Showing 3001 words to 6000 words out of 20540 words
Chapter 2 - BOYAYYEN SIRRI Book Complete writing by Chamsiya Laouali Rabo.txt
zura ta ƙasan niƙaf tana ci,kallonta yake yana dariya a fili yace "wannan akwai haɗiya wai har ta ji yunwa amman inada aiki"AMAR ke faɗar haka daga bisa bene yana kallon AMIRA yana dariyarta,kamar an ce ta ɗaga kai ta tsinkayo shi cikin kayan ƴan ƙwallo farere kayan sun yi matuƙar yi mashi kyau.
Ganin tana kallon sama yasa anna kai dubanta AMAR ta gani yana abkin murmushi gaisheta yayi da hannu kamar kullum irin yadda kurame ke yi.
Leda anna ta ɗauka ta zuba mashi ƙosai sai dai babu yaron da zata ba ya kai mashi,da hannu yayi mata alama da ta bakama AMIRA kasancewar tana jin kunyar shi ta ba AMIRA har ta kai bakin ƙofa wata tazo shiga gidan sai ta miƙa mata tace ta kaiwa wancan na saman bene karɓa tayi ita kuma ta koma wurin anna.
"Haba AMARA miye na amsowa ni da naso yarinyar ta kawo min da kanta"cewar AMAR lokacin da AMARA ta ƙaraso wurin,dariya tayi tace "yo ni nasan digin abun saƙo ta bani kuma na kawo,ina mum?"AMARA ta faɗa wacce kallo guda zaka mata ka gane ƴar uwar shi ce "tana cikin ɗaki"ya bata amsa kamin su runguɗa su shiga ciki.
Bayan sun gaisa ne mum tace "AMARA lafiya naga kin zo da uwar safiyar nan?"alamun damuwa ya bayyana kan fuskarta kamin tace "mum maganar rashin lafiyar AMAR ne ".........
💞💞💞💞💞
ABDALLAH ne zaune bisa kujera a office ta rabka uban tagumi ya zurama tulun takardun gaban shi ido,babu abinda yake sai tunanin zuci kamin kuma yayi magana cikin kuka "yanzu ni haka zani zauna ba tare da morar aure na ba ?wannan wacce masifa ce ta kunno min kai kuma?"ya faɗa kamin yayi baya da kujera yana tuna baya irin soyayyar da suka sha shi da matar shi ta farko wanda rashin haifuwar da bata yi ba ne yasa ya ƙara auren MARYAM.
Wayar shi ce da ta ɗauki ruri ta katse mashi tunanin da yake ɗauka yayi yana mai yin sallama kafin yace "ina kwana Ammy ?""lafiya lau ka zo gida ina son ganinka "ta faɗa tana mai yanke kiran.Tarkadun da ya fiddo dan yi aiki ya fara tattarawar , knocking aka yi kafin kuma abada zini aka shigo abinda ABDALLAH yafi tsana kenan shiyasa ya ɗago a hasale dan ganin wane mai izzar ne ya shigo mashi office kai tsaye sai dai suna gama ido yaji ya kasa furta komi sai ma kallonta da ya tsaya yi kamar bai santa ba.Cike da yauƙi da yanga tace "sir ABDALLAH ko baka gane ni ba ne?"RAINA ta faɗa tana motsa lips ɗinta uwanda suka sha man leɓe sai sheƙi suke,wani yawu ya haɗiye yace "kin min kyau ne sosai yau"ya faɗa yana mai ƙare mata kallo,farrr tayi da ido tace "Allah ko?amman ai ban kai ga larabawan matan ka ba"tana maganar tana wani sama da ido "ina su ina India girl ai ke ta da ban ce,ya har kun tashi ne?"cewar ABDALLAH yana mai ɗaukar makullin motar shi,har ƙasan zuciyarta taji daɗin yadda ya yabeta duk da dama ta san in dai macce fara ce to ABDALLAH zai sota sai dai bata ji daɗin saurin katse hirar tasu da yayi ba ta hanyar tambayarta sun tashi daga school "mun tashi wlh har ma zan je shopping" "ok muje tare nima ina son yin shopping ɗin da manya masu gari"daga haka suka fita daga office ɗin ya kulle sannan suka nufi inda ya paker motar shi.
Wani babban mall ya kaita sosai ta jidi kaya duk wanda ta ɗauka sai ya ɗauki biyu kalar su duk da bata tambaye shi ba ta san matan shi ya zaɓar ma wannan ya tabbatar mata shi ɗin adalin miji ne amma ba taji kishin haka.
