Showing 15001 words to 18000 words out of 20540 words
Chapter 6 - BOYAYYEN SIRRI Book Complete writing by Chamsiya Laouali Rabo.txt
sai hawaye ke mashi zuba,ruwan addu'a anna ta bashi ya sha babu laifi yaji dama zuciyar shi ta ɗan nutsu."Hajiya ba a kiran abban su ki shaida mashi tun wuri a ɗauki mataki dan kamar shafar aljanu ne"cewar anna kai kawai mum ta girgiza mata kafin kuma ta riƙe hannuwan anna "kece mutum ta farko da naji na yarda da ita har zan gaya maki damuwata,dan Allah ki riƙe wannan sirrin"kai anna ta girgiza nan mum ta kwashe duk abinda ke faruwa da AMAR ta gayama Anna wacce ba ƙaramin firgici tayi ba har take ganin gwara AMIRA da shi.
"Haƙiƙa na tausaya maku ke da ƴaƴan ki amman insha Allah zan raka ki wajan wani malamin sunnah dan taimaka maki in kin yarda yanzu na kira shi a wa Allah so gobe sai mu tafi bayan yayi ISTAHARA"haka kuwa aka yi nan anna ta kira malam MUTAƘA babu abinda mum ta ɓoye mashi daga ƙarshe yace gobe su zo.
Washe gari mum da anna suka shirya suka je gidan malam MUTAƘA bayan ta kira AMARA taje can gida dan ta zauna tare da AMAR .
"Ba shafar aljannu ne ba sihiri ne aka yi mashi,an yi amfani da aljanu na cikin iska shiyasa a duk lokacin da jikin shi ya bugi iskan waje kuma aka yi daidai da aljanun sun bayyano to sai jikin shi ya fara ƙaiƙayi yana ɓarewa,al'aurar shi kuma da ta ƙanƙance aljana JANNAYE ta aure shi dalilin fitsarin jinin kenan"cewar malam yana ma mum bayani dukan su kuka suke malam na basu haƙuri"to yanzu minene mafita malam?"cewar anna dan ita mum sam ta kasa magana "toh mafita guda ce shine addu'a domin ita bata bar komi ba ga addu'o'i da zaku yi kamar haka :
```Ganyen magarya a dafa shi ko daka sai ku zuba cikin ruwa aka SURATUL FATIHA FALAQ³,NAS³,KAFIRUN³,AMANAR RASULU²,AYATUL ƘURSIYU ¹``` bayan kun karanta sai ku tofa a ruwa a bashi ya sha ya kuma tu wanka"godiya su kayi mashi kamin su baro gidan.
Tun kafin su ƙarasa suka tsinkayo dandazon mutane ƙofar gida gaban mum ne ya yanke ya faɗi,suna shiga suka tarar AMARA da BALARABA na faɗa AMARA ta tausheta sai kishi take da kyal aka raba su,wani ƙyaci BALARABA tayi tace "sai kin san ni kika daka yarinya "ta faɗa tana shigewa ɗakinta a kunyace bakinta duk ya gwagwaɓe.
Wani farin ƙyale ta shimfiɗa tsakar ɗaki ta yayafa ruwa kamin ta kece da wata irin dariya tana wasu maganganu na tsafi a take wani ƙasunburun boka ya bayyana ta jikin ƙyalen.........
A nan book 1 ya ƙare su ku tarbe ni a book 2 dan jin yadda zata kaya.
