Showing 1 words to 3000 words out of 20540 words
Chapter 1 - BOYAYYEN SIRRI Book Complete writing by Chamsiya Laouali Rabo.txt
*ƁOAYAYYEN SIRRI*💞
*Gajeran labari...*
Story
and
Written by
*Chamsiya Laouali Rabo*😘
Dedicated to *Mss Flower🌸*
Marubuciyar :
*SO KO ƘAUNA*
*JININA NE KAI*
*HASKEN SOYAYYA*
*CIWON SO*
*ABOKIN MAGAJINA NE*
*ƳAN UKU*
*ILLAR LUWAƊI*
*ABBANA NE*
*SADAM*
*ƘAWAR MOMYNA*
*MOHAMMAD KAREEM*
*MAHAUKACIN SO*
☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION*☀️
___________________
BISIMILLAHI RAHMANI RAHIM
*In naga kun karɓi book ɗin zan cigaba,in kuma banga COMMENTS ba nasha barcina*🌚🌚🌚
_ƘIRƘIRAREN LABARI NE WANI BANGAREN WANDA KUMA YAYI DAIDAI DA RAYUWAR SHI SAI YAYI HAƘURI ARASHI AKA SAMU_
*CHAPTER 1&10*
Mirginawa yayi gefe yana mai jin wani raɗaɗi da baƙin ciki mai cike da ƙunci.
Idon shi ne ya ciko da ƙwalla jin bai da marabi da mace wanda sam ya kasa fahimtar mike faruwa da shi ne.
Toilet ya tashi ya shiga yana mai kallon Maryam wacce take sauke ajiyar zuciya da shasheka.Wankan tsarki yayi tare da alwala sannan ya fito,nafiloli ya fara jerowa yana kaima Allah kukan shi ya yaye mashi damuwar da ta kunno mashi kai kwana biyun nan,sai da ya raba dare yana addu'o'i kamin ya raɓa gefen ta ya kwanta cike da tausayin kansu su biyu.
Kiran sallah farin ya tashi yayi alwala yaje masjid yana dawowa ya tarar da MARYAM ta farka har ta shiga wanka,ƙugunta ɗaure da towel ta fito sai ɗan ƙarami wanda ta ɗaura a kai domin tsane gashin kanta sunne kai tayi tana mai jin kunyar ganinta da yayi a haka sam bata tsammaci shigowar shi yanzu ba doguwar riga tayi saurin sakawa ta gabatar da sallah.
"Ina kwana?"ta faɗa can ƙasan maƙoshi kamar wacce aka yi ma doli,bai amsa ba sai tasowa da yayi daga zaunen da yake bakin bed ya zauna kusa da ita bisa sallayar.
Hannuwanta ya riƙe duka biyun yana matsa ƴan yatsunta "miyasa baki yin addu'a in kin gama sallah ?"shine abinda ABDALLAH ya tambayeta yana mai kallon zanen lallenta"nayi cikin sujida ƙarshe"ta bashi amsa tana mai son fidda hannunta daga nashi dan hakan kawai da yake mata yana sa taji wani iri, murmushi yayi dan dama yaga ta daɗe bata ɗago ba ɗin "amman yanada kyau ki ƙara yin wasu addu'o'in bayan sallama kina mai ɗaga hannayen ki sama domin shima yana cikin laduban addu'a"da toh ta amsa mashi kamin tace "wane addu'o'i ne ya kamata ace kullum nayi su bayan ko wace Sallah ɗin?"
" *ALLAHUMMA AJIRNI MINA NAAR* ƙafa bakwai *ALLAHUMMA INNI A'UZU BIKA MINN AZABIL ƘABAR,WA MINN AZABI JAHANNAM,WA MIN SHAIRI FITINATIL MASIHID DAJAL* sau uku sai kuma *AYATUL ƘURSIYU* ita ma ya zamana kina karanta wannan au moins "godiya tayi kafin ya jata zuwa bed suka koma barci.
Ƙarfe bakwai daidai LAURAT ce ke kitchen sai haɗa kayan breackfast take,tana gamawa ta share gida ta saka turare.Abincin ta jera kan dining kafin ta shige bedroom ɗinta ta tsalo wanka,fitowa tayi cikin wata dakakiyar gizner maron wadda ta sha aiki sai ƙamshi take zubawa.
Hakimcewa tayi tana jiran fitowar su,même pas 5mns suka fito hannun su sarkaye cikin na juna sunyi kyau sosai cikin jan voile.
