa tayi da gudu tayi upstairs ganin yana nufota Aiko da sauri ya bita ganin ze kamata yasa tayi zemewan karya tareda sakin Kara Aiko da gudu ya karisa ya dagota yana duba kafan daukanta yayi ya karisa da ita saman, yana ajiyeta ta kufce tayi daki da gudu tana dariya murmushi kawai yayi yawuce. Bayan tacire kaya kwanciya tayi ta lumshe ido tana tunanin bobby se murmushi take da haka bacci ya kwaceta.
Washe gari misalin goma na safe sabreena ce tafito sanye da red mini skirt da black top ta yafa dan siririn gyale a yalayalan gashinta tsugunnawa tayi tana gaida Ammi ta amsa cikin kulawa Sabrina tace.
"Ammi ina Abbane."? tace."tun dazu suka fita da daddynku." ( daddyn Amjad) mikewa tayi ta nufi waje Ammi tace."ina zakije."? tace."Ammi bobby zan taso muyi break fast." daganan tafice bata samu kowa a main faloba dan haka ta nufi dakin amjad, yana zaune tsakiyar gado yana danna system shigowa tayi hade da sallama tayi tsaye rike da kugu tana kallonshi ganin ko kallanta beyiba yasa takai hannu tayi sama da laptop din ya dago da sauri yana fadin."please bari na kammala nakusa gamawa." tace."yanzu ba lokacin aiki bane." yace."to please kiyi saving Kafin ki kulle." dannawa tayi tareda rufewa tace."nayi saving." ta ajiye a bedside table ta juyo tana kallonshi ijiyar zuciya ta sauke tareda shagwabe fuska ta shafa cikinta tace."Bobby I'm feeling hungry." tashi yayi daga kan gadon ya shiga toilet brush yayi ya fito tareda mika mata hannu yace."let go." da sauri ta rikoshi suka fice dinning area suka nufa suna zama ta hada quater oasts tafara sha shi kuma yahada tea yafara sha tareda Arish, fried egg da toasted bread, suna cikin kari mummy ta sauko daga sama gaidata sukayi ta amsa tana fadin."se yanzu kukaga daman yin kumallon."? Sabrina ce tace."mummy bobby ne yatsaya aiki." tace."to se kuyi sauri dan wanke wanke nakeso inyi." Sabrina tace."kibarshi mummy zamuyi ki koma ciki kihuta.
" Mummy tace."to shikenan dama dansu deenarh suna hadda ne." tafadi tana hayewa sama Sabrina ta dubi bobby tana ijeye cup tace."to malam mudi se kayi sauri kagama." dariya ya fashe dashi yace."wallahi harkin tunamin Amaryar mudan." Hararshi cikin wasa ta tashi tafara hada abu buwan da aka bata tana kaiwa kitchen koda ya gama shima seya dauki plate din dayaci abinci da cup din yakai kitchen, nan suka fara wankewa a tare anayi ana fira da wasa da dariya har suka gama falo suka dawo suka zauna yana dariya saboda zolayarta da yake yana kallon yanda take fushi yana karasa dariya kauda zance tayi da fadin."wai bobby yau ina zamuje? Niko inaso naje yawo." daurewa yayi tareda fadin."Ina kuwa zamuje uwar San yawo."? tace."muje suprite muyi shopping dama ko sweets dina sun kare kuma inaso nasai sabon teddy." dubanta yayi yace."to uwar San zaqi amma nifa banada kudi, sedai idan kin yarda zaki biyamin duk abinda na dauka."? tace."don't mind bobby ai kai da kaya duk mallakan wuyane." yace."to jeki shirya nima bari naje na shirya." tatashi da gudu tafice shima tashi yayi ya nufi dakinshi dan shiryawa. Kusan a tare suka fito shi yasaka dark blue jeans da white shirt ita kuma tasaka light Orange gownt sunyi kyau sosai a waje sukayi clash dan haka suka nufi motan dukkansu gaba suka shiga har zatasa belt yace."Tabb wallahi mimi nagaji da driving koda yaushe kin maidani driver dinki." tsaki taja tace."wallahi Bobby kacika San jiki da yawa yanzu katuka mu zuwa super market dinne kake ganin kyashi." yace."to naji nagani din ke harkin Isa kice inada San jiki akwai Wanda yakai ki San jiki." tana mai wani duba tace."lallaima bobby to naji mufita mu shiga matana ni bazanyi driving a nakaba nafi jin dadin nawa." murmushi yayi yace."bana jin zanji dadin zama a tsohuwar mota." Kallan shi tayi."me kake nufi Bobby."? Yace."eh mana ai ferrary tsohuwar yayi ce yakamata ki shigo gari beb." belt tasaka tana fadin."please bobby ka tayani rokon Abba ya siyamin sabuwar mota tunda yace bazai siyaminba sena gama karatu to yanzu nagama amma ba maganan." dariya yayi yace."to ke meza kiyi da mota keda za'a miki aure da mudan." Hararshi tayi lokacin me gadi ya bude musu gate suka fice kallonta yayi yace."lafiya baby."? ta shagwabe murya."please bobby kadaina banaso wallahi ni bansan shiba se ranar kuma wallahi nace bana sanshi." yana dariya yace….