Inda ake biyan kuɗi suka zube kayan ya biya sannan aka kai masu har mota,daidai ƙofar gidan su ya ajiyeta sosai tayi godiya ta kwashi kayanta ta shige gida bayan sun yi masayar number.
Da murna INNA cewa da maihaifiyarta ta tarbeta ganin ta shigo gida da ledodi ba tare da wani bincike ba ta rangaɗa buɗa tana duba kayan "farar macce babbar ƙaddara iyeee! wannan uban kaya masu tsada ya tabbatar min kin yi babban kamu"INNA ta faɗa lokacin da tayi arba da wani mayafi,cike da jin daɗin yadda mahaifiyarta ta ke zuzutata tace "bari INNA shegen kuɗi ne da shi kaf zuri'ar su babu talaka matsala dai guda ce ke karya min gwiwa a taren mu da shi"da sauri INNA ta tambayeta "ta mi kuma ?kar fah ki kawo mamu cikas"cikin sanyi tace "INNA mijin MARYAM fa ne"haɓa INNA ta riƙe cike da mamaki "toh sai mi?ina ce dai ba uwar ku ɗaya da MARYAM ɗin ba,ke ni ba ruwana da sakarci kiyi ƙoƙari dai ki wawaro ƴan canjin da zamu kai ma boka yayi maki aikin da zaki shiga gidan ABDULLAHI ɗin"cike da jin daɗi ta rungumeta "shiyasa nike son ki INNA ta".
ABDALLAH POV.
Yana ajiye RAINA ya wuce gidan Ammy, tangamemen wurin da aka fidda dan ajiye motoci yayi parking kamin ya fito yana kaɗa key, fuskar shi a sake yana murmushi kai kace wanda bai da damuwar komi.
A falo ya tarar da ita ƴar aikinta nayi mata tausa,ganin shi yasa ta miƙe tsam ta bar gun,"amincin Allah ya tabbata ga uwata ta kaina"ya faɗa yana mai zaunawa bisa capet murmushi tayi ta dafa kanshi "tare da Ɗana abun alfaharina a ko da yaushe,har ka tashi daga aikin ne?"Ammy ta faɗa tana mai kallon shi."Eh banjin ƴan aikin ne shiyasa na tawo wajan uwata tunda yau ta tuno da ni"cewar ABDALLAH yana kwaɓe fuska dariya Ammy tayi ta dangware mai kai"oh can ban tunawa da kai?" "eh mana jiya kin ga ban kira ki ba ai kamata yayi ki kira kiji ko lafiya"
"Yarona kullum jin kan shi yake kamar jariri ko dan har yanzu bai fara ji ana kiran shi dady ba?"yanayin yadda tayi maganar cikin sanyin yasa ABDALLAH jin babu daɗi har ƙasan zuciyar shi ya kuma tuno mashi da halin da yake ciki,zufa ce ta farara tsatsafo mashi kamin yayi ƙarfin halin cewa "lokaci ya kusa Ammy ke dai kiyi ta min addu'a" "har sai yaushe lokacin zai zo?ce min kayi cikin satin auren ku da MARYAM zaka min albishir har da cewa a likitance ne ka gano hanyar da zata samu ciki amman har yanzu shiru yau 5days da auren"Ammy ta faɗa tana goge ƴar ƙwallar da ta zubo mata.....
*Ku ƙara yawan COMMENT dan har yanzu bai kai yadda zai tabbatar min kuna son labarin ba*😰😰😰
Jikar Rabo ce🌚
[05/07 à 11:03] Matar Sadauki💞: *ƁOYAYYEN SIRRI*💞
By Chamsiya Laouali Rabo
☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️
Page 15-20
"Please Ammy ..."ya faɗa cikin rawar murya yana girgiza mata kai alamun kar tayi kuka, murmushi ta ƙaƙalo taja mashi hancin kafin tace "tashi maza ka tafi gida matan ka na can na jiran ka "ɗan ɓata fuska yayi "Ammy yanzu ɗan gudadan kike kora ni da nike son nayi passé journée a nan sai dare na tafi"waro ido Ammy tayi tace "kaji sakarci sai kace wani ƙaramin yaro ?oh ni BINTU yaro sai ƙara sangarcewa yake ko lokacin da kake da mata guda ai baka wuni nan gidan balle yanzu"miƙewa yayi yana shafar ciki "Ni yunwa ma nike ji mi kika dafa?"sheƙar da shi Ammy tayi ta shiga latsa waya ,ganin ƴan ira'izan nata sun hau yasa shi fita yana dariya.