[13/07 à 06:34] Matar Sadauki💞: *ƁOYAYYEN SIRRI*💞
By Chamsiya Laouali Rabo
Page 36-37
Bayyanar bokan ke da wuya ya ɓarke da wata irin dariya wadda ba tada daɗin amo,ko kafin tayi magana shi ya fara "la'annaniya mai aikin ƴan huta faɗi buƙatar ki yanzu nan mu biya maki hhhh"gyara zama tayi ta fara koro mashi jawabi "so nike a masakantar da AMARA yadda ta dake ni da wannan ƙazaman hannuwan so nike su bar aiki daga yau dan ta gane ruwa ba sa'ar kwando ba ne"cewar BALARABA "ƙudirin ki a wannan karon ba zai taɓa cika ba har sai an zubar da jinin bil adama domin yarinyar ta fiya addu'a da tsayuwar dare doli a ɗauki mataki kamin aiwatar da shirin...."yana gama faɗin haka ya ɓace ɓat.Zirga-zirga ta kama yi cikin ɗaki tana tunanin wannan ɗanyen aikin da ɗaukowa kanta "wannan rashin imanin yayi miye na kashe rai ina ma laifin ace jinin dabba ?to wai ni yanzu ina ma zan samu jinin?kai ba zan iya ba kashin kai ai babban zunubi ne"BARALABA ke suratai ita ɗaya yayinda take saƙa da warwara, murmushi tayi da ta tuno da malam na kan dutse sarkin malumain tsubo wanda taje wurin shi jiya "yauwa na samu hanyar da zan cutar daku ku duka tsuntsu biyu zan jefa da dutsi ɗaya"ta faɗa tana mai ɗaukar waya bugu biyu malam ya daga bayan sun gaisa take ce mashi "yauwa malam ina son a buɗe bakin mahaifar nan akwai buƙatar ta haihu "duk da bata ambaci sunanta ba ya gane ko wacece take nufi "anya kuwa ayi haka?kije dai kiyi tunani ko kin manta haifuwar ta kamar barazana ce da taki rayuwar?"
"A'a malam babu abinda zai same ni dan ba zaune nike ba na san tudun da na taka"cewar BALARABA tana mai zaunawa bakin gado,ɗan nisawa yayi yace "shikenan tunda haka kike so amman wlh naga wani haske ya mamaye su yayinda duhu ke tunkaro ki kuma da na auna haka sai nike ganin kamar zuwan yaron haske ne"
"Malam tunani ne fa kake babu tabbas dan haka kawai ka aiwatar"tana gama faɗin haka ta kashe kiran yayinda shi kuma malam yayi sudabarun shi na kwance mahaifar.
"Ba zan bari ɗan ya girma zan salwantar da shi sai naga ta yanda zai zamo hasken bayan na sheƙe shi,in dai jinin BALKI ne ba zan taɓa jin ɗigon imanin shi ba kuma ma ai ba laifi ba ne dan ka kashe abokin gaba"BALARABA ta faɗa tana mai shiga toilet.
A ɓangaren su mum kuwa suna shiga part ɗin su ko tambayar ba'asi basu yi ba suka ɗebo ruwa a bawo tare da zuba garin magarya da malam ya basu,mum tayi addu'o'i tana mai kallon gabas.Ruwan aka bashi yasha kamin sauran yayi wanka da su wuri mai tsafta,yadda kasan wani yaro ko nakasashe haka yayi ziziɗa yaje ɗaki.
Ruwan da yayi wanka ba a zubda su ba kasancewar akwai ayoyin Alkur'ani,duk bangon ɗaki da terrasse mum ta wawatsa su a cewar ta in ma akwai wani abu da ya shafi iska ya baje.
Sosai AMAR yaji daɗin ruwan har sai da ya ƙara sha ganin haka yasa mum ta sake yin wasu dayawa aka ɗura ga bududuwa aka sa a frigo dan ya maida su ruwan shan shi.
***
"Anna yau ina kika je ne?na ga tun kafin na ɗora tuya kika fita"cewar AMIRA tana mai sake ƙirga kuɗin ƙosai na cinikin da tayi,karɓar kuɗin tayi ta ɗaure a haɓar zane kamin tace "yaron Hajiya a ba shi da lafiya shiy..."saurin katseta tayi da wata tambayar "mai kyau ? Anna ba dai mai kyau na bisa bene ba?"yadda take maganar take dafar ƙirji yasa Anna kallonta na wani ɗan lokaci kamin tace "to kar naji kar na gani kin fita daga gidan nan ,na san ki da shegen karanbanin tsiya"anna ta faɗa tana mai cire kayan jikinta tayi ɗaura gaba.Ta faɗi haka ne saboda sanin halin AMIRA na ƙididdiga da son sanin abinda yafi ƙarfin kwanyarta.
Washe gari ta kama asabar,tun da wuri ta gama aikin gida kafin ta shirya cikin shigar makaranta kamar kullum.
Yau ba su yi ƙosai ba hakan yasa taci ɗumame kamin su fito ita da anna wace ta shige gidan su AMAR ita kuma ta tafi makaranta.
Tun kafin ta shiga aji zuciyarta ke tsinkewa sakamakon ganin malam NURA na bada karatu,sallama tayi ta tsaya bakin ƙofa tana jiran izini da hannu yayi mata alama ta shigo.