"Aiko bazan dainaba har sai kin fito mana da miji." ta sake shagwabe murya."Allah bobby banaso ,ko sena maka kuka."? dubanta yayi yana dariya yace."Aiko da kinga bacin raina kam kinsan babu abunda na tsana irin kuka balantana kukan mimina." tace."to kadaina bobby ko kuma se......." juyowa yayi yana dubanta saboda shirun da tayi tana dariya yace."ko seme."? tace."bazan fadaba zaka dakeni." kauda kai kawai yayi yana murmushi domin yasan me zatace da wannan suka karisa babban mall din dake unguwan rimi, A tare suka fito suka jera zuwa ciki tsaye yayi yana nuna mata cart make kafada tayi tace."Aa kaika jamana." Murmushi yayi yace."lallaima yarinyar nan kin cika San jiki." Yaja yayi gaba bayanda ta iya hakanan itama taja tafara zaga yawa shima zaga yawa yayi yana zaban abinda yakeso seda tacika da kaya fam sannan ta gungura zuwa gurin da za'a mata calculate tabiya, shima a dai dai lokacin ya iso sedai shi bamasu abubuwa me yawa ya daukaba kasancewar bameshan zaki da yawaba domin kusan duk ba kayan zaki yazaba ba, Mika nashi kayan yayi ."ki hada da nawa tare muke." Aka kirga aka fada musu kudin Amjad yadubi Sabrina yace."ki biya." jaka ta bude sedai dubu dari kawai ta dauko dan batasan zasuyi siyayyan daya hau rawa dubu dariba Rufe jakar tayi ta dago tana kallon bobby daya rike kunci yana leken jakarYace."kibiya hajiya ko babune? kawo jakar nagani." ta kauce da miko hannun da yayi ta marairaice tace."dan Allah bobby kabiya in munje zan baka
100k kawai na dauko kuma na manta da ATM dina a gida." Dariya yayi tareda zaro walet a aljihu yabude ya Ciro ATM yamika mata yace."gashi ki cire kudin." ta amsa tayi amfani da pos ta cire kudin daganan tasa musu a ledoji ya amsa nashi ya wuce da kyar Sabrina ta amsa tayi waje a bayan mota ta ijiye kayan tafada motan tana fadin."gaskiya bobby ka batamin rai yanzu kana gani na amsa kaya ko katayani."? kallanta yayi da tsiwa besan sanda dariya ta kufce mishiba haushi sabreena taji tafara kai mai duka a kirji tana fadin."meye kake dariya kamai dani cartoon ko."? cikin dariya ya hade Hannayen shi yace."sorry Amaryar mudan." Haushi ne yakara kamata tajuya baya tanajin yanda yaci gaba da dariya kukane yazo mata takasa jurewa ta dukar da kai tasa kuka, lokaci guda yadaina dariyar yana kallonta yace."sorry mimi stop shedding ur tears please." yakai hannu ya tabata a tsiwace ta bugemai hannun ta dago tana kuka tace."meyasa zan daina kuka bayan kamai dani Mahaukaciya sannan nace banaso Kana cemin Amaryar mudan amma kaman ina cewa kacene dan haka kabarni naci gaba da kukana ba ruwanka dani......" bata rufe bakiba ya janyota bisa faffadan kirjinshi ya rungumeta yana shafa bayanta yana fadin."sorry mimina bazan kuma cewaba tunda bakiso." yanayin data shigane da kuma Kamshinshi daya mata dadi yasa tayi shiru kaman ba ita ke kukaba tareda sauke karfaffan ijiyar zuciya, jin tayi lamo a kirjinshi yasa yakara janyota ya zaunar da ita a cinyarshi yayinda yafara tuki kokarin sauka tayi yarikota da sauri yana fadin."no mimi kada ki sauka nafiso naji dumunki." shiru tayi tareda gyara zamanta a cinyar nashi ta daura kanta kan kirjinshi tanajin yanda yake harbawa da sauri da sauri, yana tuki yace."yanzu da da duk dayane aguna mimi,kokin manta lokacin dakike bacci akan kirji nane Ammi tayi tayi tadaukeki ki makale jiki Tashi ." murmushi tayi saboda ta tuna abubuwan da tayi a baya tace."sannan kuma ince dole kai zakamin wanka inba kaiba ranar bazanyi wankaba." Yayi murmushi yace."idan kina kuka ingoyaki ina jijjigaki har sai kinyi