Ƙarar motar shi ya bayyanar da zuwan shi,da gudu LAURAT ta fito ta faɗa jikin shi tana dariya, kiss yayi mata a goshi sannan yaja hannunta suka shiga ciki ba tare da sun lura da MARYAM wacce ke jikin window tana leƙo,saurin rufe window tayi zuciyarta na mata ƙuna dama jin ƙarar motar shi ne yasa ta leƙo.
Suna shiga falo ya saki hannu RAULAT ya nufi ɗakin MARYAM ,a tsaye baki window ya tarar da ita tana shafe hawaye.
Zuciyar shi ta raya mashi ƙila ta ga lokacin da yayi kissing LAURAT, kawai sai jikin shi yayi sanyi dan yasan irin zafin kishin da MARYAM ke da shi tun a lokacin da suna soyayya.Ƙarasawa yayi ya kama hannunta ba tare da yace mata komi ba. "sannu da zuwa"MARYAM ta faɗa tana mai ƙoƙarin danne kishin da ya taso ,"yauwa baby kina lafiya dai ko?"kai ta ɗaga mashi kafin kuma ta shiga toilet ta tara ruwa cikin bawon wanka,ƙofar da taji an buɗe yasa ta waigo ABDALLAH ne tsaye bakin porte yana kallonta.Saurin rumtse ido tayi ta juya mashi baya ganin babu komi jikin shi ,takowa ya fara yi a hankali har ya zo inda take ruwa ya ɗebo ya watsa mata a fuska da gudu ta fito waje shi kuma ya rinƙa yi mata dariya.
Ko kafin ya fito har ta fitar mashi da wasu ƙananun kaya,sai da ya shirya sannan suka nufi falo wajan LAURAT wacce ta cika tayi fam dan takaici.
Duk irin yadda take ji bata nuna ba sai ma abinci da tayi siving su cikin tray guda,bayan sun gama ne ya jasu zuwa mota suka kwaso kaya.
Ko wace ya san favorite coulor nata LAURAT rose MARYAM kuma rouge(ja)sai dai ko waccen su da aka zo rabon kayan na ƴar uwarta take hange.
"In sayayyar bata yi maku ba ku kawo na bayar saraka🤨"ABDALLAH ya faɗa cikin ɓacin rai dan yasa suna son kawo mashi rainin hankali,jin haka yasa ko wace ta kwashi nata ta kai ɗaki kamin su dawo su cigaba da kallo suna ɗan taɓa hira.
Dare mahutar bayawa,gari yayi tsit baka jin motsin komi sai kukan tsuntsaye da haushin karnuka.
Cikin ɗarɗar ABDALLAH ya nufi ɗakinta, domin a al'ada amarya sati guda gareta kafin ayi rabon kwana,
"Ni fah na fara gajiya da Wannan abun "cewar MARYAM tana maida lumfashi,jawota yayi jikin shi "sai mi kike so?"ABDALLAH ya faɗa mata cikin kunne kamar mai raɗa turo baki tayi tace "nima ban sani ba "ta faɗa cikin jin haushi.
Wani abu yaji cikin zuciyar shi nayi mashi yawo shi ba daɗi ba kuma ba akasin shi ba "babyna gayamin mi kike son faɗa um?"
"Am abinda ke sa mutum ya haifi yara mana dan gaskiya ina son babies dayawa sannan kuma ko ba dan wannan ba ai yana cikin haƙoƙin aure"ta faɗa tana mai dariyar kanta,yadda take magana yasa shi lumshe ido yana jin wani abu na tsarga mashi nan kuma ya fara tunanin rayuwar su tun MARYAM na jiran amsa har barci ya ɗauketa.Wayar shi ce ta fara vibré alamun kira na shigowa,hannu ya zura ya ɗauko daga inda take ajiye "baby RAINA"shine sunan da ke yawo akan screen ɗagawa yayi ba tare da yace komi ba,jin yayi piking ta sauke ajiyar zuciya yayinda shi kuma ya lumshe ido.
Gaisawa suka fara yi kamin daga bisani su fara hira wacce rabinta duk RAINA ce ke yinta shi amsa mata yake da um..kawai.