Kishin da ya taso mata tayi ƙoƙarin maidawa kafin ta miƙe ta ƙirƙiro murmushin doli "barka ku da fitowa da fatan kun tashi lafiya?"LAURAT ta faɗa tana mai masu iso izuwa dining amsawa suka yi cikin sakin fuska yayinda ABDALLAH ya kama hannun LAURAT ya sakar mata kiss a goshi bayan ya ja ma MARYAM kujera,"da fatan ke ma kin tashi lafiya my ƙalbi?"ya faɗa yana murza hannunta ta wutsiyar ido ta kalli MARYAM wacce ke kallon su fuskarta babu walwala ganin haka yasa LAURAT riƙe mashi ƙugu a shagwaɓe tace "alhamdullah"ta bashi amsa a takaice.
Ja mata kujera yayi ya zaunar da ita kamin shima ya samu wuri ya zauna yana kallon MARYAM wadda ta game fuska.
LAURAT tayi servir ɗin su da lafiyayar rice wacce ta sha kifi da tarugu sai ƙamshi ke tashi,duk da abincin yayi daɗi bai sa MARYAM taci wani na kirki ba hoton yadda ABDALLAH ke ririta LAURAT kawai ke mata gizo ture abincin tayi ta tashi, kallonta ABDALLAH yayi wanda tun ɗazu yake lura da yanayin ta "ki zauna ki ƙarasa mana "ya faɗa yana mai kama hannunta kai kawai ta girgiza mashi ta nufi ɗakinta ko ruwa bata tsaya ta sha ba.
Wani shu'umin murmushi LAURAT tayi tana mai jin sanyi a ƙasan zuciyarta ,tashi yayi zai bin bayanta amman ta hanashi ta hanyar ce mashi "sweetyna ka bar baby ta huta mana ka san amare ba su cika son kwaramniya ba",ba don ABDALLAH ya so ba ya zauna.
A ɓangaren MARYAM kuwa tana shiga ɗaki ta fashe da kuka sai da tayi mai isarta kamin ta cire kayan jikinta ta watso ruwa .Daga ita sai towel ta zauna bakin gado ta rabka uban tagumi,sai yanzu take nadamar auren mai mata duk wani tuggu da munafurci babu wanda kishiya ba ta iya haɗa maka shi.....
*** KANO
Kyakyawan saurayi ne tsaye ta saman bene yana kallon mutanen da ke wucewa,yana ganin fitowar wata yarinya wacce take cikin niƙaf ya maida duk illahirin hankalin shi da nutsuwar shi kanta yadda take tafiya shi yafi komi burge shi,kamar ta san yana kallonta kawai sai ta ɗaga kai ta kalli benen ƙoƙarin janye idon shi yayi kanta amman ya kasa duk da ba a ganin idonta domin niƙaf ɗin da tasa har ido take rufewa, amman ya san shi take kallo.Ta ɗauki kamar 1mn kafin ta wucewarta hijab ɗinta na jan ƙasa ta yadda ko kayan jikinta ba a gani,ajiyar zuciya ya sauke kafin ya koma cikin gida.
"AMAR daga ina kake kuma naje ɗakin ka baka can? please ka bar fita waje kasan yanayin jikin ka bai son iskan waje"wata latizuwar mata ta faɗa tana shafa gefen kyakyawar fuskar saurayin,langaɓar da kai yayi yace "ban yi nisa ba fah ina bisa terrasse ina hangen masu wucewa"murmushi tayi amman wanda kana ganin shi kasan bana jin daɗi bane sosai "ka tafi kallonta ko?kayi haƙuri ka cireta a ranka tunda kasan larurar da kake da ba zai yiyu ku zauna innuwa guda ba"ta ƙarashe maganar da damuwa kan fuskarta yayinda ta jawo shi jikinta kamar wani ƙaramin yaro tana bubuga bayan shi "mum amman ina sonta sosai ina ji a raina kamar ita ce ruhina sai da ita zani iya rayuwa,duk da ban taɓa ganin fuskarta ba amman ita ɗin kyakyawa ce"cewar AMAR muryar shi na ɗan rawa janye shi tayi daga jikinta taja hannun shi suka zauna bisa ƙayatatun kujerun da ke falo,duban shi tayi da kyau kamin tace "AMAR ko ka san da babu wanda ya taɓa ganin fuska AMIRA kaf a unguwar nan?"cike da mamaki yace "a'a mum amman miyasa?"ajiyar zuciya ta sauke kamin tace "ta yiyu ita ma akwai wani *ƁOYAYEN SIRRI* a tattare da ita kamar kai"zuciyar shi ce ta buga jin batun mum a take yanayin fuskar shi ya canza damuwa ta bayyana ƙarara.