bacci idan ko kina kuka mimi bana iya sukuni bare har nayi bacci." tayi saurin fadin."idan zanje school nadage se nasaka teddy a lunch box dina Ammi suhana kai kuma kazaga kasakamin a jakana saboda yanda kake sona." Shafo gefen fuskarta yayi yace."kinasan mugun wasa sosae akwai lokacin da har karyewa kikayi garin mugun wasa." ta amshe da sauri."a lokacin kowa yayi fushi dani sekai kaika dingaa jinyana kamin wanka ka kaini duk Inda nakeso." A tare sukayi dariya saboda sun tuna abubuwa dadama, yayinda Sabrina ta zagaya da hannunta ta bayanshi ta kara rungume shi ta lumshe ido tana tuno abubuwa da dama tana murmushi, to Kafin sukarisa gida bari mu waiwaya baya danjin waishin su wayema wannan bobby da Mimin.
Please kuyi hakuri insha Allahu a next page zakuji cikakken tarihin bobby da mimi, Kunajin dadin book din amin afuwa nagode.
11/13/20, 10:30 AM - Mimi: ????????
??????
????
??
*RAYUWA SEDA KEE!!*
????????
??????
????
??
By
*Ummu Ramlat @2020*
?? *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*????�
```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da aiki da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.
```?¥°
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp
____________________
Page 7&8
Flash back
Asalinsu Shuwa arabne dangin daya faro tun daga larabawa kaf dinsu kyawawane ga yalwar arziki da nasaba Allah yabasu ga matayensu yara da manyansu da gashi kaman India kyau da kuma sura, tosu asalin tushensu yafara daga sokotone a can kakansu yake mesuna Abdullahi inda yakeda mata biyu Amina da surayya inda ko waccensu Allah ya azurtata da da daya tak Amina nada Abbas Wanda shine babba surayya kuma mansur Wanda shine karami, mansur Nada shekara hudu surayya ta rasu dan haka a hannun Amina yataso tareda Abbas Kansu a hade ko kadan Amina bata nuna bambamci tsakaninsu, har suka kammala secondary school suka shiga fafutukan Neman admission Abbas yasamu a Kaduna (kasu) shikuma mansur a bauchi(ATBU) dan haka suka fara karatunsu har Allah yasa suka kammala, Anan Kaduna Abbas yasamu mata ya aura mesuna Asma'u dayike lokacin uba da uba duk sun rasu yasa ya gina madaidaicin gida anan kd yazauna da matarshi kasancewar tunda ya kammala karatu har lokacin be samu aikiba, shikuwa mansur a bauchi ya hadu da Ruma wacce su ukune adakinsu itace auta sauran duk mazane ya aura kasancewar shima bayada wani takwa mamman aiki yasa suka zauna a gidan yayanshi Abbas dake Kaduna suka zauna da Asma'u, Anyi haka ba jimawa mansur yasamu aikin costom babu Wanda beyi murnaba nan danan mansur ya daukaka yagina musu wani babban gida suka tashi suka koma can gaba bayansu a dai dai lokacin ne Asma'u matar Abbas ta haifi da namiji Wanda yaci suna Amjad, amjad nada three years wan Ruma matar mansur yasama ma Abbas aiki a wani babban company dan haka suka taru suna biyawa juna bukata kuma suna zaune cikin kwanciyar hankali Kansu a hade. Amjad yataso cikin so da kauna besan komaiba se farin ciki a lokacin dayakai shekara goma sha biyu bayada buri daya wuce ya ganshi da kanwa abokiyar wasa a lokacin mahaifinshi ya gina company na kanshi ya tsayu akan kanshi shima mansur an kakkara mai matsayi dan haka alokacin sun canza gidaje yakai sau biyar kuma sunada kadarori da dama, sannan shi mansur baya Satan kudi aikinshi yake tsakani da Allah dan haka kadarorinsu da guminsu suka tarashi, a wannan lokacin da arziki ya yalwata Ruma ta haifi kyakykyawar yarta mace wacce taci suna sabreena, amjad yayi farin ciki da haihuwan Sabrina da akamai saboda tsananin san da yake