RAINA na kashe kira ABDALLAH ya shiga saƙa da warwara "tashin hankali" faɗa a bayyane kamin ya kunna hutar ɗaki kallon MARYAM yayi yana mai jin tausayinta har ƙasan ran shi yau kusan sati guda amman ya kasa sauke haƙinta na aure,a duk lokacin da zai kasance ta rasa martabar shi yake ta ɗa namiji,wani tsoro mai game da tashin hankali suka ƙara dirar mashi da kyal ya iya shiga toilet yayi wanka.Tapis ya shimfiɗa yayi raka'a biyu Fatiha ~Ƙulhuwa lahu yana sallamcewa ya maida goshi ƙasa ya karanta *LA'ILLAHA ILLA ANTA SUBAHANAKA INNI KUNTA MINA ZALUMI sau 43* sanan ya fara gode ma Allah a bisa ni'imomin da ya bashi na rayuwa kamin ya fara yi ma Allah kirari "ya ubangijina kai ka hallaci samai da ƙasai ba'a wajan wani ka kwaikwaya ba,ya Rabbi kai ne ke ba bawa abinda kaso a sanda kaso ga wanda kaso a lokacin da kaso,duk ni'imar da ka ba bayinka kai kayi niya ka basu ba iyawar su ko dubarar su bace ta basu haka uwanda basu da shi kai ka hana masu ba kuma dan baka son su ba sai dan haka kayi niya.Ya Rabb ina roƙonka ka yaye min dukannin wata damuwa da matsalar da ke damuna Ya Allah!Ya Rabb!Ya Samad..."kukan da yaci ƙarfin shi ne yasa shi ƙyalewa ya koma yin addu'ar a zuci baka jin komi sai sautin kukan shi wanda hakan ya tayar da MARYAM.Tsakiyar gado ta rabka uban tagumi tana hawaye tashin hankali biyu ga abinda ya gani cikin mafarki ga kuma mijinta na kuka.Hawayenta tayi ƙoƙarin tsayarwa kafin ta shiga toilet tayi wanka da alwala,bayan shi ta tsaya ta kabarta sallah ita ma cikin kukan take addu'a "ya Allah kar da kasa mafarkina ya tabbata kabarni ni da mijina mu rayu kamar ko wane ma'aurata duk masu biyar mu da sharri Allah ka mayar masu kayan su"haka tayi ta addu'a kafin ta shafa, rungumeta ABDALLAH yayi sai yaji jikinta yayi zafi alamar zazzaɓi ac ɗakin ya kashe kafin ya ɗauketa su koma bed,tsam ya rungumeta a ƙirji yana tofa mata addu'a ganin idonta kawai ya tabbatar mashi iskokai sun shafeta.Idonta ya fara canzawa babu baƙi sai fari wanda take juyawa kamar tana son bashi tsoro,suratul baƙara ya kuna yana kuma mai cigaba da yi mata addu'a har barci ya kwashe su.
Washe gari ABDALLAH ya tashi a gaugauce ya shiga toilet dan sun makara,a gida yayi sallah sanan ya tasheta tayi a dadafe.Jikinta yayi zafi sosai kamar huta cikin tausayinta ya fita ya haɗo mata tea sannan ya bata magani,bisa cinyar shi ya kwantar da ita bayan ya rufeta da blanket a nan tayi ta barcinta mai cike da mugayen mafarkai sai mitsirniya take amman taƙi farkawa,irin yadda jikinta ke rawa take ɓata fuska yasa shi fara mata addu'o'i.
Sai wuraren shaɗayan rana ta farka a lokacin jikinta yayi dama,wanka tayi ta shafa mai sai wani cin magani take tana game fuska shi da ABDALLAH kallonta kawai ya ke kamin ya shiga wanka ko da ya fito bata nan.
A falo ya tarar da su ita LAURAT suna karyawa sallama yayi masu kamin uwar gida ta gaishe da shi ya amsa yana kallon MARYAM wadda tayi kamar bata san da zuwan shi ba.
Zaunawa yayi yasa hannun shi dan cin abinci kawai sai MARYAM ta tashi,bai ce komi ba suka cigaba da ci shi da LAURAT.Bisa salon ta kwanta tana rawar sanyi har haƙoranta ke gamewa suna ƙara da sauri ABDALLAH ya fidda hannun shi ya nufeta yadda yaji jikinta ya ƙara yi fiye da na ɗazu yasa shi surarta sai mota dama da hijab ɗinta a jiki.Wani ƙululun baƙin ciki ne ya tokare maƙoshin LAURAT tayi wani ƙyaci kamin ta shiga ɗaki tana murmushin mugunta.
Wani privé asibiti ya kaita,ɗibar jini suka yi kafin daga bisanin su ƙara mata ruwa.
