Showing 18001 words to 19859 words out of 19859 words
Chapter 7 - RAYUWA SAI DA KE Complet by Mimi queen.txt
kune jigon Ilimina bangon Rayuwata kune kuka tarbiyantar dani kuka ilimantar dani har nakawo yanda nake a yanzu ba Abinda zan iya biyanku dashi face addua?¤²*
*Nagode nagode sosai????*
*Mamana da Babana Allah kara dankon soyayya ya kuma barku tare Ameen ya rab?¤²?¤²*
Page 29&30
*****************************
*Bayan Shekaru shida*
*Wani kyakykyawan yaro* na hango zaune a daya daga cikin royal chairs din da ke kayataccen paurlon.
Tsayawa fada muku kayatuwar falon bata lokacine.
Me karatu kuyi imaging kawai Amma falon ya hadu ba karya.
Yaron na matukar kama da Sabrina danba abinda ya barota.
He is not above six years yana sanye da short jumper da armless riga kyakykyawane yaron nakin Karawa wanda ko a kasar larabawa samun me kyanshi se anyi scanning.
Katuwar pink teddy ne a hannunshi yakura mata ido sedai ba wasa yake da itaba.
Daga kaina nayi saman benen dake falon na hango wata kyakykyawar yarinya tana saukowa.
Bazata wuce five years ba tana sanye da doguwar riga pink gownt Mara hannu be karisa har kasaba.
Kanta anmata 6line da sumarta ya zubo har gadon bayan jelar gashinta da aka kama mata da pink band yanata lilo a gadon bayanta.
Kitson ya zubo har gaban goshinta kitson yasha duwatsu masu ruwan gold dan idan baka saniba sekace duwatsun na gold ne.
Kunninta na makale da dan kunnin gold me kyau siririn wuyanta ma siririn sarkace iri guda da dan kunninta shima na gold.
Gurin wannan handsome boy din naga tayi tana mai murmushi.
Cikin sweet and cool voice dinta me matukar zaqi wanda seda na waiwaya ko sarewa ake busawa.
Tace." *D* give me my teddy I'm looking for it since."
Mika mata yayi ta amsa tareda rungume wa.
Ta karisa kusa da shi ta zauna tana fadin."D where is my cerelac."?
Baki ya bude zeyi magana sedai kafinnan najiyo taku daga sama dan haka na juya tareda gyara zaman *alkalamina* na kurawa staircase ido.
Asim ne ya sauko manne da khairy.
Khairy ta dubi yaran cikin kulawa tace." *A boy, Little* kutafi gurin Aunty ta shiryaku Daddy da mummy suna hanya."
A boy ne yatashi yariko little sukayi wani part hannun su manne da juna.
Asim ne yakara matsawa setinta yace."My Abnah da alama Little Sabrina da Little Amjad zasu taso kamar su Bobby da Mimi ne."
Rungume shi tayi tana fadin."da alama kam bakaga yanda suka shakuba har suna suka canzama juna
Mudai ba zamu taba raba suba koda kam basasan juna
Balle suma mu rasa su kamar yanda muka rasa Aunty didi da ya Amjad."
Face dinta Asim ya kamo ."kuma mu zamuci gaba da rike A boy koda ko Aman ne yanemi damu bashi danshi
Sedai kam mu hadasu da Little."
Dariya tayi tace."namasan yaya bazece hakaba."
Nan suka shiga kitchen dan shiryawa su Aman delicious.
A tare sukayi komai tanayi yana tayata har suka gama komai.
Bayan sun gama suma daki suka shiga dan shiryawa.
Shige kala daya Little da A boy sukayi cikin blue din shaddansu gizna wacce tasha aiki bakaramin kyau sukayi ba.
Shi riga da wando se hular zanna bukar data dace da shigenshi.
Little kuma doguwar riga me igiya ta baya wacce ta sha aiki an zubo mata da gashinta gaban goshinta
sunyi kyau ba karya kuma kallo daya zakuyi musu agane cewa yan hutune kuma yan gata wa'inda naira tayi zaman dirshan a jikinsu.
Suna manne da juna har basaso wani Abu ya raba su.
Misalin 12pm sukaji horn
Me gadi ya bude jerin gwanayen motocin suka shigo sukayi parking a parking space.
Khairy najin haka ta tashi da sauri
Asim ya kamota da sauri yana fadin ."My Abnah wannan mikewa haka kada fa ki wahalarmin da baby."
Murmushi tayi
dai² lokacin sukaji knocking ta tashi da sauri tabude.
Aman ne ya shigo shida matarshi A boy dagudu ya rungume daddyn nashi.
Aman yayi sama dashi ya rungume yanajin dadi
Khairy dake tsaye tana kallon tulelen cikin matar yayanta tace."Lallai Aunty ferry wannan fa."
Harararta Ferry tayi tana fadin."So nawa zance miki sunana Farida Ferry sunan school ne."
Asim ne yayi saurin fadin."To Afwan Aunty ferry."
Murmushi tayi ta karisa ta zauna gefen mijinta daya zauna shima.