Kafaɗar shi mum ta da dafa tace "ban fah da tabbas haka dai nike tunani tunda naji ƴan unguwa na gulmar wai batada kyau ne shiyasa"kallon mum yayi yace "mi zai hana ki shiga gidan su in an jima sannan ta dawo daga islamiyya sai ki ganta"ɗan jim mum tayi ba ta ce komi ba kamar mai tunani ganin batada niyya yin magana yasa shi tashi direct room ɗin shi ya nufa.
Kayan jikin shi ya fidda ya ɗaura towel ya shiga toilet ya yo wanka kafin ya fito ya fara shiryawa ,zuciyar shi ce ta fara tafarfasa yayinda ɗaya wajen kan shi ke sarawa "hasbunallahu wani'imal wakil"shine abinda yake ta nanatawa a zuci har ya fara jin sauƙin ƙunci da takaicin da yake ciki.
A ɓangaren AMIRA kuwa tana zuwa islamiyya ta samu guri ta zauna ba tare da tayi ma kowa magana ba dan ko tayi babu mai amsawa,sabon malamin da aka kawo masu ne ya shigo bayan kowa ya gaida shi ne ya lura da AMIRA ita kaɗai ce a ke sanye da niƙaf.A tsawace yace "ke cire min niƙafin nan ko kinfi kowa ne"malamin ta faɗa yana mai miƙewa tsaye,duka ƴan ajin duban su suka maido gunta jiki na rawa AMIRA ta fara bashi haƙuri amman yaƙi sai ma dorunar shi da ya ɗauƙo dan ya daketa kasancewar ta mai tsoro yasa tayi saurin ɗage niƙaf ɗin sama "Masha Allah Tubarkallah"shine abinda ƴan ajin ke faɗa suna sake baki wasu na cewa kaga madarar kyau,banda malam NURA da ya kasa motsi ɗalibai basu tantance ba sai ƙarar faɗuwar shi suka ji timmm ai ko ajin ya ruɗe wanda hakan ya jawo hankalin sauran malumai har suka zo suka fitar da malam NURA.
Wasu ɗalibai suka dawo kusa da AMIRA wai su ƙulla ƙawance amman ko jin su ba tayi dan tana can duniyar tunani sai ji tayi ɗaya na cewa "ah malam an ga ƴar fillo an suma"ɗaya tari caraf tace "yaga madara kyau ba doli ba daman an ce son mata gare shi".Nan dai ɗalibai suka shiga faɗin albarkacin bakinsu kafin shugaban makarantar ya bada izinin kowa ya tafi gida sai kuma gobe lura da yanayin jikin malam NURA kamar shafar iska sai sambatu yake,jiki na ɓari AMIRA tayi saurin ficewa sai sauri take tana shirin shiga gida ta ɗaga kanta tana kallon benen yau bai nan bata gan shi ba da mamakin mi ya hanashi fitowa ta shiga gida ko sallama babu,ɗaki ta shiga ta fara cire tenue sai a lokacin ta tuna lokacin tashi bai yi ba shiyasa a bata ga *mai kyau* na saman bene ba dan shine sunan da ta raɗa mashi.
Anna ce ta shigo da ɗaurin ƙirji alamu daga wanka ta fito "to lafiya kika dawo da wuri haka?"ta tambayi AMIRA maimakon ta bata amsa sai tambayar da ta kaɗa hanjin anna ta jefo mata ganin ta ƙyale yasa ta ƙara cewa "anna ki faɗa min wai dagaske inada kyau ?"kallonta anna tayi tace "waya gaya maki kinada kyau ɗin?"kwashe yadda aka yi ta gayawa anna kamin ta ƙara "kinga yanda mutane ke son su yi ƙawance da ni kum..."marin da taji a kumcinta ne ya hanata ƙarasawa, murya anna taji cikin faɗan da yawan yi mata shi yasa ta hardace komi "ban yarda wani namiji ya kalleki ba kuma ina sake jaddada maki kar ki saki ki kalli madubi"wannan kalmomin biyu na ƙarshe kawai taji dan zafin marin ba kaɗan ya shige ta ba.
Sallama mum ta fara yi, fitowa anna tayi tana amsawa kamin ta fara mata kallon sani ganin haka yasa mum cewa "matar nan gidan ce "ta faɗa tana nuna tsalelen gidan da duk unguwar shi kaɗai ne mai doran zabo,cikin sakin fuska anna tace "ko ke ce hajiya BALKI?"kai kawai mum ta ɗaga tana mai zama bisa kujera da anna ta aza,gama zamanta ke da wuya ta hango wata tsalelliya yarinya ta jikin labule tana leƙo,ganin mum ta kafe wurin da ido yasa anna dubawa AMIRA ce ke tsaye tana leƙo jin an ce hajiya BALKI mum ɗin mai kyau na bisa bene......