Tun shigowar ta malam NURA ya koma ɗari-ɗari hatta ɗalibai sun kula da haka a tsorace yake karatun kasancewar tun radda abun ya faru shugaban makarantar yayi mashi bayani a kanta kuma bata sake dawowa ba sai yau.Wurin da ta saba zama ta zauna ta kafe malam NURA da ido,shi ma ta wutsiyar ido yake kallonta ganin direction ɗin shi take kallo ya gane kenan kallon shi take tunda niƙaf ɗin ta ba ta fiddo ido waje.Ya na gama darasi ya tambayi ɗalibai sun gane suka ce eh "toh masha yanzu wa zai tashi yayi mamu jawabi tare explique' abinda mu ka yi?"cewar malam NURA yana mai addu'ar Allah sa kar AMIRA tace zata iya tunda an bashi labari ilimi gare ta,addu'ar shi bata karɓu ba dan ko ita ɗaya ta ɗaga hannunta bai da wani zaɓi doli yayi interrogé ɗinta.
"يجب الغسل من ثللثة أشياء wanka na wajaba akan abu uku الجنبابة janaba والحيضda haila والنفاسsai kuma biƙi.
Uwannan su ne ke sa ya wajaba ga mutum dan haka doli mu kula musamman wajan janaba sau tari wani kan samu janaba ba tare da yayi la'akari ba domin wasu sukan kasa banbanta maniyi da mazayi musamman mata ba wai doli sai ta hanyar jima'i ba kawai ke samun janaba,ta hanyar tunani,kallo,shafa duk ana iya samu san..."ganin mutane duk sun maida illahirin hankalin su kanta yasa ta ƙyale ba dan komi ba dan mafi akasarin ƴan ajin ƴan mata ne sun girme mata wasu ma suna shirin aure,"malam ta cigaba"cewar ɗaliban malam NURA da yayi tsaye yana kallonta cike da mamakin yadda aka yi take koro jawabai dan shi bai gaye su ba,izini ya bata ta cigaba ai kam kamar jira take"um...akwai banbanci tsakanin maziyi da maniyi.
_ *Maziyi* wasu tsinkakun ruwa ne da ke fita gaban mace a yayin ƙaramar sha'awa,ya kan fito ta hanyar tunanin wanda kake so,tunanin aure to a nan wanka bai wajaba sai dai in har sha'awar ta wuce ƙarama kamar miji yayi wasa da matar shi ta fitar hayyaci ba tare da ya sadu da ita ba to a nan wankan ya wajaba domin babbar sha'awa ke haifar da fitar maniyi.
_*Maniyi* wasu ruwa ne tsinkaku fatsi-fatsi masu kabri da ke fita a farjin mace yayinda saduwa ko wasa da wasu sassan jikinta.Wanka kuma na wajaba a mace in azakarin namiji ya taɓa farjinta ko da kuwa bata fitar da maniyin ba"tana kawowa daidai nan ta zauna "Masha Allah barakallahu feeki lokacin récréation yayi ku fita ku ci abinci"cewar malam NURA yana mai zama kan kujera har AMIRA zata fita ya kirata gabanta ne ya faɗi ta dawo tayi tsugunne gaban shi,sai da duk ɗaliban suka fita sannan yace "AMIRA wa ya koya maki wannan karatun?"ajiyar zuciya ta sauke ta zata wani laifi tayi "cikin wayar Anna naji wani malami na faɗa kullum in tana gyaran kaya shi take kunna to daga nan na riƙe a kai"cewar AMIRA tana wasa da ruwan da ake goge tableau hannunta ya kalla wanda yake fari sol mai zaratan yatsu sun sha jan lalle,ɗan nisawa yayi kamin yace "AMIRA shin zaki aure ni?"........
💞💞💞💞💞
Shiri ya ke ya na tsuki ya rasa ko mi ke mashi daɗi,kallon LAURAT yayi wacce ke kwance kan bed tsirara tun bayan da suka gama sex ba ta tashi ba sai ma wani mayen kallo da ta take bin ya da shi.Wata sha'awar shi ce ke taso mata ganin ya shirya tsaf cikin jeans blue da riga fara ya shace gashin shi sai ƙyalli ya ke,agogon hannun shi ya gyara kamin ya ɗauki key yayi waje ba tare da yace da ita komi ba.
Motar shi ya ma key bai tsaya ko ina ba sai gidan su RAINA ,a ƙofar gida ya zauna cikin mota sai gashi ta fito cikin riga da wando ta baza gashi kamar baturiya.