A boy nakan cinyarshi yanajin kaunar yaron na dada shiganshi.
Hannu A boy ya mikama Little itama tazo ta zauna a kusa dashi.
Delicious kala da kala tareda kayan marmari dana shaye² aka shiga jero musu.
Kadan sukaci haka A boy yayita ba Little abaki itama tana bashi.
Bayan sun natsa Aman ya fara magana kamar haka
."Ba abinda zance muku ke kanwata da mijinki daya wuce godiya ina gode muku bisa rikemin dana da kukayi."
Asim yace."bakomai ai muma dan mune."
Aman yaci gaba."to ina neman alfarma daku bamu shi mu tafi dashi can Istanbul din nadan wani lokaci."
Asim yace."Ai ba matsala duk dayane."
Aman ya dubi A boy yaga yayi kini kini da rai yace
."ya akayi Son ko bazaka je bane."?
Kai ya gyada Aman yace."Saboda mene."?
Cikin muryarshi me cikeda sanyi yace."Ni bazan iya tafiya nabar *My Amnah* ba sedai atafi damu tare ko My Amnah."?
ta daga kai."Eh *Droon* dina."
Murmushi Aman yayi yace."badamuwa da dukkanku zamuje kunji dadi."?
dukkansu suka daga kai suna murmushi.
Aman ya dubi Asim yace."yanzu zamu wuce gidansu Ammy acan zamu kwana gobe jirginmu ze tashi zuwa California jibi idan nagama abinda zanyi a California se mu wuce Istanbul."
Cikin farin ciki A boy yakamo hannun Little."My Amnah zo muje mu fadama Aunty."
*(Nany me kula dasu)*
tace."To My Droon."
Nan sukayi ciki da gudu suna kiran."Aunty, Aunty."
Kowa yabisu da kallon sha'awa.
Cikin murmushi Aman ya dawo da dubanshi Kansu Asim yace
."Tun yanzu ina nemawa dana auren yarku saboda banaso suma mu rasasu."
Gaba dayansu suka sa dariya.
Se wuraren *two* sannan suka dau hanyan gidansu Ammy.
Motan gaba Aman ne da ferry se A boy da Little.
Motan bayansu kuma Asim da khairy ne se bodyguards dake binsu a baya.
A boy da little se surutu suke zasuje gidan Grandma Suga Aunty deenarh da Aunty sukainat.
Little ne ke fadin."Dee dina wallahi nayi missing dinsu."
Murmushin shi me kyau yayi wanda ya bayyanar da cutes dimple dinshi.
siririn yatsanshi yakai setin inda Kumatunta ke lotsawa.
Sunaci gaba da murmushin cutes dimple dinsu nadada lotsawa madaran kyansu nadada bayyana.
Anje dai² round about Aman sukaji yaran sun hada baki tareda yiwa driver shouting ."Wait wait."
Da sauri yataka wata uwar burki dukkansu suka juya suna kallonsu.
Hadaddiyar jakar A boy yadauka ita kuma ta dauki kwalayen sweets dana chocolates din suka bude kofa suka fice.
Suma su Asim tsayawa sukayi suna kallonsu dukda ba yau suka sababa.
Harde hannu Aman yayi akirji yana kallon yaran cikeda sha'awa.
Karisawa sukayi gurin mabaratan dake bara gefen hanya.
A boy ya balle jaka yafara raba musu kudi ita kuma little ta bude kwalin tafara raba musu sweets, chocolates harda goro.
Se addua sukema yaran suna gode musu.
Shiru Aman yayi yana tunanin Sabrina sak yaran halinta suka biyo na tausayi da temako.
Ferry ma bobby da Mimi tadinga tunawa suma haka suke da tausayi dasan temako.
Har batasan sanda hawaye yafara bin dakalin fuskarta ba.
Bayan sungama raba musu sunata musu addua se kuma suka fara waige waige
Asim ne yafito daga mota yadubesu cikin kulawa yace
."Little A boy Ku koma mota mu wuce rana nayi."
Little ta langwabar da kai cikin shagwababbiyan muryarta tace."Abun bamufa ganshi bane kayi hakuri inmun ganshi zamu koma mota."
Tana fadin haka suka shige karkashin wata tsohuwar mota.
Murmushi driven yayi yace."Wa'innan yaran na kaunar mahauka cin nan mutumin dayake duka ammasu baya musu komai
Ko school zasuje idan sun tsaya bada sadaka
Se sun nemeshi sun bashi abinci idan kuma basu ganshiba to ranar sun dingi kuka kenan suki cin komai harse ankawosu sunganshi.
Shiru Aman yayi a zuciya yana godema Allah daya bashi me kyansu hali irin Sabrina gayinan yanzu bayanta suna koyi da ita.
*(Shiyasa yanada kyau mu zabama yaranmu uba nagari suma mazan yanada kyau su zabama yaransu uwa tagari saboda suyi koyi damu) Allah bamu mazaje nagari suma Allah basu mata nagari Allah sa mudace Ameen ya rab?¤²*
Bayan yaran sun ganshi suka koma motan.