Kusa da gadon yaja kujera ya zauna yana kallonta cike da tausayi guguwar sonta na taso mashi,hannunta ya kama yana ɗan murzawa kafin tunanin ya kiwo Ammy ya faɗo mai a rai.Bugu biyu ta ɗauka a yadda taji muryar shi kawai tasan babu lafiya"Ammy ina kwana kin tashi lafiya?"'lafiya lau mike damun ka?"
"MARYAM ce ba lafiya gamu a asibiti"yana gama faɗa ya gintse kiran sakamakon muryar shi da ta fara rawa, kasancewar Ammy tasan asibitin da suke zuwa a duk sadda wani bai lafiya yasa bata tambaye shi ba cikin sauri ta ɗauki mayafi hankali tashe dan yadda take son MARYAM ko ABDALLAH bata so hakanan.Cikin motar gida driber ya kaita a hanya gani take bai gudu saboda tashin hankalin da take ciki dan duk rashin lafiyar da ta sa aka kai MARYAM asibiti to ba ƙarama ba ce,zuciyata kuma taji ta ɗan kwanta tuna tayiyu ciki ne gareta bata san lokacin da tayi murmushi ba kuma a daidai nan suka shigo harabar asibitin.
A tsaye ta hango ABDALLAH da alamu isowarta yake jira "ya mai jikin?"ammy ta faɗa lokacin da ta ƙaraso wurin shi "tana ciki da sauƙi"ya faɗa yana mai tura ƙofar daƙin.Fuskarta Ammy ta shafa wajan idonta da suka yi zuru-zuru kamar wadda ta daɗe kwance,kamin ta juyo ta tambayi ABDALLAH"mike damunta?"ɗan sosa ƙeya yayi yace "zazzaɓi ne amman likita ya ɗibi jininta bai kawo result ɗin ba har yanzu"murmushi yaga fuskar Ammy wanda yasa jikin shi yin sanyi dan ya gane ko na minene take.Dr ne ya shigo ya miƙa ma ABDALLAH result sai kuma yace "biyo ni office na faɗa maka abubuwan da ya kamata taci da uwanda zata bari ka san halin mata sai da kula"ya ida maganar cikin dariya bin bayan shi yayi kamar yadda ya buƙata bayan sun shiga office sun zauna yace "ulcère olser ke damunta sai kuma damuwa wanda hakan zai iya haifar mata da wani ciwon daban in ba ayi takatsantsan ba,sannan tana yawan cin yaji da abu masu yami wanda basu dace da lafiyar ta.Ya kamata ta kiyaye duk abinda zai tado mata olser sannan ya zamana tana shan ruwa sosai dan yana hana kumburewar ciki"godiya sosai ABDALLAH yayi kamin ya dawo room ɗin da MARYAM take.
Tunda ya shigo Ammy ta ƙureya da ido sai ya sunne kai yana murmushi dan ɓoye damuwar shi bai san kau a wajan Ammy ɗaukar shi tayi na farin ciki ne.
"Sannu baby kin tashi?"Ammy ta faɗa kai kawai ta iya ɗagawa kamin ta buɗe baki kaɗan "ina jin yunwa"har gamin baki suke wajan tambayarta abinda zata ci "taiba da ruwan tsamiya"
"No ki canza wani likita yace abar barin ki cin abu mai tsami"cewar ABDALLAH yana mai fidda mata ƙarin ruwan da aka sa mata.Turo baki tayi tana kallon Ammy tana wani ƙwal-ƙwal da ido kamar zata yi kuka "bari na kira LANTANA tayi maki"Ammy ta faɗa cewa ga ƴar aikin su "no Ammy ni taki nikeso"MARYAM ta faɗa tana ƙoƙarin tashi ABDALLAH ya taimaka mata "toh bari naje gida nayo maki" "am please Ammy kar asa yaji"ABDALLAH ya faɗa murmushi kawai Ammy tayi ta fita.
Juye fuska tayi tace "ni kabar kallona tunda ..."sai kuma ta ƙyale, murmushi yayi mai sauti yace "tunda ba ƴar gidan mu ba ce ko?"ya faɗa yana mai haurowa bisa gadon ya jawota ,magana yake mata cikin kunne mai kamar raɗa ture kan shi tayi wanda ke bisa kafaɗarta tace"ni yunwa nikeji ka sakeni"rigarta ya ɗaga kasancewar ta fidda hijab yana shafa cikin nata a hankali turo ƙofa aka yi tare da shigowa kai tsaye saurin janye hannun shi yayi daga cikinta yana