Tun da ta fito ya kafe forme ɗinta da ido yadda cinyoyinta suke manya sai kuma suka ɗan lanƙwasa wajan ƙugunta kamar ƙwarya hakan ya ƙara ma shap ɗin ta kyau wanda ya ke kamar coca cola,mota ta buɗe ta shiga gidan gaba ko kafin ta kai ga gaishe shi yace "yanzu sabida Allah RAINA a haka kike fita salon duk a kalle mani ke?"yadda yayi maganar zaka tsinci ya na kishi sosai,langwaɓar da kai tayi tace "ayya masoyi kawai da kwalliya nayi maka kuma layin mu bai cika jama'a ba"cewar RAINATU sai wani fari take da ido .
Lumfashi ya furzar yana jin duk jikin shi ya mutu sanadiyar shaƙar turarenta da yayi bisanin yaji kan shi na juya mashi, murmushi tayi réaction ɗin shi kawai ya tabbatar mata aiki yayi kyau "nace ba?ya kuka yi da Ammy ?"ɗagowa yayi daga duƙen da yake ya dubeta sannan yace "na gaya mata saura dadyna""to mi kake jira ka kira shi yanzu kace Ammy ta gaya mashi maganar auren"kamar jiran umarninta ya ke haka ya kira dady shi kam bai yi wani mamakin auren ba dan ya san gadon shi ABDALLAH yayi "ok son kar ka damu in naje gida mu tattauna yadda komi zai kasance"cewar dady bayan ABDALLAH ya sanar da shi "please dad nan da 1week nike son auren"murmushi dady yayi "ok ba damu bari nace ma MUSSA ya haɗo maka kayan lefen"cike da murnar da bai taɓa ji ba ABDALLAH ya yanke kiran, rungume shi RAINA tayi cike da murna.
***Abu kamar wasa sai gashi har an kai kuɗin aure kuma juma'a mai zuwa za a ɗaura aure amarya ta tare asabar.
Tunda aka kai kuɗin auren MARYAM ta fara zazzaɓi kuma taƙi yarda a kaita asibiti sai da ABDALLAH ya tausheta yayi mata allura da ɗuren magani da abinci.
Duk tausayinta ya kama Ammy wai a haka ma bata san wacce ABDALLAH zai aura ba ne.Lipton Ammy ke bata dan shi kaɗai take iya sha ya zauna cikinta ko mi taci sai ta amayar ga zuciyata da ke faman yi mata ciwo duk in ta tuna ABDALLAH aure zai ƙara tafi jin zafin wannan fiye da lokacin da tayi na LAURAT.
Rana ba ta ƙarya a yau aka ɗaura aure RAINATU NASIR da angonta ABDALLAH AHAMED ɗaurin auren ya samu mutane kasancewar a masallaci aka yi shi.
Wani sanyi ne ya ratsa zuciyar ABDALLAH lokacin da aka ɗaura auren sai yaji kamar an janye mashi wani dutsi bisa zuciya can kamin auren ji yake kamar yayi hauka tunanin auren kawai ke cikin ranshi ko lokaci bai ba LAURAT dama-dama MARYAM in yaje wajan Ammy yana ɗan tsayawa kallonta wani sa'in romance duk da ta na ture shi.
Da murna ya shigo gidan amman lokaci guda ta ɗauke jin kukan Ammy tana bubuga ƙofa da sauri ya ƙarasa inda take,ɗauke shi Ammy tayi da mari "wlh wlh wlh kaji na rantse maka ko?in har ta kashe kanta wlh kaima sai na kashe ka kowa ya huta"tana gama faɗin ta bar gun ajiya zuciya ya sauke lokacin da wata dubara ta zo mashi "haba Ammy ya zaki ce haka wlh saboda son da nike ma baby na fasa auren nan yanzu haka ana can ana rigimi wasu sai zagina suke,yauwa ga dady nan ma je ki tambaye shi yadda aka yi"yana maganar ne ƙwarai ta yadda MARYAM zata ji ai ko kunne ta kashe tana saurare.Bubaga ɗakin yayi "babyna zo ki buɗe min kinji wani lab..."tun kamin ya ida ta buɗe wuf ya shige ɗakin tare da maida key.Jawota yayi ta faɗa ƙirjin shi jiƙaken gashinta ya fara shafawa alamu yanzu da tayi wanka ta wanke shi,goshin su ya game yana dogara mata tsinin hancin shi kamin ya lalubi lips ɗinta na ƙasa ya ɗan ciza.