Jikar Rabo ce🌚
[05/07 à 11:03] Matar Sadauki💞: *ƁOYAYYEN SIRRI*💞
By Chamsiya Laouali Rabo
Page 10-15
Ƙyafƙyaf da ido take kamar wata aljana manyan idonta farare wanda ɗan boule ɗin cikin su yake baƙi ƙirin,saurin sakin labulen tayi ganin hararar da anna ta jefo mata.Kallonta mum tayi ta sakar mata murmushi kamin tace "zan koma sai an jima,dama cewa nayi bari na leƙo na ganki kullum AMAR na bani labarin irin yadda kike fama"mum ta faɗa tana miƙewa tsaye yayinda anna ta rakota murmushi kan fuskarta tace "Allah sarki ashe AMAR sunan shi?yaron kirki ai kullum yana gaishe ni a duk lokacin na fito tuyar ƙosai yana kuma aiko min da abun arziki kullum ina son shiga amman karnukan gidan ku nike tsoro"dariya mum tayi tace "ai kowa haka yake faɗa amman ni da nike son ɗaukar ki aiki in babu damuwa gashi kuma kina tsoron gidan namu"ɗan saƙe anna tayi kamin tace "toh zan duba in gani dai,nagode sosai hajiya"anna ta faɗa lokacin da mum ta fice daga gidan suna ban kwana.
"Miyasa baki jin magana ne AMIRA? ba nace a duk lokacin da kika ji nayi baƙi kar ki fito ba?"anna ta faɗa cikin sigar faɗa tana mai ɗaga labulen ɗakin,saurin miƙewa AMIRA tayi ta maida hannunta baya tace "anna ai gani nayi macce ce kuma ma ban fito ba kawai leƙowa nayi"maimakon anna ta sake wata maganar kawai sai wajan AMIRA ta ƙarasa tare da tara mata hannu "bani abinda kike ɓoyo"ja da baya AMIRA tayi har ta dangane da bango a tsawace anna tace "bani nace"ai AMIRA bata san lokacin da ta saki abinda take ɓoyewa ɗin ba,duƙawa anna tayi ta ɗauki ɗan ƙaramin gidan hoda mai game da madubi.Wani marin ta kifa mata kamin ta rufeta da duka cikin murya kuka tace "ban san mi nayi maki ba da kullum kike ƙoƙarin yin abinda ya haramta gareki saboda kwanciyar hankalin mu na nisantar da kaina da familyna yanzu minene kike shirin yi da ban zo ba da madubin zaki duba ko?"anna ke faɗar haka tana kuka lokacin da ta dakata da dukan AMIRA.
A can jikin bango inda ta samu malaɓa tsakanin gini da drawer ta fara girgiza kai "anna ina son ganin kaina ko sau gu..."naushin da aka yi ma bakinta ne yasa ta ƙyalewa tana mai dafe bakin.
Bakin gado anna ta zauna ta rabka uban tagumi tana tunanin abinda zai je ya komo wata rana,a take tsoro da fargaba suka shigeta na tonuwar *ƁOYAYYEN SIRRI* wanda take da yaƙini wataran doli ya tonu balle yanzu da taga AMIRA na ƙoƙarin ɓallo mata ruwa.
Hannu taji a tafin fuskarta ana share mata hawayen da ke zuba kamin ta tsinkayo siririyar muryata wacce ke ɗan rawa saboda kukan da tayi tana faɗar "anna ki rubuta ki ajiye ni AMIRA ni da madubi mun yi hannun riga amman dan Allah Anna ki sanar da ni miyasa baki son maza su ganni alhalin ni ɗin kyakyawa ce duk da ban taɓa ganin kaina ba amman naji ƴan makarantar mu sun faɗa"tunda ta fara magana anna ta kafeta da ido a yadda take maganar ba za a ce ƴar 13years ce ba,tallabo fuskarta anna tayi da duk tafin hannunta "zan sanar da ke komi a lokacin da na tabbatar shekarunki da kwanyar ki zasu iya ɗaukar *ƁOYAYYEN SIRRI* ɗin da ke tattare da ke kinji my MIRA"yadda taga murmushi a fuskar anna yasa ita ma ta murmusa.
A ɓangaren mum kuwa da murna ta nufi gida tana zumuɗi ta sanar da AMAR kan yau taga ruhin shi AMIRA,tun kamin ta shiga gidan nasu take jiyo haushin karnuka .