A boy yadubi Aman tareda rike kunninshi ya marairaice."Sorry daddy we keep u waiting."
Murmushi yayi tareda shafan kwantaccen sumar A boy yace."badamuwa Son Amma meyasa kuke wannan abun."
Gyara zama A boy yayi tareda fadin
."daddy babu Abu me falala a duniya irin sadaka Allah (SWA) yace kubada kadan zan baku meyawa
Amma yanzu mutane basu dauki temako abakin komaiba musamman masu kudin mu na yanzu se su wulakanta dan Adam ko ajikinsu bayan sun mata irin falalan da ubangiji yama dan Adam sannan kuma da talaka dame kudi dukkansu halitta ne na ubangiji kuma be wuce ubangiji ya kwace wannan arzikin dakake kuri dashiba yabaima wannan talaka daka raina
Dan haka mumuna temako ne saboda yanada kyau kuma ubangiji yayi umarni dashi."
Zuba mai ido Aman yayi yana murmushi cikeda mamakin jin yanda A boy yasan wa'innan abubuwan a yan shekarunshi
Kara shafa kan yaron yayi tareda fadin."kafin mu dawo daga kasar waje zansa a gina orphanage house asa sunanka dana little da niyyar Allah ubangiji yakai ladar kabarin Bobby da Mimi
Sannan su wa'innan bayin Allah din da suke bara za'a maidasu can nakassassun cikinsu kuma za'a kaisu asibiti
Inyaso insun samu sauki se a maidasu can gidan marayun sudaina kwanan titi.
Shikuma mahaukacin zansa a daukeshi akaishi gidan mahaukata inyaso inya warke tunda kuna kaunarshi ko school ne seya dinga kaiku."
Jikinshi suka fada dukkansu su namai godiya cikin farin ciki.
Bayan sun dau hanya little tadubi Ferry tace."Momy."
Duban yarinyar tayi tareda shafa gefen fuskarta tace."Na'am Little."
Tace."Mummy waisu waye *Bobby da Mimi* dinnan damu ke jin nida Droon Mamy da Abun nata maganan su harma kowa Mummy."
Kasaitaccen Murmushi Ferry tayi ta juya tana kallon mijinta.
Shima murmushin yayi....................
*Leeymart*?�ï?
*Alhamdulillah*
*Tammat bissalam*
I thanks Almighty Allah to give me opportunity to complete this Book
and I really thanks for him to bless my *beloved fans*????
*Akwai darisa masu yawa acikin littafin RAYUWA SEDA KEE Amma nidai shawara na anan shine*
*Mudaina zurfin ciki akan abinda mukeso domin wannan yazama izina bamasu yin zurfin ciki akan soyayya*
*Sannan Readers kumin Afuwa na kashe muku Bobby da Mimi da nayi kusani haka yazo a asalin rayuwar wa'inda abun yafaru dasu dan haka team Sabrina da team Amjad amin afuwa domin nima kwaikwayon rayuwar wasu nayi nakara da nawa basiran*????
*Kada Ku mantafa wannan littafin gaba dayanshi Sadaukarwane ga uwa ma bada Mama*
*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*????�
Sedai amin Afuwa na kyautar pages da Nayi????
*Bazan iya mantawa da kuba koda ko mena zama ayau*
*Aunty Jameela da Aunty Binta*
Ku kuka zama gatana a kungiyar *Manazarta writer's Association*????�
Ba Abinda Zance muku daya wuce *Nagode nagode*
Allah ubangiji ya kara hada kanmu yakuma barmu a tare?¤²
*Sisi kona manta da kowa bana manta dake ba*
*Sister Hafsat Amjad wallahi bansan da wani baki zanyi Amfani ba wajen gode miki domin ke kikazam mafarin cikar burina*
*Nagode nagode Sisi na Ina sanki ina kaunarki ?¤ï??¤ï?????Allah barmu tare Siso na yakara hada kanmu My bestie ???? ????*
*U are special in my Life?Œ¹?Œ¹*
*Kana raina My Abnah, Nurul hayatee, Nisful hayatee, Nurul qalbee . Ana Uhibbuka hubban jadidan*?¤ï???
*Allah ubangiji yabarmin kai Suleiman dina ina kaunarka sosai Allah ubangiji ya bakani a matsayin mata nima Allah bani kai a matsayin mijina*????
*Allah barmu tare ina kaunarka har abada Abu Ramlat dina*?¥°?¥°?????Œ¹?Œ¹
Allah Ubangiji ka karemu daga sharrin wannan Annobar data addabemu wato *Corona virus* Allah ubangiji kamana tsari da ita kanisan tamu daga gareta Alfarman Annabi da Qur'ani?¤²
*Story and written*????ï¸�ğ??
*By*
*Herleeymart*
*Sadeeya*
*Isah*
*Idrees*
*Bakori*
*Taku koda yaushe*
*Ummu Ramlat*
(Insha Allahu)
???????Œ¹?Œ¹?Œ¹
*09035221937*
*Twelve-November-2020*