Ba tare da yace mata komi ba,ya ɗan fara bata kulawa ta mata da miji ta yadda zai kwantar mata da hankali.Ya ci nasara kuwa dan sosai jikinta ya saki,sai ya ɗauke cak ya aza kan bed kafin ya tsugunna gabanta yana kallonta cikin ido.
Baki ta turo gaba alamun jin haushi, murmushi yayi ya dawo kusa da ita yana mai ɗan janyo ta jikin shi.
Wata sanyayar ajiyar zuciya ta sauke lokacin,ba tayi ƙoƙarin hana shi abinda ya ke dan ita ma tayi kewar shi,cike da soyayyar da suke ma juna suka raya sunnah cike da kewar juna.
A tare suka yi wanka MARYAM sai wani kumbure-kumbure take da shagwaɓa,dariya ABDALLAH yayi yace "yarinya ta sha daɗi amman da alamu bai ishe ta ba"matashin kai ta buga mashi tana dariya shi kuma ya tsaya kallon kumatunta yadda suka lotsa dimple ɗinta ya fito sai hushiryar ta wadda tafi komi burge shi.
Tsagaita dariya tayi ta ɗaga gira "ya a kayi ne kallon fa na minene?""na kin ji daɗi ne kuma baki so a faɗa "ya bata amsa yana mai daidaita fular kanshi, murmushi tayi ta kwanta tana latsa waya shi kuma ya mata kiss a goshi ya fita.
Contact ɗinta ta shiga sai lambar RAINA ta lalubo ba ɓata lokaci ta danna mata kira har sai da ta kusa tsinkewa sannan ta ɗaga "ƙawalliya ke baki nemana ko yau wajan 2week ba mu ga juna ba"cewar MARYAM tana dariya "ba ita ba ce tana can wajan lalle ta bar wayar"cike da mamaki wai RAINA da kullum suke faɗa akan mata lalle tace bata so shine ake mata a yau"lalle kuma RAINA ce ta yarda aka mata lal..."saurin katseta wadda ta ɗauki kiran tayi da cewa "eh lallen bikinta ne ko ba ta gaya maki yau aka ɗaura aurenta ba?"kamin ta bata amsa crédit ta suka ƙare hijab ta saka ta fito falo tana mai cewa "Ammy wai RAINA ..."goron da ta gani gaban dady ya hanata ƙarasawa,tasowa Ammy tayi ta zaunar da ita "kiyi haƙuri baby tun can dama Allah ya ƙaddarta miji guda zaku aura ke da RAINA tun farko na ɓoye maki wacce zai aura ne dan kar ki shiga damuwa,ki sani babu wani abu da Allah ya gindiya zai faru ga bawa face sai wannan abun ya tabbata"wasu hawaye masu ɗumi ne suka sauka kan kuncinta uwanda ta rasa na murnar yau RAINA tayi aure abinda kullum take da burin gani (don RAINA ta kasance mai yawan sha'awa kuma tunda take babu saurayin da ya taɓa cewa yana sonta duk da ta nada kyau,wani sa'in zuciyarta na ruɗarta ga fara zina amman MARYAM ke hanata)ko kuma na kishin mijinta "allahuma ajirni fee musibatih wa'alkhlifini khairin minha"shine abinda MARYAM ke nanatawa kamin ta mike tsaye wani jiri taji ya ɗibeta luuu tayi zata faɗi Ammy ta tareta.Ganin bata lumfashi yasa suka talalabeta a ruɗe suka kaita asibiti ,jini Ammy ta gani a jikin kujerar mota ga saura a zanenta wani irin ihu Ammy tayi wanda bata san tayi ba kamin ta fara nanata "innalillahi wa'inna ileyhi raji'un".
Ɗan jim kaɗan nurs ta fito ta ba su ordonnance na maganin da za a siyo,dady ya amsa yayinda Ammy ta fara zarya cikin asibiti.An ɗauki lokaci mai tsayi kamin a turota cikin gado na maras lafiya aka kaita wani room,farar takarda Dr ya miƙa ma dady kamin yace "ina mijinta ne ?"sai yanzu suka tuna da ba a ma shaida ma ABDALLAH ba "bai nan wani abu ne?"Ammy ta tambaya "tanada shigar ciki ne na sati guda da ƴan kwanaki sai dai sanadiyar firgici yasa cikin fara zuba mun yi nasara