"Innalillahi wa'inna ileyhi raji'un"shine abinda mum ta faɗa lokacin da tayi tozali da BALARABA(kishiyarta)hannunta riƙe da kwanon yaji(barkono)tana watsa ma TARZAN wato ɗaya daga cikin karnan,duk ta baɗe mashi jiki da shi a ƙarshe kuma ta watsa mashi a ido kukan da yake ne yasa sauran karnukan biyu kokawa suna kubce-kubce kamar zasu katse sarƙar da aka ɗaure su da ita.
"Wane kiciyi ne kuma?ina ruwanki ina ce dai karnuka na ne ko yanka su nayi ba abinda ya damu mutum"BALARABA ta faɗa tana watso ma mum harara wacce tayi tsaye tana kallon TARZAN cike da tausayin shi,"Allah baki haƙuri"cewar mum tana mai nufar ɓangarenta da yake can saman bene.
Part ɗin shi ta nufa tun kafin ta ƙarasa take jin kururuwar AMAR yayinda tagogin ɗakin shi suke bada wata ƙara "garam-garam" sakamakon buɗewa da rufewa da suke,da sauri mum ta buɗe ɗakin zuciyarta na bugun tara-tara a duƙushe ta tarar da shi yana kuka sai ƙanƙame jikin shi yake hawaye na zuba a idon shi yayinda gaban shi ke fitar da jini.
Da sauri mum ta rufe tagogin (window, fenêtre)gama rufewar ke da wuya jinin ya bar zuba fatar jikin shi ta fara komawa daidai.Can kamar 10mns ya dawo normal,kallon mum yayi wacce ke zaune bakin gado tana kuka hannunta ya kama tare da jimƙe shi sannan ya shiga girgiza mata kai "zubar hawayen ki sune karayata domin sai naji duk banda wani ƙwarin gwiwa ko kuma sai naga kamar ba zan warke ba mum"cewar AMAR hannunta da ya riƙe ta gama da nashi ta kai saitin zuciyarta"wannan dokawar da kake ji zuciyata nayi duk dalilin kana raye ne domin duk radda kabar duniyar nan ba zan sake kwana ɗaya cikinta ba,AMAR rashin lafiyar ka na bani tsoro sosai ace duk lokacin da iskan waje ya bugeka babu lafiya ranar kai kuma Allah yayi maka bala'in son iskar da ke kaɗawa"mum ta faɗa cikin damuwa muryarta na rawa yayinda idonta ke zubar da hawaye.
"Mum tun daga nan zaki gane irin jarabawar da Allah ya nufe ni da ita kenan,wlh sam banjin daɗin sheɗa in ban buɗe window ba sai naji kamar lumfashina bai fita daidai"
"Please ka bar buɗewa tunda kaga hakan na haifar maka da matsala"mum ta faɗa tana shafar kanshi "toh mum zan kiyaye,yane kin ga beauty ɗin?"murmushi mum tayi kamin ta kwashe yadda suka yi ba ƙaramin daɗi yaji ba mum tace tanada kyau.
*Washe gari* tun da sassafe anna ta fito da kayan ƙosanta kamar yadda ta saba,AMIRA ta tayata fito da kayan sannan ta hura huta sai da mai yayi zafi aka kwashe tuyar farin AMIRA ta zuba a leda ta shige gida.
Tana gama cin ƙosan ta sha ruwa ta fito dan taya anna tuya kamar kullum duk ranar da babu islamiyya.
Tuya suke suna kwashewa yayinda mutane sai tururun saye ake da yake anna ta iya ƙosai sosai wani zubin har daga wata unguwa ake zuwa saya.Duk wannan tuyar da mita take fuskarta rufe take da niƙaf duk wanda ya zo sai dai yayi ta kallonta.
A tsaye yake kamar kullum sai kallon santalelen hannunta yake wanda ke riƙe da majuyin ƙosai ,tun bayan sallah asubahi ya kasa komawa barci ya ƙagu gari ya fara haske ya fito sai kuma yayi sa'a tun lokacin da suka fara tuwa yake tsaye yana abkin kallonta.
Abu biyu ne ya ɗaure mashi kai na farko gudan tulun ƙosain da AMIRA ta shiga da shi gida ta cinye ita ɗaya dan ya san su biyu ne kaɗai gidan,na biyu kuma yadda yaga yau da ita ake tuyar alhalin yau ranar islamiyya ce.
Bai gama mamaki ba yaga ta ƙara zube wani ƙosan a tray tana daga yaji sai ta