mata yake kiranta da mimi itama ganin yanda yake tarairayarta yake shagwaba ta yasa take kiranshi da bobby, tun bata iya fadin sunan kowaba ta iya fadin nashi dan zan iya ce muku a lokacin harta Ammi bata Sani sosaiba kaman yanda tasan shiba, A haka suka taso ko mai shi suka shaku har takai 7 years duk da haka berage ko kadan daga cikin kulawar da yake bataba haka ze mata wanka ya wanke kazantarta ko a jikinshi infact dai amjad shiya shagwaba mimi yasa tazama shagwababbiya, indai tanasan Abu duk yanda zeyi sayyaga tasa meshi, tanada 7years mummy (mahaifiyar amjad) ta haifi twins sune deenarh da sukainat deenarh akasa mata sunan mahaifiyar Abbas sukainat kuma mahaifiyar mansur duk d haifo twins din da mummy tayi besa amjad yarage koda kadan daga cikin kulawar da yakeba sabreena ba, dan haka mimi batada magana se bobby kome aka mata shi dan haka suka zama kaman hanta da jini sun shaqu har ake ganin soyayya ce sedai su sunsan shaquwace kawai da haduwar jini da amintaka sedai ni nace Allah kadai yabarwa kanshi Sani, Amjad yayi karatunshi me zurfi fannin math com inda a yanzu ya zama new casting na gidan tv yayinda ita kuma Sabrina yanzu ta kammala karatunta fannin jornerlist domin sun tasone kusan choice dinsu daya, Amjad bayada aminiya data wuce ita haka itama shi sedai friend amma babban abokinshi shine Asim ita kuma Ferry, yan mata da dama sunsha kaima Amjad hari tun bare shima Me farin jini ma'akacin gidan tv dan akwai wa'inda suke sumewa idan suka ganshi a tv saboda kaunarshi sedai shi be taba amsa musuba hakama Sabrina itama bawanda ta taba amsawa kuma gashi sun Isa aure amma sunki tsaida manema kuma basan juna sukeba sedai sukadai suka barwa Kansu Sani se kuma ubangiji, am akwai wani me suna Aman yaron babban wansu Ammine yana matukar San Sabrina sedai yakasa fada mata Wanda yarasa dalili Amma dai muje zuwa.... Lol
Wannan kenan zamuci gaba
da haka suka karisa gida kowa da abinda yake tunani yanayin parking ya rabata da jikinshi ta tashi suka fice yayinda suka kwashi kayansu a baya suka shige sashinsu Amjad.
11/13/20, 10:30 AM - Mimi: A ????????
??????
????
??
*RAYUWA SEDA KEE!!*
????????
??????
????
??
By
*Ummu Ramlat @2020*
?? *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*????�
```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da aiki da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.
```?¥°
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp
____________________
Page 9&10
Washe gari tana bacci taji ana danna mata door bell tashi tayi kasancewar pant da brane kawai jikinta yasata daura bedsheet ta karisa tabude Bobby tagani tsaye da Leda a hannunshi ta kauce ta bashi hanya ya shiga a bedside table ya ajiye ledar yana kare mata kallo yace."ga ice cream nan me sanyi na siya miki." cikin farin ciki tace."nagode sosai bobby." Hannu yasa a aljihu ya zaro key din mota ya mika mata cikin mamaki ta amsa tana jujjuyawa tace."bobby key din is for what."? Yace."sabuwar motar kice tana parking area." Wani murmushin farin ciki tayi ta fice da gudu bedsheet din data daura yanaja da kasa. Shima bayanta yabi yana murmushi A pake ta hango motar pink colour Mercedes Benz C300 ta ruga da gudu tana karewa motar kallo takai face dinta ta sumbaci motar da sauri tasa key ta bude ga kamshi da air control available a ciki, tukawa tayi zuwa tsakiyar gidan sannan tayi parking tafito da gudu dai dai lokacin Abba da daddy suka fito a tare suna tambayan."meke faruwa."? Amjad ko yayi tsaye hannu bisa aljihu yana kallonta yana murmushi da